Showing 162001 words to 165000 words out of 178317 words
tsakar gida na alfarma,wanda daga nan yake iya hango kyakyawar balcony din dake lullube da shuke shuke,balcony din da ita zata sadaka kai tsaye da qofar makadeden parlor din me martaba.
Guri ne da muddin ka iskoshi baka buqatar iso game martaba,dukka shingen daka tsallaka ka wuce suka baka daman isowa ga nan din sun gama tantanceka,don haka kai tsaye ya dinga takawa yana nufar balcony din.
Sanye yake da wata jubah me sulbi kalan gray color kalar data haska ta kuma fidda tsananin kyan fatarsa na asalin qabilar oromo me hasken kala data dara ta sauran asalin qabilar. Daga wuyan jubah jallabiyyar da hannuwanta wasu irin maballai ne masu tsananin kyau da daukan hankali.
Kansa kuwa hiram ne me kyau daya masa wani irin nadi da mafi yawan matasan larabawa 'yan birni keyi masa,shi ba yafashi yayi ba,amma yafi shigen kama da daurin dankwali da aka saki jelarsa ta baya,wata kuma ya sauko da ita kafadar hagunsa.
Tattausan unique scent dinnan nasa ke fita,iska tana kadashi gami da kwasarsa tana watsashi sassanni daban daban na sashen me martaba dama kewayensa,qamshin da yakan jimma manne a guri bar tafi ba,yakan dauki kwana uku ma musamman idan har haisam ya zauna a gurin ne na wasu awanni.
Qafarsa wani lafiyayyen farin takalmin fata ne,wanda ya dace da torches din jikin amama din kanshi(hirami) da kalarsa ta kasance gray da torches na white. Koda sau daya ka aza idanu a kansa lallai zai burgeka,komai nasa yana nuna tsantsar ilimin addini daya cakuda da wayewa ta fannin sanin duniya da abinda ke cikinta. Wata irin wayayyar siffa ce dake kwance cikin duk wani motsinsa,wadda ta cakuda da tasirin addini da wani iri kamala da kwarjini da alqur'ani yake zubawa dan adam.
Can qasan maqoshinsa yayi bismillah a sanda yake dora qafarsa saman step din farki na balcony din,bismillah din da adams apple dinsa ne kawai ya motsa,wanda ya fito sosai daga saman maqoshinsa kaman idan ka sanya hannu zaka iya ciroshi.
Manyan idanun nan nashi da shigowar dare ya sanya suka rusuna kadan ya ware a hankali,yana duban mutumin da baya iya ganin fuskarsa sai faffadan bayansa,yana maqale sosai da wani irin salon tsaiwa jikin tafkeken window din dake kai iskar tsirrai me sanyi dake busawa a gurin zuwa cikin ainihin parlor din.
Kaman yadda ci gaba da takawan da yakeyi bai hanashi ci gaba da kallon bayan mutumin ba......wanda da ganinsa basai an gaya maka ba qaqqarfa ne......hakanan takunsa bai dauke hankalinsa ko na mutumin daga tsaiwar da yakeyi ba. Qasan takalminsa yana da laushi kaman yadda saman takalmin keda laushi,wannan ya sanya hankalinsa ya gaza daukowa don da alama bayajin kowanne irin sauti,sai sake maqalewa da yakeyi jikin window din sosai,da alama akwai abinda yake tsananin buqatar yaji,abun kuma daya kasance me muhimmanci qwarai da gaske a tare dashi.
Sannu a hankali mamaki ya soma wanzuwa qasan zuciyar haisam,ya kuma katse duk wani nazari da yakewa katangun dake kewaye da sassan sultane din ya maidashi kacokam kan mutumin.
Wani zuzzurfan kallo ya masa guda daya daya dasa masa wani qaqqarfan zargi me girma a zuciyarsa game da mutumin da ko fuskarsa bai samu daman gani ba,bai kuma yarda yayi wani motsin da zai alamta masa tahowarsa ba,har sai daya isa saitin qofar parlor din,ya soma zame takalmin qafarsa ta hanyar yin amfani da dunduniyar daya qafar sannan ya saki wata taqaitacciyar gyaran murya mara amon sauti idanunsa kafe akan mutumin.
"Waaqa!(god!)" Ya fadi a razane sanda yake waiwayowa da hanzari cike da mamakin wanzuwar wani dan adam a gurin bayanshi.
"OROMIA?" Haisam ya furta can qasan ransa cike da zallar mamakin jin fitar yaren oromo daga bakin mutumin,mamakin da ya gaza boyuwa ya wanzu saman fuskarsa dama idanunsa,ya kuma kafe TAMIM da kallo duk da a lokacin bai kamata cikin tsarin aikinsa yayi hakan ba.
