Showing 135001 words to 138000 words out of 178317 words
zama zabin nanny?.
Kai take girgizawa da sauri.....da gaske wannan yaqin yakeso ya cita......da qarfinsa ya tunkarota.......dole itama ta cire kowanne irin tsoro daga ranta,ta tunkari kowa......ta tunkari komai......ta kuma tabbatar da cewa mafarkinta burikanta.....ra'ayinta dama muradinta dukka babu guda daya daya rushe a ciki.
Hannun aisa ta saki,taja da baya a hankali tana duban aisa,sannan ta juya tana takawa da dan sassarfa.
"Akhnan!......biftu!" Aisa tayi kiranta da sauri tana daga hannunta tamkar zata kamota. Mamaki da tsoro ya cika zuciyar aisa........tana kokwanto da shakka da kuma jin d'ar d'ar din kada fa da gaske akhnan sultane zata tunkara?,kada ya zamana da gaske zata je garesa ne ta tabbatar masa hakeem ba zabinta bane.
*HAISAM*
Cikin kebantattun mintunan da suka shafe da sultane wani kima da martabarsa ya dinga ji yana daguwa a ransa. Wani girma irin na UBA yakejin yana bashi. Mutum ne da ya fifita lahirarsa akan duniyarsa.......qabarinsa da aljannarsa akan mulkinsa. Ta wanu fuskar sai yake kallon kamar motii abba jifar ne a gabansa,wasu lafuzzansa.......da wasu daga cikin kalamansa kamar dai motii. Wani sashe kuma na zuciyar haisam yana tabuwa da tausayin sultane kadan kadan sanda yake fadin.
"Zaka iyayimin alfarmar zamemin D'A,ka kalleni da idanun da kowanne d'a yake kallon ubansa........ka zama mashawarcina makusanci kamar yadda kowanne d'a yake da ubansa?". Shuru yayi yana sunkuyar da kansa qasa cikin girmamawa,kafin a hankali ya saki numfashi.
"Umarni ne daga Allah S A W cewa,haqqine a wuyan kowanne musulmi idan an nema shawara ya bayar.....zanyi dukkan iya abinda iko ya bani,zanyi kuma daidai gwargwadon ikon da bai shallake iyawata ko hankali ba" Kai sultane ya gyada a hankali,murmushin nutsuwa na bayyana a fuskarsa.
Sake gamsuwa yakeji yana yi da haisam din har a yanzun da yake zaune a gabansa. Tun daga wancan ranar daya fara sanyashi cikin idanunsa yakejin kamar ba ranar ce ranar farko daya taba saninsa ba cikin rayuwarsa.
"Allah yayi maka albarka.......ya kuma albarkaci iyayen da suka samar dakai......zanso in sansu.....zanso sanin iyayen da suka ci nasarar mallakar kadara me tsada irin wannan,diyan qwarai din da yake tamkar haske cikin duhu". Sosai maganganun sultane suka sauka saman zuciyarsa......kalamansa na buqatar sanin iyayensa sukayi kyakkyawan masauki a zuciyarsa.
Bai shiryawa wannan ba.......hasalima baizo agadez domin zama ba. Aiki ne ya kawoshi,aikin kuma da ya gama lissafinsa cikin duk wani tsare tsarensa,iya wuyarsa dadewarsa ko nauyin aikin ya cinye watanni uku.......ya bawa kansa tabbaci zaburarwa da horon da yayi yaqinin bazai wuce watanni uku ba ya zaqulo wanda yazo nema,don haka baiga muhallin da zai bar wani alama ko gurbi cikin masarauta da zasu san wayeshi ba.....a cikin aikinsa ko kuma bayan ya kammala.
"Daga yanzu......kuma daga yau kana da cikakken ikon shiga kowanne guri shiyya ko muhallin da jinina je kadai suke da wannan.....daga yau kana da matsayi cikin masarautar agadez daidai da data CIKAKKEN D'AN SULTANE MUHAMMAD HAMMUD...sannan kuma ina meyi maka tayin dawowa cikin masarauta ka rayu a cikinta,bisa kyautar gida a cikinta da zaka rayu iya adadin yadda kakeso".
Zamansa ya gyara cikin girmamawa,yana jin akwai abubuwa daya kamata ya gyarasu tun a yanzun,tafiyarsu a haka zasu iya taba aikinsa.
