Showing 141001 words to 144000 words out of 178317 words

Chapter 48 - LU'ULU'U COMPLETE

Ta fadi rai bace tana duban murdeden qaton da shine ya buda mata qofar dakin,bayan tayi dukkan qoqarinta don tayar da almaz din amma bai wani motsa ba.

Hannunsa yasa ya juya almaz yana kuma wancakalar dashi gefe,har sai da mammina taji abun har zuciyarta.

"Kada ka sake kwata irin wannan......kada ganinsa a haka ya sanya ka dauka wani wulaqantaccen kaya ne maras daraja......shi din daraja ce gareshi me yawan gaske". Qas yayi da kansa sannan ya furta.

" A gafarceni" Kana yadan ja baya daidai sanda almaz ke buda idanunsa da qyar wadanda sukayi masa nauyi.

A karo na biyu ya sake ganin inuwarta cikin idanunsa. A karo na biyu bayan hankalinsa ya fara kutsawa sassan jikinsa yana sake maimaita masa karatunta.....fuskarta......sunanta......alaqarsu......dangantarsu.......da kuma tarin wasu tsarika daya soma shiryawa kansa.

Tsarikan da ya jima yana gayawa kansa ba masu cika bane......tulin mafarkaine kawai masu qaryata zahiri.....kwatsam sai wani dan mitsitsin qyalli ya wulqa da sauri ya fara haska masa wata qofa.

"Ana" Ya fada da wani sauti me nauyi,wanda shi zai gaya maka zahirin nauyin dake cikin jikinsa dama hankalinsa. Idanunta ta dauke daga saman kyakkyawar fuskarsa......wannan fuskar dake tuna mata da tarin abubuwa masu yawan gaske da suka shude mata......wannan fuskar da kullum ta kalleta take tone wani birnannen abu da takejin ya kamata yayi nisan da ba zata iya koda tunawa dashi ba.......wannan fuskar dai da a haka take da wata irin kamala da nutsuwar da tasha banban da abinda ke shimfide a ruhin mamallakin fuskar.

"Ku sashi ya dawo daidai nan da minti sha biyar kacal ku fito ku sameni a parlor.......babu lokaci,kafin cikar wa'adin a nemomin tamim ya iskeni a nan yanzu" Ta furta gaba daya tana juya gami da ficewa a dakin.

Idanunsa ya maida ya lumshe kaman zai sake komawa baccin,saidai kuma wannan basamuden bai qyaleshi ba,ya kamashi yana tayar dashi. Bai musa ba ya miqe,don shima ya gaji da kwanciyar,yana buqatar wanda zai taimakeshi yace kwanciyar ta isa haka.

Zaune kawai tayi a falon,idanunta kafe guri daya,yayin da zuciyarta ke shirya mata yadda lamarin almaz zai iya zama barazana a gareta muddin komai bai hau kan saiti ba.

Mission da qudurinta akan almaz me girma ne.......wani abune da batasan yawan adadin shekaru darare da sa'o'in data laqume tana lissafin zuwansa ba.

Wani irin murmushi me bayyana tsananin qololuwar nishadin da zuciya ke ciki ne ya subuce mata,saita dauke hannuwanta tana goyesu a qirjinta tana kuma ci gaba da takawa d'ai d'ai.

Iya tuna yadda al'amarin zai kasance kadai walwala yake bata......wani irin sukuni yake saukar mata,tare da mantar da ita daya bangaren muhimmin aikin nata,duk kuwa da cewa wancan aikin zai iya zama mafi muhimmanci fiye da wannan.......saidai kuma ita din tana bawa MAIDA MARTANI da BADA SAKAMAKON ABINDA KA SHUKA da matuqar muhimmanci fiye da maida hankali ga abinda zai iya jawo mata asarar dukiya.