Idanunsa ya maida ga goshin tamim dake tsatstsafar da zufa,abinda ya sanya tamim wanda shima ya zubawa haisam idanu kai hannunsa ga goshinsa,ya kuma shafo gumin yana dubansa hannunsa.
Idanunsa ya sake maidawa kan fuskar haisam,zuciyarsa cike da wani irin madaukakin mamaki da kuma tarin tambayoyin
"Waye wannan?......waye shi?,yaushe ya wanzu cikin masarautar agadez?,a wanne lokaci ya samu matsayi irin wannan?,matsayin ketawa ta sassan sultane kanshi tsaye?. Ba dan rakiya?,ba iso?,ba tsarewa daga gurin masu tsaron sassan?.
So yake yaci gaba da kallon idanun haisam ko zai iya karanta ko sansano wani abu tattare dashi,amma wani irin kaifi da kwarjini dake fita daga idanun haisam din sun danne nashi. Kasa jurar ci gaba da kallon fararen manyan idanun haisam din yayi,sai ya janye nasa,yana maidasu wani sashen cikin Tsananin mamakin jin wani baqon abu tattare dashi.
A hankali haisam ya janye dubansa daga kan tamim din,ya tura sliding door din falon,abinda ya sanya tamim samun daman waiwayawa yana kallon haisam din a sanda ya fara takawa yana barin farfajiyar cikin jin wannan nauyin yana zartawa yana son murqushe zuciyarsa da duk wani karsashi nasa. Tashi guda kuma yana jin wani irin nauyi da wani abu me kama da tsoro yana son lullubeshi.
"Bappi....." Akhnan ta kira sunan sultane din da wani irin rauni daya cika muryarta,raunin da sultane din kadai ta yarda ya ganshi,raunin da bata taba yarda ta bayyanashi gaban kowa idan ba sultane din ko mammina ba.
"Bappi.......kayi haquri,kayimin alfarma bappi,ka janye maganan nan,bazan iya auren hakeem ba......ka yafemin bappi na roqeka" Ta fadi da sanyin da sai daya daki zuciyar sultane din,saboda abune da ya jima shi kansa bai ganshi ba a tattare da ita,saidai kuma tunawa da yayi cewa wani gatan zai sake yiwa rayuwarta,sai ya gayyato wannan jarumtar tasa ya aza saman ranshi. Wani kallo ya aje mata me nauyi,kallon daya soma ratsa duk wani jini dake yawo a jikinta da wani irin sarewa da lamarin sultane,kallon daya bata tabbacin yin nasararta abune me matuqar wahalar gaske.....hasashen daya kusa tarwatsa mata kwanya saboda razani,tayi qasa da kanta cikin jiran tsammani,abinda ya sanya lullubin saman kanta ya hadu da sassalkar sumar nan da tsananin kulawar da take samu ya maidata me sulbi,ya zame daga saman kanta zuw kafadunta.
Saidai kafin shi ko akhnan wani a cikinsu ya sake cewa komai amon muryarsa ya gauraya a parlor din.
Cikin muryar nan tasa dake da wani irin zurfi da kuma amo ya yi cikakkiyar sallamar dake nuna yasan haqqinta yasan kuma cikakken ladan da ma'abota cika sallama suke samu.
"Wa'alaikumussalam warahmatullah" Sultane ya maida martanin sallamar fuskarsa tana washewa da wata kwantacciyar fara'a,abinda ya d'arsa wani babban abu saman zuciyar mammina,tana kuma jin nauyin sautin muryar haisam har saman zuciyarta.
Waye wannan daya samu nasarar gusar da fusata da bacin rai daga zuciyar sultane da sallamarsa kadai?. Kaman sultane yasan me take tattaunawa da zuciyarta,cikin nutsuwa da girmamawa yace.
"Bismillah sheikh muhammad........kai da falon mahaifinka?".
" Mahaifi?" Mammina ta maimaita kalmar can qasan zuciyarta,tana kuma jinjina girma da nauyinta. Wannan kalmar da wannan furucin na sultane ya sanya zuciyarta cikin zaquwa da son sanin waye wannan?,abinda yaja hankalinta kenan ta zubawa qofar shigowa idanu don ganin bayyanarsa.
Cike da wannan cikakkiyar kamalar wadda ta cakuda da kaifin kwarjini da haibar jinin sarautar OROMIA dake jininsa ya sanya qafafunsa cikin parlor da cikakken nutsuwar nan tasa. Karon farko idanun mammina suka sauka a kansa,wata irin matsananciyar faduwar gaba ta saukar mata ba tare da tasan dalilinta ba.
Dukka idanunta ta zuba masa sanda yake ketowa cikin gurin,tana jin wani irin yanayi da batasan wanne iri bane yana ratsa jikinta har zuwa cikin b'argonta a hankali,kamar wadda ake fifitawa iska tsakiyar sanyin hunturu.
