Showing 105001 words to 108000 words out of 178317 words
mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 6k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba pills shaki matse masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 11k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, da maganin sanyi wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne
Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 4k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka
Karku manta promo kwana 3 ne an kare insha Allah
_____________________________
Kafin tamim ya shigo,sai ta dinga jin kamar lokacin yayi mata tsaho. Ta miqe tsaye,ta taka a hankali zuwa bakin qofar shigowa gurin tayi tsaye goye da hannayenta tana jiran qarasowarsa.
Bata cika mintuna biyu ba cikakku tamim ya bayyana a gurin,da wannan suffar tasa dake nuna qarfi da lafiyar da yake da ita. Zubewa yayi a gabanta,kwatankwacin bawa da uban gidansa,kansa a maqasqancin qasa yake magana.
"Barka da wannan lokaci,barkanki da warhaka uwar gijiyata". Sauke hannayenta tayi tana fesar da iska daga bakinta,ta kuma koma da baya ta zauna tana fadin.
"Ba lokaci bane na gaisuwa yanzu.......lokaci ne na aiki,aiki kuma tuquru,lokaci ne na cimma muradai.......banaso lokaci ya quremin,banaso ya kasance komai ya kasance cikin qurataccen lokaci......har yanxu banji kalar labarin da nakeso ba" Ta qarshe maganar cikin girma tana zama saman daya daga cikin kujerun dake zagaye da gurin,ta ware tafukan hannayensa tana miqa masa.
Murmushi ya fidda me sauti,sannan ya miqe tsaye. Babbar riga ce a jikinsa wadda aka fi sani da malum malum,wadda aka yiwa aikin hannu dake dauke da zanen tambarin gidan sarautar agadez manya manya,abinda zai gaya maka ya narkar da kansa,ya kuma maida kansa mallakin gidan sarautar halak malak.
Hannunsa ya zura daga cikin babbar rigar,wadda kafin ita akwai riga da wando har iri biyu a jikinsa. Rigar farko daga wajen cikinsa ya zura hannu ya zuge wani zip,ya cusa hannun nasa,ya kuma ciro wasu takardu a nannade,abinda ya sanya tumbinsa komawa,ya kuma rage tudun da yake dashi.
Zubewa yayi a qasa yana miqa mata takardun da dukka hannayensa guda biyu,ta saka hannunta guda daya ta karba zuciyarta na wani motsi da fatan ganin abinda takeso ta gani din,sannan ta soma warwaresu cikin dauki tana dubasu daya bayan daya.
Wani irin murmushi ne ya subuce mata,wanda kana kallon fuskarta zakasan yayi nisa da zurfin da ya taba zuciyarta sosai. Tsaf ta kammala dubasu,sannan ta daga kanta tana duban tamim.
"Na jima banga mutum me hatsarinka.......na jima kuma ina tunanin kalar sadaukarwar da zanyi maka.......saidai nan gaba kadan.......lokaci taqaitacce kawai nake jira na baka zabin abinda kake so na sadaukar maka dashi.....domin kuwa ka cancanci komai tamim" Wani irin murmushi yake yana gyada kai.
"Ina nan ina jiran wannan ranar.........ina kuma me baki tabbacin daga randa na zabi abun sadaukarwa......kuma kika sadaukarmin din......na rantse miki harga Allah daga ranar zan damqa rayuwata da numfashina dukka a hannunki" Ya fadi yana dunqule hannunsa gami da dukan qirjinsa.
Wani amintaccen murmushi ta saki. Alwashinsa kadai ya sake rura mata wutar son akai gabar da zata tambayeshi ta kuma bashi dukkan abinda takeso. Tamim nata ne zata iya cewa,tsahon shekaru masu yawa yana bauta a qarqashinta,bai kuma taba bijirewa umarninta ba. Batasan iyakar adadin umarninta da tamim ya cika ba,daga randa ya zame mata bawa zuwa yau,bata da wannan lissafin.
Batakai ga cewa komai ba muryar yalwa ta ratso gurin.
"Anyimin izinin shigowa?".
"Anyi miki" Mammina ta fadi tana nannade takardun da kyau gami da maida dubanta ga bakin qofar.
A ladabce yalwa ta qaraso,ta kuma zube gaban mammina wadda ta kafeta da ido.
"Komai ya lalace Allah shi dafa miki,komai bai tafi yadda ya kamata ba" Dubanta sosai mammina keyi,saidai izzarta ta hanata tambayar yalwa komai,tana ganin ita din ba sa'arta bace.
"Allah ya baki yawan rai.......shima tayi watsi dashi yadda ta saba......wannan karon ya samu tsaraba mafi girma da ba wanda ya taba samun irinta......tsarabar mari". Waje mammina ta fidda idanunta,cikin matsanancin mamaki. Yayin da tamim ya runtse idanunsa dukka biyun da kyau yana hasashen wani abu.
