Showing 174001 words to 177000 words out of 178317 words
hankali wajen cikar burinki.......". Waiwayawa tayi bayanta,ta kuma qwalawa birra kira data tabbatar batayi nisa da gurin ba.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Ki tabbatar baki bar kowa ya shigo gurinta ba.......a barta ta zauna ta nutsu ita kadai,a samar mata da dukkan abinda zata buqata har sai zuciyarta tayi sanyi".
" In sha Allah" Birra ta fadi a girmame,tana jin tsananin tausayin uwar gijiyar tata yana ratsata. A kwanakin tasan bata samun wani cikakken bacci,duk wasu yanayinta ba irin wanda ta sani bane a baya,ta juya tana bin bayan mammina don itama ta bata space sanda taga ta cusa yatsunta dukka goma cikin gashinta me santsi.
Murmushi takeson ta saki na yadda hannu daya ke tafiya da yanayin daya dace,amma kuma har yanzu tana jin lokacin da zata saki murmushin bai qaraso ba. Agogon hannunta ta kalla sanda yalwa data bari a qofar farko take biye da ita.
"Ki koma cikin gida.....anaso naci gaba da samun labari akan komai......idan nace komai ina nufin kowanne irin nau'in baqon motsi,babba ko qarami,banajin zan sake fitowa yau duka haraba,motsina da kai kawona a kwanakin nan yana yin yawa,yana kuma sauyawa daga yanayin da aka saba ganinsa a tare dani,banason zargi ko d'iso,wanzuwarsa a guri komai qanqantarsa MATSALA ce,ita kuma matsala kalma ce da mukayi hannun riga da ita". Kai yalwa ta jinjina.
"Angama" Ta fadi tana juyawa gami da sauya hanya daga ainihin hanyar da suke kai.
Su biyu suke takowa zuwa sassan nata,daga ita sai shehnaz din da bakinta ya kasa hutawa daga qorafin da mitar da takeyi tunda suka fito daga sassan nannie.
"Duk yadda zaka yiwa nannie bayanin kafiya da taurin kan akhnan ba zata fahimta ba" Abinda aisa ta fada kenan bawai don hankalinta yana kan maganganun shehnaz da mitarta dari bisa dari ba,sai nisa da hankalinta yayi kan wani abu na daban.
Tun daga waccan ranar da mammina ta gaya mata,ita zata bude office din akhnan,ta kuma ci gaba da tafi dashi hankalinta ya gaza gamsuwa da hakan. Tayita qoqarin ganin akhnan amma lockdown din data sanyawa kanta ya hanata faruwar hakan.
Taje don ganinta sau babu adadi amma bata samu dama ba,ba kuma wai don batayi isar da zata karya tsarin akhnan ta shiga har inda take ba.....aah,tayi hakanne saboda kare aikinsu birra wadanda a sanda suke mata bayanin ta kafa musu sharadin kada subar kowa ya kusanci inda take tsoro ne fal idanunsu. Tsoron irin tashin hankalin da zasu fuskanta idan suka karya mata doka daya cikin tarin dokokinta. Tana respecting mutanen,don sun sadaukar da rayuwarsu da lokutansu gurin kula da buqatunsu,wannan ya sanya tabi umarni itama don kare musu aikinsu da mutuncinsu.
Kwana daya tsakani kuma suka tafi diffa da nannie,sai dazu da azahar suka iso,ta kuma tarar da abubuwan da basa nan wasu a ciki suka kasance.
"Mammina tace kada kowa ya shiga,a barta ta samu nutsuwa ita daya" Birra take sake shaidawa aisa a karo na biyu,tana jin nauyin girma irin na aisa amma a karo na biyu tana sake gaya mata ba zata samu ganin akhnan din ba,duk da tarin matsayi da kusanci da take tare dashi.