Kallonta ta maida kan sultane wanda ya miqe yana fadada fara'arshi.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Barka da zuwa sheikh......ga guri zauna na qarasa ganawa da me dakina" Ya fadi yana yiwa haisam din nuni da mazaunin dake daura dashi.
Iska ta sake shaqa a karo na uku tana jin kamar kwanyarta ta fara birkicewa,kaman komai ya soma dagule mata,kai kaman hauka ne ma yakeson kama ta?,ko kuma depression ne yake mata sallama?. Banda haka ta yaya?.....ta yaya a irin wannan lokacin?,a daidai lokacin da take tsaka da gwabza yaqin neman sauko da sultane daga kujerar naqin da yahau,kuma sannan a lokacinne wai hancinta zai dinga dauko wannan ajiyayyen qamshin yana kawo mata kusada hancinta?.....shin da wanne zataji?,da qoqarin soke auren hakeem a kanta ko kuma case din wancan mutumin?.
Mutumin da tun daga wancan ranar zuwa yau bata sake lafiyayyen bacci ba ita kadai?,mutumin da tun daga wancan ranar zuwa yau bata taba kwanciya ta tashi lafiya qalau ba tare da taga gilmawar wadannan idanun masu wani irin magnet cikin baccinta ba?,wannan idanun da take zargin ta sake ganinsu ko ganin irinsu a wancan ranar,a ranar data kawo kanta wajen sultane.
Kamshin wani irin ajiyayyen abune da kwanyarta da zuciyarta ta yiwa mugun ajiyar da koda cikin baccinta zata shaqeshi ta tabbatar saita farka,komai nisa ko nauyin baccin,koda zata manta komai daya shafi wancan ranar,ba shakka ba zata taba manta wadannan abubuwan biyu ne WADANNAN IDANUN da kuma WANNAN QAMSHIN da har yanzu ta kasa samar da irinsa domin hujja.
To ta yaya ma zata mance dasu?,bayan yana cikin manyan burikanta?. Bata da buri a yanzu days wuce zaqulo SHI. Wannan baqon da yaso tozartata ya tozarta nasararta da ajiyayyen tarihinta name tabbatacciyar nasara?. Muddin ta barshi ko ta haqura ko kuma ta manta ita din bata cika HALASTACCIYAR DIYAR SULTANE MUHAMMAD HAMMUD BA.
Sam ko kusa ko alama bai lura da ita ba,har sai zuwa sanda ya tako da zummar zama inda sultane din yayi masa tayin zaman.
Kanta yana qasa,abinda ya sanya wannan kyakkyawar sumar me kyau da daukan hankali bayyana sosai fiye da fuskarta. A hankali kuma cikin ba zata idanunsa sauka saman sumar tata,ya janye qwayoyin idon nasa da wani irin sauri yana canza direction dinsa zuwa wata shiyyar ta daban. Wani irin abune ya tsarga masa tun daga saman kansa zuwa tafin qafafunsa.
"Subhanallah" Ya fadi can qasan maqoshinsa,adams apples dinsa suna yin sama da qasa duka lokaci daya.
Gashin mace yana daya daga cikin al'aura a jikin mace,zai iya cewa tsahon girmansa bazaice ga randa yaga wani sashe na jikin mace haka ba,don hatta dasu Anani suna da doka a kansu kai tsaye daga gareshi,bai yarda dayin kowacce shiga da sukaga dama ba muddin ba'a cikin dakinsu bane,don haka zaiyi wuya ka samesu kansu a waje ko wani sashen jikinsu muddin ba'a dakinsu suke ba.
"Bismillah muhammad.......nan dukka na gida ne,kaima kuma ka zama dan gida......ga mamarka nan zaituna........ga qanwarka kuma babbar diyata khadeeja akhnan".
Sosai ta zuqi qamshin da qarshen harafin sunanta da sultane ya furta. Sake cika gurin da qamshin da yakeyi da kuma yadda wani ya samu darajar da zai shigo a sanda take ganawa da mahaifinta,har kuma sultane ya ajiye komai......ya tsaidata ya kuma tsaida uzurinta da hanzarinta,ya tsaya saurarensa da dukka girmamawarsa.......daga qarshe ya dinga hada dangantaka tsakaninta dashi,irin dangantakar ma ta YAYA da QANWARSA.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer ๐ณ๐ช*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA๐*
*HUGUMANKU CE*โ๐ฝ
๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
PAGE 77
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________
Dukka wadannan tunane tunanen suka harzuqata,ta daga fusatattun idanunta da taketa qoqarin controlling fushinta da bacin ranta da zummae saukewa koma waye wulaqantaccen kallon da zai sanya ya fahimci iya darajarsa,saidai kuma a sanda idanunta suka fada saman fuskarsa da take yau full opened......suka sauka kan wadannan kewayayyun idanun da suka shiga rayuwarta,suka kuma shiga dukka mafarkanta sukayi kane kane,sai dukkan komai ya kwance mata.
