Showing 90001 words to 93000 words out of 178317 words

Chapter 31 - LU'ULU'U COMPLETE

Bata iya yin sallama ba,sai sallamar mammina data wakilci tata. Cikin muryar sultane ta tsinci muryar momma din,wadda ke zaune daura da tuntum din da sultane ya dora hannunsa dake dauke da ayabar da momma ta bare masa tana kuma yanka abarba taba ajiyewa a plate din dake tsakaninsu.

Janye idanunta momma tayi,bata fiya son kallon mammina a tare da akhnan ba,yawan kallon yana qoqarin wargaza mata duk wani kafiya da cijewarta da kuma tsarinta na shekara da shekaru da take tafiya kuma take aiki a kai.

"Sannu da aiki" Mammina ta fadi tana zama daura da momma din cikin sakakkiyar fuska me nuna kulawa da damuwa da mutum.

"Yauwa" Ta fada tana dauraye hannunta adan wani qoqo na zamani dake gefe ba tare dako ta kalli fuskar mammina ba.

Janye ido akhnan tayi daga kansu. Har abada morsa safiyya bata da wani buri illa ta wulaqanta mammina?,akan meye ne?,me mammina tayi mata haka?. Me yasa mammina ba zatayi zuciya ba?,me yasa ba zata haqura ba ta daina damuwa da dukka lamuranta ba?. Tunaninta ya tuqe sanda ta zube gaban sultane tana fadin.

"Barka da warhaka bappi.....barka da wannan lokacin"

"Yauwa barkanki" Ya fadi a yana dubanta kafin ya janye idonsa daga kanta ransa yana motsawa.

"Barka da dare" Akhnan ta fadi tana waiwayawa sashen da momma ke zaune ba tare data kalleta da idanunta ba.

Murmushi sosai ya wadata a fuskar momma din,cikin sakakkiyar murya dake nuna kulawa ta amsa.

"Barka kade biftu,ina fatan kina lafiya?"

"Alhmdulillah". Ta fadi har qasan ranta bataji ita ko kulawarta suna burgeta.

"Ya baku taho dukkaninku ba?.....kamata yayi ace dasu aisa din kukazo ai ko?" Ta qarasa maganar tana maida dubanta ga sultane.

"Ba buqata,hakanma ba laifi" Ya furta yana turawa akhnan plate din kayan marmarin.

Maganar morsa safiyya qwaya daya tak ta d'arsa wani abu saman zuciyar mammina. Nazartarta takeyi kaman yadda zargi me girma ya d'arsu a zuciyar akhnan. Taji a jikinta duk wani kira da sauran b'urbushin fushi da take gani daga fuskar sultane yana da alaqa da momma din.

Wai me yasa har abada matar ba zata daina bata ciwon kai ba?,me yasa ba zata daina zama silar bacin rayukanta ba?. A hakanne zata dauki duk wani karatu akan girma da martabarta kaman yadda mammina da sultane sukeso ta dauka?.

Abinda ya qara birkita mata tunani shine......hira da sultane ya fara yi shida momma din. Wani abu ya motsawa mammina,ta gyara zamanta cikin sakin murmushi tana jefa bakinta cikin hirar tasu.

Bata taba yarda ta zama saniyar ware a gaban sultane,bata kuma yarda da kowanne irin abu yayi mata shamaki ko katanga tsakaninta dashi ba......kamar yadda bata laminci ki na second daya hankalinsa ya juya daga kanta ba.

Cikin second biyar kacal sultane din ya jefa tambayar data saka kowacce jijiya tsinkewa daga jikin mammina da akhnan.

"Me yasa ba'a shaidamin shirya tseren dawakai guda biyu ba da aka gabatar a Niamey cikin satittika biyu da suka wuce?" Yayi tambayar yana aza idanunsa akan fuskar mammina,tambayar data fita daga bakinsa cikin wani irin calmness hankali kwance,ba alamun fushi fada ko bacin rai,amma kuma cikin qasa da second uku tambayar ta huda qirjinta ta kuma soma yaga bangarorin zuciyar akhnan da tsoro.

Maganar tazo mata da wani irin ba zata,ba zatar da bata taba hasashe ba. Cikin ranta taji wannan din shiryayyen abune......wani abu ne da aka shirya faruwarsa,don bataga ta inda maude zai fidda labarin nan ba koda dambunsa za'a yi.

Koma dai menene ita din har kullum tana juyawa ne da tsalle a tsakanin lissafinta,bata taba bari wata lamba ko gido qwaya daya ya bacewa ganinta ballantana lissafinta ya shiga rudu. A gaban sultane take,qasqanci kuwa muddin a gabansa ne tayi imanin DAUKAKA ce da kuma cimma nasara me yawan gaske,don haka ta sadda kanta,da muryar ta da tayi matuqar laushi ta fara magana.