Daidai lokacin suke fitowa daga dakin. Almaz yana gaba yana biye da almaz din. A karo na biyu ya sake dubanta,yana tuna shekarun daya dauka bai sake sanyata a idanunsa ba,idan ba mantawa yayi ba shekaru shida kenan cif cif. Tana nan a yadda ya santa a baya,ba wani abu daya canzata,tsufa ko wani yanayi da zai nuna shekarun mutum suna tafiya sam babu ko daya a tare da ita. Idan har yana lissafi a daidai......ganinta yana samuwa a gareshi ne bayan kowacce shekara shida,a tsahon shekarun daya dauka a rayuwarsa,shekara ashirin da tara kaman yadda yaji ana fadi,sau uku tak! Ya taba ganinta,wannan shine cikon na hudun.

Gani ukunnan wani gani ne da yasha banban da dukkan wani gani da zaiwa kowanne dan adam,alaqa da kusanci da ake gaya masa wanda ke tsakaninsu har yanzu yana jinsu a wasu abubuwa da basu gama shiga damuwarsa ba......saidai a duk sanda zatazo ta tafi tana tsayewa a ransa da idanunsa da kuma tunaninsa,har xuwa sanda zata cike shekaru shidan ta sake dawowa. Dubanta yake sakeyi,yana mamakin abinda ya hanashi ganinta a shekaru shidan daya kwashe gidan prison yana zaune?......to amma kuma sai ya taqaita mamakinsa sanda ya tuna WAYE SANADIN FITARSA A YANZU DA YAKE TSAYE A NAN DIN?.

(08187255862 lu'u lu'u)

A nutse ta zauna tana dubansa gami da masa nuni da inda zai zauna din shima. Bai musa ba ya zauna da yanayin jikinsa da babu wani qarfi sam sam. Wani irin rashin qarfi da qwaya da kuma miyagun kayan shaye shaye suka dade da yin gaba da duk wani kuzari na jikinsa.

Idanu ta sake zuba masa,kaman yadda shima ita yake kalla,saidai kafin takai ga cewa komai tamim ya shigo bakinsa da sallamar neman izini.

Daga masarauta yake,kuma a wannan yammacin ya gama biyan salary din masu kula da dawakan sultane,wanda kusan duka ire iren wadannan abubuwan masu muhimmanci da suka shafi sultane a hannunsa suke. Da kayan ma'aikatan cikin gidan ya kamata ace sune a jikinsa,amma a yanzun sanye yake da wasu kaya. Wani irin yadi ne me kyau da tsada da aka yiwa dinkin 'yar shara,sai ya saka wata farar riga a ciki,sai dogon wandonta mahadin kayan,yayin da kansa ya kasance sanye da wata hula ire iren hulunan da akasan fulani na ta'ammali dasu.

Shigar shigen ta fulani ce,saidai sam shi din baya zubi ko kama dasu. Abune me wahalan gaske ka iya gare yare ko qabilan tamim,don yayi kamanni da wasu yaruka na qasar niger din,kaman yadda yayi zubi sosai da su.

Iya kallon mammina a gareshi kawai yana iya gaya masa matakin farinciki baqinciki ko tuhumarta a kanka. Don haka a yanzun yana shigowa ya ratsa a hankali ya yiwa kansa mazauni a inda yake ganin yafi dacewa dashi,wanda yana kammala zaman duk wani mahaluki dake numfashi a parlor din ya juya ya fice,mutum na qarshe kuma yaja musu qofar yana rufeta,sa'annan sukayi tsaye a nisan tazarar da aka lamunce musu suna kuma gadin koda tsuntsu daka iya nufar qofar da zummar shigewa.

"Anya zaka iya?.....anya ka shirya aikin nan almaz?" Mammina ta fadi fuskarta a hade tana dage dukka girarta guda biyun idanunta cikin na almaz din.

Duban seconds yayi mata,sannan ya janye idanunsa daga kanta yana sakin wani irin murmushi,hankalinsa kwance ya soma magana.

"Ana ko?.....Duk da iqirarin dangantakar da kike a tsakaninmu.....amma har yanxu bakisan waye almaz ba......bana tunkarar komai saina shirya masa.....bana kuma tunkarar komai saina tabbatar zan iya".

