Showing 21001 words to 24000 words out of 178317 words

Chapter 8 - LU'ULU'U COMPLETE

Jarrabawar zaitun kenan.......yana daya daga cikin abubuwan daya kawo kyautatawa me dimbin yawa tsakaninsa da ita......baya ga wata irin tarin biyayya da take masa tamkar siyanta yayi a mazaunin baiwa bawai matar aurensa ba. Yana da qwayaye biyu a duniya da zai nuna yace nashi ne.....mallakinsa ne......mammina bata da ko guda daya,amma koshi da ya mallaki qwara biyun cikin bege da kewar samun masu yawa yakeyi.

"Ranka ya dade......me yasa ka yarje mata?,me yasa ka aminta ta koma Niamey tun a gobe gobe?,baka tunanin zata koma ne taje ta zauna ita kadai tayita tunani tana sakawa kanta damuwa?". Idanu ya zuba mata na wani dan lokaci kafin ya janye idanunsa. Irin wannan kulawar da qauna me yawan gaske yake gani a idanun mammina akan akhnan tsahon shekaru ashirin cif kenan. Har yanzu kuma baiga abinda ya canza wannan damuwar qaunar da kuma kulawar ba.

"Zuwa yanzu ya kamata ki rage sanya kanki a damuwar al'amuran akhnan.......ba biftun ki ta shekaru ashirin baya bace......wannan wata biftu da muke sanya ran aurar da ita nan gaba kadan,ta kuma bamu jikoki masu tarin yawa" Yayi maganar ta qarshe yana jin kwadayin son aurar da ita yana taso masa.

Yana tsananin son yara.....yayi burin tara iyali masu fadi da girma......saidai hakan bai samu ba......tashi rubutacciyar qaddarar kenan.

"Ita din wani sashe ce na zuciyata kamar yadda nasan sashe ce ta rayuwarka.......bazan taba iya daina qaunar biftu ba har gaban abada,don Allah ka tayani baiwa morsa haquri" Tayi maganar fuskarta na narkewa alamun zuciyarta ta karye sosai.

Hannunsa ya miqa ya riqo nata a tausashe,cikin salon son kwantar mata da hankali yake dubanta.

"Baki laifin komai ba zaitun.......kawai safiyya nada zafi.......tana da fushi......wannan ne tazara da banbancin dake tsakaninku......amma bata da riqo,bana tunanin abun zai dade". Kai mammina ke girgizawa,wani abu yana mat yawo cikin zuciya.

"Ka tayani fahimtar da ita.......ya kamata ta sassauta fushinta a kaina......indai akan qaunar biftu ne.......muddin kulawa da yawan adadin soyayyr da nake gwadawa biftu zata iya zama laifi......ka fahimtar da ita zanyita dawwama a mazaunin me laifi a wajenta" Tayi maganar tana riqe hannun sultane da kyau,wani hawaye me dumi yana zarto mata.

Hannunsa ya miqa a hankali yana qoqarin kauda hawayen daga fuskarta.

"Ba zaki taba zamowa me laifi ba.....don ba inda qauna ke jawowa qiyayya.....ko bata fuskanta yau ba.....koda bata fuskanta gobe ba tabbas wataran zata fahimta". kawai matsawa mammina tayi ta dora fuskarta saman kafadarsa tana sakin wani boyayyen kuka daya sake daga hankalinsa.

Gaba daya ranar zuciyarta a quntace take,a quntacen kuma cikin fushi da bacin rai ta qarasa yinta. Don tunda ta isa sassanta raji wani abu me kama da ciwon kai ya saukar mata,saita sallami kowa ciki harda cooks dinta dake hada hadar ganin sun shirya abincin da zasu burge uwar dakin nasu dashi a wannan ranar. Duk da cewa babu tabbacin fitowarta cin abincin a kowacce rana,amma hakan bai sanya sun gaji ko sun daga qafa da tunanin girka abinda zai burgeta ba.

Sun sani yardarta da amincinta idan mutum ya samu cikin masarautar agadez to ya taki babbar sa'a a rayuwa,wannan ya sanya basa wasa da duk wani abu daya shafeta ko ya danganceta.

Lamo kawai tayi cikin duvet,tana jin kamar wani irin zazzabi zazzabi yana son kamata,wanda ta tabbatar zallar bacin raine kawai dake sasaqar zuciyarta.

