Showing 57001 words to 60000 words out of 178317 words
a zuciyarta,ta kuma sanya hakan har can qasan ranta. Idanu ta kafeshi dashi sosai cikin salon nazarta da karantar mutum kamar yadda ta saba. A nutse saidai da wani irin sauti me tarin ma'anoni tace masa.
"Wannan jarumtar.......wannna zarrar.......ita na gani......ita ta sakani zabarka na sakoka cikin wani sha kundum din sirri da ya shafi rayuwar zaituna gaba daya........zaituna bata jiran banza.......bata taba jiran wani abu a rayuwarta har haka ba.......dole ya wannan abun dake binne a tonoshi!.......dole wannan damar da muke ganin qyallinta take mana b'aton dabo ta ruskemu.......koda mu bamukai ga takawa izuwa muhallinta ba........har zuwa yaushe komai zai qare?!......ya kamata ya fahimta.......ya fahimci akwai mafarauta.......akwai masu tarin buqata.......ya kamata a sanyashi ya waiwaya.......ya kuma yiwa kansa da kansa karatun da bai buqatar me fassara!"
"Biyan buqatarki itace muradina........amma har yanzu inason tuna miki cewa............ZAKI NE dake qarqashin kulawar DAMISA!!". Tamim yayi maganar kowacce gaba ta jikinsa tana motsawa.
Kamar daukewar ruwan sama bayan shafewar dogon zango yana zuba haka shuru ya gifta a dakin. Sosai maganar ta daki zuciyar mammina da wani irin qarfi daya tilasta tsaiwar bugawar jini zuwa ga sassan jikinta na wasu qananun daqiqu.
"Tamim......." Ta kira sunansa,saidai kafin takai ga cewa komai ya rigata dora maganarsa akai.
"Za'ayi........za'ayi......za'ayi.....bansan meye zai dakatar dani daga qarasa wannan aikin ba!"
"Haka nakeso naji!" Ta fada cikin wani qwarin gwiwa daya lullubeta gaba daya.
"Ban miki alqawarin komai zai kasance kamar yadda ya kasance a baya ba......saboda komai din a yanzun ba yadda yake bane a baya!"
"Na baka wannan amannar.......na kuma baka wannan yardar" Ta fada tana bude tafukan hannayanta kamar wadda kewa qasa daquwa.
Idanunta a kansa har ya fice gaba daya. Dauke kallonta tayi tana qoqarin maida dukkan qwarin gwiwarta gangar jikinta.......taja wata sassanyar iska da garin ya fara saki sakamakon hadarin da ya kammala haduwa ya kuma hade jikinsa guri guda.
Miqewa tayi ta fara takawa,tana jinta a wata sabuwar zaituna......wata sabuwar mammina......wata zaituna ta daban ba wadda take jinta a yanzu ba.
★K'arfe bakwai da rabi ne na dare a garin addis ababa dama Ethiopia gaba daya. A daidai wannan awannin wasu sirrintattun awanni ne da suka kammale abba muhammad dawud......omari.......da haisam guri guda cikin wani kebantaccen office dake da wani irin tsaro da sirri.
Abba muhammad dawud din yana zaune ne cikin kujerarsa swivel chair,yana jinsa yana sake narkewa a cikinta saboda maganganun da suka kammala yi a yanzu.
Daga can saman wasu swivel chair din omari ne.......wanda ya soke yatsunsa guda goma cikin na juna.......yana jin wani abu yana masa amsa kuwwa cikin kunnuwansa shima tun bayan daukewar kalamai daga bakin kowannensu. Haisam din,wanda ke zaune sosai saman wani table dake ajjiye musamman saboda karatu,a maimakon cikin kujerar,ya nannade hannun kurta pyjamas din jikinsa,yatsunsa dauke da biro yana kadashi a hankali,manyan idanunsa da suka lumshe kadan suna saman allon dake gabansu da suka gama rubuce rubuce mintuna kadan da suka rage.
Daga muhammad dawud har omari hankulansu suna kan haisam ne. Omari cike yake da fatan yaji haisam yace ya janye zuwa NIGER ya janye shiga birnin AGADEZ. Tarin hadurran suna da yawa......tarin sharuddan sunyi nauyi da girman da yake ganin haquri da tafiyar yafi alkhairi.
"Na shirya......zanje!" Haisam din ya shammaci ji da ganinsu dukka ya furta yana ajiye abun rubutun hannunsa,sannan yayi qaramin tsalle yana dira daga saman table din yana ware hannun kurta dinsa daya nade.
Dukkansu idanu suka zuba masa,zallar mamakin qarfin halin haisam da jarumtarsa tana kad'a Muhammad dawud. Yanzun nan......da kansa ya sakeyin wadansu binciken........da kansa ya duba komai,ba wani bane ya duba ba......ba wani bane ya bincika ballantana yayi tunanin bai fahimci abun daidai ba ta sigar bayanin da sukayi masa.
