Showing 153001 words to 156000 words out of 178317 words

Chapter 52 - LU'ULU'U COMPLETE

mutumin dake adawa da dukkan wani jin dadi da kuma walwalarka......bashi da amfani musayar numfashi da mutumin da yayi sila ko sanadin shigarka wani qunci,saidai kuma komai ya sauya......wannan tunanin ya canza daga sanda idanun su suka gauraya dana morsa safiyya.

Kallon kallo suka yiwa junansu,kowannensu abinda yake yawo daban a ranshi. Batasan me ya hanats tashi ba har zuwa sanda morsa safiyya ta tako a hankali ta zauna a gefanta.

"Biftu" Ta kirata a tausashe,sunan da haruffan kuma suka sauka har cikin kunnen haisam dake takawa ta gefan farfajiyar a hankali yana duba wasu irin furanni da aka zagaye katangar gurin da aka samar da ita ta wannan bangaren da itacen bamboo masu daraja. Kadan yadan juya,amma fuskantar ba wani bane a gurin,murya ce daga can wani guri sai yaci gaba da abinda yakeyi din hankalinsa kwance ba tare daya damu da neman daga inda sautin yake ba.

"Biftu.....me yasa zaki daga hankalinki har haka?,me yasa zaki nemi cutar da kanki akan abinda yake ibada ne?......biftu,ki kori shaidanin da yake miki saqa a mugun zare,ki yaqi baqin tunanin dake wahalar da kanki da kuma rayuwarki mana......ba ta inda aure yake qasqantar da darajar diya mace,face ma daga mata martaba da kima da yakeyi,koda bata samun dukka abinda tayi buri ko hasashe a cikinsa.......amma martabar wannan igiyar da darajar sunan AURE dake kanta kadai ya isheta girma da alfahari......don Allah biftu,ki kyautata zato a rayuwarki ta gaba.....kiyi haquri ki fahimci zahirin rayuwa.......muna buqatar ganin wanzuwar jinin safeena......muna buqatar zuri'ar safeena ta wanzu a doron duniya a doron qasa kaman yadda kowannenmu ya samu nasa rassan.......safeena ce kawai bata samu wannan ba.....ki tausaya mata ta zamu zuri'a mara yankewa,ba wanda zai mata wannan sai ke......ba wanda yake da wannan ikon a hannunsa yanzu sai ke......inda ahmad yana raye......dukkan fatanmu da burinmu zaifi karkata a kansa fiye dake,amma zuwa yanzu,duk wani me sauran FATA da BURI akan AHMAD ya gama sarewa,ya gama lullube babin taba wanzuwarsa a masarautar AGADEZ. Daidai da sultane bashi da wani sauran BURI ko mafarki a kansa.....ke dindai.....ke kadai ce yanzu duk wani burinmu game da zuri'ar SAFEENA" Morsa safiyya ta samu takai qarshe da qyar muryarta na rawar dake nuna bayyanuwar raunin nan nata dake da wahalar bayyana.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

*HUGUMANKU CE*โœ๐Ÿฝ

๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž


*H U G U M A*


Page 72
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
__________________________



Idanu alkhnan din ta zuba mata,duban morsa safiyya takeyi fes kanta tsaye. Fata take.....so take ta tashi tabar mata gurin salin alin ba tare da tace komai da ita ba,amma a yanzu da takejin zuciyarta na cike da ita......tana jin a yau kadai data samu dama ta furzar mata da wani abu ko yaya ne......ta gwada mata bata buqatar wannan alaqar.....wannna dangantakar gaba daya,ahalin salsalar da nasabar dukka basu cikin buqatun rayuwarta da suka zame mata dole.

"Karki bari zuciyarki da shaidan su raya miki komai........safiyya ce.....shaqiqiyar safeena......qanwa a gareta,qanwa mafi kusanci mafi shaquwa ga mahaifiyarki......kisa dukkan hankalinki da nutsuwarki a wannan karon na roqeki......ki karbi shawarata koda sau daya ne tak a rayuwarki,nayi miki imanin ba zakiyi dana sani ba......"

