Showing 51001 words to 54000 words out of 178317 words

Chapter 18 - LU'ULU'U COMPLETE

yawa yawan shigarsa kenan a ranakun aiki. Shiga ce da ba za'a kirashi na qananun kaya ba,hakanan ba za'a kirashi da manyan kaya ba kai tsaye. Kamfani na musamman dake samar dashi daga qasar india yake saka order dinsu a duk sanda suka fidda sabon design.

A nutse yaqaraso babbar qofa ta farko dake zagaye da katangun hukumar tsaron dake da wani irin matakan tsaro daka iya zama barazana ga dukkan wani maras gaskiya,su sake kuma bayyana girma kima da darajar da gurin yake dashi.

Cikin mamaki kuma tsaye suka wangale masa babban gate din. Ganinsa yau shi daya tsurarsa yana tuqi kuma hankalinsa kwance. Da sassauqan murmushi akan fuskarsa ya daga musu hannu,jami'ai da masu gadin dake a wajen suketa qoqarin gaidashi.

Sam yau baya buqatar komai da zai tsaidashi,aikin nan da zai karba yake ji har cikin b'argo da jininsa. Yana jin wani zaquwa da kuma son zama da abba muhammad dawud. Akwai tarin sirrika dake binne cikin zuciyarsa.......akwai abubuwa masu tarin yawa daya binne a ransa,yabarwa kansa da kansa shi daya.

Cikin personal elevator nasu ya samu ya isa office dinsa. Ya murda handle din a hankali bakinsa yana motsawa da sallamar nan data zame masa jiki a duk inda zai shiga.

Da maida qofar da sauke idanunsa saman agogon office din nasa gami da shaqar daddadar iskar dake kadawa da sassanyan turaren office din nasa duka lokaci guda ya yisu. Yanason yanayin office din.......saboda yana son qamshi. A rayuwa kyautar abu biyu a wajensa tana da matuqar muhimmanci......kyautar littafi da kuma kyautar turare.

Zai iya cewa baya jin akwai wata rana da zai rabu da zain me masa shara gami da kula masa da office dinsa,domin kuwa yasan kowanne yanayi da tsari da yafiso office din nasa ya zamana akai.

Jakarsa kadai ya ajjye,ya taka a hankali zuwa wani sashe na office din,wanda aka yiwa dan qwarya qwaryar kitchen dake dauke coffee maker cups masu wani irin nau'i da kala da zasu tabbatar maka shi din JININ SARAUTA NE daga qabilar OROMO na yankin JIMMA.

Komai nasa classy ne.......me tsari tsada da kuma nutsuwa ne. Bai zauna ba sai daya cika wata butar shayi da coffee.....wadda tafi kama da zungureren jug,ya zari cups har biyu sannan ya qarasa saman kujerarsa da yake iya juyata ya kuma sarrafata a duk yanayin da yakeso.

Ba wai zama yayi hakanan a kanta kai tsaye ba,sai daya karanta falaq nasi da qulhuwallahu hadi da ayatul kursiyyu,sannan ya qarasa a nutse ya zauna akai yana ambaton bismillah. Hakan wani sabo ne da ya yiwa kansa bisa koyarwar nanay. Duk abu da yake cikin jama'a irin wannan daya tafi ya barshi na wasu awanni ko kwanaki,muddin ya dawo sai ya ambaci sunan Allah a kansa,takance.

"Kana da tarin baiwar da ba lallai kai kan hangota ba......kana da quruciya da qananun shekaru......ka taka wani matsayi ka kuma taka wani matakin da wani yayi shekaru masu yawa yana harsashen samu......sai kayi tunanin kowa ne irin hakan zata kasance ya dauke idanu daga kanka?.......wannan matakin dakai kake rainawa......wannan matsayin da kake ganinsa ba'a bakin komai ba.......yana can wala'alla ya hana wani bacci.......yana can wataqila ya hana wani sukuni". Ko sau daya bai taba kawo wannan hasashen a ransa ba......har sai da nagartacciya uwa irin nanay ta ankarar dashi,daga wannan ranar,daga wannan lokacin kuwa bai sake yarda ko sau daya ya sauka daga abinda ta dorashi akai ba.

Wayoyinsa ya hada gaba daya ya kashe don yana son maida hankali sosai akan aikin nasa. Ya zare takalman qafarsa yabar tattausar socks din dake qafarsa ya zuba coffee dinsa ya kuma daidaita AC din dakin sannan ya kunnna system dinsa. Bai shiga ko ina ba sai daya binceta tsaf,ya kuma tabbatar da komai yana kan saiti da tsari sannan ya fara hada aikin da yakega ya kamata ya hadasu tsaf kafin barinsa addis ababa.

