Showing 99001 words to 102000 words out of 178317 words
jin dadin karatun bane.
"Ya dai?" Morsa ta tambayeta tana zama daga gefe hadi da qoqarin gyara lullubin tattausan mayafin jikinta.
Ajiyar zuciya falaak din ta sauke tana rufe littafin.
"Gaba daya momma ji nake kaman karatun ya fita a kaina,oustaz Ousmane ya iya karatu morsa,gani nake kaman ba zamu samu wanda ya kaishi ba". Murmushi kadan momma ta saki tana daukan remote don sauya channel din dake aiki zuwa TRT africa.
"Ba'a gaggawar yanke hukunci,kuma kowanne dan adam da irin baiwarsa,sani ne bamuyi ba". Kai ta gyada a hankali falaak din,momma taci gaba da cewa.
"Ya iso tun tuni,suna masallaci da sultane,bayan sallar la'asar din zai shigo,kuma naji ma an idar da sallar.......ki yiwa baraka magana ta hada miki kansu Aafreen ku wuce gurin daukan karatun,kar a fara saba dokarsa tun a ranar farko". Numfashi falaak taja tana tabe baki. Wannan malamin me tarin doka da tsarin tsiya zataso ta ganshi,zataso ta gani ta kuma san irin ilimin da yake dashi haka da har ya zarta oustaz Ousmane yake sanya dokokin da ko shi bai taba sanya musu su haka ba.
*SULTANE*
Yadda haisam ya saba zama yayi musabaha da mutanen dake bayansa bayan kammala salla a masallacin juma'a na jimma,haka ma yanzun yayi. Abun da ya baiwa mutane da dama.mamaki aka shiga kallon kallo ganin yadda ya baiwa sultane hannu kansa tsaye. Irin wannan kwarjinin da yake musu kaman sam shi bai masa ba?.
Qasan ran sultane yake murmushi,wani irin nutsuwa na shigarsa tattare da haisam din. A cikin ayyukansa da dukka motsinsa ya fahimci yadda ilimin addini ya wadaceshi qwarai da gaske.
"Ayi masa tattaki zuwa,sannan a sake inganta gurin karatunsu idan yanayin da aka tanadarwa gurin bai masa ba" Umarnin da sultane ya bayar kenan. Cikin girmamawa haisam ya rusuna,da hausarsa da bata bada miqaqqen sauti da amo irin na cikakken bahaushe ba yace.
"Godiya nake".
Duk wani taku nasa yana tafiya ne da ilimi ankarewa da kuma karantar kowanne motsi na gidan. Kowanne taku da zaiyi yana yinsa ne cikin sanyawa abubuwa da yawa alama.......haddace yanayin abubuwa da kuma gilmawar kowanne mutum da motsin iskar dake kaiwa tana kawowa.
Kafin su isa gurin ya gama rarrabe tsarin sassannin da ainihin kebantacciyar daular da iyalin sultane ke ciki,adadin sassan ya kuma fahimci sassan matan nasa......banbancin hadimai na kowanne sashe,duk da bai gama tabbatar da hadiman sassan mammina da na momma ba.
Basu gama shiga gurin ba,amma tun daga farko yaji gurin yayi masa,tun daga farkon gurin kuma yasan gurin kebantaccen guri ne na musamman koda kuwa a cikin gidan.
Kai tsaye zaka iya kiransa da gandun daji,saboda yadda aka qawata gurin da nau'ikan shuke shuke 'yan qasar France. Akwai wata qirqirarriyar qorama me wasu fararen duwatsu da kifaye masu nau'ika daban daban dake kai.kawo a ciki. Ido ya lumshe ya shaqi iskar gurin a sirrance. Saita tuna masa da nasa sassan daya ajiye musamman a jimma,wanda yake da kwatankwacin wanna tsarin gaba dayansa.
A duk sanda yakeson duba wani babban littafi,yin research akan wata mas'ala,ko kuma yin research game da wani security issue daya shafi security intelligence yafi zama a nan,zai kammala komai a nutse yana kewaye da hadimai,don a irin wannan lokacin nanay kawai yake bawa izinin ganinsa,sai kuma mooti,wanda yawa yawan lokuta yafi zuwa ya sameshi a gurin hutawarsa dake cikin gidan,ko cikin fadarsa idan buqatar ganin ta canne.
Kanta na sunkuye tana ta qoqarin sake duba karatuttukan baya,yayin da har yanzu zuciyarta keta kai kawo,ta kuma kasa jin wani cikakken aminci da malamin.
Alamun takun da taji shi ya sakata daga kanta tana tsammanin ko su aeera ne suka tashi daga gurin da zasu dinga nasu karatun da yake gefanta kadan.