"Ina godiya qwarai da gaske da dukkan karramawa martabawa da kuma karamci......na karbi dukkan komai daga gareka......batun gida shima na karba,saidai dawowar da zama a cikinsa zai dan bani wahala haka lokaci guda,zanyi qoqarin daidaita abun daidai da yadda jikina da zuciyata zasu saba". Murmushi sultane ya qara saki,yana sake jin dadi,bai taba tunanin komai zaizo masa da sauqi haka ba,bai taba tunanin samun makusanci haka me debe masa damuwa a kurkusa irin haka ba.
"Kada ka damu,kayi komai a hankali yadda zai dace da ra'ayinka"
"Na gode......zan iya tafiya?".
" Zaka iya,Allah yashi albarka" Sultane ya fadi sannan ya miqe da kansa ya masa tattaki har zuwa bakin qofar dakin ganawa da baqinsa na musamman,haisam din ya taka a nutse ya fice,sultane kuma ya juya zuwa ciki yana jin yadda zuciyarsa ta cika da wani irin sanyi da nutsuwar daya jima bai samu irinta ba.
Ba kasafai nutsuwa kan bar jikinsa ba komai girman abinda ya tunkaroshi. Mafi yawan lokuta yakan sanya hankalinsa da nutsuwarsa gaba da komai da zaya faru komai girman wannan qalubalen. Sassanyar iskar hadarin farkon damina dake kadawa a kebantaccen sassan sultane muhammad ke ratsa wani sashe na jikinsa,yake sake wanke masa qofofin zuciyarsa da dukkan wata mahada ta tunaninsa da kan kaishi zuwa ga dogon nazarin da yakan shiga lokaci zuwa lokaci. Fuskar nan dake dauke da cikakkiyar kamala da nutsuwa a dinke tsaf,ba wani digon fara'a saboda tunanuka da suka cunkushe masa kai masu yawan gaske. Wasu suna hawa wasu suna sauka,yana qoqarin ture wasu yayin da yake qoqarin yiwa wasu muhallin da zasu zauna sosai kan mizanin awonsa ba tare da girgidi ko rawa ba.
๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
PAGE 64
Cikin jikinsa yakeji lokaci yayi,lokaci yayi daya kamata ya qarawa aikinsa himma.......ya qarawa aikinsa gudu,ya kuma qarawa aikinsa energy don tabbatuwar kammaluwar aikin cikin watanni ukun daya qididdige tun a farkon lissafinsa.
Kamar gilmawar kibiya ya hangi giftawar mutum,sanye da irin wadannan tufafin.....wadannan kayan daya jima yana nazarin a inda idanunsa da zuciyarsa suka taba saninsu. A ranar da yaga wannan motar.....motar da ya tabbatar daga cikinta yaji sautin yaren OROMO na fita daga cikinta,yaga kuma gilmawar mutum sanye da irin wannan tufafin.
A sanda hankalinsa ya dauko ga son iya gane wadda ke sanye da kayan,a sannan ya sake ganin wata sanye da irin tufafin,sai lissafinsa ya soma komawa baya,cikin qasa da second biyar kwanyarsa ta harba BA LAUNIN SUTURAR MACE DAYA BANE sautin ya buga cikin kansa,sai ya lumshe idonsa ya kuma zuqi numfashi,numfashin da baikai ga saukeshi ba idanunsa suka dauko masa hotonta tana dab da shi,da nisan tazarar da baikai koda taku guda a tsakaninsu ba.......kafin kuma kwanyarsa ta gama tantance masa komai.......kafin tunaninsa ya gama gaya masa abinda ya dace yayi......kafin wannan kuzarin da wannan zafin naman yayi aiki yadda ya saba yi masa ta daki faffadan qirjinsa da dukkan jikinta,wannan ya sanya ta koma da baya kaman an hankadata zata fadi.....faduwar kuma da ya tabbatar idan tayi ta munanan raunuka zata samu saboda shimfidaddun qananun duwatsun dake a wajen,tilas ya miqa hannusa da wani irin zafin nama ya riqo nata hannun,tafukan hannuwansu suka gauraya dana juna,abinda ya tsaida bugun zuciyarta na wasu daqiqu,ta kuma daga blue eyes dinta da a dazun ta zubesu kan duwatsun tana wassafa yadda suka daki bayan kanta ta maidasu kan wanda take tunanin ya dakatar da ita daga faduwa.
