Showing 93001 words to 96000 words out of 178317 words

Chapter 32 - LU'ULU'U COMPLETE

Allah....domin shine taka ribar a duniya da lahira.......banaso ki fiya zurfafa bincike,banaso kuma ki fiya zurfafa bin qwaqwaqwafi akan alaqa da dangantakar dake tsakanina da biftu......tsakaninki da ita daban,tsakanina da ita daban" Shuru tayi maganganun momma suna neman gurbi da muhallin sauka cikin zuciyarta,saita jinjina kai,ta sanya hannu ta dauki kwandon tana yiwa momma sallama.

Duk wanda ya tareta cikin hadiman da zummar karbar kwandon a hannunta saita dakatar dashi. A haka har ta cimma sassan mammina din,bakinta dauke da sallama.

Cak mammina ta dakata daga kai chips din bakinta,ta sauke spoon din tana duban falaak dake takowa ainihin falon daya zama kebantacce. Ba kowa bane yake da ikon shigowa wannan shiyyar ba sai wanda mammina din ta amincewa,yarinyar ta shigo ba tare da an sanar da ita shigowarta ba.

"Tana jin cewa jinin sultane ce ita......ta cancanci shiga dukkan wasu iyakoki da sauran mutanen gidan basukai su shiga ba". Wannan batun ya saukar da murmushi saman fuskar mammina,ta haqura da cin chips din,ta soma marabtar falaak din da fadin.

"Yar uwa tazo ganin 'yar uwarta,yau ma dai kaman jiya,bansan me tasa a cikinta ba,har na gaji da magana tacemin ta qoshi,ban sani ba ko zuwanki zai sanya taci wani abu" Mammina ta fadi tana yiwa hadimarta dake tsaye a gurin magana taje ta kira akhnan.

Mintuna a qalla uku barira ta dawo,kanta a qasa take shaida mata.

"Nayita taba qofar amma ko magana batayi ba bare ta tambayi ba'asin bugawan".
(08187255862 lu'u lu'u paying)

" Koma ki sake taba qofar kice tazo injini" Mammina ta fadi tana duban barira. A tsorace barira ta sauka tana komawa,dukka ba'a son ranta ba,tayi ne kawai don cika umarnin uwar gijiyarta,don bata da tabbacin meye zai faru idan har taci gaba da buga qofar akhnan din.

"Idan kikayi kuskuren sake zuwa kika bugamin qofa......ki tabbatar zaki hadu da fushina" Iya abinda tace da ita kenan ba tare data damu da sanin waye yake buga qofar ba.

Idanunta ta janye tana jan wani dogon tsaki kamar ta tsinke harshenta,saita maida kanta kanta saman pillow din ta kwantar,taja wayarta taci gaba da buga game dinta,tana kuma ci gaba da irgen awannin zuwan ME GANGANCI HADE DA KUSKURE sunan data sakawa baqon da bata damu tasan koda sunanshi ba.

Kai a qasa barira ke maimaitawa mammina abinda akhnan ta fadi,ta kuma qarashe da fadin

"Ki gafarceni". Kai mammina ta gyada a hankali tana fesar da iska. Mamaki ya kama falaak......sai ta miqe kawai,mammina ta bita da kallo.

" Kiyi haquri da halayyar 'yar uwarki,kada kice zakiyi fushi,tana da kafiya da taurin kai......dabi'unta sunsha banban da wadanda kika saba gani". Murmushi falaak ta saki tana rolling mayafin abayarta a kanta. Ita sam bataga ma dalilin da zai sanya sai anyi mata iso gurin akhnan nan. 'Yar uwarta ce fa?,jininta kuma.

"Ba dalilin da zanyi fushi da ita mammina.....ko yaya take......ko me tayi hakanan nake qaunarta,jinina ce,bani da kamarta ballantana sama da ita" A nazarce mammina ke kallon falaak sosai tana kuma sakin murmushi.