Wani irin lallausan murmushi ya sakewa sultane daya qara masa haiba,ya canza gurin zaman daya tabbatar zai sake nesantashi da ganin wani sashe na surar gashinta,yana qoqarin maida idanunsa kan wayarsa dake hannunsa wadda tayi blinking har sau biyu,alamun shigowar saqonni a jere.
"Allah yasa buqatata bata takura ka ba". Miskilin murmushin nan daya qarawa idanunsa wani irin sheqi ya saki,ya motsa labban nan nasa dake wani irin glowing su kadai,saika zargi ma ya shafa musu lip gloss ne.
"Gayyata irin wannan girmamawa ce sultane........"
"Bappi......zanfi son ka kirani da sunan,don sunan da diyoyina ke kirana dashi kenan" Ya qarasa fada yana maida dubansa kan akhnan.
Da qyar ta jefa hannunta baya ta jawo mayafinta,cike da tsammani da kuma yaqinin haisam din zai maido dubansa kanta,saidai a maimakon hakan kai ya jinjinawa sultane kawai ya maida wadannan idanun mash kaifi da nauyi saman wayarsa yana qoqarin sanya ta a silent yana kuma furta
"Barka da dare".
"Barka kade yarona......ya qoqari?,Allah ya dafa ya saka da mafificin alkhairi"
"Ameen ameen" Ya sake fadi cikin girmamawa.
"Ammm.......mammina ga muhammad nan,sabon d'anmu,kuma malaminsu falaak dake daukansu darasi duk yammaci" Sultane ya fada yana duba mammina din.
Wani irin numfashi ta fusgo,kafin kuma ta biya ta hado da aron murmushi daga wani loko can na zuciyarta,kafin kuma a nutse ta saci kallon yanayin zamansa da kuma saqar jubah din dake jikinsa,ta kuma dora da.
"Barka da warhaka sheikh,muna maka maraba da shigowa cikin da'irar ahalin sultane,haqiqa lallai ka taki babbar sa'a da har ka samu matsayin D'A sukutum daga sultane.......kinga daga yau biftu kin samu dan uwa ko?". Murmushin farinciki sultane ya saki,yana jin haisam kamar da gaske d'ansa ne har cikin jininsa.
Ido haisam din ya lumshe tare da budesu lokaci guda yana dan jinjina kai. Sautinta da yadda karin harshenta ke fita yake qoqarin harhadawa cikin kansa. Wani irin accent yakeji daga bakinta daban,accent din da yake ji daga bakinta kamar ya banbanta da sauran harsuna da yaji sunyi magana cikin agadez.
Idanunsa ya daga a hankali ya sauke kan mammina,wani kallo qwaya daya amma da aka yishi da tarin manufofin dake dauke da harsashe me zurfi.
Idanunta ta lumshe tana qoqarin daidaita wancan qamshin a hippodrome......wannan qamshin a ranar da ya saketa ta kusa faduwa kusa da dakin hutawar sultane......da kuma wannan lokacin a yanzu da qamshin ya mamaye ko ina da wani irin yanayi da taji yana harbawa har saman kanta yana kuna sake dawo mata da ranarsu ta hippodrome data yiwa laqabi da BAQAR RANA. Ranar da har ta koma ga mahaliccinta bata jin zata bace a kwanyarta.
A nutse mammina taci gaba da satar kallonsa qasa qasa,kowanne abu a jikinta daka iya bata signal akan komai yana motsa mata gami da ajiye mata wasu baqin yanayi a jikinta. Ba tambayar dake neman dakusar da nutsuwarta irin son sanin WAYE SHI?. Duk da cewa kunnuwanta sun jiye mata kuma kwanyarta ta ajiye mata batun MALAMINSU FALAAK ne. Sai takejin kamar sultane na zolayarsu ne......sai takejin kamar sultane na son tsokanarsu ko gwada hankalinsu ne. Ta aminta zai iya zama malaminne,saboda wani irin haske da ajiyayyen kwarjini da take hanga tattare dashi,amma ko da malaminne bawai malaminsu falaak ba,yafi kama da qasaitaccen malamin da gata da hutu suka huda jikinsa. Yaushe ma ya shigo masarautar amma bata samu labari ba?,yaushe ya soma rayuwa cikin ta ita bata taba sani ba?......hakan yana nufin tayi sakaci kenan?,hakan yana nuna akwai sauran qofofi data bari a bude wanda bata toshesu ta hanyar zuba masu bata masaniya ta wannan qofar ba.
"Akwai sauran gyaran daya ragemin" Ta fadawa kanta,tana jin bata da sukuni har sai tasan wayeshi. A tsarinta cikin lokaci me muhimmanci da tsada cikin rayuwarta irin wannan,bata buqatar