Tsaf idanunta suka sauka daidai cikin wadannan rusunannun idanuwan.......wadannan idanun da idan ya rusunar dasu zaka dauka irin idanun mutumin da bacci ko gajiya suka yiwa mugun kamu ne. Tun daga cikin qwayar idanunta har zuwa tafukan hannunta zuwa tafin qarqashin qafarta taji wani irin abu,wani irin yanayi......wani irin magnet me qarfin gaske gauraye da qaqqarfar faduwar gaba da taji tana barazanar tsinko zuciyarta daga qirjinta......wannan feelings din kuma ya gauraya da wani irin matsanancin tsoro cikin second guda kacal jin yadda ya zame hannunsa daga nata ya saketa ta tafi zata fadi a inda take tsoron faduwar,Allah ya taimaketa ta dafe hannunta guda daya wanda saida taji ya amsa.
Tsananin mamaki da wani irin abu da taji yana zagayawa a jininta ya hanata daga kai ta kalli wanda yayi mata wannan danyen aikin?. Wayeshi cikin masarautar agadez gaba daya?.....me yake taqama dashi?. Ya sanya hannunshi cikin nata......ya kuma saketa har ta kusa kaiwa qasa......sannan kuma a hankali taji wani calm sound yana furta.
"Astagfirullah" Fusatattun idanunta ta sake dagawa zata dubeshi,daidai sannan ta tsinci yana yarfar da hannun daya riqe mata hannu dashi,ya kuma saka daya hannun yana maida rawaninsa daya sauke kadan,yana qarasa rufe bakinsa zuwa hancinsa........take yanayin daxun ya dawo mata.
Irin wadannan idanuwan da take gani sak a mafarki ne.....wannan idanun da suka zame mata barazana......idanun mutumin mafarkinta.....mahayin dokinta,abokin tserenta,abokin gasarta,abokin adawarta.......mutumin da TAFI TSANA DUK DUNIYA......Mutumin da qiyayyar morsa safiyya a ranta ma saidai ta biyo bayan tashi.
Miqewa tayi a matuqar fusace,saidai kafin ta samu daman cewa komai har ya bada tazara daga inda take,sai wannan qamshin da har yanxu ba zata iya mantawa dashi ba.......wannan qamshin da ta taba ji a wancan ranar......a hippodrome Niamey....qamshin da taji a jikin wancan mutumin da a yanzun take sake jinsa.
Wannan qamshin da aqalla a sirrance ta sanya an kawo mata kalar turaruka daga qasashe daban daban da manyan riders na dawakai na kowacce qasa sukafi using nashi......a qalla sama da kwalba dari bakwai.......saidai ko me kama da wannan qamshin bata samu ba........ya akayi shi wannan da bata san waye ba ya samu qamshin?.
Daukuwa hankalinta yayi,ta sake shaqar iskar da kyau tana fesar da ita gami da lumshe idanunta. Ganin sultane a yanxu yana da matuqar muhimmanci......kamar yadda sanin waye wannan mutumin me tsananin tsaurin ido........karbar kalar turaren da yake amfani dashi bayan tasa an ladabtar mata dashi akan abinda ya aikata din a yanzu.
Maida dubanta tayi ga inda take tsaye.....ba guri bane na wasa,ba kuma guri bane da kowa da kowa yake da damar takowa xuwa ciki ba,don koda masu tsaron gurin suna ta wajen gurinne bata cikin gurin ba. Dukkan wanda ka gani yana kai kawo a gurin tabbas yana cikin AHALI ko jinin sultane,kusanci kuma bana wasa ba. TO WAYE?.......KO ALJANI NE?. Wani tsinkewa zuciyarta tayi,idanunsa irin idanun nan da take gani a mafarki ne,irin wadanda ta gani a hippodrome ne sak!....wasu iri idanu haduwarsu da nata a jikinta takejin ba gama garin idanu bane.....kamar su din an cirosu daga cikin wani abu na dabanne bawai daga nau'inkan idanuwan mutane data sani ba......qamshin sa.....dama abinda ya faru a yanzun,komai kamar ya maimaita kansa ne.