"Banga alama ba......" Ta fada tana katse hanzarinsa. Idanu ya zuba mata alamun neman qarin jawabi da idanunsa da suke a shanye koda yaushe saboda yawan buguwa.

"Kasan a yau ya kamata nazo na sameka a shirye kana karbar horo tsarikan dana baka?!" Tayi maganan a dan tsawace rai a bace tana dubansa. Still dai baice komai ba,don a rayuwarsa ya tsani tsawa ko ka gaya masa magana kai tsaye haka kome zaka bashi. Fahimtar hakan wataqila ya sanya mammina sassauta muryarta tana dubansa.

"Almaz......na baka dukkan wata masaniya,na kuma baka dukkan wani kundi......na baka shafukan rayuwarta kaf gaba daya.......tun daga quruciyarta har kawo yau.......me takeso?,me ta tsana?,me yafi burgeta?......shin me ya rage maka almaz?.....me ya rage banda nazo na sameka ka fara qoqarin zama irin wannan mutumin?.......ko kasan daga yau ya kamata komai ya fara motsawa?,daga yau ya kamata ace komai ya fara tafiya?". Shanyayyun idanunsa ya janye daga kanta,tsaki yakeso yaja saboda hayaniyar da take masa amma ya taushi kansa.

"Wannan yarinyar.......tsaurinta da tsarinta yayi yawa,banga kuma ta inda zan farauto soyayyarta harta aure ni ba".

"Dama kana tunanin kyanka iya kalamanka ko wani quality dana tabbatar baka dako daya ne zaisa ta soka ta aureka?.......a matsayinka na qasqantacce maras daraja?!.....ni zaituna ni zan sanya akhnan ta aureka ba tare data shirya hakan ba......ni zan tsara yadda zata mallaka maka zuciyarta bawai qoqarinka nakeso kayi wajen faruwar hakan ba......kawai kayi qoqarin daidaita kamalarka da hankalinka......kayi qoqarin zama BASARAKE kayi wanka da ruwan da 'ya'yan sarakuna keyi......ka siffantu da IZZA wadda ita daya ce makamin daka iya janye hankalin biftu akan d'a namiji. Izza gadonta ce......izza wani abu ne a jininta,so dole taso namiji ME IZZA ba tare da tasan da wannan abun cikin ranta ba" Takai qarshen tana nuna qirjinta.

IZZA da mammina ke maimaitawa ta sanya yaji ya kwadaitu dason ganinta. Shima a jininsa ne......mace me izza tana burgeshi.....ba mace ba koda namiji ne me izza hakan yana qawatar dashi,to amma dole ne kaman yadda ta buqata ya saisaita nutsuwarsa. Zata iya hangen finsa samun alfanun komai......to amma kuma shi yana hangen alfanun da zai samu saiya ninka nata.

"Dole kayi nisa da dukkan wani nau'in kayan maye......dole ka haqura dasu na wasu watanni......kana iya ci gaba bayan komai ya saitu ya kammala......amma yanzu kyanka da hankalinka mukafi buqata" Ta fadi da sautin dake nuna da gaske kowacce kalma ke fita a bakinta.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

*HUGUMANKU CE*โœ๐Ÿฝ


๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 67
____________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________


Idanunta ta juyar zuwa ga tamim tana maida kallonta a kansa. Bai zaci zata maida dubanta a kansa haka da wuri ba,sai yayi saurin sake sadda kansa qasa saboda nuna tsantsar biyayya.....saidai kuma,can qasan ransa da zuciyarsa wata iri nau'in wuta ce me zafi take tartsatsi.

"Nutsuwarsa tana hannunka........a duk lokacin daya sake fita daga saitinsa laifin baya wuyan kowa saikai.......zansan yadda za'a rage maka ayyuka da nauye nauye a masarauta......don ka samu cikakken lokacin tarbiyyantar dashi da al'adu da yanayin sarauta ta yadda zatabi jininsa........abu na qarshe daga yau.......daga kuma sanda zai fara fita don sajewa da mutane da shiga masarauta,sunansa ya sauya daga almaz......sunansa ya koma FARRE ABBA JALAAL sunansa dana mahaifi". Jinjina kai tamim yayi da wani irin nauyin dake gwada ya karbi dukkanin umarninta,ta miqe a hankali tana takawa.