Kafin ya kammala aikin daya daukeshi awanni biyu cur ya shanye coffee dinsa,har yana jin buqatar qari. Shan coffee wani abune dake cikin jinin mutanen Ethiopia,musamman mutanen yankin jimma qabilar oromo. Noman coffee sukeyi da gasken gasken cikin manya manyan gonakin da idan ka gani zakasha mamaki. Ba wani cikin qabilar oromo da yake zato gari zai waye,rana ta fito ta fadi ba tare da ya kurbi coffee ko sau daya ba,walau yaro ko babba,mace ko namiji.

"Alhamdulillah" Ya furta yana relaxing bayansa jikin kujerar sannan ya lumshe idanunsa yana qarasa rufesu ruf yana jin gajiyar zamansa waje daya yadda take bin sassan jikinsa.

A hankali zuciyarsa ta nemi daukan hankalinsa a dan zaman da yayi yana son bawa zuciyarsa da kwanyar tasa hutu ta soma lulashi duniyar tunani,cikin nasara ya bude idanun nasa a hankali yana mamakin yadda ba wanda ya nemeshi a awanni biyun,duk da dama idan yana irin wannan aikin yana barin sanarwa a reception kan kada wanda ya nemeshi ko ya dameshi,idan ya kammala zai sanar,sai ya miqe yayi taku biyu yana jawo wata mini printer da yake using da ita wajen fidda bayanai da hadasu a matsayin document.

Sau uku yana gwada fidda bayanan amma taqi bashi hadin kai,sai ya fuzar da iska daga bakinsa,ya koma a nutse yana maida takalmansa qafarsa,ya dauki system din nasa sannan ya kunna wayoyinsa ya juya yana fita a office din. Yana buqatar bayanan as document,babban sirri ne da ya shafi hukumar,so bazai iya bawa wani ya hada masa kundin ba,wannan ta tilasta masa fitowa da kanshi..

Dole ya duba wani department din dake da tsaro ya samu inda zai fidda files din.

Yayi mamakin yadda shurun ma'aikatar ya yawaita,duk da yana ankare da kowanne motsi daga kowanne sashe,amma sanda yayi nisa a aikin sa sai ya turawa sashen kula da cameras ba kamfanin yace su nadad nad'ar masa kowanne motsi tsakanin mintuna da dukka awanni kowanne department zaiyi nazari akai.

"AKHANAN MUHAMMAD HAMMUD.........AKHANAN MUHAMMAD HAMMUD.. . ....the princess of agadez" Wannan jimlar ita daya yaji ta maimaituwa daga inda bututun amsa kuwwar da ake kallon da ita. Baisan dane suke kallon ba



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


PAGE 25
___________________________

https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500 dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. ⁠married femfresh wash 2k
3. ⁠garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. ⁠Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. ⁠Tsimin mallaka 2500
6. ⁠maganin infection 1500
7. ⁠matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
__________________________


"Kai........dama da gaske akwai yarinyar nan ba labari bane cikin rubuce rubucen media?" Yaji muryar salana daya daga cikin jami'ansu yana fada da wani irin sauti da excitement.

"Gashinan sun fadi sunanta.......da alama kuma fadin rai zatayi yarinyar......har yanzu taqi fitowa sai dokinta data gabatar,duk ya kashe idon kowa a wajen" Ya sake ji barrak ya fadi.

"Yadda dokinnan yayi kyau na tabbatar kyakkyawa ce itama.......na qagu na ganta wallahi" Semere ya fadi. Samere din irin mazannan ne mash idanun kalle kalle da shegen son mata,wannan dabi'ar nashi ya sanya sam kanwarsa da suhaim basa jiquwa guri daya.

Mugun shakkar suhaim din yake saboda kwarjinin da yake masa,yayin da suhaim din ba kasafai ya fiya shiga shirginsa ba.

"Kamar gata nan.......gata can daga right side tana fitowa". Muryar data bashi mamaki,muryar omari ce......ko mene ya kawo omari cikinsu?. Yasan halinsa sarai ba irin shirginnan shima yake shiga ba.......amma tunda yaji anyi batun doki akwai alaqa me qarfi tsakaninsa da wasan dukka daya shafi doki,ba kuma omari din kawai ba......dukkan 'yan team dinsu ma. Wani abune da suka wareshi ya zame musu abu na nishadi a rayuwarsu cikin wasannin nishadi na halal. Wasan tseren doki,don kuwa halastaccen wasa ne tun zamanin ma'aki,don haka suka maidashi shima wasansu da sukanyi duk qarshen wata ko sati.