"Wannan karon zan dan taba tsarin aikinki birra ki haquri......tana buqatar wani a kusa da ita" Aisa ta fada cikin qarfin gwiwa. Matsa mata birra kawai tayi,saboda ita a karan kanta tana ganin gaskiya a maganar aisa fiye da maganan mammina.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 82
____________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
_____________________________
Me damuwa a rai ai wanda zai sassauta masa damuwar yake buqata,bawai a barshi da saqe saqen zuciya ba da ba'a da tabbacin me zata saqa masa.
A hankali taji an sanya hannu an kuma zare hannuwanta dake cikin gashin kan nata,abinda ya sanyata daga kanta kenan tana sauke blue eyes dinnan dake cike da damuwa kan fuskar aisa dake gabanta da kuma shehnaz dake gefanta.
Dukkaninsu su biyun saida jikinsu yayi sanyi,saboda wani irinn yanayi suke hanga tattare da akhnan din,wani irin yanayi da basu taba ganinsa tattare da ita ba.
"Don me yasa zaki bawa damuwa dama ta nemi wargaza miki rayuwa?......me yasa zaki kashe wannan jarumtar juriyar da kuma dakiyar daga cikin jininki da jikinki?" Aisa ta fadi a tausashe. A yanzun dukkan abinda zai dawo da karsashin akhnan take nema,a yanzun abinda zai dawo da ita ainihin AKHNAN dinta take buqata,dukkan wasu dalilai da hanyoyi. Tana hango faduwar sahel couture haka kawai cikin mafarkanta,abinda zai iya zama babbar barazana ga akhnan din dama masarautar harma da yardar da sultane ya dauka ya basu.
Bata zargin mammina ko daya da yin wani abu ba daidai ba,amma tana ji a ranta kamar mammina bata hangi abinda ita take hanga ba.....kamar mammina bata fahimci abinda takeso ta fahimta ba,wannan ya yanke mata hukuncin dole ta farfado da akhnan daga suman wucin gadin da tayi,wala'alla ta dauko matsalar daga inda ta dace da kyakkyawan gyara.
Idanunta ta lumshe ta kuma ja numfashi me zurfi sannan ta fesar dashi ta bakinta. Batasan me yasa kwanyarta ke rikicewa ba......batasan me yasa take kasa gane kanta ba.
"Mu koma ciki......akwai maganan da zamuyi" Aisa ta fadi kanta tsaye tana miqa hannu ta kama hannun akhnan din.
Kai tsaye suka dinga ratsawa ta gurin,har suka bulla sassanta. Daya daga cikin parlor dinta suka dakata,dukkaninsu suna yiwa kansu mazauni.
"Ki raba kanki da damuwa......tana iya ruguza kowanne kyakkyawan tanadi da ka yiwa kanka.....komai yana iya zuwa ya wuce a duniya,ba wani abu me tabbata" Kai ta girgiza tana duban aisa da wani irin yanayi,har cikin jikinta takeji ta gaji da wannan matsalar......wannan damuwar ta isheta haka.
"Banda matsala irin wannan aisa......gobe na akeson ruguzawa......mafarkina da burina akeson wargazawa".
"Don ance kawai kiyi aure akhnan?.....shin wai meye aibu ko matsalar hakeem?" Shehnaz ta fada mamaki yana kamata. Anya kuwa abinda zuciyarta ke raya mata na akwai wata matsala kebantacciya tattare da akhnan din ba haka bane kuwa?.
Wani kallo akhnan ta ajjiyewa shehnaz. Akwai tarin banbance banbancen ra'ayi tsakaninta da su,bama su kadai ba.....tarin mata har yanzu bata hangi mace kamarta ba. Nata ra'ayin nata tsarin da nata rayuwar yasha banban dana kowacce mace,ba kuma zasu taba fahimtarta ba,kamar yadda itama ba zata taba fahimtarsu ba.