"Dauka mata kwandon barira" Ta furta tana duban falaak din still.

Kai ta girgiza tana sunkuya ta dauka.

"Zan iya mammina.....saina fito,na gode qwarai da karamci" Ta qarasa maganar tana nufar hanyar da zata sadata da dakunan.

Da kallo mammina tabi bayan falaak din. Tana iya tuna yaushe aka haifi falaak,a nata idanun kamar yau ne......amma gashi a yau din ta zama mutum,tama zama cikakkiyar budurwar da zaka dauka tafi qarfin shekarunta goma sha bakwai,saboda yanayin cima da gata da kuma kulawa,uwa uba kuma nutsuwarta saita sanya kaman tafi qarfin shekarunta. Anya kuwa iya wannan abun data gindaya ya isa?,ya isa kuwa?.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽


💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


PAGE 43
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________



"Falaak ce ke neman izininki......wannan falaak din guda daya da jininku ya kasance iri daya sak da sak" Lafuzzan falaak din da suka shiga kunnenta kenan sanda ranta ke kaiwa qololuwar baci jin an sake buga mata qofa,bayan dukka gargadi da jan kunnen da tayi,sai kawai ta danna remote din dake gefanta,hakan ya bawa qofar damar bude kanta da kanta ba tare data tashi ba,wannan ya bawa falaak daman tura qofar dakin ta saka kanta ciki.


*BAYAN AWA UKU*


Idanunta da dukka nazarinta yana kan akhnan sanda take shigowa dakin. A tausashe tayi mata sallama,abinda ya sanya akhnan din daga kai daga kan system dinta tana duban mammina din.

Duban second uku tayi mata,sannan ta motsa labbanta tana amsa mata gami da janye qafafunta da kuma kallonta daga kan mammina din.

List din sunayen ma'aikatan da aka dakatar daga sahel couture take dubawa,neesha ce ta tura mata tana neman samun tabbaci daga gareta. Batasan sanda akayi korar ba,batasan kuma dalilin korar ba. Dukkanin mutanen a iya saninta ba wanda aka taba kamawa da wani laifi na cin amana ko zamba cikin aminci,hasalima suna aiki dasu ne tun kafin kamfanin ya koma hannunta kuma mallakinta. Wasu daga cikinsu ma su suka tallafi rauninta zuwa sanda tayi tsaiwar daya kamata ace tayi din.

Sauke idanu mammina tayi akan kwandon da falaak ta shigo dashi a wannin baya. Yana na a gurin,ga kuma kayan ciki da aka fito dasu da alama anci wasu abubuwan a ciki.

"Wasa wasa nima tawaye akeson yimin kenan?" Ta kasa jurewa ta fada tana zama gefan akhnan,saidai kuma fuskarta tana qunshe ne da murmushi. Idanu akhnan din kawai ta zuba mata,abinda ya alamtawa mammina bata fahimta ba,neman qarin bayani takeyi.

"Eh mana......falaak na neman qwacemin ke cikin kwana biyun nan,nawa abincin ya zama hoto" Qoqari tayi tadan sassauta fuskarta,saita dauke hannunta daga saman system din tana gyara zamanta,abunda ya danja hankalin mammina kenan

"Mammina.......akwai wani abu da akayi ne game da sahel couture?" Kai mammina ta jinjina a hankali,idanunta cikin na akhnan

"Akwai......kuma ban gaya miki bane saboda yanayin da kike ciki,jira nake ki samu nutsuwa tukunna sai mu zauna nayi miki bayani" Shuru kadan akhnan din tayi,tana jin abun wani daban a ranta,saboda wannan din shine canje canje na farko da aka fara yi cikin kamfanin,tunda ta karbi ragamar tafi dashi shekara kusan hudu kenan.

Ba wani abu data gani wanda zai sanya ayi buqatar canza komai,to amma batasan me mammina din ta hango ba. Idonta ta mayar ga fuskar mammina din,sannna ta gyada kanta a hankali.

