Showing 120001 words to 123000 words out of 178317 words
Har tayi taku uku ta dakata,tana tuna cewa birra batace komai ba akan maganganunta,koda kalmar TO data saba cewa a duk sanda tayi umarni da wani abu.
"Kamar kinsan wani abu da yake ni bansan dashi ba.......meye wannan abun?" Ta jefawa birra tambayar tana waiwayowa gami da zube mata kyawawan blue eyes dinta.
Qasa birra tayi da kanta,aminci ne zalla a tsakaninsu tsahon shekarun da suka diba suna hidimta mata,alqawari ne da kuma rantsuwa sukayi akan ba zasu taba cutar da ita ba sam sam......amana da sirri sune zasu wanzu a tsakaninsu har abada,komai tsanani. A sanyaye ta motsa labbanta
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer ๐ณ๐ช*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA๐*
*HUGUMANKU CE*โ๐ฝ
๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
PAGE 57
___________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________
"Morsa safiyya ce ta karbi ragamar shirin tarbarsa". Sosai ta zubawa birra idanu tana qoqarin hado bakin zaren maganar tata. Morsa safiyya?......a hannu cikin shirin zuwan baqo gareta?.
"Indai har a wannan karon morsa safiyya keda hidimar tarbarsa......tabbas ya riga daya fadi.......ya kuma rasata tun kafin ya sanya qafafunsa masarautar agadez" Ta raya hakan a zuciyarta tana gyada kanta gami da jin wani abu yana tasiri a ranta.
"Daga wanne yanki zaizo?" Ta sake tambayar birra tana jin kwanciyar hankali a ranta.
"Zinder......daga zinder ne uwar gijiyata".
"Jeki......iya haka kawai ya wadatar" Ta fada tana sake samun sukuni cikin ranta.
Koda morsa safiyya bata da alaqa da zuwansa......koda bata da alaqa dashi,amma akwai wani abu a tare dashi da tayi liking,har takejin ya cancanci wannan tarbar irin tata. Wani qasaitaccen murmushi ya subuce mata......wataqila tarin addu'o'inta ne a yau Allah zai amsa mata......tarin fatanta ne yau qila zai cika......koda a iya wannan ranar......koda a iya wannan lokacin kadai ta nunawa morsa safiyya iyakarta ita ya wadatar da ita......ko yaya tanason ta gwada mata batakai ba,wataqila hakan ya zama silar da zata fita a rayuwarta,ta kuma nesanta kanta da dukka abinda ya shafeta kamar yadda ta jima tana buri da kuma muradi.
"Kayi kuskure" Ta fada qasa qasa tana hayewa saman qasaitaccen gadon da aka kashema lokaci da kudi kafin wanzuwarsa a dakin. Ta lume sosai cikin duvet da comforter tana lumshe idanunta. Tana wassafa irin sallamar da zatayi masa......tana wassafa irin bankwanar da zasuyi dashi.......irin bankwanar da zata zamewa duk wani me gigin sake zuwa gareta izinar da bazai kuma sha'awar ganawa da ita ba bare ya buraci ta zama MATARSA!.
"wai mata?" Ta sake maimaita kalmar a fili tana sake maida idanunta ta lumshesu. Tana sake cika da mamakin tsaurin ido iri na maza.......tana same tariyo wadanda suka taba zuwa gurinta. Mutum daidai har goma sha uku.
Dukkaninsu babu wani qasqantaccen mutum........babu wani me muni ko talaka a cikin su,hasalima su da iyayensu dukka sannanu kuma manyan mutanene tsakanin qasar niger din,Nigeria,Gabon,Camaro,Chad harma da algeria da kuma Egypt. Sai YANAAR da yayi tattaki tun daga Istanbul.
Wani siririn tsaki taja,haushi yana sake cikata. Waisu dukkaninsu gani sukeyi suna da wani quality isa ko qarfin kaiwa da zasu mallaketa?. A nasu yaudarar kawunansu,sun cika nauyin mizani da ma'aunin aure da mallakar akhnan?.