"Ka tabbatar ka shirya muhammad haisam?" Muhammad dawud ya fada a ransa yana fatan ko yaya ne haisam yace ya janye.
Da wannan qasaitar tasa ya tako a hankali,ya qaraso gaban table din muhammad dawud,ya janyo kujera qwaya daya ya aje a gaban nasa sannan ya zauna.
"Karanto komai kawai......ka karanto yadda komai zai kasance" Ya fada yana cire murfin biron dake hannunsa ya rufe biron ya ajiye gaban Muhammad hammud......abinda me gaya masa haisam din baida buqatar rubuta komai......kwanyarsa ta shiga yanayin da zai iya riqe komai da basirarsa kamar yadda ya saba a yawancin lokuttan da ya dauki abubuwa serious da gasken gaske.
_TOFA_
★★★★
Awa guda cur suka shafe suna tsarawa da tattaunawa gami da shirya yadda komai zai kasance kafin su kammala. Tsam ya miqe,ba wani rauni daya bayyana a gangar jikinsa bare kuzarinsa ko kadan,daya daga cikin abubuwan dake burge abba dawud kenan matuqa tattare da haisam din. Yasha fada yana kuma maimaitawa
"Tabbas haisam halastaccen jinin abba jifar ne.......da gaske shi din sarauta cikin jininsa take......gado ce ta tun usul......irin wadda idan ta ratsa mutum take maidashi jarumi na gasken gasken. Jarumtarsa tafi kama da jarumtar kakanninsa da suka shude a yawancin lokuta,wadanda suka tsayawa qasar Ethiopia......tsaiwar data sanya aka gagara yi mata irin mulkin fyadiya da aka dinga yiwa qasashen africa a wancan lokacin.
Hannu abba muhammad dawud ya miqawa omari dake tsaye a gefan haisam din yana sauke numfashi. Dariya ta kufcewa abba muhammad yana finciko omari din da shima dariyar ta qwace masa.
"Omarul farouq fa kake........me wannan sunan jarumi ne da baisan tsoro ba ko kadan.......jarumtar data sanya hatta da shaidan baya iya hada hanya dashi ka manta?". Murmushi ya sake kubcewa omari yana girgiza kansa.
"Muhammad ya fini jarumta......kuma ya fini son kasada da rayuwarsa......abba bakaji me yake fada ba?,so samu muje har niger a mota......me yayi zafi?,kawai don zuciyar dutse gareshi?" Ya qarashe maganar yana zube kallonsa akan haisam dake hada kayayyakinsa cikin wata jaka ta musamman. Baiko waiwayo ya kalli omari ba......saboda shi ko sau daya ko alama baiji wani fargaba ko shakka akan komai ba. Hankalinsa kwance yake,bayajin akwai abinda zai sanyashi ya janye.
Ya sani......gagarumin abune shiga wata qasar ba tare da izinin qasar ba......shiga wata qasar da zummar aiwatar da aikin da ya shafi tsaro bincike da samo bayanai daga wasu ahalin qasar.......to amma hadarin dake fuskantarsa.......hadarin dake fuskantar masarautar jimma ya kere dukka wadancan hadurran a ransa.
"Karka damu......na yadda da muhammad.......bani da tsoro ko fargaba a kansa.......amma nasan halinka.......indai baka yiwa mootii bayanin aikinnan da kyau ba ni da kaina zan masa.......don kada ka tafi ka barshi da tsammanin dawowa kwanaki kadan a nan kusa" Abba Muhammad ya fada yana qoqarin boye tashi fargabar.
"Alfarma daya abba". Haisam ya fada yana goya backpack dinsa a baya gami da gyara zamanta.
"Uhummmm.......fadi muhammad" Abban ya fadi yana dubansa.
"Ba yadda zaa canzamin wannan b'eran?" Dariya taso kama muhammad dawud. Daga ganin idanun haisam da gaske yake fadi,ba tun yau ba ya sani,duk wani aiki da zai shiga ko zai jagoranta to ba shakka sai ya zabi mafiya nagarta wajen jarumta da qwarewa sannan yake aiwatar da aikin.
"Kasan dokar aikin mu haisam.......indai kasan wani abu a ciki ko akai......to ka shiga cikin aikin ko ka shirya ko baka shirya ba". Muhammad dawud ya fada yana danne dariyarsa ganin kallon da haisam ke jifan omari dashi. Idanun nasa ya dauke daga kan omari din,ya fara takawa zuwa qofar fita daga office din,yayi scanning card dinsa qofar ta bude masa,ya saka qafarsa daya a waje sannan yayi magana ba tare daya waiwayo ba.