Kowannensu gwani ne kuma qwararre,saidai a tarihin tafitar kaf haisam ne kawai ba'a taba cinyeshi ko fiddashi ba.

Sau tari sukan zolayeshi da cewa.

"Masu abu da abinsu ne.......kukam tun kuna jarirai aka tabbatar ana koyawa yaro komai daya shafi sarauta a masarautar jimma" Murmushin nan nasa dake cakude da wata charisma yake saki kawai. Duk wani abu da zai nuna martaba da girmansa ko ya tuna masa shi din wai wani ne daban da yasha banbam da sauran mutane bai fiya so ba,yafiso kullum su barshi ya dinga jin kansa kamar kowanne mutum......su daina tuna masa shi din dan sarauta ne.

"Itace......wallahi itace" Daidai sanda semere yake fadin haka yana kasa daidaita zamansa saman kujerar da yake kai suhaim ya murza handle ya bude qofar yana shiga da sallama a bakinsa cikin husky voice dinnan nasa daya qara wani zurfi da fidda nutsuwarsa. Idanunsa na akan inda zai lalubo Omari,ya tuhumeshi da idanunsa akan dalilinsa na zuwa ya zauna a shirmen gurinnan bayan aikin dake gabansu?,cikin sa'a sai ya samu Omari din yana can gefe yana hada wata folder,abinda ya alamta masa akwai aikin daya shigo dashi office din kenan kamar yadda shima dalili ne ya shigo dashi.

Hadiye maganarsa yayi,cikin ransa yana furta.

"Subhanallah" Tare da sake imani da yaqini ga Allah. Tabbas shi yasa ubangiji ya jaddada muhimmancin yin bincike akan komai.

Shigowar tasa ya sanya kowa a cikinsu miqewa cikin girmamawa suna kai masa gaisuwa tare da shan jinin jikinsu. Somawa motsawa kowa yayi don barin office din,don doka ne hakan a garesu,sai idan shi ya basu izinin ci gaba da zama.

Ya fahimci wannan sak din da sukayi a yanayinsu,sai kawai ya basar yana amsa gaisuwar tasu,ya kuma doshi fannin da printers dinsu ke ajiye zai soma operating,salana ya dan matso.

"Sir.......me kake buqata?"

"Kebantaccen aiki ne" Ya fada a nutse yana daga masa hannu. Ya Fahimci yaren don haka ya koma mazauninsa,ya kuma dauki remote cikin dabara ya rage sautin tv din.

Ba kasafai a guri irin wannan kowa ke nuna zurfin alaqa tsakaninsa da wani ba saboda dalilai na tsaro,kamar hakan ce tsakaninsa da omari. Girma yake bashi kaman kowa,duk da ana ganinsu sau tari da omari din fiye da kowa a cikin ma'aikatar,don haka bayan gaisuwa basuce da juna komai ba.

A tsaye yake kyam yana aikinsa,dukka hankalinsa yana kan aikin ganin kowanne page ya fita daidai. A sannan dukka hankalinsu yana kan zazzafan wasan da ake kaftawa cikin birnin Niamey dake qasar agadez,wanda gidan TV na wasanni ta qasar yake daukoshi live tana watsashi a sassan duniya gaba daya.

"Ya salam" Semere ya fadi yana rasa inda zai saka kanshi.

"Kai subhanallahi"

"An tashi kaina!"

"Da gaske sarauniyar ce......ko a gudunta ma akwai izza da mulki a ciki" Wadannan dama ire iren maganganun nan su suke tashi cikin dakin cikin sauti na can qasa saboda wanzuwar haisam din a ciki. Suna zaton baya jinsu ko bazai jisu ba,saidai wani mugun kaifin ji Allah yayi masa tamkar dan maciji. Yana ji amma yayi kamar baiji ba.......yana gani sau tari amma yayi kamar bai gani ba......saboda qoqarin koyi da fadin ma'aiki YANA DAGA CIKIN KYAWUN MUSULUNCIN MUTUM.........YABAR ABUNDA BABU RUWANSA. Musamman idan abunnan bai shafi hani ko umarni ba akan wani abu daya zaman sabawa mahalicci ne.