Wani murmushi ta saki tana aza kanta sosai saman pillow,tana jin adadin yaudarar kawunansu dake tattare dasu,zallar wauta da kuma wawantar da kansu. Hankalinta a yanzun a kwance yake ba kamar dazu ba,lokaci kawai take jira,shi yasa takejin baccin da batayi jiya ba isashe a yanzun yana kama idanunta,tana jin gwara tayi baccin ta sake tashi fresh.
Har saman kanta taja comforter din ta rufe,lallausan qamshin jikinta da wanda yake fita daga shimfidun alfarma na gadon suka hadu suka gauraya,suka bada wani kalar qamshi me wani irin sanyi tare da nuna ajin mamallakin dukka wannan qamshin.
*FALAAK*
A nutse take fitowa a dakinta tana kuma takowa zuwa ainihin parlor din morsa na musamman da take hutawa.
Sakakkiyar doguwar riga 'yar turkey ce a jikinta da mayafinta dukka da suka kasance kalar olive green.
Littafine dan qarami a hannunta data manneshi a qirjinta,idanunta akan morsa dake kashingide sanda take takowar,sai badee'a dake tsugunne a gafenta,kusa da ita wata kyakkyawar leda ce a ciki da ta tabbatar hijabanta ne a ciki.
Dab da zata qaraso morsa safiyya ta daga kai tana qare mata kallo. Daga jiya zuwa yau tana gani wani baqon yanayi tattare da falaak din. Ba zatace ga irin yanayin ba,ko kuma ga abinda ya faru,saidai tasan akwai wani baqon abu tattare da ita.
Da farko ta dauko ko daga malamin ne,amma kuma yadda ta zauna tana mata bayanin gamsuwar da tayi da Sheikh haisam sama da oustaz Ousmane sai hankalinta ya kwanta.
"Da gaske na dabanne momma........har yanxu na kasa aminta wai koyarwa yakeyi momma.......".
"Me yasa kika ce haka?" Kai falaak ta jinjina idanunta kan abincin gabanta da take juyawa da cokali.
"Ban taba ganin sheikh irinsa ba momma.........wani irin izza nake hange a jininsa,yafimin kama da jinin sarauta ko basarake" Ta qarasa maganar tana sauke idanunta akan momma.
Idanu momma din ta zuba mata,sai kuma ta janye dubanta tana son gano wannan yabon da falaak ke masa na kusan mintina talatin,to amma saita tuna,ko sultane sai daya kirata ya masa maganarsa,ya kuma tabbatar mata ya gamsu dashi dari bisa dari. Har sultane din yaso bata dariya sanda yace.
"So samu ko sau daya a sati mu dinga zama dashi yana karantar dani safiyya" Murmushi me kama da dariya ta saki.
"Sultane guda?,kuma ina kaga lokacin?". Ta fadi duk da tasan halinsa. Mutum ne me sauqin kai idan ka fahimceshi,hakanan ma'abocin son karatuttukan addini ne. Sau da dama idan ya kebe baya komai,zaka sameshi yana sauraren karatuttukan malam da ya aminta da koyarwarsu ne. Yakance.
"Muna mulki ne kawai don ya zama dole a kanmu,amna shugabanci masifa ce da saidai mu roqi Allah ya fiddamu ranar qiyama,duk yadda mukakai ga kwatanta adalci kuwa.......rayuwa duniya ba komai a cikin ta safiyya face rudu,idan baka nema ilimi ba.....duk girman rawaninka ba ruwan Allah da wannan,ranar qiyama zai saita hanyarka zuwa wuta"
To ko a yanzun ma murmushi shima ya maida mata.