Duk abinda ke zuciyar aisa ta dauki wani qatoton abu ta danne. Ta riga ta gama aminta ba wani fahimtar kalaman da zasuyi ita dasu,a yanzu matsalar sabgar saheel couture tafi buqatar a magance......ta shanshano ta kuma fahimci muddin akaci gaba da tafiya a haka,tabbas makauniyar tafiya kawai za'ayi wadda qarshenta zai kasance mafi munin abinda hankula da idanuwa zasu iya kalla.
"Duba nan" Aisa ta fada tana zube mata takardu. Da idanu kawai ta bisu da kallo ba tare data sanya yatsarta ko daya ta taba kowacce ba,saita janye gajiyayyun idanun nata tana duban aisa dasu.
"Ba abinda zan iya dubawa a ciki......me ya faru?". Shuru aisa tayi ta zuba mata idanu,bacin ran da mamaki yafi yawa a cikinsa yana zagayawa da ita. Yadda akhnan din tayi maganan tasan da gaske iya abinda yake ranta kenan,ita kuma tana buqatar ceton kamfani,dole ta motsa ta fara mata bayani.
Tsahon mintuna akhnan tana kallonta,kafin aisa ta rufe da fadin.
"Akwai barazana me yawa dake tunkarar kamfanin,akwai kusakurai da gyararraki cikin salon tafi dashi,wanda ba inda zai kaishi saiga durqushewa qarshe ya rushe gaba daya,akwai sabbin mutanen da suke buqatar horaswa da gwaji kafin zamansu saman kujerun da aka basu yanzu haka suna tafi dashi.......mammina tace na bude office dinki na shiga naci gaba da gudanar dashi......"
"To me zai hana kiyi hakan?" Kai tsaye ta yanke hanzarin aisa din ta fada tana dubanta. Idanu aisa ta fidda.
"Me zaisa nayi hakan?". Ido akhnan ta lumshe kadan
"Mammina fa kika ce?.....ita ta hangi dacewar hakan,don me ba zaki aiwatar ba?". Kai aisa ke kadawa.
" Aisa ba zata taba zama daidai da akhnan ba. Nazo miki da dukka bayanan nan ne don ki watsar da dukka wannan raunin da kika azawa kanki,ki tunasar da kanki akwai nauye nauyen wasu a kanki,ki karbi aikin da yake dama naki ne. Idan da akwai buqatar na karba naci gaba da jagoranci da babu gurbin zuwa miki da wadannan bayanan......shine your eyes biftu!" Aisa takai qarshen maganar da qarfin gwiwa da kuma wani emotion da yake tasowa daga qasan zuciyarta.
Shuru ne ya ratsa parlor din,wuta tana daukewa kowa daga cikinsu. Saidai a shirun kowa da irin abinda yake kai kawo cikin ransa.
Aisa.....shurunta yana da alaqa ne da jiran motsi daga akhnan ko ta maida martani ga maganganunta......yayin da shurun akhnan ya karkata ne zuwa ga sabon hayaniya me qarfi da take jiyowa daga can farfajiyar gidan.
Hayaniyar ta mata kama da ire iren hayaniyar da kan motsa a gidan a duk sanda sultane yayi wasu muhimman baqi. Haka kawai taji qirjinta ya doka,wata irin fargaba tana saukar mata,fargabar data sakata miqewa a hankali tana dosar 'yar harabar dake maqalena falon wadda aka yita ta fuskar da zata iya ganin kusan duk abinda yake kai kawo cikin gidan.
"Akhnan....." Aisa ta fada da zafi,sai shehnaz ta daga mata hannu,abinda ya sanya aisa dakatawa kenan,don tasan tabbas akwai dalilin daya sanya shehnaz din yin hakan. Suna a zaune suna hangen sanda ta fita farfajiyar tana kuma aza dubanta dukka ga inda take hangowar.
★Sake duban yalwa tayi da kyau da wani irin hautsinannen kallo.
"Me kike cewa?" Ta maimaita tambayar yalwa,duk kuwa da cewa ta mata bayanin da koda baka fahimtar kowanne yare kana iya gane me yalwa ke fadi.