"Tuba nake......tuba nakeyi ranka ya dade......akwai dalilai da suka......" Hannu ya daga mata.

"Ta wuce zaitun....ta wuce,amma akwai na gaba da wala'alla basuzo ba bare su wuce" Sai ya maida dubansa ga akhnan. A lokacin tana jinta ne kamar an tsomata a Kogin qanqara,sai takejin ta gwammace ko wanne hukunci ne sultane ya fadeshi,wataqila ta iya jureshi,wataqila ta samu sassucin fargabar da takeji.

"Akwai cikin masu son aurenki da zaki iya gabatarmin dashi a gobe?". Wani gigitaccen abu taji ya dira tsakiyar kanta,ta daga idanunta a birkice tana kallon sultane. Tayi zaton idan ya mata magana zata samu relief ne,ta dauka komai zai soma sassauta,amma sai taji har gwara shurunsa,har gwara baice komai ba.

Kai take girgizawa da sauri tana jin wani tashin hankali. Ko kalar wannan tambayar bata shirya amsawa ba bare ita kanta tambayar.

"Akwai?" Sultane ya sake tambayarta cikin dakewa yana dage dukka girarsa sama. Ta kasa cewa komai sai kai da take girgizawa. Zamansa ya gyara sosai yana fuskantarta,abu guda daya dake tabbatar mata magana zaiyi kenan da dukka gaskiyarsa.

"Ba damuwa bace......ni ina da wanda zan gabatar miki........a gobe ne kuma zaizo......bawai zaizo don ki gane yayi miki ko baiyi miki ba......zaizo ne don ki shaida fuskarsa,ki kuma sakashi cikin mafarkanki na shine mijin aurenki,mijin rayuwarki na dindindin,daga lokacin kina da damar yin tseren dokuna iya dukka adadin gudun da kikeso idan har shi ya lamunce miki".

Bata taba yarda zama zai iya gagarar mutum ba sai a sannan. Tana daga zaunen amma neman abinda zata dafa takeyi don ji take faduwa zatayi.

"Bappp....." Ta kasa furtawa saboda kallon daya aje mata,saita waiwaya tana duban mammina wadda takejin ita daya ce ta rage mata,itace kawai damarta ya qarshe.

Cikin rashin sa'a saita samu mammina din kanta yana a qasa ne tun sanda tayi magana ta farko,kuma har yanzun bata dago ba.

Abinda bata sani ba,maganganun sultanate akan akhnan din sune suka qara mata nauyin da takejin kamar ma bazata iya daga kan nata ba har sai an taimaka mata. Wani irin kalar tashin hankali takeji yana sakko mata yana lullube kowanne sashe na jiki da zuciyarta

Iya sautinsa,iya kuma yanayinsa kadai ya gaya mata,ko duka duniya zasu taru basu isa su sanya sultane yanjanye hukuncinsa ba a dadai wannan lokacin. Inda kuma akhnan zata fuskanci hakan data hutar da kanta,da bata bata bakinta ba gurin kiran.

"Momma......ki taimaka min". Har qasan zuciyarta takejin tausayinta yana narke mata,to amma wata soyayyar wani nuna tausayin wa yaro bashi da wani rana,bashi da wani muhimmanci face jagula komai da yake sakeyi.

"Kiyi haquri akhnan......darajarki kenan......mahaifinka bazai taba iya cutar dake ba" Ta furta tana lanqwasa muryarta da zummar ganar da akhnan din,saidai a maimakon ta gane din,sai wani matsanancin jin haushi da jin tsanar momma din ta saukar mata.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITAπŸ‘‘*

*HUGUMANKU CE*✍🏽


πŸ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*πŸ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 42
____________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*

*Assalamualaikum*

*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*

*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*πŸ‘˜πŸ₯»

*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin Aminci???*

*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*

*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana goma KACAL!✌🏽*

*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*

*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*πŸ™ŒπŸ½
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*

*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*

*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT da yardar Allah*

+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791

https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
_____________________________


β˜…Sai data tattara dukkan wani qarfin halinta da qwarin gwiwarta sannan ta iya kiran sunanta.

Daga inda take zaunen,gurin da tunda suka shigo dakin ita da mammina din bata iya motsawa daga gareshi ba. Tana jin gangar jikinta ne kaman ba'a liqe take da ruhinta ba,infact tana jin gangar jikinma gaba daya kamar ba tata ba. Abinda kawai zata iya banbancewa shine,yadda tafukan hannayenta dama na qafafunta suka dauki dumi,kaman yadda taji fuskarta tana wani irin huci ita kadai.

Tana sake maimaita da nanata zantukan sultane ne kawai.......a taqaice dai abinda sultane yake nufi shine.......yayi mata miji?.