"Ki tashi buhaina zata shigo ta shiryaki" Mammina ta fadi tana duban fuskarta. Jim tayi tana duban mammina din,da tarin mamaki kan fuskarta,saita jinjina mata kai.

"Eh,lokaci yana qara tafiya idan da kin duba agogo.......gwara ta shigo da wuri ku kammala da wuri" Sake zubawa mammina ido tayi,takaici yana kamata. Wannan mutumin wannan baqon da batasan wayeshi ba......batasan meye capacity dinsa ba shine zaa tsaya shiryata a kanshi?.

Ta gaji da wannan walagigin da akeyi da ita na babu gaira ba dalili. Na meye zata dinga bata lokutanta masu muhimmanci saboda zuwan wani gareta?.

Dauke idonta tayi daga kan mammina din,tana jin bata aminta ba,bata kuma gamsu ba,hakanan bataga dalilin da zai sanya a bata mata lokaci saboda wani ba,saita fara kashe system dinta.

"Akhnan" Mammina ta kira sunanta da wani yanayi,ta kuma kira sunanta da sunan da ba kasafai ta fiya kiranta dashi ba.

Manyan lumsassun blue eyes dinta ta daga tana duban mammina din.

"Ba don shi ba.....
Saboda ke,saboda darajarki,saboda martabar da kike da ita. Kinfi qarfin kowanne namiji ya kalleki ba tare da ado na qasaita a tare dake ba,ba abinda ke qarawa mace kwarjini irin ado......adonma da sarauta ta bata ta kuma baki kema.......ba donshi bane akhnan " Shuru tayi tana juya maganar mammina a ranta.

Kamar yadda ta tsani FADUWA haka ta tsani aga kasawarta......kamar yadda take ji da duk wasu martabobi da darajoji nata hakanan take fatan riqe wannan martabar tata,kawai saita maida idanunta qasa,bata sake cewa da mammina komai ba,kaman yadda bata sake musa mata ba,abinda ya bawa mammina tabbacin ta sauko daga dokin naqin da tahau.

"Bana buqatar wani shiri me nauyi,shigar dana saba irin ta yau da kullum kawai" Ta fadi a nutse da wani irin izza,daidai sanda mammina ke hanyar fita a dakin.

Murmushi mammina tadan saki tana kada kai.

"Koma dai meye.....kawai ki girmama ra'ayin mahaifinki". Tace da ita sannan ta juya tana fita a nutse.

Sai da mammina ta fita din sannan ta daga kanta anutse tana duban hanyar da tabi din. Fashin baqi takeson ta yiwa lafuzzan mammina,ta girmama maganar sultane?.....kodai mammina na shirin goyon bayan ra'ayin sultane da morsa safiyya ne?,matar da dukka zatonta yake gaya mata da dukka shirinta da kuma masaniyarta aka qulla mata komai.

Janye idanun nata tayi sannan ta miqe a nutse,har cikin ranta batajin akwai wani dalili da zai sanyata ta janye ra'ayinta ko ta amshi wani d'a namiji a yanzun cikin rayuwarta,koda akwai yiwuwar hakan saidai nan gaba. A yanzun bata shirya rayuwa qarqashin umarnin kowa ba......bata shirya rayuwa qarqashin tilastawa da zabukan da suka kasance na wani ba,abinda ta sani shine 'YANCINTA.....DUNIYARTA.......KUMA RAYUWARTA.


★★Tun daga saman fuskarsa zuwa shigarsa kadai zaka iya hangen tarin wani irin ajiyayyen kwarjini. Wani irin kwarjini na musamman dake cakude da kwarjinin jinin sarauta dake zagaya masa da kuma tarin haske da nutsuwar da ilimin addini yake shimfidawa saman fuskar mamallakinsa.