"Garin yaya haka ta faru yalwa?,kina ina?" Mammina ta sake tambayar yalwa din.
Qasa yalwa tayi da kanta,a sanyaye ta furta.
"Gefan mayafinta ya riqe ranki ya dade". Da sauri ita da tamim suka zube mata idanuwansu,shuru ya baqunci gurin,kafin mammina ta gyada kanta.
"Yayi kuskure ba qarami ba,amma kuma hakan ma yayi......ki kiramin laraba,taje ta duban halin da take ciki a sassanta,ina buqatar fara zuwa ganinta,ina buqatar fara ganinta kafin kowa,don nasa nan da awanni kadan tabbas sultane zai buqacu ganinta". Kai yalwa ta girgiza sannan ta miqe ta juya tana fita.
"Tamim" Ta kira sunansa,abinda ya sanyashi daga kansa daga sunkuyon da yayi.
"Ina buqatar wanzuwarsa a wannan duniyar tamu kaman kowanne dan adam,ina buqatar rayuwarsa tahau saiti.......kwanaki satittika ko kuma watanni kadan masu zuwa zamu samu buqatuwa da wannan wanzuwar......da wannan sabuwar rayuwar". Kai ya jinjina sannan ya miqe cikin ban girma,ba tare da ya sake cewa komai ba ya juya yana ficewa.
Guri daya ta zubawa idanu tana wani gajeran nazari,daga bisani kuma sai ta fara gyada kanta a hankali qaramin kwantaccen murmushi yana subucewa daga fuskarta.
*SHEIKH HAISAM*
Tun a cikin motar da hambal ya dawo da kansa ya daukeshi bayan tattakin da yayi daga cikin masarautar agadez din har zuwa inda yace su jirashi baice da kowa komai ba.
Tsakanin maher da hambal din suke hira kadan kadan kan yanayin garin da kuma al'adunsu. Fiye da rabin hankalin hambal din yana kan haisam,kamar yadda maher shima hankalinsa ya karkata ga haisam din. Wannan mode din ba dashi ya shiga agadez palace ba,to amma sunsan halinsa. Idan ba yaso bane fadi maka abu,bai fiya son a tambayeshi ba,wannan ya sanya suka ja bakinsu sukayi shuru.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
Mintuna kadan suka iso gidan,wanda da sauri daya daga cikin hadiman gidan ya matso ya bude masa qofar. Qafafunsa ya zuro waje yana cewa.
"Kuyi alwala,zan fito yanzu mu wuce masallaci" Ya sauke qafafunsa yana takawa a nutse zuwa cikin gidan.
Har ya isa bedroom dinsa bai hadu da kowa ba,tunda dama sassan mallakinsa ne,sai omari da suke zaune tare kowa da shiyyar dakunansa. Baiga omari ba,kuma baya cikin mode din tsaiwa tambayar inda yake,sai ya rage cloak robe din jikinsa ya ajiye,ya zare rawanin kansa a hankali ya ajiye saman dressing table,abinda ya bawa sumarsa me santsi damar bayyana wadda ke kwance saman kansa cikin wani irin tsari.
Fadawa idanunsa sukayi kan fuskarsa,fuskar da tayi wani fresh tayi tarwai saboda tsananin hutu da kuma kulawa,kawai sai ya samu kunnuwansa da dawo masa da sautin marin kamar a sannan aka yishi.
Almond eyes dinsa ya bude sosai cikin madubin,yana son ya gano wannan sautin dama shine abinda yayi masa tsaye a rai tun dazu?,ashe shine abinda ya dunqule masa a wuya yaqi kuma wucewa?. Ta yaya d'iya mace zata daga hannu ta mari namiji?,namiji ma baligi Aaqili?. Imagine ace noory ko rumaisa ne zasu aikatawa wani haka?,waninma da yazo ganinsu da shirin auren sunnah.
Wani mahaukacin tsaki yaja kamar zai tsinke harshensa. Ta yaya ma hakan zata faru a masarautar oromo?. Ta yaya suma zasu fara aikata hakan?. Ya tabbatar daga shi har nanay sun musu wani irin horo da babu yarinyar da zata iya soma kwatanta hakan,sai yaja da baya yana jin yadda ranshi ke motsawa,irin abinda a dazun baijishi ba sai yanzu,ya fara tattare hannun jubah dinsa yana tafiya a nutse zuwa toilet.
Alwalar daya daura ne kawai ta bashi relief,dama kuma yana cikin dabi'unsa,duk yadda yakejin fushi cikin ransa muddin zaiyi alwala to zai samu sassauci cikin ransa( a duk sanda kike jin fushi kije kiyi alwala,in sha Allah zakiji sanyin ruwan yana ratsa har zuciyarki).