Kaman an doka ganga tsakiyar kanta sanda lissafinta yazo a nan. Tana jin komai ne kamar almara.......a ra ta takeji wannan abun bame yiwuwa bane. Bada ita ga wani kamar kyautar kofin shayi?,bada ita ga wani mutum da batasan meye mataki ko darajarsa ba arayuwa?. Wai waye wannan ma wanda zaiyi ganganci nutsar da rayuwarsa cikin nata?,waye shi da har ya samu wannan galabar a taqaitacce lokaci?,yake nema raba soyayyar dake tsakaninta da sultane?.

Yin wasan tseren doki kadai shi zaisa sultane yanke mata wannan hukuncin da yake daidai da mutuwarta?. Ina qaunar da sultane yake mata?,ina soyayyar da yake mata gaba daya ta tafi saboda kuskure daya tak?!.

"Biftu" Mammina ta furta tana qoqarin hadiye abinda yake mata kai kawo tana zama a gaban akhnan.

Da qyar ta daga idanunta da suka sauya launi,wadannan kyawawan blue eyes din da suka jirkita zuwa launin ja,ta zubawa mammina su ba tare data iya cewa komai ba.

"Ki nutsu ki kwantar da hankalinki........sultane bazai miki auren dole ba". Wani murmushi da sam bashi da nasaba da dangantaka da halin da take ciki ta saki,ta zauna sosai daga sunkuyon da tayi tun a dazun.

"Ba sultane ba mammina......ni da kaina bazanwa kaina auren da banaso ba......bazan yi musu da sultane ba,bazan kuma bijire masa ba.......amma ina me miki rantsuwa,ko waye zaizo a goben sai ya kwashi kashinsa a hannu,zan sakashi ya banbance tsakanin aya da tsakuwa......saina sashi yaji nadamar yunqurin neman auren gimbiya khadeeja akhnan......wannan alwashina ne" Tana kaiwa nan ta miqe,duk da a zafi take amma yanayin tafiyar nan tata mai cike da qasaita bai sauya ba,ta nufi dakinta kai tsaye tana shirin maida qofar ta kulle mammina na qwala mata kira. A yau kam ko mammina batajin zata tsaya jin abinda zata ce mata.......kwanyarta ta cika da dimbin tunanin WAYESHI?. Me ya taka?,me kuma yake taqama dashi?,yasan wacece ita ko kuwa ganganci kawai zai gwadawa rayuwarsa?.

Idanun mammina akan qofar har zuwa sanda akhnan ta bacewa ganinta. Dauke dubanta tayi daga wajen,ta sauke hannuwanta ta soma takawa tana barin wajen. Ba haka take so ba.....zamanta a daki ita daya zai sanya ta qulla wani tunanin na daban da bashi ya cancanta yazo kanta ba,tana buqatar zamanta a kusa da ita......a daidai wannan lokacin bai kyautu ba bai kuma kamata ta zauna ita daya ba,sai ita kanta tana buqatar kebewa,tana buqatar ta kebe ita daya,kebewar da zata kasance daga ita sai numfashinta kadai,wataqila zatayi wani tunanin daya kamata ya kuma dace da ita.

Wani irin birkitattun tunani ne suke zuwa kanta sanda take shiga qasaitaccen bedroom din nata,ta kuma maida qofar ta kulle.

"Anya bazan makara ba?" Ta furta a hankali tana dora yatsanta saman labbanta. Takawa taci gaba dayi tamkar me tsoron taka qasa. Kai tsaye ta nufi wata qofa da yanayinta da adon jikinta yasha banbam da sauran qofofin dake maqale a dakin. Murzata tayi sannan ta turata ta shiga ciki.

saika shiga sannan zaka fahimci ma'adanar suturu ce,wadda tafi kama da katafaren shagon siyayyar kayayyaki na zamani.

A hankali take kutsawa ciki,tana ci gaba da ratsawa harta isa sassan da atamfofi ke ninke,wasu kuma a saqale jikin hanger. Hannu ta saka ta turesu gefe,ta sanya hannun nata qasan ninkakkun atamfofin ta ciro wani qaramin muqulli,sannan suma ta sake turesu gefe,take wani alamu kaman tsaga ya fito daga ainihin ginin katakon da kayan ki shirye wasu a maqale a jiki.

Muqullin takai jiki,wanda a haka ba zaka taba cewa akwai wani gurbi da za'a iya zura muqulli ba,take ya shige,tayi murxawa uku sai ga wata qaramar ma'ajiya ta fito. Hannunta ta miqa,a miqawar farko kuma ta fiddo wani file,saita maida qaramar qofar ta kulle sannan ta dawo da baya ta dawo ainihin dakin suturun.