"Wannan shine babban danasanin da zanyi a rayuwata irin wanda ban taba yinsa ba......" Ta furta da wani irin calmness,saidai kuma idanunta suna qaryata nutsuwar dake tattare da kalamanta.

Wani irin shock morsa safiyya taji,tayi sak tana duban alkhnan duba na zallar mamaki. Duban da take matan sam bai sanya ta rusuna,ko taji bata aikata ba daidai ba,kota rage kaifin kallon da take mata ba.

"Don Allah....." Ta motsa labbanta tana sake fadi da wani irin sanyi.

"Don Allah wannan dangantakar.....wannan alaqar.....wannan ahalin na safeena......wannan dangin dukka bana buqatarsu,don Allah.....nima ina roqonku.....ni khadeejatul akhnan......a yau,a karo na farko cikin tarihin rayuwata,na karya record dina......ban taba roqar kowa komai ba.......ban taba tambayar kowa yayimim komai ba,amma a yau ina roqarki momma safiyya me laqabin qanwa ga mahaifiyata......ku janye ku kuma fita daga dukkan wani sabga daya shafi rayuwar akhnan ".

Wani irin harbawa yaji wannan jijiyar dake gefen kanshi yaji tayi har cikin qwayar idanunsa. Harbawar da yawanci idan tayi to ba shakka ransa yakai maqurar baci. Da sauri ya jefar da furen daya ciro a qasa,wanda ya tsinko shine don ya tantance launin qamshinsa,jifarwar da zaka zaci kunama ya kama bawai fure ba. Idanunsa ya daga a hankali yana kallon katangar da yake kyautata zaton itace ta rabashi da ganinsu,yana jin yadda idanunsa ke masa zafi zafi.

Tun daga sanda yaji fitar sunanta daga bakin matar da bai tantance wace ba......tun daga sanda ya fahimci yana jin maganganun wasu ne da zai iya yiwuwa sirrinsu ne da bai kamata wani yaji ba,ya qara kuzarinsa na duba dukkanin flowers din yabar gurin,don yasan zai wahala ya iya sake dawowa ya duba din idan yabar gurin,yana da abubuwa da yawa daya tsara cikin satinnan.

"Calm down.....calm down" Ya samu wani sashe na zuciyarsa yana gaya masa,yana kuma ji har cikin kunnensa.

"A'uzu billahi minash shaidanirrajeem......la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimeen" Ya furta yana ja baya a hankali yana qauracewa gurin. A hankali yaji yana dawowa saitinsa,ya soma tuhumar kansa kuma da rashin gaggauta barin gurin don gujewa jin abubuwan da zasu bata ranshi irin wannan.

"Astagfirullah" Ya samu kansa da furta a hankali yana motsa kyawawan labbansa.

Wani irin girgiza morsa safiyya tayi da wani nau'in madaukakin mamaki......kalaman akhnan a yau sai takejin sunfi komai yi mata muni a rayuwa......ba ita morsa safiyya kawai ba......dukkan family din DIOURI ta hada tace bata buqata?,wannan wacce irin mummunar illa mammina ta yiwa ahalinsu?. Tunanin yazo qarshe da wani irin tawagar hawaye cikin idanun morsa safiyya,saidai kuma cike da wannan sadaukantakar tata ta soma maidasu cikin cikin idanunta a hankali a sanda ta jiyo muryar mammina din tana shigowa gurin.

"Biftu?......biftu??" Tana kiran sunan akhnan din da wani yanayi dake nuna hankali sam ba'a kwance yake ba,yayin data kafe bayan wanda take gani da kallo.

Bata iya ganin fuska ko wani sashe na jikinta,face shimfidaddiyar rigar data suturta jikin morsa safiyya din.......amma already tun kafin ta fito zuwa nan din ta samu cikakken bayanin morsa safiyya din tana tare da akhnan din a madaidaicin kebantaccen lambunta.