Suna takawa zuwa masallacin dake layin,wanda qananun taku ne kawai zai sadaka dashi zuciyarsa na sake yi masa tariyar yadda al'amarin ya wakana. A lokacin ya gayawa kansa ne ba wannan ne ya kawoshi cikin masarautar ba.......ko meye zasuyi daidai da tsarinsu ne da rayuwarsu,aiki ya shigo yi,shi ya dameshi,kuma shi ya kamata ace ya kula dashi,amma baida jib'i da komai na rayuwarsu,sai gashi a yanzun yana jin kamar ba haka ba,abun yana neman tsaye masa a rai.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer ๐ณ๐ช*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA๐*
*HUGUMANKU CE*โ๐ฝ
๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
PAGE 49
___________________________
*_INA MASU BUQATAR QAWATA GIDAJENSU DA KALAR TSUNTSAYE DON ADO DA DEBE KEWA?_*
*_INA MASU BUQATAR FARA SANA'AR SAIDA TSINTSAYE.....SANA'A ME TARIN RIBA DA ALBARKA DA KUMA SIRRI A CIKINTA?_*
*HALY JASHERU VENTURES.*
munada tsuntsaye na kasashen waje masu kyau da daukar hankali kmn haka.
TATTABARU
French modain(Argentina)
Indian faintail (3in1)
indigo,opal,Andalu,Lahore,busa,Bukhara, indomie,Jacobin dasauransu.
KAJI.
Brahma,silkie,silver lace,coshine,dawisu, parrot (aku)dasauransu.
,
Munada kayan Islamic center.habbatus saudah,hulba,zaitun,qusdul Hindi,minannas,Rose water dasauransu,dangin garinsu ,mansu yayansu ,ganyensu. munada original Zuma,yar chad da mombila.
Munada kayan gwanjo masu kyau daga jariri zuwa babba,
Overall,Rumpers, bodysuit, sweaters,wanduna, tracksuit dasauransu,munada kaya masu kyau na bacchi na gwanjo.
Munada Ethiopian magic hair oil ๐ช Wanda yake Kara gashi,yayi tsaho laushi,yayi Baki drct daga Ethiopian muke kaisa ko Ina afadiin duniya.
Don Neman Karin bayani number waya
07046665338.
____________________________
*AKHNAN*
Ko kafin takai ga idar da sallar taji an mata knocking ya kusa sau biyar. Tana sallan amman ranta yana baci. Ba wanda take buqata yanxu haka a kusa da ita,ba wanda take buqatar tayi magana dashi,kebewa kawai take so,sai kuma jiran kiran sultane. Kiran da inda tana da dama tabbas da zata tsere masa ne,amma kuma tasan bata da damar hakan,hakan kuma bame yiwuwa bane. Dole ne ta amsa tambayoyin sultane,dole ta tsaya ta fuskanci sultane muddin tana neman 'yancinta,dole ta masa bayani ta yakice kowanne irin tsoro dake a ranta.
A hankali ya fado mata a rai sanda take zauke daidai saman daddumar,tafukan hannayenta akan saman fuskarta. Wancan lokacin da kalmar.
"Subhanallah" Ta fita a bakinsa,sanda take dab da shan qasa daga saman thunder dinta. Har yanxu wannan sautin yaqi barin kunnenta,har yanzu wannan sautin ya sha tashinta daga baccinta a darare masu yawa. Tasha sake ganin wannan abun daya faru yana sake maimaituwa a cikin baccinta.
Qamshinsa da har yanzu bata sake jin makamancinsa ba,har kwanan gobe tana iya hakaitoshi,saidai kuma da tarin wata irin matsananciyar tsana da kuma jin haushi.
Inda tana da hali,tana kuma da dama lallai da sai ta laluboshi a dukka inda yake a fadin duniya. Tana da wannan qudurin,amma kiran sultane da maganar da sukayi a jiya kawai ta warware duk wani karsashi da take dashi.
A yau kawai tsanarsa ta ninka a zuciyarta ninkin baninkin. Shine silar duka wani hukunci da sultane ya dauka a kanta. Shine sila,ta tabbatar wannan video clip din ya gani........ya kuma zame mata dalilin wannan horon da sultane yake shirin yi mata.
Ta sake yadda abun shiryayye ne,dama ya shirya ne kawai don yaci mutuncinta ya kuma ci zarafinta. Tunda ga shaida da alamu dukka ta gani,ta tura musu request tana son a sake shirya wasan,amma sun maido mata amsar wannan dan wasan isn't available.......amma idan tana da sha'awar sake yin wasa,akwai tarin 'yan wasa available da zata iya karawa dasu.