Karon farko idanunta ya sauka a kansu. Mutum uku ne......da guda biyu kawai ta sani a cikinsu. Maher daya kasance kaman dalibin oustaz Ousmane,sannan kuma jifa jifa takan ganshi tsakanin sassansu duk da batasan me yake zuwa yi ba. Na biyun bala ne......daya daga cikin manyan hadimansu,sai na ukun......
Mutum na ukun daya banbanta da kowa a cikinsu,mutum na ukun da ta ganshi ya fita daban,tamkar gold din da aka jefa tsakiyar gama garin qarafa.
Cikin nutsuwa yake maganar da bata iya jin me yake fada,amma dai ya janye rawaninsa zuwa qasar habarsa,abinda ya bawa kyawawan labbansa masu sulbi damar fitowa,suna kuma juyawa a hankali.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Ta furta da sauri da qaramin sauti tana janye idanunta gefe daya saboda wani mummunar faduwa da gabanta yayi zuciyarta na qara wani irin mahaukacin bugu da bata taba jin haka a tattare da ita ba sai yanzu.
Cikin jikinta takejin qarin kusantowarsu da gurin,yayin da bugun zuciyarta har yanzu yaqi daidaituwa,wasi wasi kuma ya cika mata zuciya tanason rarrabe waye malamin a cikinsu?.
Bala dai ta sanshi,saboda haka ba wata magana a kanshi,Maher kam bata tunanun oustaz Ousmane zai kawo Maher a mazaunin malaminsu bayan dalibi ne shi kansa a wajensa. Sai kuma na ukun?.......
Sam bai mata kama da malamin da zai shiga gidan sarauta da zummar koyarwa ba. Ta kowacce fuska kamanni dama yanayinsa. Wani irin kwantaccen kwarjini take gani yana haska kowanni motsi nasa,irin kwarjinin da a fuskar sultane kawai take ganinsa.
Eh akwai kamala me yawa da wata irin nutsuwa shimfide saman fuskarsa......yanayin shigarsa ya sake tabbatar mata da yawan ilimin daya ratsa halittarsa gaba daya,to amma......"
"Sheik haisam ya iso ranki ya dade....." Muryar bala daya tsugunna saman qafafunta ta dauko hankalinta zuwa wajen.
"SHEIK HAISAM" Ta maimaita sunan tana motsa labbanta,tana kuma jin wani irin sanyi da taushi a iya sunan kawai.
"Eh gashi can Allah ya taimakeki......sultane yace a gaya miki,a bashi dukkan girmamawar da shi zaa bashi,a yanzun sheik malaminsa ne". Kai take jinjinawa a hankali tana jin kanta kaman ya mata nauyi,bugun da zuciyarta kuma keyi yana nan bai sauya ba. Da iya saqon sultane kadai tana iya fahimtar muhimmancin da ya bawa abu
"Na barku lafiya" Bala ya fada yana tashi gami da juyawa suna barin gurin shida Maher.
Shurun da taji sai muryar Aafreen kadan take tashi ya sanyata waiwayawa kaman me ciwon wuya.
Fuskarsa shine abu na farko data soma sauke idanunta a kai. Wasu irin zagayayyun idanuwa masu girman da suka bayyana kansu tsakanin fuskarsa data zama circle cikin rawaninsa. Yana zaune sosai saman babban kilishin dake shimfide a wajen ba tare daya damu ya zauna kan kujerun da aka ajjiye masa ba a wajen masu tsananin taushi.
Aeera ce zaune a gabansa,ta bude littafinta na nuraniyya,ya dora yatsansa akai itama haka,da alama karanto masa takeyi,sai Aafreen dake zaune daga bayan aaera kadan,ta tallafe habarta da hannunta tana kallonsu fuskarta yalwace da fara'a,da alama akwai abinda yayi mata dadi.
Sake janye idanunta tayi tana kiran sunan Allah. Sai take jinta gaba daya kamar a rude take,kaman ta fita daga nutsuwarta ta dazu.
Canki canki takeyi,ita zata kai kanta?,ko kuma idan ya gama da yaran zai nemeta?.
To amma tunda suka shigo gurin bataga wani alama da zai nuna yasan da wanzuwarta a gurin ba,baiyi wani motsi ko yaya da zai alamta mata yasan tana gurin ba.
Bata da wani karsashi ko qwarin gwiwa,don haka ta zabi ci gaba da zama a gurin,ta sunkuyar da kanta kan littafin,duk da bata gane komai,bata kuma fahimtar komai,kacokam hankalinta yana wajensu da bata iya jin tasa muryar,sai muryar yaran kawai,su dinma yau cikin nutsuwa suke magana.
Jifa jifa tana satar kallo su,saidai ko sau daya ba wani alama daya nuna ansan da zamanta a wajen. Ta sauke ajiyar zuciya daidai sanda taji muryar aeera saman kanta.