"Safiyya......ilimi kogi ne,ta inda ka qare ta nan wani ya fara......na hangi wata irin nutsuwa a tare dashi,da wani irin hasken ilimi,zai wahala nan gaba kadan ban shugabantar dashi ba,inaji a jikina na samu wani mashawarci na kusa kusa da bani dashi sanadin rashin haihuwar d'a namiji".
Dukka bayanansu shida falaak itama ya sake saka mata nutsuwa dashi,duk da cewa bata samu ganawa dashi ba a ranar,don kafin ta fito har ya wuce bayan ya sallami su falaak.
"Ba asalin dan qasar nan bane,ba wani bane kuma,almajiri ne mai tarin ilimin addini,kawai kinsan ilimin addini yana sawa mutum wani irin kwarjini ne.........to amma alhamdulillah......dama abinda ake gudu a samu qasa da wanda ya kai oustaz Ousmane din" Kai falaak ta jinjina.
"Amma da gaske yana da doka momma......yace dole saidai na samu me rakani karatun,ko mu dauka tare,ko ta zauna ta jira a kammala qaramin".
"Ba damuwa bane......ga badi'a"
"Nima itace tazo raina" Falaak ta fadi tana diban abincin takai bakinta.
A gefe ta ajiye littafin tana hawa saman babbar daddumar da momma ke kashingide akai.
"Allah yasa manya ne hijaban badi'a".
"Manyan kike sha'awa kuma?" Momma ta fada tana juya wani dan qaramin akwati a hannunta wanda ke dauke da wata irin azurfa me daraja da aka sarrafata daga turkey.
"Haka yace......sheikh haisam ne yace shi zan dinga sakawa" Ta furta idanunta akan hijaban da badi'a ta zazzage tana daga mata su. Murmushi ya qwacewa falaak,ta hade hannunta guri daya.
"Wanne irin jilbab ne haka masu kyau badi'a?".
"Huguma closet.......can na shiga na dubasu......yanzun nan sarkin gida ya aika aka karbosu,har qofar gida daga garejin mota suka bayar takanas aka kawo". Kai falaak ta jinjina,bata sake ma cewa komai ba don tasan irin kayan da huguma closet din suke saidawa. Wani irin quality garesu,price din su kullum mamaki yake bata. Tana hira wani lokaci da hadimanta da sukan shiga Nigeria siyayya,sun sha gaya mata ko cikin kano ba kowanne kasuwa da shago bane yake da irin nata price din ba.
08187255862
Join our WhatsApp group.
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
(Muna aika kaya ko ina cikin Nigeria,nijer,ghana da Cameron).
"Ki kaimin ciki badi'a,saura awa biyu lokacin shiga aji yayi"
"An gama ranki ya dade". Ta fadi ta yunqura tana kwashe kayan.
Barin badi'a gurin morsa ta ajiye akwatin zoben hannunta. Ta dubi falaak,har qasan ranta tana jin dadin yadda karatu ya kama zuciyar falaak din,inama ace hakan zata faru da akhnan ko sau daya ne?.
"Momma.......don Allah ba gulma ba" Falaak ta fada tana murmushi. Itama qaramin murmushin ta saka.
"Gulma mana falaak" Murmushi tayi sosai,har sai da jerarrun haqoranta suka bayyana.
"Allah ba gulma ba kawai inason sani".
" Fadi falaak" Morsa ta fada tana kallon agogon dake daura dasu.
"Don Allah wanne kalan baqo wannan karon yaa akhnan zatayi......ina fata ya zama shine miji na qarshe da zata zaba" Shuru kadan morsa din tayi,abinda yaja hankalin falaak ta zubawa morsa din idanu. Nisawa tayi a hankali,ta miqe ta zauna tana duban falaak.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
"Shine mijinta in sha Allah......miji me addini.......mijin da zai saita rayuwarta,ya fiddata daga duhu zuwa haske.....mijin da zatayi alfahari dashi duniya da lahira.......HAKEEM JALAAL". Idanu falaak ta waro kafin ta samu ta hadiye wani yawu,tana duban morsa kaman ba zata daina ba,kafin daga bisani ta tattaro qwarin gwiwarta tace.