Bata da buqatar ko daya a cikinsu,tana buqatar karawa da shine don cire masa dukkan wani abu da yakeji a kanta......don cire masa tunaninsa na yayi nasara akan akhnan muhammad hammud..........da wannan tunanin ta wayi gari,saidai a yanzu sultane na shirin dakushe wannan shirin,ya kuma maida akalar tunaninta kan wani abu na daban.
A karo na uku da aka buga qofar saita miqe a fusace ta isa qofan da kanta maimakon tayi amfani da remote ta bude. Cikin ranta tana me cin alwashin ko waye saita wanke masa fuska da zafafan mari tukunna,ko waye.....koda falaak ce,saidai kuma tana bude qofar sai taci karo da fuskar da tafi qarfin mari a gurinta.
Mammina ce a tsaye yana fuskantar qofar dakin. Dukka wani yanayi na alhini rashin jin dadi da kuma damuwa gashinan kwance saman fuskarta. Jiki a sanyaye ta saki qofar tana komawa ciki,mammina ta biyo bayanta.
"Don meye zaki kulle kanki akhnan?,bakya tsoron lafiyarki?,ko bakya tsoron wani abun ya sameki?" Ta fada tana riqo dukka hannayenta cikin tsantsar kulawa.
Blue eyes dinta da suka rusuna ta waiwayo yana zubewa mammina su,tana ji a ranta har tsakiyar zuciyarta.......bata da wani sauran gata daya rage mata a duniya bisa dukkan alamu idan ba mammina din ba......sultane ne taqamarta na farko,to amma kuma alamu sun nuna kamar sultane din ya fara yi mata nisa,ya fara nisa da muradinta. Ba zatace ga a abinda yake faruwa ba kai tsaye,amma tana da yaqinin zai wahala idan ba MORSA bace ke shirin rusa wannan kyakkyawar alaqar ba.
Duk wasu halaye da sultane ke gwada mata a yanzun baqi ne a tare da ita,tunda ta mallaki hankalin kanta bata taba ganinsa da wadannan dabi'un ba.
Ci gaba tayi da kallon mammina kawai,abinda ya bawa mammina damar karantar abinda yake kai kawo a zuciyarta.
"Tsoron me kike biftu?,kin manta alqawari na?......kina zaton idan sultane zai iya manta alqawarin dake tsakaninku ni zaituna zan iya mantawa?......duk runtsi duk tsanani ina tare dake akhnan" Sosai maganganun mammina suka karya mata zuciya. Bataso tayi kuka,don batajin ya kamata zuwa yanzu ta fara samun rauni har haka a zuciyarta,amma kuma tana buqatar kafadar da zata jingina da ita don samun sassaucin abinda takeji,don haka ta qara taku biyu,ta aza kanta saman kafadar mammina din.
Hannunta ta dora saman sassalkar sumar akhnan dake da tsaho santsi da kuma sheqin baqi tana shafawa a hankali,kaman yadda uwa keyi ga qaramin yaronta da sigar lallashi.
"Indai ina raye ba wanda zan bari ya aurar dake ga mijin da baki aminta dashi ba......ko baki fada ba yalwa ta gayamin.......sultane mahaifinki ne......indai ba zugashi akayi ba,bazai taba aurar dake ga mijin da baiyi miki ba......" Saita daga kan akhnan daga kafadarta tana riqe hannayenta dukka biyun.
"Ki sa a ranki da mahaifinki kike magana.......ki bude bakinki ki gaya masa bai miki ba!". Ta qarasa maganar da wani sauti dake nuna akwai wani abu daban daya taba zuciyarta.
Shuru akhnan tayi tana duban tsakiyar qwayar idanunta,irin duban da a yawan lokuta da dama yake qarfafa mata gwiwa tun daga yarintarta. Kallon idanun mammina din na bata wani irin qwarin zuciya tare da bata qarfin gwiwar aikata abinda take ganin bame yuwuwa bane ko ba zata iya ba.
"Shirya muje.....ya aiko a kiraki,ni zan tsaya miki koda hakan yana nufin yin baqin jini,baqin jini a idanun sultane.......baqin jini a idanun morsa safiyyah".
Zame hannunta tayi daga na mammina,iya Kiran sunan morsa safiyyah kadai ya sake harzuqa zuciyarta,sai ta juya da baya da sauri,ta kai hannunta kawai kan dogayen rigunan dake zube saman gadonta,wadanda dukkaninsu sabbi ne,birra ta soma gyarasu zata zuba mata a closet dinta tace ta barsu ta fice ta bata guri.
Duk yadda take jin zuciyarta ta tsayu amma sai fargaba ta fara ratsata sanda suke nufar sassan sultane din. Tsinkewa kawai takeji zuciyarta tanayi zuwa pieces a cikin qirjinta.
Ta fahimci hakan mammina.......saita damqe hannunta da suke cikin nata tana magana qasa qasa.
"Karkiji tsoro......ina tare dake"