"Biftu?......wanne irin shashanci ne haka?,wacce irin wauta ce wannan kika aikata?,kinsan adadin dagin hankalin da kika sani?" Mammina ta furta tana dafa dukkan kafadun akhnan ba tare da tabar wata alama da zata gwadawa morsa safiyya cewa ta ganta ba.

Iya wanzuwar mammina a gurin ya karya zuciyar akhnan gaba daya,sai takejin dukkan gatanta kamar ya dawo,sai takejin kamar matsalarta taxo qarshe,don haka ta sanya fuskarta jikin mammina din tana riqeta da kyau gami da sakin wani boyayyen kuka da mammina din kadai taji sautinsa ta kuma fahimceshi.

JINI YAFI RUWA KAURI wata nau'in karin maganan bahaushe kenan,duk da bataga fitar hawayen ba......duk da bataga wani alama ba.....amma har cikin jininta taji fitar kukan daga zuciyar akhnan din.

GANIN RAUNI a tattare da ita,shine abu na qarshe da baza bari idanuwan mammina su gani a tare da ita ba....KOMAI GIRMAN TSANANI....KOMAI QARFIN BALA'I,wannna ya sanya ta miqe tsam daga inda take zaunen tana jifan mammina da wani irin kallon da tsana da tsananin qiyayya ce fal shimfide a cikinsa.

"Komai nisan dare gari zai waye.....komai nisan jifa qasa zai fado.....komai girman gona akwai kunyar qarshe. Jini yafi ruwa kauri......nasaba da gaurayar jini cikin tsatso da tushe guda ba wani abu da zai iya sauyashi.....duk duniya ba wani sinadarin da zai kwashe wannan tabbatuwar jinin nasabar ya sauyashi zuwa wani na daban" Ta qarasa maganar wani sassanyan murmurshi yana fita daga saman fuskarta,kai bakace baqar wuta ce ke zabalbala qasan zuciyarta ba a daidai lokacin.

Zuzzurfan kallon kallo suka yiwa juna na wasu sakanni,sannan morsa safiyya ta juya a hankali tana takawa cike da nutsuwa take barin gurin,saidai ko mintuna daya tak batayi da bawa mammina baya ba,hawayen da take maqale dasu suka maye gurbin wannan murmurshi da tabbas tasan fake ne,na bogi ne......murmurshin da suka d'arsa wani qaqqarfan abu a zuciyar mammina.......ta kuma gaza dauke dubanta daga dukkan wani taku na morsa safiyya da daukeshi.
(08187255862 lu'u lu'u paying)

"Na gode" Morsa safiyya ta fada a hankali labbanta suna rawa sanda ta shafo hawayen da yatsunta ta kuma bisu da kallo,sannna ta rab'e ta wani kebantaccen guri daya zama nata ita daya don ta rage nauyin dake qirjinta ba tare da kowa yasan da wannan ba. Ta godewa hawayen ne saboda basu bada ita gaban mammina ba......ta yaba musu ne saboda basu fita a sanda bai kamata su fita ba,ya kuma jinjinawa zuciyarta data iya dauke wannan nauyin me girma bata bari anga gazawarta ba har sai data kaucewa idanun kowa.

Zare idanunta tayi daga hanyar wucewar morsa safiyya cikin jikinta tana jin tabbas akwai wani abu........cikin tsakiyar wannan murmurshin lallai akwai wani abu. Ba kowanne murmurshi ne yake kasancewa murmurshi ba.....kaman yadda ba kowanne murmurshi ne yake dauke da ma'ana ba,wani murmurshin fanko ne......wani saqo ne......wani kuma barazana ce,wani kuma yakan kasance gargadi ne.....batasan a wanne muhalli ko bigire zata aza na morsa safiyya ba.

Cikin nutsuwar da iyakacinta saman fuskarta take duban akhnan,cikin dakin daya kasance babu kowa a ciki,daga ita sai akhnan din suna fuskar juna. Duban akhnan din take tana mamakin fitar hawaye haka daga saman fuskarta.