"Morsa......hakeem zinder?......hakeem din abba liman?" Kai morsa ta jinjina tana duban falaak cikin tsakiyar idanunta. Sai falaak din ta zare idonta tayi gefe dashi tana jinjina kai.
"Bai dace da ita ba?.....ko bai cancanta ba?" Morsa tayiwa falaak tambayar da ajiyayyar manufarta. Tanason gwada mizanin hankalin falaak din,tanason kuma gano zurfin nata burin akan kalar nata mijin auren.......cikin fargaba da fatan kada zaqin sarauta ya sanya tabi sahun burika da zabukan 'yar uwarta.
Da sauri ta maido dubanta ga morsa tana girgiza kai.
"Ko kadan morsa......hakeem fa?,ba shine yake zuwa ma niger na daya a gasar karatun qur'ani ba shekara biyar a jere?.......ba shine wanda ya wakilci niger ba a gasar izu sittin da tafseer na duniya ba?......ko ba shine dalibin da yafi kowa hazaqa ba a shekarar daya bar jami'atu ummulquraa?" Kai morsa ke jinjinawa tana jin tashin hankalinta kan kokwanton bin sahun akhnan daga falaak yana raguwa.
"Shine falaak" Sai data saki murmushi sannan tace.
"Ya cancanta morsa.....wallahi yakai......Allah yasa yaa akhnan ta fahimci hakan. Akwai wata nutsuwa ta daban tattare da maza irinsa......" Sai kuma ta dakata da maganan ganin yadda morsa ta zuba mata ido.
"Meye naki burin game da mijin aurenki?" Morsa safiyya ta samu kanta da tambayar falaak kai tsaye.
Wani irin nauyi da kunyar morsa irin wadda bata taba ji ba ta saukowa falaak. Sai ta miqe kawai da dan saurinta tana qunshe dariya tana barin gurin da sauri sauri.
Samun kanta tayi da kifewa saman gadonta,tambayar morsa na mata amsa kuwwa a kunne,sai ta tsinci kanta da tambayar kanta ta hanyar maimaita tambayar da morsa tayi mata yanzu yanzu.
"Meye zabinki?....ko kuma burinki dangane da kalar mijin aure?" Ta maimaitawa kanta da kanta wannan tambayar,wadda ta taho ne gilmawar kamannin hakeem kafin cikin qiftawar ado ya kauce,hoton sheikh haisam ya maye gurbinsa.
Wani matsanaciyar faduwa gabanta yayi,har tana jin sautin bugun zuciyarta cikin kunnenta,ta runtse idanunta da sauri tana jin kamar kowacce kafar jikinta na tsatstsafo mata da gumi. Da hanzari ta miqe ta zauna,ta laluba makunnin qwayayen dakin nata tana qara musu haske,don wani irin qara tsananta bugu zuciyarta keyi da duk gilmawar second da wanzuwar wannan tunanin cikin kwanya da idanunta.
โ
Cikin babbar saharar data kasance wani guri na debe kewa,wani guri na gudanar da bukukuwa ko kwanan al'ada daya zama wani abu da aka saba dashi cikin yarensu da qabilarsu ta buzaye.
Filinne me cike da sahara.......saidai kuma wannan saharar wani irin farin rairayin yashine mai taushi,amma kuma duk da tsananin taushin nasa tana jin yadda take iya zabga gudu saman raqumin da yake tafiya da wani irin kuzari kamar yana raka tsandaurin qasa bawai yashi ba.
Nishadi takeji sosai,raquminta.......yashin dama suturar jikinta dukkaninsu farare ne,sai wata irin iska me dadi dake kadata hankali kwance.