Sanye yake da wata cloak robe da aka saqata da wani irin tattausan yadi me dan sheqi sheqi......sheqin da zai gaya maka tun daga auduga zare da kuma saqar da akayi mata me tsananin daraja ce. Riga ce da yawancin manyan malamai na larabawa......manyan malamai na harami sukan sanyata,irin rigar da kake hangota me zubin abayar mata daga jikkunan attajiran larabawa.

Fara ce,saidai ba fari qal baa,wadda aka yiwa aiki da gold din zare daga gabanta zuwa hannuwanta. Jubah ce a ciki wadda da yawa mukafi kira da jallabiyyar maza,saidai wannan din ta musamman ce da tasha banban da irin jallabiyyar da sukafi yawa a gurarenmu,don wani irin qawataccen dinki akayi mata. Iya wuyan rigar da hannun kawai ka kalla zakasan tasha banban da sauran jallabiyyu,hannun da lafiyayyen agogon rolex daya daura masa ya sake zama wani ado na daban gareshi,ya kuma dace da zoben azurfa me sheqi qwaya daya dake tsakiyar yatsarsa. Rawani ne me kyau daya zauna saman kansa,ya kuma fitar da anihin sassanyan kyan nan nasa,ya zauna a kansa,banda jelar rawanin data sauka kafadar hagunsa zaka dauka wata sabuwar plain cap ce da tazo tare da cloak robe din jikinsa.

Wani half shoe ne a qafarsa daya kwanta ya kuma dace da yanayin shigar tasa na asalin fata qirar kamfanin qasar Italian.

Su uku ne tare dashi,abdii yana a gefan damansa,hamdi yana daga hannun hagunsa,sai Maher daya kasance sanannen dan gari.

Tun daga nesa kadan motarsa qirar Mercedes AMG g63,wanda zuwansa agadez ya siyeta da tarin daloli masu yawa.

Salawi ne yayi driving nasu,saidai kusan tazarar taku d'ari ya tsaida salawi din.

"Ka koma gidan,idan na kammala mu sake haduwa a nan ka maidani gida". Ya furta yana sanya hannunsa saman murfin motor zai bude,saidai kafin yakai ga budewar har hambal ya zagaya ya bude masa cikin matuqar girmamawa ya kuma ja baya yana jiran fitowarsa. Sanda yake fitowa beeno ya soma gyara masa zaman cloak robe dinsa,ya daga kai a nutse ya sauke masa wani kallo daya saka hantar cikin beeno din kadawa. Baya yaja yana sadda kanshi,ya mace da irin nasa tsarin,sam sam irin wadannan al'adun basu sha mishi kai ba,hasalima ba sonsu yake ba,to amma shi din amanarsu ne,da kuma umarnin mooti suke aiki,dole ne su bashi dukkan wata kulawa data kamata,su kula da dukka motsinsa da lafiyarsa koda ba kai tsaye ba don sauke amanar adalin sarkinsu mooti abba jifar.

"Of eeggannoo godhaa....hin irra deebi'iin(ka kula....kada ka sake maimata hakan)" Ya furta da yaren oromo yana dauke brown eyes dinsa da hasken rana ya sake maidasu wani launi me fusgar hankali.

"Am dhiifama...Dhiifama naaf godhaa(kayi haquri,ka gafarceni)" Ya furta yana ja baya.

Abdii ke binsa da kallon mamaki,yanason magana amma kuma yadda sukayi da beeno ya sanyashi sawa bakinsa sakata. Wacce rayuwa *PRINSII SHEIK MUHAMMAD HAISAM ABBA JIFAR* ke shirin yi a agadez?. Rayuwa ce irin ta kowanne mutum me matsayi daidai dana dan uwansa......ya manta waye shi wai a qasar jimma da Ethiopia gaba daya?.