Kasa yalwa tayi da kanta,ta sani wannnan labarin ba kalar labarin da uwar dakin nata zataso ji bane,amma kuma labari ne me matuqar daraja da tsadar da zai ya qara daga martabarta a idanunta.
"Me martaba ne yake karbar baqi daga zinder.....wazirin qasar zinder,da shugaba limamai na zinder gaba daya wato mahaifin hakeem,wadanda sukazo da kayan neman auren gimbiya akhnan". Wannan karon ji tayi kaman ta koma ta zauna ko zata daina jin kamar ana hajijiya da ita,to amma kuma nuna rauninta a kowanne irin yanayi abune data jima da nesanta kanta dashi.
Tana da tarin rauni,yana kuma bayyana,amma a muhallin da babu wani mahaluqi da zai gani,daga ita sai ita daya qwallin qwal,domin tana ganin nuna rauni gazawa ce da zata janyo maka raini gurin wadanda ke qarqashin sarrafawarka.
"Ya akayi labari me girma irin wannan ya boyu har sai bayan ya tabbata?,labarin dani ya kamata na fara sanin da shi?" Ta yiwa yalwa tambayar. Kai yalwa ta jinjina.
"Abun akwai daure kai,don ina tabbatar miki kaf! Fadin masarautar nan,ba wanda yasan da zuwansu......banqi ko morsa safiyya ba" Tayi maganan tana juya kai cikin alhini da jimami.
"Morsa safiyya" Ta maimaita fadin sunanta kamar tana jinjina girman sunan. Kai ta jijjiga a hankali. Tunda har ya kasance sultane bai shaida mata ba.....tunda har sultane bai gaya mata ba bata zaton safiyya ma ta sani.
Ita daya ce mutumin dake sanin boyayyun abubuwan sultane wanda ba wani mahaluqi da yasan dasu........ita kadai ce wadda yake shawarwarin da ba wanda yakeyi dasu. Koda batanan sukan zama ajiyayyun shawarwari har sai randa ta dawo ta fadi nata hangen akai.
"Yaushe sultane ya fara koyon boye abubuwa?" Ta yiwa kanta tambayar da batasan ta fito sarari ba,har sai da taji yalwa tace.
"Allah masani,amma dukkan alamu sun nuna akwai giftawar magauta a ciki". Dubanta ta maida ga yalwa.
"Karbar gaisuwar sarkin zinder da mahaifin hakeem.....hakan na nuna tabbatuwar auren hakeem da akhnan?" Ta yiwa yalwa tambayar da ita kanta tasan amsarta EH ce.
Sultane baya magana ya sauyata,bama sultane kadai ba.....dabi'a ce ta dukkan wani basarake data taba sani.
Indai haka ya tabbata kenan akwai yuwuwar faruwar komai......akwai yiwuwar komai zai iya kasancewa......kasancewar da take nufin tarwatsewar abubuwa da dama.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Ginannen BURI.....ajiyayyar MANUFA......tsohuwar FANSA da aka jima ana mata tanadi. Kai ta jijjiga da wani irin qarfi. Koda komai zai jagule......koda za'a rasa rayuka da lafiya na wasu mutanen ba zata bari haka ya faru ba......akwai SADAUKARWAR LAFIYA da RAYUKA da zata faru cikin masarautar agadez kenan. RASHI zai faru,koke koke zasu yaiwata,har sai ta tabbatar komai ya tafi mata yadda takeso. Ba zata damu da koma waye ZAI SAMU ko ya rasa ba.....ba zata damu da koma waye ZAI QUNTATA ko ya shiga masifa ba....FANSARTA........BURIKANTA suna gaban komai. Ba zatace Allah ya taqaita ko ya sawwaqe ba......idan ya taqaita ko ya sawwaqe tana yiwa wadanda abun zai shafa BARKA DA MURNA.