A gajiye ta zare jikinta daga cikin duvet din,ta zuro dogayen kuma dogayen qafafunta qasa cikin jin kasalar miqewar kafin ta tattara dukka sauran qarfin da ya rage ta yunqura a nutse cikin yauqinnan nata daya cakuda da yauqinta na halitta

A hankali take takowa gaban balcony din sassanta wadda aka qawatata da wani irin yanayi na lafiyayyun shukoki masu bada ni'imtaccen qamshe. Furanni ne masu yawa a jikinsu da suka bada launin fari da pink,abinda ya sake qawata gurin kenan sosai ya kuma bada wani launi da yanayi da musamman.

Wata gown ce a jikinta ta wani irin yadi na musamman da aka yiwa sassauqan dinki,saidai gown din ta saukar mata sosai ta rufe har saman qafafunta,duk da bata da wani hannu na kirki ko kuma hannun azo a gani.

Tsaye tayi jikin qawataccen qarfen balcony din,tana jin yadda sassanyar iskar yammacin ke kadawa da wani yanayi dake saurin cire damuwa aran dan adam. Sosai irin wannan iskar take mata dadi,wanda mafi yawan lokaci anfi samunta ne tsakanin sallar bayan sallar asuba zuwa yammaci da farkon dare irin wannan,yammaci zuwa daren da damina ta soma sauka a wasu maqwaftan qasashen da garuruwan,wanda gari zai hada hadari ya kuma bada iska me kyau me cakude da qamshin qasa.

Sosai ta zuqi iskar tana kuna fesar da ita ta hanyar hancinta dake zaune das saman fuskarta da wani irin zubi da tsari daya qarawa fuskartata matuqar kyau. Hannu ta sanya ta janye gashinta dake yawo saman fuskarta sakamakon busawar iskar data maida gashin nata kamar wani abun wasa,don babu ribbon ko band ko daya data kama gashin dashi,hasalima tana jin kamar ciwon kai zai saukar mata ne,wannan dalilin ya sanyata barinsa a haka kawai.

Tana samun view me kyau na masarautar agadez a irin yanayi irin wannan.......tana samun damar kallon cikin masarautar da kyau dake qawace da wasu irin qananun fitilu masu tsananin haske da suke sake qawata idanun me kallo,su kuma sake qawata masarautar da qara mata kyau da kwarjini.

A karo na hudu ta sake maida gashinta gefan kunnenta saboda yadda yadda iska ke sake kwasoshi kaman zai shiga mata idanu. Ta sauke ajiyar zuciya me nauyin gaske tana jin yadda zuciyarta da kwanyarta gaba daya suka gaji da wannan tunanin. Tana jin kamar daren yayi mata tsaho zuwa wayewar garin da zata bar agadez zuwa Niamey.......tana jin masarautar duka ta mata zafi,sai ta dinga jin me yasa ta zabi kwana a agadez ba Niamey ba?.

Ta soma jin gajiya sosai cikin dukka tunaninta,har yanzu kuma ta gagara gano amsar nan guda daya dake wahal da tunaninta. Me zatayi da aure?,me zatayi da wani d'a namiji?,bayan bata rasa komai ba?,ba abinda kuma take da buqata?.......bata jin kuma akwai ranar da zata buqaci wani namiji a cikin rayuwarta.

Ba komai cikin halittar d'a namiji face zallar sonkai....... Mugunta,rashin imani ga mace da kuma tsananin son juya mutum da mulkarsa ta duk hanyar da suka dama.

Ita dukka wadannan abubuwan bata shirya tunkararsu ba.......bata shirya zama qarqashin umarnin wani ko hanin wani ba........bata shirya zama qasan juyawar wani ba.......bata shirya karbar umarni ko hani daga hannun wani ba. Ita ke umarni.......ita ke hani......ita ke alfarma......yardarwa wani ya zame mata miji yana nufin dukka wadannan damarmakin sunbar hannunta.

Kai ta girgiza a hankali,tuna wannan kawai yana sanya ranta ya baci,ina ga ace ya tabbata a zahiri hakan ta kasance?. Sam bata ga inda zata ita rayuwa a hakan ba.......ita akhnan ta zama qasan mulki umarni hani da gadarar wani ba.......mutum biyu a duk duniya taji ta aminta su samu wannan damar a kanta,SULTANE DA MAMMINA.

"Gata na sameta a balcony.........okay to yayi ba damuwa" Ta tsinkayi muryar aisa daga bayanta. Batayi wani yunqurin waiwayawa ba tunda tasan aisa din zata iso,sai kawai taci gaba da kallon farfajiyar dake gabanta,tana kuma jin yadda muryar aisa ke sake kusanto inda take.

Cikin qasa da minti daya saiga aisan a kusa da it,still dai wayar take amsawa. A jikinta takejin idanun aisa din a kanta,ta kuma gama fahimtar suna magana ne da Shehinaz.