Har yanzu da suke dab da SULTANE PALACE yana jin wani fargaba. Kada dai yaje yace zaiyi rayuwa irin ta qasqantattun mutane?. Idan hakan ya kasance anya zai iya jurar gani kuwa?,zai iya cin amanar nanay da sultane ba tare da ya gaya musu ba?.

"Ku koma......zamu shiga ne da iya Maher" Ya bada umarnin na kai tsaye,wanda a take dukkansu sukaja baya,banda abdii da yayi tsaye cak a wajen.

"Maaloo....(please)......." Abdii ya fadi yana duban bayan haisam da sukaci gaba da takawa shi da maher zuwa babban katafaren qofar gidan.

"Andii!" Yadan kira sunanshi a kausashe ba tare daya waiwayoshi ba.

Duk yadda abdii keson ya bisa bazai bar shi ya soma taka gidan yanzu ba,zai iya wargaza komai,don ba lallai yaga an masa ba ya iya dauke kanshi kaman ba kowa ba. Koda zai fara shiga da abdii ba yanzu ba,sai yayi masa kyakkyawan training da bazai sauka daga qa'ida ba.

Daya bayan daya suke wuce sassanni da shinge shinge na gidan,har zuwa sanda suka fara shiga hurumin jinin masarautar kadai da na kusa dasu da kuma wadanda aka yarjewa.

Babbar qofa ta qarshe daya daga cikin hadiman morsa safiyya ya qaraso,a bayanshi mutum uku ne da duka marabci haisam din.

"Zamu fara yin sallah tukunna" Ya amsa musu yana duban agogon hannunsa.

"Babu laifi.....me martaba yana buqatar ganawa dakai dama kafin soma zaman karatun.....shi dinma yana a masallacin". Kai ya jinjina kawai,ya kuma nemi su masa jagora zuwa cikin masallacin.

Akwai ragowar lokaci,don haka ba cika sosai a masallacin,uwa uba kuma me martaba da yake ciki yana ganawa da wasu baqin. Ganinsu tare da hadiman morsa safiyya ya sanya basu samu wani wahala ba,dakarun dake tsare lafiyar sultane din cikin shigar kayan sulke suka dinga janye manyan gororin hannunsa da mashi suna basu hanyar wucewa,daga nan har zuwa ainihin cikin masallacin.

"Iyakacinmu nan.....amma kai kana iya shiga,lokacin shigarmu baiyi ba yanzu" Suka fada suna dakatawa. Idanunshi kawai ya dauke a kansu,sannna ya juya a nutse da zummar zare half shoe din qafarsa. Da hanzari ya murxawa Maher yatsuntsa guda biyu,abinda ya sanya Maher din saurin tashi daga duqawar da yayi ya zummar zare masa takalmin
(08187255862 lu'u lu'u paying)

"Hin dagatinaa" Ya masa magana da yaren oromo qasa qasa,ta yadda yayi imanin babu me fahimta koda yaji,sai ya tsaya qyam yana daidaita nutsuwarsa,kafin su taka a tare suna shigewa masallacin.

Wani irin katafaren masallaci ne me wani irin girma da kuma daukan hankali. Tun gabanin su shiga cikin masallacin haisam din ya gama karantar yanayin gininsa,gini ne da yake nuna zallar qwarinsa da kuma hikima sosai gurin ginashi.

Duk da yaune karon farko da yayi ido da ido da masallacin me tsohon tarihi,amma ya jima yana haduwa da rubuce rubuce a kansa. Abinda yafi bashi mamaki shine maganar bawa Allahn da ya zama jagoran ginin masallacin wato mallam zakariyya daya bada tabbacin duk wanda yaga faduwar ginin masallacin,to ba shakka zaiga tashin qiyama.

Ba wani abun mamaki bane gane me sarauta daga jinin wani masaraucin,musamman ga nutsatsen mutum ne tsananin tsinkaye da dogon tunani da kuma hangen nasa irin haisam din. Sultane din na dabanne......kamar yadda kwarjininsa ya zama wani na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login