"Inason a yanzu basai wani lokaci ba,ki isar da saqon zuwan wadannan baqin ga kunnen akhnan" Ta bawa yalwa umarni. Tana kyautatawa kanta zaton samun mafita a zuwa da dawowar yalwa,tana jin motsin akhnan daga shi kadai zata tsago mafitar da zata bata haske a gaba.
"An gama" Ta furta da sauri tana miqewa daga tsugunnon da tayi a gabanta.
"TURQASHI!" Mammina ta fadi a sarari tana dunqule hannunta gami da kaiwa daya tafin hannun nata duka.
"Ki nutsu......ki nutsu zaituna" Shine abinda zuciyarta ke maimaita mata,sai tabi shawarar zuciyartata,ta zuqo iske me yawan gaske tana aikawa hunhunta,sannna ta zauna a nutse saman kujerar tana qoqarin tattaro dukka kuzarinta da kuma kowacce qofa dake cikin qwaqwalwarta dake taimaka mata wajen bada tunani me kyau.
Tana kallonsu amma tana son qaryata kanta.......tana duban sultane da baqinsa amma tana qaryata abinda zuciyarta take raya mata tattare dashi.
Kayan sarauta na masarautar zinder......kayan hadimansu dama dukka wani yanayi irin nasu ba baqon abu bane tattare da ita. Dukkan baqon da sultane zaya fito da kansa ya tarbeshi ba shakka ba qaramin muhimmanci baqon yake dashi ba a wajensa.
A hankali qafafunta da hannuwanta sukayi wani irin rauni sanda take hangen hakeem a cikinsu. Wata irin faduwar gaba ta daki qirjinta data sanyata dafe qarfen gurin da kyau. Kai ta girgiza a hankali tanason tankwabe kalar tunanin da zuciyarta ke kutso mata dashi. Daidai sanda taji birra na fadin.
"Mammina ta aiko da saqo ta hannun jakadiya yalwa". Kai kawai ta iya gyadawa birra din,wanda ta kauce kadan,abinda ya bawa yalwa daman kutsa kai farfajiyar gurin.
Tsam aisa ta miqe,tana jin hankalinta bai kwanta da tsaiwar akhnan a gurin ba. Uwa uba wanne saqone haka yalwa ke tafe dashi wanda yanayinta dukka ya nuna alamun a gaggauce take.
Taku uku aisa tayi shehnaz itama ta miqe tabi bayanta.
"Tace na gaya miki ki tattara hankalinki da nutsuwarki guri guda......baqi ne daga zinder wadanda ke dauke da dukiyar aurenki......a yaune kuma sultane zai basu tabbacin bada ke ga dansu bayarwa ta har abada da zata halasta aure a tsakaninki dashi". Kaman kunnuwanta basu jiye mata daidai ba haka taji,sai kuma ta soma jin kamar ana turata baya kafin ta dangane da jikin shehnaz da tayi tsaye a bayanta. Bata damu tasan waye ya riqeta ba,idanunta akan yalwa kamar itace sultane din.
"Bayar da aure na?,karbar dukiyar aure na?.....ga hakeem din?" Ta fada da wani sanyi a muryarta,ba kuma kalar sanyin dake cikin zuciyarta kenan ba,don wata irin kalar wuta zuciyarta ke fiddawa da adadin zafinta da zuginta ya zame mata na daban.....kalar wanda bata taba tunanin rai da zuciya zasu iya d'an d'ana su kuma jure a rayuwarta bane.
"Ba shakka.....haka abun yake". Da wani irin hanzari ta sanya dukka hannayenta biyu ta ture shehnaz dake riqe da ita,aisa tayi kan shehnaz da turwar tazo mata a bazata don kai mata dauki,gudun kada ta fada kan kujerar qarfen dake bayanta ta zame mata ciwo,wannan kuma shi ya baiwa akhnan daman ficewa daga farfajiyar da wani irin yanayi kamar name ficewar hayyaci. Da wata irin madaukakiyar murya me qarfin gaske take fadin.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700