"Zan aiko da yalwa da wasu CFA din da dukkan adadin nauyin da kuke buqata....."

"Godiya nake uwar gijiyata" Ya fadi yana tattara dukka qarfin halinsa ya miqe,daidai sanda almaz ya karkace ya koma saman lalallausar sofa din yayi kwanciyarsa yana ji a ransa duk duniya bai taba jin abu me laushi kaman gadonsa na can dakin ba da kuma wannan kujerar.


*AKHNAN*

Da qyar takai kanta daya daga cikin bedrooms dinta,ta kuma samu ta zube saman gadon da yake shimfide da wata shimfidar alfarma tana tura kanta cikin comforter din dake saman gadon tana jiran a buqaci amfani da ita.

Batasan yaya ba......bata kuma san daga ina ba,dukkan wani qwarin gwiwarta ya soma kwaranyewa. Dukkan wata jarumta tata ta soma sulalewa tana barinta da iya zallar halinta,abinda ya sanya wani irin kuka tsinke mata,a karo na farko tun bayan data mallaki hankalin kanta da kuka me nauyi irin wannna me cike da kadaici ya tsinke mata. Wani irin kadaici kawai takeji yana ratsata,tana maimaita kiran sunan mammina. Ina mammina ta tafi ta barta a irin wannan yanayin?,a irin wannan lokacin da tafi buqatarta sama da ko yaushe?,a irin wannan lokacin da komai yake shirin jagule mata?.

Ko da imagination ba zata ita hakaito hakeem a mazaunin mijinta ba......koda zata rasa soyayyar sultane ba zata iya aminta da hakeem a mazaunin mijinta ba.

Hakeem fa?,mutumin da yafi dukkan mazan da suka taba zuwa don ganawa da ita qansqanci?,mutumin da shine mafi qaranci matsayi......daukaka.....wayewa da sanin ilimin zamani dame duniya take ciki?. Ba hakeem ba......koda wanda ya fishi komai.....koda wanda zai iya cika sharudda ya kuma hada qualities din da takeso bata jin zai samu amsa cikakken sunan miji a gareta,ballantana hakeem din da ko cikin 'yan uwanta na jini ba zata lamunce masa ya samu ba.

Malamin addini fa?,me qarancin wayewa?,banda bai iya boko ba sam.....wanda baisan komai ba sai karantarwa......baisan komai ba sai wa'azi?,bazai taba iya tsaiwa a guraren data tsaya ba a duniya,cikin dubban yaruka.....cikin dubban masu jajayen kunne......cikin qwarrarrun doctors masana masu tsananin wayewa. Tana running company irin sahel couture taje ina da malamin addini?,tana zuwa taruka na duniya da qasashen da suka isa,ta tsaya gabansu tayi magana da salon harshen da yake burge kowa ya kuma girgiza kowa,ya daga darajarta......ina zataje da malamin addinin da baisan kowacce kalar wayewa ba?.

Me yasa sultane bazai fahimta ba?,me yasa bazai gane babu kima ko guda daya game da wannan tunanin nasa ba?.

Hankali kwance take takowa cikin gidan,a nutse kuma tana karantar akwai wani abu daya canza tattare da gidan. Motsi da karsashin da kowa keyi yadan ja baya kadan,abinda ya alamta mata akwai abinda ya faru tabbas da gaske kuma.

Sanda qafafunta suka taka sassanta yalwa ta hange tsaye tana jiran isowarta,wanda ganin shigowarta ya sanya yalwa matsowa cikin girmamawa.

"Allah shi baki yawan rai......ina tunanin akwai matsala yau cikin gidan nan,akwai damuwa" Yalwa tayi maganan da sautin da zai sanya ka tsammaci batasan komai ba,bata da masaniyar komai daya faru.