Saman wani babban tuntum ta zauna,wanda takan zauna a yawan lokuta idan ta fito daga wanka zata shirya. Dora file din tayi saman cinyarta,ta ware wani zare da aka daureshi dashi. Koda ba'a gaya maka ba,a kallon farko idan kayi masa zaka fahimci tsohon file ne daya kwashe adadin wasu shekaru,tun daga yanayinsa da yanayin takardun ciki kawai zasu gaya maka hakan.

Ci gaba tayi da karanta takardun daya bayan daya,har zuwa sanda tazo kan wata takarda dake manne da wani hoto.

Hoton ta zubawa idanu tana kallo sosai,sannan a nutse ta maida dubanta kan adress din dake qasan hoton tana karanta rubutun.

"Anya ba yanzu bane lokaci yayi?......anya lokaci baiyi ba" Ta dinga nanatawa ita da zuciyarta kadai. Zataso ace akwai wani a gefanta.......zataso ace akwai wani a kusa da ita da zai gaya mata EH ko A'AH,wanin zai bata tabbacin lokaci yayi ko baiyi ba,saidai wannan din wani babban ajiyayyen sirri ne da idan ka dauke zuciyarta dake rayuwa a qirjinta tun daga haihuwarta har kawo yanzu.......bata tunanin akwai wata halitta ta daban da tasan dashi.

Ajiyar zuciya me nauyin gaske ta sauke,tana kuma fesar da iskar hunhunta daga bakinta.

"Lokaci yana dab da qarasowa......taku daya zuwa biyu kacal ya rage" Taji tana gayawa kanta da kanta.

"Dagin qafa gwaya daya tal tana iya zubda kowacce dama.......kubucewar dama daga hannun dan adam ba wani abu bane me wahala.......wannan din wani karatu ne data jima da haddaceshi,wani karatu ne daya zame mata babban darasin rayuwa,darasin rayuwar kuma da har yau yake kan biyashi,ba kuma zata sake kuskure ko yarda da qaddararta ta ninku sau biyu ba. Agogon cikin dakin nata ta kalla,daga rana irin ta yau tana jin ya kamata ta haramtawa kowa shiga dakin sai ita daya,koda kuwa yalwa ce. Daidai lokacin da agogo ya buga mata qarfe sha daya daidai na dare,sai ta taka a hankali zuwa saman dressing table dinta,ta sanya hannunta ta dauki wata qaramar waya da alamunta suka nuna nan ne gurin zamanta na dindindin,ta soma laluben lambobin wayar tamim.

Bugu daya tak aka daga wayar daga bangaren da tayi Kiran

"Akwai wasu abubuwan da suke buqatar gaggawa gurin sanyasu a gurabensu da kuma muhallinsu......wasu abubuwan nawar yinsu takan iya zama babbar illa da zai zama sanadin rugujewar komai......awa daya mai zuwa......ka hallara a gurbinka".

" An gama ranki ya dade" Abinda yace da ita kenan,tun kafin kuma ya ajiye wayar ita ta kasheta,ta maidata inda ta dauko ta ajiyeta,sannan ta yiwa file din hannunta kyakkyawar ajiya,ta taka zuwa bakin qofa ta murza tana fita a dakin.


β˜…β˜…β˜…Daga saman tableware din dake shimfide a qasan dakin cin abincin momma na zaune tana kallon yadda falaak ke shirya komai a wani kyakkyawan kwando,yau din da kanta da hannunta,duk da cewa dama can ita din bata dauki qananun hidimawa kai irin wannan a wani abu me girma ba.

Bata dogara da komai sai hadimanta sunyi ba,kafin suzo suyi wani abun ita tuni ta kammala abinta. Da murmushi a fuskarta ta juyo tana kallon momma.

"Ku cika alqawari.......domin shi alqawari abun tambaya ne......zanje naga yaa biftu,nakai mata gift din safe" Idanu momma ta lumshe tana jinjina kai.

"Amma kuwa zaki samu ganinta a yau dinnan?" Momma din ta fadi. Ba ita ta raini akhnan ba......bata kuma tashi a tsakanin hannuwanta ba,amma ta tashi a cikin zuciyarta. Bata kwana da akhnan ta tashi da ita ba,amma tana qididdige da dukkan halaye da kuma dabi'unta. Batajin a dukka halayenta akwai wani baqo guda daya,bata tsammanin zata kasa sansano wani dabi'a tata. Jini ba wasa bane,tayi imani yana da qarfin ikon yin abinda zato bai taba zato ba.

"Zanje koda bazan ganta ba.....ai nasan zatasan naje ganinta......amma momma" Falaak ta fadi tana gyara dankwalin abayar kanta dake shirin zamewa saboda santsi.

"Tunda tazo.....bata shigo ta gaidaki ba" Ta fada a sanyaye tana duban momma.

Murmushi ta sake sakin mata tana girgiza kai.

"Idan zakayi abu kayi domin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login