"Biftu......" Ta kirata a tausashe,saidai akhnan din taqi barinta ta qarasa fadin abinda tayi niyyar fada din ta soma girgiza ma mammina kai

"Wallahi mammina.......bazan iya jurewa ba,bazan iya aurensa ba.......baiyimin ba......bana sonsa!.....bana qaunarsa,don Allah,ki gayawa sultane......karkice zaki juyawa alqawarinmu baya" Ta fada tana kama hannun mammina din tana dubanta da dukkan wani hope nata.

Shuru mammina din tayi,fuskarta da yanayinta suna suna nuna rashin gamsuwa da maganganun akhnan din.

"Na roqeki mammina......na roqeki,a yanzun bani da wani fata akan kowa sai ke,bani da sauran yaqini sai a gurinki".

" Amma biftu....kinsan yadda sultane ya dauki maganan hakeem da girma kuwa?.....ke kanki kin sani,shawarwarin morsa safiyya na days daga cikin shawarwarin da sultane kewa kyakkyawan riqo da gasken gaske?". Idanunta ta lumshe sannna ta budesu,tana jin wani irin matsanancin zafin morsa safiyya cikin ranta. Daga sanda taji cewa ita ke riqe da ragamar karbar baquncin baqonta,daga sannan tasan cewa ba wani al'amari kuma da zai kasance me kyau a tattare da ita.

"Bana son koda jin sunan matar nam mammina.....ki daina kiramin sunanta" Akhnan ta fada da wani irin matsanancin kaushi cikin muryarta. A zahiri idanu mammina ta watso waje tana duban akhnan,saidai batakai ga fadin abinda zata fada din ba akhnan ta miqe

"Basai kin sake kiramin sunanta a nan wajen ba,iya kiran sunanta a kunne na yana daidai da kiran gagarumar matsala ko rashin sa'a a tattare dani......shikenan mammina.......shikenan tunda ba zaki iya nema min alfarma gurin sultane ba......shikenan na tabbata cikakkiyar maras gata data rasa tsayayyar uwa.....na tabbata wadda tafi kowa rashin gata a duniya..." Ta fadi maganan tana dosar qofa.

Tsam mammina ta miqe,sannan ta kamo hannun akhnan din ta jawota da baya.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

*HUGUMANKU CE*โœ๐Ÿฝ


๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 73
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
__________________________








"Indai ina raye baki rasa gatanki ba......indai ina raye kuma na shirya sadaukar da komai a kanki muddin hakan zai sakaki farinciki.....koda hakan yana nufin sadaukar da fahimtar junar dake tsakanina da sultane ne,zanyi iyakacin bakin qoqari na,har sai naga abinda ya turewa buzu nadi" Ta fada tana bawa akhnan tabbaci da yaqini da dukka idanun data zubawa akhnan din su.

Wani irin abu akhnan taji yana sauka saman zuciyarta dangane da mammina din. Wata irin qaunarta me girma ta taso ta soma lullubeta,a duniya tana da masoyi sama da mammina kuwa?,anya mammina batafu sultane sonta ba kuwa?,wanne abu ne a duniya zatayi ta sakawa mammina da dimbin tarin tulin soyayyar da take mata?,wannan soyayyar bata da kama......bata da daidai,sai kawai ta fada jikin mammina tana rungumeta da kyau,itama mamminan saita riqeta tana dan bubbuga bayanta gami da fadin.

"Calme-toi,tout ira bien".




โ˜…Tsaki ya sake ja sau adadin da baisan yawansa ba,sannan ya ture system din gabansa gefe yana murza tafukan hannunsa cikin na juna.

A nutse abdii ya daga kai ya kalleshi,tunda ya shigo yakeson tambayarsa abinda ya tabashi yau amma yana tsoron saba dokokin da aka shimfida masa kafin ya samu ya aminta da qyar su zauna tare. Maher kawai ya zaba su zauna dashi cikin gidan,saboda shi din ya kasance kamar wani ido ne gareshi cikin masarautar,saidai kuma kaida fata abdii yaqi aminta ya fita,dole haisam ya barshi,bayan ya zauna ya jera masa dukkan sharuddan da abdii kansa tsaye yace ya amince,duk kuwa da cewa yasan ba komai bane zai iya bi ba a dokokin.