"Me ya faru?" Mammina ta fadi tana zame takalmanta,daya daga cikin hadimanta ta tsugunna tana kwashesu gami da ajiye mata wasu masu sauqi ta soma zura qafafunta a ciki.

"Gimbiya akhnan ce.....ta shigo dazu a birkice tana nemanki,kiran sunanki kawai takeyi". Sosai fuska da yanayin mammina ya sauya yana juyawa zuwa yanayi na razana.

"Me ya faru da ita?,me ya sameta?,me yasa ba wanda ya sanarmin?,wanne irin sakaci ne wannan da rashin sanin martaba da muhimmancinta?,hakan yana nuna kenan ko bayan babu raina babu wanda zai iya kula da ita?,ba wanda zai iya kula da damuwarta?,ina morsa safiyya?,me yasa batayi komai akai ba?" Tayi maganganun cikin fadan daya sanya kowa ya sake rissinar da kansa,suna jin tabbas su masu laifi ne,jikinsu kuma yana sake yin sanyi. Dukkaninsu sunsan cewa akhnan din wata halitta ce me matuqar muhimmanci a garesu......ita din wata halitta ce da damuwarta taba ta ko shiga rayuwarta kayi mata wani abu na ba daidai ba babban kuskure ne a tare da kai.

"Muje na ganta" Mammina ta fadi tana sauya akalar tafiyarta zuwa kebantacciyar hanyar da zata sadata da sassan akhnan.

Daga yanda taga dukka hadimanta a cure a guri daya ta tabbatar lallai abun babbane,hankalinta ya tashi hankalin kowa ma a gidan ta tabbatar sai ya tashi. Da alama ta shiga wannan yanayin nata na tsananin fushi da fusata,tasan kowa dole yaji a jikinsa,komai nata kuma zai canza. Tako ina gaisuwa suke saukewa mammina din,suna kuma sake rusunawa zuwa qasa.

"Me kukeyi a nan?,meye amfaninku da kuka barta ita daya a ciki kuka dawo nan?!" Ta jefa musu tambayar a tsawace tana dubansu.

"Allah ya huci zuciyar giwa.......ita ta buqaci hakan,dole ne cika umarnin gimbiya akhnan,mun nisanceta ne bawai don haka yake muradinmu ba" Birra ta fadi cikin tsantsar ladabi. Shuru tayi dake nuna alamun tana calming fushinta,sannan ta juya a hankali tana wucewa qofar farko da zata fara sadaka da sitting room da falukan alfarma kafin kakai ga isa ainihin shiyyar bedrooms dinta.

Dan qaramin murmushi ta sauke,duka falukan ba gilmawar kowa sai na'urori daketa aiki abinsu suna bada qara mara sauti sosai wadda bata da damuwa sam. Ta dora hannunta kan qofar dakin data gani a bankade ko.maidata ta rufe bata samu daman yi ba,ta tura da sallama,sannna ta lalubi makunnin hasken dakin ta kunna,take haske ya gauraye dakin,daidai kuma sanda ta miqe daga saman gadon sukayi ido hudu da mammina din.

Da sauri ta ture comforter din kuka yana sake narke mata,ta sauko da sassarfa ta nufo mammina tana jin duk duniya damuwarta ta yaye da ganin mammina kadai da tayi.

"Meye haka biftu?......me ya sameki?,waye ya sakaki kuka?" Dukka mammina ta hada tambayoyin ta jefa mata su tana ware hannayenta akhnan din ta shige ciki tana sakin wani kukan.

"Sultane ne mammina......sultane ne" Ta qarasa maganan da yanyin da zai gaya maka zallar sakalci da gata data samu a dukkanin rayuwarta.

"Subhanallah......sultane dai kuma?,me kikayi masa?" Ta tambaya tana dan bubbuga bayanta alamun lallashi.
(08187255862 lu'u lu'u paying)

"Don na sallami hakeem......bana sonshi mammina baiyimin ba,malamin addini ne fa mara wayewa sam sam.....yanxu kina ganin irin wannan mijin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login