"Kaja masa kunne.......ka sake karanta masa komai,bazan dauki sakaci ko ganganci ko wani tsoro ba.......mu ba mata bane......an haifemu don mu fita muyi farauta......an haifemu don mu zama garkuwa......bango majingina" Ya qarasa fada yana qarasa ficewa ya maida qofar.
Sanda yake saukowa daga escalator yayi mamakin hango abdii sosai. Tsaye yake a lobby din shi daya,cikin shigar qananun kaya. Hannayensa zube a aljihun wandonsa yana duba wayarsa.
"Abdi" Ya fada qasa qasa yana motsa labbansa idanunsa a kanshi. Baisan wanne irin qauna yaron yake masa ba......wannan qaunar ita ta sanya ya gutsira abdii kadan daga sirrinsa da ko nanay bata sani ba.
Boyayyen murmushi ya saki da bai bayyana akan fuskarsa ba. Ya sani zai wahala abdii ya iya zama sai ranar daya tsara zai dawo din,ya tabbatar tunda ya taho shima hankalinsa yayo addis ababa,yanzun kuma da zai tuhumeshi me yasa ya yanke hutunsa tun yana da ragowar lokaci zaice wani uzuri ne ya taso daga makaranta.
Kamar a jikinsa yaji haisam din yana wajen,sai ya daga idonsa a hankali ya sauke kan escalator din. Murmushi ya sakarwa haisam din yana maida wayarsa a aljihu,ya kuma matso a nutse bakin escalator din yana jiran qarasowarsa.
"Saurin na meye abdii?" Haisam din ya furta a nutse yana dauke idanunsa daga kan wata mace dake shigowa gurin wadda kafatanin hankalinta da idonta yake kansa.
Sumarshi ya shafa a hankali yana miqa hannu zai karba jakar wajen haisam din,wanda aiki ne na hadimansa da guards dinsa,wanda baisan me yasa wannan karon yake nesanta kanshi dasu ba.
"Uzurine daga makaranta obbo" Ya fada yana shafa qeyarsa. Dole a wannan karon wannan murmushin dake da gurin ajiya na musamman ya subucewa fuskar haisam,yadan lumshe kyawawan idanunsa yana kuma budesu duka akan abdii.
"Abdii......qaryafa tana cikin manyan zunubbai".
"Obbo mana......ba qarya nayi ba.......uzuri daga makaranta,kai din makaranta ne obbo.....akwai uzurin da yafi wani ya kasance dakai?.....hankalin mooti yaqi kwanciya kaman yadda nawa ya kasa kwanciya......shine kawai mukayi shawara dashi na biyoka......daga nan har AGADEZ " Idanunsa masu nauyin nan ya zubawa abdii,har sai da abdii din ya gaza jure kallon nasa,yaja baya kadan yana cewa
"Obbo.......your eyes obbo" Yadda yayi maganar da gaske kallon ya masa nauyi,sai haisam din ya janye idanun nasa ya soma takawa zuwa qofar da zata fiddashi daga gurin ba tare da yace da abdii komai ba. Qasan ransa yana juya yadda tafiya da abdii zata iya yiwuwa da kuma rashin yuwuwarta......duk da qiris ya rage abdii ya zama wani bangare na national intelligence agency a department dinsu.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 28
__________________________
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500 dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. married femfresh wash 2k
3. garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. Tsimin mallaka 2500
6. maganin infection 1500
7. matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
____________________________
Driver dinsa da baisan sanda ya biyoshi ba shi ya bude masa qofar motar,ya shiga a nutse ya zauna yana sauke numfashi. Batun tafiyar da dukka maganganunsu shida muhammad dawud ke masa yawo,indai har zai gayawa mootii komai game da tafiyar......to bai kamata yabar nanay cikin duhu ba,yana jin ya kamata ko yaya ya haska mata,ya kuma buqaci addu'arta.
Abdii keta masa hira yana saurarensa kawai. Bai gaza ba don yafi kowa karantar yanayin haisam din a mabanbantan lokuta. Ya sake kallon agogonsa,yana jin omari yaja lokaci da yawa bai fito ba,mutum ne shi bai baza uzuri sosai......bayason kiran omarin,bai sani ba ko suna magana me muhimmanci da muhammad dawud ba......amma ya gaji,gida yakeso ya qarasa ya samu ya bawa kwanyarsa hutu.
Ya daga ido da zummar yin magana ya hango omari din,sai kawai ya gyara zamansa yana jiran isowarsa.
Ko cikin mota shuru ya zabi yayi,don yayi doguwar maganar da shuru yafi buqata din a yanzu. Yawan magana ko doguwar magana wani abune da suke sanyawa yanzu yanzu qirjinsa ya fara zafi,ballantana kuma akai ga hayaniya,sam basa shirginsa.