Wani irin sanyi qafafunta taji sunyi,tsoro taji ya shigeta,ga yanayin gurin daya soma lullumewa saboda gabatowar magariba. Me zai faru idan ya zamana aljanu sun fara wasa da hankalinta ne da tunaninta?. Tafin hannunta takai saman fuskarta da niyyar shafa don bawa kanta relief,saidai kuma wannan qamshin dai taji fes cikin hannuwan nata kamar an diga mata turaren ne a cikin su.
Da sauri ta janye hannun tana duban tsakiyar tafin hannun. Hannun dai nata ne,wannan lallausan tafin hannun da kowacce rana cikin wankeshi ake da nau'ikan mayukan wanke hannu,ta kuma shafeshi da ajiyayyen cream na musamman saboda hannun kawai,amma qamshin nasa ne......qamshinsa ne.
"Kina dab da rasa ganin sultane" Wata zuciyar ta yunquro mata da lamarin da ya sanyata takowa ganin sultane kai tsaye ba neman izini ba iso. Damqe tafin hannun nata tayi tana jin cewa wannan shine issue na gaba mafi muhimmanci a gareta. Ta tsani wanzuwar qamshin a tare da ita......amma a yanzun tana buqatarsa a hannunta zuwa awannin da zata kammala ganawa da sultane.
Tun a parlor din farko data hangi sultane din tsaye kowanne karsashi nata ya soma sulalewa. Wannan kwarjinin dake lullube da fuskarsa dama gangar jikinsa gaba daya suka soma dakushe nata kwarjinin dama jarumtarta,sai wani irin rauni ya fara sauko mata,irin raunin da d'a kanji a sanda yake neman alfarmar da ba wanda zaiyi masa shi sai iyaye,sai kuzarinta ya ragu,tayi qasa da kanta tana takowa zuwa gabansa,ta iso dab dashi sannan ta sulale saman gwiwarta tana kafe gwiwoyinta a qasa.
Wani abu qwaya daya da duk duniya sultane keda wannan girman da zatayi masa shi......wani aiki da a duniya banda mahaliccinta babu wata halitta data taba zubewa hakan a gabanta,sai ta saki siririn kukan da bata taba yarda ta yishi gaban kowa sai gaban mutum biyu SULTANE DA MAMMINA. Don koda cikin addu'a da salla batasan yadda ake kuka ba,bata zama doguwar addu'a saboda bata taba hasashen tana da wata buqata ba. Rayuwarta ta cike mata tako ina cif cif a nata idanun,bata da sauran abinda zata kuma roqa,rabbana Aatina fiddunya hasanatan wafil Aakhirati hasanatan wa qina azabannar kadai take iya maimaitawa.
Yana tsaye kawai goye da hannuwansa a qirji. Baice mata ci kanki ba,kaman yadda baice ta tafasa sauke ba. Indai akhnan ce......indai khadeejatu ce,indai kuma shine ya haifeta yasan tabbas zatazo. Ya shiryawa zuwan nata kuwa da kyau,ya kuma shiryawa ko meye zata ce,ya riga ya yanke hukuncin da ba abinda zai sanyashi maida hannun agogo baya. Lokacin aurar da AKHNAN daga masarautar agadez yana ji a jikinsa yayi,babu kuma abinda zai sauya wannan. To amma ta wani Fannin.....idan har yace kukanta baya taba ranshi......ko kuma kukanta bata mintsinin zuciyarsa yayi qarya. Kowanne iyaye akwai cikin 'ya'ya wanda Allah yake jarrabarsu dashi,shi kam ya amince da akhnan din aka jarabceshi. Baya iya dauke idanu daga dukkan wani ko wani abu da zai kusata da ita ya illatata ko ya cutar da ita.....bashi da juriya jumuri ko jarumta game da ita.....ba kuma wai haka kawai ta samu dukkan wadannan ba....Aah SAFEENA ce sila.
A duniyarsa ba wata halitta sama data safeena......ba wani mutum a jiya ko a yau shekaran jiya ko gobe da zai iya wafce matsayin safeena a rayuwarsa,har zuwa ranar da numfashinsa zaibar gangar jikinsa.