Tsaiwa tayi saman raqumin maimakon zama saman bayansa saboda dadin gudun da yakeyi da ita,ta ware dukka hannayenta kamar me shirin kama iskar dake wuceta da wani irin gudu,saidai ba zato ba tsammani ta hangeshi yasha gabanta yana nashi gudun ba tare daya ko juyo ya kalleta ba.
Jikinta a sanyaye ta zauna saman raqumin tana sake bashi qaimi don isa gareshi,ta kuma wuceshi.kamar yadda shima ya wuceta,tana gudun tana duban bayansa.
Shiga yayi irin ta cikakken buzu,rawaninsa da wandon yadin jikinsa,saidai kuma maimakon yasa rigar kayan,fara qal din t.shirt ce a jikinsa.
Tana gudun tana qara kusa dashi,amma still bai waiwayo ba bare ya duba ta kusa cimmasa,wannan farincikin ya sakata miqewa kaman dazu tana ware hannayenta,saidai a wannan karon sai taji an cafki hannun nata,abinda ya sanyata juyawa bangaren hagunta inda aka riqe mata hannun don ganin waye.
Saman wani raqumi yake shima,fuskarsa nannade da baqin rawanin da bazaiyiwu ta fahimci waye ba,kwanyarta bata gama daidaituwa ba mutumin dake riqe da hannun nata ya wani finciketa,abinda ya sakata sakin wani razanannen ihu tana duban nisan dake tsakanin raqumin nata da qasa a razane,qarar kuma data sakashi cin wani irin birki ya juyo da raquminsa da akalarsa gaba daya yana tunkaro nata raqumin da kuma mutumin da har yanzu yake niyyar kaita qasa.
Dab da zata isa ga qasa taji ya cafkota,shige yadda ya cafketa a wancan karon da thunder yake shirin kaita qasa. Duk da a razane take amma hakan bai hana haduwar idanunsu ba,wata irin iska ta taso zata yaye nadin dake tsakanin bakinsa da hancinsa.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer ๐ณ๐ช*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA๐*
*HUGUMANKU CE*โ๐ฝ
๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
PAGE 58
A hankali taja ana janye lullubin jikinta,wanda yayi kusan yi mata daidai da lullubin mayafin da tayi cikin filin sukuwar dawakan,abinda ya sanyata riqe mayafin da kyau,tayi wani juyi daya tilastata bude idanunta da sauri ba tare data shirya ba.
Saman fuskar aisa suka sauka,aisar dake tsaye a kanta tana duban fuskarta cike da mamakin kalar wannan abun da takeyi cikin baccinta,wanda ta tabbatar da cewa ba komai bane mafarki ne.
Maida idanunta tayi yana lumshesu,gabanta yana wani irin dokawa,zuciyarta na wani irin gudu tamkar yadda taji a sadda komai ya faru a zahiri.
Wani matsanancin bacin rai ne taji yana saukar mata,haushin aisa da haushin kanta da kanta yana cikata. Don me yasa aisa zata tasheta a sanda take dab da ganin fuskarsa?,me yasa ita din bata kai hannunta ta yaye lullubin da hanzari ba kafin aisa takai ga tashinta?.......me yasa aisa zata mata haka?,fuskar data jima tanaso ta gani ko hakan zai taimaka mata wajen gane wayeshi?.
"Ki tashi hakanan da wannan mafarkin naki........ko ba'a fadi ba wannan mafarkin ne daya zame miki jiki.......awa guda kacal ta rage baqonki ya qaraso inji mammina......ki tashi birra na jiranki". Blue eyes dinta ta bude a nutse,tana kuma watsasu saman fuskar aisa din.
Muhimmancin mafarkin.......da kuma muhimmancin da ganin fuskarsa yake a wajenta yafi muhimmancin baqon da aisa din ke magana akai,inda aisa tasan muhimmancin abun a gurinta da bata soma tadata ba akan wani mutum can da tuni ta gama yi masa nasa kalar matsayin. A yanzu duk duniya bata jin tana da buri na