Ya soma gajiya da jin soki burutsunsu da maganganunsu,don haka yaja kujera ya zauna yana sauke boyayyen numfashi. Zuciyarsa yaketa kaiwa nesa,baya so yace musu komai,don ba a kowanne muhalli da kowanne guri yake magana ba,kowacce magana tana da tata gurbin da muhallin a wajensa.

"Na jima banga wasan dokin da ya burgeni irin wannan ba" Omari daya bar abinda yake ya dawo cikinsu yaja kujera ya zauna ya fadi. Duk yadda yaso wasan kada yaja hankalinsa ya gagara yin hakan,wani irin wasa ne daya dauki hankula da idanun duniya. Zazzafan wasan da aka dauki dogon lokaci ba'a ga irinsa ba,saboda wanzuwar kallabi tsakanin rawunan dake cikin wasan wato AKHANAN MUHAMMAD HAMMUD sarauniyar yankin agadez.


Futar "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da kuma

"Subhanallah" Daga bakin omari kusan lokaci daya shine abinda ya fusgi hankalin haisam da hannuwansa ke saman shafukan takardar daya fitar ba tare da ya shirya ba. Kalmomi ne masu girma da nauyi a zuciyar kowanne musulmi,ya juya a hankali yana aza idanunsa kan allon television din,karon farko kenan da yayi hakan tun shigowarsa office din.

Faffada kuma yalwataccen filin wasan dokunan ya fara yi masa maraba. Tarin ingarman dawakan da suka dauki idanunsa daketa qoqarin tserewa junansu suda mahayansu......suke kuma yunqurin kamo wani qosashen farin doki qal daya kusa isa iyakar da zata tabbatar da nasararsa.

Ba'a zaune take saman dokin ba,ta miqe ne gami da duqawa kaman me shirin ruku'un riqe da linzamin dokin da wani irin zafi da yanayin dake nuna a yunwace take da isa ga nasararta don tserewa mafarautan mazan dake bayanta. Qarfin iskar dake ketasu ce ke dage alkyabbar dake jikinta,wannan ya bawa shape dinta dama skinny jeans din jikinta daya lafe a jikinta damar bayyana ta gefe da gefe.

Da sauri ya dauke idanunsa yayi qasa dasu yana furta

"Astagfirullah......astagfirullah" Wani bacin rai ya sauko masa,sai ya miqa hannu a zafafe ya kashe printer din ya kuma kwashe takardunsa yaja wani qaqqarfan tsakin da yaja hankalinsu. Dukkaninsu suka bishi da kallo yadda yake fita a office din a zafafe,kafin ihun da semere ya saki duka ta maida hankalinsu ga tv din.

Baiyi nisa da wajen ba sautin muryoyinsu ya biyoshi har inda yake takawa don ficewa daga block din. Ihun daya tabbatar masa suna taya gwanar tasu murnar samun nasara daga dukkan alamu.

Shi kadai yasake sauke ajiyar zuciya. Sam baiga alfanu ko dalilin da zai sanya mace irin wannan wasan ba. Idan har ta fito ne daga gidan sarautar da suke girmama addini da al'ada.......hawa dokin mace me haramun bane,ba kuma abu bane me muni,saidai yana da qa'idojin daya kamata a kula dasu. Qaramin tsaki yaja a ransa yana kuma ture maganar daga ransa. A yanzun akwai abubuwa masu yawa da suka fi wannan shirmen muhimmanci da suke a gabansa,sai ya miqa hannu ya dauki wayarsa wadda ya samu miscal din nanay har guda hudu.

"Subhanallah" Ya fada yana komawa a hankali saman kujerar ya zauna yana qoqarin maida kiran. Tun safe yaso ya kirata kamar yadda ya saba......amma tashi da yayi da ayyukan yau a ransa yasa bai samu chance ba.

*DAIDAI WANNAN LOKACIN*


*_AGADEZ SULTANE MUHAMMAD HAMMUD PALACE_*


"Lokaci tamkar takobi yake,idan kai baka yankeshi ba shi zai yankeka......kamar yadda lokaci baya jira........bai kamata muma mu jirashi ba........dogon jira wani lokacin kuskure ne......ganganci ne.......kuma wasa da dama ne........a wannan zamanin......a wannan qarnin TAMIM inajin cewa nakai iyaka......haquri na kuma yazo gaba.......kwadayina da buqatata akan taskokinnan sunzo iyakar da bazan iya juresu ba" Ta fada tana sake sarqe hannayensh da goyesu guri daya a bayanta,tana kuma takawa d'ai d'ai gami da zurfafa idanunta cikin na tamim dake zube

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login