"Inda zaki sauqaqawa kanki khadeeja ki tashi hakanan,don babu abinda zai sauya wannan hukuncin......ZARTACCEN ABU NE kuma tabbatacce da ikon Allah......ban taba tunanin akwai lokaci da zaizo da zan iya zartar da haka ba a kanki......sai gashi yanayi yazo da bayanan da suke gwada hakan shine gata na qarshe da zan gwadawa rayuwarki......ki tafi ki fara shirye shirye......na baki watanni biyu kacal ki horas da kanki yadda zaki zauna da HAKEEM a mazaunin mijin aurenki na dindindin". Ya qarasa maganar yana soma barin wajen bayan ya dauki carbinsa da alkyabbarsa ya maida saman plain jallabiyyar jikinsa.
Tafi kowa sanin sultane bawai don tafi kowa doguwar rayuwa dashi ba......tafi kowa saninsa domin shi din jinin jikinta ne. Daga yadda ya nuna mata ta sake karaya da samun tabbacin hukuncin sultane na wannan karon BABU GUDU BABU JA DA BAYA!. Indai hakan ta kasance ta cika marar nasara.....tozartacciyar da zata auri namijin da yafi kowanne nau'in mazaje rauni da kuma rashin NASARA.
Namiji me ilimin arabiyya kadai?......koda yana da ilimin nasaara ba zabinta bane,hakeem da ire irensa dukka sun kasa .....namiji irin hakeem koda aisa ko shehnaz bare falaak ba zata yiwa fata ba.
Koda tana ra'ayi muradi ko burin aure......tsayayyen namiji.....jan zaki.....me budaddun idanun da suke iya hangen duniya a tafukan hannuwansa.......me iya sarrafa tunani dama abinda duniya ke ciki.....me idanu a kowanne fanni na rayuwa,gwarzo jarumin da ba abinda ke iya raunanar da zarrarsa......irin wannan ne WATAQILA......WATAQIL ta iya bashi dama cikin kaso daya cikin dari ya gwada sa'arsa.....sa'ar da idan ta tabbata wala'alla ta bashi daman ci gaba da nemanta har zuwa sanda zata iya jin cewa ita KHADEEJA MUHAMMAD HAMMUD zata iyayin aure a rayuwarta.
Sanda takai qarshen tunaninta sultane ya dade da bacewa ganinta. A hankali yakai yatsarta kan fuskarta tana taba dumin da taji yana gangaro mata. Duban yatsun ta sakeyi,hawaye ne......farare tas masu dumin da batasan sun sauko mata ba.
Kuka ba dabi'arta bace......amma akan sultane da hukuncinsa zata iyayin sama da kuka dinma.
โ
"Me yasa ka nuna masa kana iya zama a gidan nan gaba?". Omari da ya zuba masa idanu yayi tambayar ga haisam din kai tsaye.
A hankali ya bude idanuwansa,duk da cewa bai motsa ba ko kadan daga yanayin yadda yayi relaxing cikin kujerar. A nutse yake duban omari,yana kuma son hotonta ya bace bat daga idanunsa.
Muryarsa can qasa,cike da gajiyar da yake ji cikin sassan jikinsa yace.
"A wannan karon...cikin jikina nakeji akwai wani abu cikin masarautar,da akwai wani abu cikin gidan,jikina ne kawai yake bani hakan,ba don ina da tabbaci ba.....komawata bata lokaci daya bace.....komawata zata zama kadan kadan ne har izuwa wani lokaci idan komawar ta tabbata gaba daya.......naji oromian language a muhallin da naga gilmawar tufafin hadiman cikin gidan.....tabbas dole yana kasancewa akwai alaqa ko sanayya ta juna tsakanin duk mutumin da kuke yare daya dashi.... Qabila daya a sanda kuka tsinci kanku a wata baquwar qasar da ba taku ba.... Tabbas akwai wannan zumuntar" Ya qarasa maganar yana jin tabbaci har cikin ransa. Shuru omari yayi yana jinjina kai,hasashe da maganganun haisam a bisa layi suke,baisan dalili ba,amma shima a jikinsa yake jin kamar nasara ce take tunkarosu.
"Meye sunan yarinyar da ka hadani race da ita?". Haisam yayi tambayar sanda