Sau tari idan suka hadu dukka dasu taarik,hira da rudu irin na abokai shikam nashi baya nisa. Ba yanzu ba,tun a makaranta sanda suke tsakanin shekaru goma sha biyar zuwa sama. Littafi kawai zai dauka yayi maka wannan dogon zango,ya jima yana karantashi ba tare daya gaji ba......hakanan qur'ani da zai jima zaune shi kadai a kebantaccen guri yana tilawa abinsa.
Susan ya yanayi da dabi'arsa take,wannan ya sanya sau tari idan sukaga yayi shuru irin haka ko ya kebe kansa basu fiya damunsa ba.
Ba jimawa suka isa kazanchis layout,unguwar dake cike da wata irin nutsuwa da kullum take qarawa haisam son zama a cikinta.
"Mu sauka muyi sallah kafin mu.....shi ya qarasa gida da motar" Haisam ya furta. Dukkansu sun aminta da hakan,don ba wanda ba'a gajiye yake a cikinsu ba.
A babban masallacin unguwar suka qarasa ciki bayan sunyi alwala,tuni har an daidaita sahu,saidai shigowarsa ya sanya limamin neman ja da baya don bawa haisam daman jan sallar. Hannu ya daga masa yana girgiza kai,don ba kasafai ya fiya son haka ba. Yanajin kamar an aza masa nauyi ne an kuma banbamtashi da sauran mutane.
Basu jima ba suka baro masallacin. Tare suke takowa su ukun,duk da abdii ya danyi gaba dasu dasu kadan bai jera kafada dasu ba.
"Haisam" Omari ya kirashi a hankali.
"Na'am" Ya amsa masa,don dama tun dazun ya fahimci akwai maganar dake bakin omari din,yanayinsa daya gani na rashin son hayaniya ya hanashi cewa dashi komai.
"Baka hango kowanne illa da hadarukan dake cikin aikinnan?......me zai hana ka haqura a aika wani?" Omari ya fadi da sigar dake nuna daga zuciyarsa maganar ta fito. Bai zabi ya amsawa omari da wuri ba,har sai bayan shudewar wasu sakanni.
Tsaiwar da dakatawar da haisam yayi da tafiya shi ya sanya omari shima tsaiwa. Manyan zagayayyun idanunsa ya zube akan fuskar omari.......muryarsa d alamun gajiya sosai,gajiyar da bata hana jarumtarsa bayyana cikin muryar tasa ba yace.
"Bana tunanin akwai wanda ya fini cancantar aikin nan........abu daya ka sani......ajani amintaccen mooti ne.......amma kasan cewa mooti ABUN FARAUTA NE?!" Da wani bahaguwar ma'ana maganar ta saukarwa omari a sanda baiyi zaton jinta ba,wannan ya sanyashi bude idanunsa sosai saman fuskar haisam yana kallonshi.
Koda omari baice bai gane ba......koda omari baice qarin bayani yake nema ba.....amma iya kallonsa kadai da yakeyi ya fahimtar dashi hakan.
"Eh.....ina nufin abinda na fada omari.....mooti abun farautarsu ne da suka gaza cimmasa........suna raye kosu waye suka aikata wannan aikin......jikina yana bani ba mission na mutum daya bane......ba kuma sashe daya bane yake farautar MOOTI.....kasan sau nawa a cikin shekaru goman nan na tare yunqurin kaiwa mooti hari ba tare dashi kansa ya sani ba?". Sake dukan omari maganar tayi......ta dakeshi da wani irin yanayi da har sai daya kamo hannun haisam.
"Mooti kuma......meye hadin mooti da wannan case din har na tsahon shekaru goma?"
"Abota da dangantakarsa da ajani" Haisam ya furta wani abu yana motsawa qasan zuciyarsa.......wani abun daya motsa bacin ran dake qasan ransa ya kuma tuna masa da yadda yayita daqile yunqurin isa ga mooti din ba tare da ya bari ya sani ba,don samar masa da cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankalin da zaiyi sarautarsa ya sauke haqqi da nauyin al'ummarsa.
"Mooti shine abun harinsu.......a shekaru gomar nan ba wani abu daya sauya........ta yaya zanyi bacci yadda nakeso?.....ta yaya zanyi rayuwa yadda nakeso bayan ni daya nasan da wannan yunqurin?......ka taba tunanin me yasa nake rasa sukuni duk qarshen sati idan banzo jimma ba?" Ya qarasa maganar yana zube idanunsa masu nauyi akan omari. A hankali omari ya girgiza kansa mamaki yana sake narkar dashi,da gaske kenan hasashen da yasha yi gaskiya ne.......har yanzu bai gama sanin haisam ba da gasken haka take.
"Har abada......baka taba bawa