Numfashi ya zuqa sosai yana fesarwa ta bakinsa

"What wrong with you haisam?" Ya furta da wata murya da daga shi sai zuciyarsa kadai ke iya jinta.

Sake lumshe idanunsa yayi,yanajin wani bacin rai kadan kadan yana lasar zuciyarsa.

"Why she's so stubborn?.a silly girl.....ya akayi ta kasance d'iyar kamilin mutum me daraja da dattako irin sultane.

"Yukhrijul hayya minal mayyit?" Ayar tazo cikin kansa. Numfashi ya sauke a ransa,yana ji a rayuwarsa bai taba jin wani abu da yaji sam baiyi masa ba,bai taba jin wani abu da yakejin haushinsa yana ginuwa cikin ransa ba irin yarinyar.

Totally irin matan nan ne masu tsananin girman kai?.....rashin iya magana?.....masu jin cewa izzarsu gaban na kowa yake?.

Tunda ya soma jin maganganunta bisa akasi,ba wani magana me dadi da yaji ta iya da wani,ba wani kyakkyawan lafazi data iya fiddashi daga bakinta. Ya jima baiga mace me tsaurin ido irin nata ba.....who's she?. Tambayar qarshe da ya yiwa kansa kenan wayarsa ta dauki sassanyan ringing dinnan nasa mara hayaniya da yawa,kafin yakai ga dagawa anyi knocking,sai abdii ya bude ya tafi budewa shi kuma ya daga wayar.

A nutse ya kammala wayar,ya kuma ajiyeta a nutse yana duban abdii daketa kai kawo yana zube wasu riguna a gabansa. Da idanu kawai ya tambayi abdii din ba tare da yace komai ba,sai ya dawo ya zauna yana murmushi.

"Me martaba ne ya aiko,yana gayyatarka cin abincin dare tare dashi nan da awa daya". Idanu haisam ya zuba masa a nutse,wani lokaci quruciya da wautar abdii tana damunsa,duk da tarin nutsuwarsa da kaifin basirarsa,to amma bai sani ba,kaman shi daya abdii din yakewa haka.

"Hakan da kake yana sakani tunanin anya zaka samu gurbi kuwa a NISS?". Idanunsa gaba daya abdii ya zaro waje yana duban haisam din.

"Captain obbo......" Yayi maganar yana kwantar da murya da alamun damuwa. Haisam bai daina kallonsa ba,sai ma girarsa daya dage sama yana duban idanun abdii din.

"Inajin kaman za'a dauki kalar ma'akacin da ba'a taba dauka ba........"

"......wajen iya aiki obbo" Abdii ya qarasa masa maganar da ba hakan yayi nufin qarasawa ba. Ido haisam ya rufe yana dafe goshinsa da tafin hannunsa. Kome zai cewa abdii xai sakashi doguwar magana ne a yanayin nan da sam shi bai shiryawa hakan ba,don haka ya yanke wancan maganar

"Me kace musu?".

" Kana godiya kuma zaka halarta in sha Allahu,kaga zamu shiga muga yadda yanayin nasu qarfin ikon yake.......ina duba maka rigar daya kamata ka saka ne" Yayi maganan yana daddaga kayan dake ajiye gaban haisam din.

Sake duban abdii yakeyi,wanda yayi burus kaman bai gane ba. Zuciyarsa na sake jin qaunar yaron,ranshi kuma yana dariya can qasa da bata bayyana ba. Bilhaqqi abdii yana mantawa aiki ne kawai abinda ya kawosu agadez,bawai nuna qarfin sarautar da masarautar Ethiopia ke dashi ba,ba kuma sunzo bane don a girmamasu ko a basu girma ba,hasalima hakan na iya nakasta tasirin aikinsu.

Maher ne yayi sallama,haisam ya amsa masa,ya qaraso cikin a nutse yana rusunawa cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login