"Kizo inji sheikh haisaaam". Yadda yarinyar ta furta sunan da wani irin tone sai taji sunan ya sakeyi mata dadi,ya kuma qayatar da ita dari bisa dari,qasan zuciyarta da dan mamakinsa na yadda ya aika tazo din ta tattare litattafanta ta miqe tana sake satar kallonsa. Tanason ta banbance yaushe ya kalleta har ya fahimci tana gurin ma?,saidai kuma har ta isa gurin ta tube takalmanta ta zauna a nutse bata gane komai ba.
"Wa'alaikumussalam warahmatullah" Ya furta Kansa yana saman littafin Aafreen da oustaz Ousmane yake basu aiki lokaci lokaci.
Qara tsanantuwa bugun zuciyarta yayi,har ta gaza yin qasa da kanta ta daga kanta tana dubansa kai tsaye. Abubuwa biyu suka rikitata,na farko wani baiwa dake cikin sautinsa da muryarsa da bata taba jin irinsa ba,na biyu kuma tasan yana son gaya mata batayi sallama ba.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer ๐ณ๐ช*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA๐*
*HUGUMANKU CE*โ๐ฝ
๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
PAGE 46
__________________________
HALY JASHERU VENTURES.
munada tsuntsaye na kasashen waje masu kyau da daukar hankali kmn haka.
TATTABARU
French modain(Argentina)
Indian faintail (3in1)
indigo,opal,Andalu,Lahore,busa,Bukhara, indomie,Jacobin dasauransu.
KAJI.
Brahma,silkie,silver lace,coshine,dawisu, parrot (aku)dasauransu.
,
Munada kayan Islamic center.habbatus saudah,hulba,zaitun,qusdul Hindi,minannas,Rose water dasauransu,dangin garinsu ,mansu yayansu ,ganyensu. munada original Zuma,yar chad da mombila.
Munada kayan gwanjo masu kyau daga jariri zuwa babba,
Overall,Rumpers, bodysuit, sweaters,wanduna, tracksuit dasauransu,munada kaya masu kyau na bacchi na gwanjo.
Munada Ethiopian magic hair oil ๐ช Wanda yake Kara gashi,yayi tsaho laushi,yayi Baki drct daga Ethiopian muke kaisa ko Ina afadiin duniya.
Don Neman Karin bayani number waya
07046665338.
___________________________
Ba dabi'arta bace rashin yin sallama idan ta riski guri,sosai aunt hairaan ta dabi'antar dasu da wannan dabi'ar. Su din rainon hairaan ne,hairan kuma rainon morsa safiyya ne,don haka sun samu ladabi da kuma horaswa wajen qanqan da kai me yawan gaske.
Miqewa tayi,tayi taku uku ta sake dawowa sannan tayi sallamar.
"Assalamu alaikum warahmatullah". A nutse ya daga idanunsa,yayi mata kallo daya sannan ya maida kansa yana amsa mata,kallo guda dayan daya tilasta mata sulalewa ta zauna saboda rauni da jikinta taji yayi mata. Ya danji mamaki kadan qasan ransa,bai tsammaci haka da sauri ba......amma sai ya tuna da wasu daga bayanan Maher.
Zata iya cewa bata taba ganin kyawawan idanu irin nasa ba,wasu irin idanuwa masu wani irin kwarjini a cikinsu.
"Bata litattafan da kukeyi mu gani" Ya fada yana nuna aeera. Duka ta miqawa aeera litattafan,ta kawo gabansa ta ajjiye,ya saka hannunsa a nutse ya daukesu ya soma dubawa bangon daya bayan daya.
Sanda ya kammala sai ya gyara zamansa. Tambayoyi ya fara jefa mata,a nutse yake mata tambayar,bai kuma tsaurara da yawa ba,amma duk da haka a rikice take jinta,abinda ya sanya wasu tambayoyin ta amsasu da qyar,wasu kuma ta kasa amsa su din saboda da gaske bata sansu ba.
Shuru yayi bayan ya gama tambayoyin,yana dan danna wayarsa a hankali,yana ganin kimar macen me tarin ilimi sosai......hakan kuma yana burgeshi,wannan ne ya zaba sila kuma dalilin da bai bar su rumaisa sarauta ta sakasu sun zama daban da mutane a duniyar ilimin addini ba. Ya sake qarfafa hakan akan noory ita dake tasowa yanzun. Duk da yayi qoqari......amma akwai tambayoyin da yake ganin ya kamata ta amsa su compulsory. Sam ba wadannan litattafan ya kamata ta fara dasu ba,har cikin ransa yaji ya aminta zasuyi karatu na gaske da yaran,bawai karatun da bincike ne ya shigo dashi ba. Yadan dauki sakanni kafin ya motsa labbansa.
"Wadannan litattafan za'a canzasu da wasu"
"To" Ta fada tana gyada kanta. Haka kawai tun daga gabar farko takejin wani sauyi a tattare da ita.
"Hizb nawa kike dashi a qur'ani?" Ya sake tambayarta yana ajiye wayarsa a gefe a gefe hadi da karbar aikin gwajin daya bawa Aafreen ta kuma kammala.
"Ashirin da biyar" Ta samu kanta da amsawa haka kawai tana jin nauyi. Bai sake cewa komai ba yaci gaba da duba aikin Aafreen,yana mata bayani a nutse a guraren da tayi kusakurai.
*_AKHNAN_*
Tanajin ne kaman bata da wani cikakken qwari a jikinta,tana jin kamar iska ce ke sarrafata ba qafafunta ba. Ita kanta iskar kaman tasan a yanayin da take,kamar tasan me takeji taci gaba da kadawa a hankali tana watsa sassanyan qamshin turaren jikinta zuwa kowanne sassa na gurin.
Buhaina da birra na daga bayanta suna kula da inda take dagawa da sauke qafarta. Daga bayansu kuma yalwa ce,tana biye dasu ne bisa umarnin mammina,ta turowa akhnan ita ne kawai,ita ma bata ce komai ba tunda tasan wace yalwa?,wanne matsayi take dashi a gurin mammina. Tasa a ranta mammina tayi hakanne kawai don ta sake bata tsaro kulawa da kuma damar sakewa.
A kowacce hanya da zata sadata da inda ta saba ganin baqin nata.......masu tsaro ne data tabbatar ba na masarautar agadez bane,sunfi kama da masu tsaron lafiyar 'yan siyasa ko kuma masu kudin da suka ci suka tayar da kansu.
Dukkaninsu cikin baqaqen suit suke da baqin gilashi da suka manne fuskokinsu dashi. Wasu daga cikinsu akwai bindiga rataye a qugunsu.
Ba iya gurin ba kawai,ta fahimci masarautar ma gaba daya kamar an sake qara tsaronta sosai.
Qaramin tsaki taja,ba wani abu guda daya burgeta tun daga nan. Ba jama'ar da suke debowa suzo dasu ba......har yanzu bata tunanin akwai wanda zai taba fahimtarta,akwai wanda zai iya karanta mind dinta ya fahimci komai.
Lallausan gurin ma'abocin shuke shuke da akayi linking nasa da sabuwar RAUDHA inda zai zamana gurin zaman karatun su falaak kamar yadda morsa safiyya ta bashi suna. Daga kowanne taku irin wadancan mutanen ne data gani daga hanya suna qame. Kusan dukkaninsu sama suka kalla ballantana kayi tunanin hankalinsu yana kanka.
Daga can nesa kadan take iya hangen mutumin da dukka jikinta da zatonta yake bata tabbacin shine baqon nata.
Matashin saurayi ne,fari sol dashi,me wani irin haske da yake bata tabbacin BUZU ne d'an qabilarsu,ko kuma wanda yake da alaqa ta asalin mutanen Istanbul na daular turkiyya.
Kaman ragowar mutanensa,sanye yake shima da baqaqen kayan da suka mugun shan banban da na jikin mutanensa. Saboda shi din trouser ne da shirt a jikinsa da suke bayyana irin asalin tsadar da yadin da aka samar dashi yake dashi.
A tsaye yake yadan bada baya yana amsa waya,hannunsa daya soke a aljihun wandonsa yana dan tattakawa daga hagunsa ya koma dama.
Idanunta taja ta lumshe tana jin wani baqinciki yana kamata. Ko na qiftawar idanu......koda na qaramin taqi bata ga wani dacewa ko hadi ba ko guda tsakaninta da shi ba.
Bata ma hangi wani kamala a tare dashi ba......baiyi zubi ko komanceceniya da mutanen da sukasan meye ma'anar class ba a cikin dabi'unsa da halayensa ba.
"Wow" Kalmar ta sauka a kunnenta sanda take dab da isa gurin,lokacin da bacin ranta yake sake ninkuwa a duk sanda take qara taku zuwa gabansa.
Manyan blue eyes dinta ta daga tana dubansa,wani irin kallo yake qare mata daga samanta har qasanta,fuskarsa shimfide da wadataccen murmushin dake nuna zallar maqurar burgeshi da tayi. Duk kuwa da cewa baya iya ganin komai tattare da ita banda kyakkyawar fuskarta. Baya iya ganin komai nata sai zara zara yatsun hannunta data sanya ta dafe bayan kujerar data ja tunga kusa da ita tana kasa qarasowa.
Wani irin abu ne yaji yana mamayarsa me girman gaske dangane da ita. Iya tsahon rayuwarsa,idanunsu basu taba sauka akan wata mace da yaji ta burgeshi haka