"Bansan ta yaya zan miki bayani ba Shehinaz........da ki bari kawai saikin iso din" Aisa ta fada muryarta na nuna tasirin bacin rai kadan.

"Okay......gata" Ta fadi tana miqawa akhnan wayar. Girgiza kai kawai tayi ba tare data karba ba.

"Kice mata idan zuwa zatayi kawai karta wahalar da kanta zuwa agadez.......ta sameni a Niamey" Ta fadi a nutse tana sakin qarfen,sannan ta taka tana juyawa zuwa ciki a hankali. Wanda dab da zata shiga parlor din da zai gangara da ita zuwa ragowa falukanta sukayi kacibus da birra da wayarta a hannunta. Ta rusuna tana miqa mata.

"Kiranki aketa yi tun dazun ranki shi dade" Sai tasa hannu kawai ta karbi wayar ba tare da ta tsaya tambayar me kiran ba.

Duk yadda aisa taso tayi mata maganar abinda ya faru tsakaninta da altaab a daren akhnan taqi yarda hakan ya faru,sai zuwa washegarin ranar sanda birra ta taimaka mata ta kammala shirinta tsaf cikin wata tsadaddiyar riga da bata da taqamaimen suna......saidai tana zubi da abaya......irin abayar da yaran sakunan qasashen larabawa ke alfahari dasu,suke kuma amfani dasu a manyan bukukuwansu na alfarma.

Kwallin data zizarawa idanunta da lip gloss din data shafa su kadai ne baqin abu dake saman fuskarta idan ka dauke powder din da take using na wani brand dan qasar France,jikinta na fidda unique scents dinnan nata. Komai nata natural ne.......duk da tana da son ado sosai. Tana da wani irin gayu na fitar hankali.......gayu na daban kuma na musamman me jan hankali. 'Yar gayu ce irin gayun daya amsa sunanshi,wanda hakan ya tasiranta a kanta ne saboda haka aka gineta tun tana tsummar goyonta. Daidai ba brush dinta na musamman ne......kuma designer,don yawancin lokuta takan tashi dare daya ta musanya komai nata da take amfani dashi,koda kuwa soson wanka ne zuwa new design da kamfanin dake mata wannan aikin suka fidda a shekarar ko a watan.

Tana cikin amsar LV bag dinta daga hannun birra data gama zuba mata komai a ciki aisa data kammala nata shirin ta kalleta.

"Komai naki ya cika akhnan.........amma duk da cikar nan da yayi akwai sauran gurbin da babu abinda zai cikeshi sai aure da miji". Blue eyes dinta masu almond shape ta daga a nutse ta zube ma aisa su. Yan miskilancin suka motsa,ta motsa bakinta kamar zatayi magana sai ta fasa,ta gyara mayafinta da yake kafadarta ta soma takawa da wata iri nutsuwa saman high hill shoe dinta,wanda saboda tsininsa ba zakayi tunanin wata halittar dan adam zata iya tafiya dashi ta dadin rai haka ba.

Ba haka aisa taso ba,don da biyu tayi maganar,ba shurun akhnan take buqata ba......bude bakinta takeso tayi tace mata wani abu. Ba kasafai kake fahimtarta ba muddin bata ce maka komai ba,shurunta yana da wasu irin tarin ma'anoni da suke sanyaka ka gaza fahimtar wace ita?,ina ta sanya gaba?.

Sanda ta fita dining room ma ta samu barra'u na shimfida mata tattausan farin yadi saman cinyarta don gudun bata jikinta. Yayin da bushira ke hidimar shafa mata avocado da dafaffen qwai cikin bread din da zataci,kasancewar bata cin bread haka zallarsa gudun qiba. Tana da mugun son lafiyarta,tana qaunar lafiyarta sosai,don haka bata rabo da dukkan wasu nau'ikan abubuwan gyara jiki da zasu dawwamar mata da lafiyarta kyan jikinta dama kyan fatarta. Akwai nau'ikan motsa jiki da takanyi duk safiya irin wanda suka dace da mata dake qara fidda musu shape dinsu,su kuma tsayar da boobs dinsu da sauran sassannin jikinsu.

Komai bushira ta gama shiryawa ta ajiye a gabanta,ta matsa kadan tana ajiye wayarta a gefe ta jawo plate din tana duban buhaina.





*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*

PAGE 09
____________________________
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500 dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. ⁠married femfresh wash 2k
3. ⁠garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. ⁠Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. ⁠Tsimin mallaka 2500
6. ⁠maganin infection 1500
7. ⁠matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
______________________________



"Banji kince komai ba game da ranar juma'an data wuce" Ta qarasa maganar tana daukan mug din coffee da aka zuba wadatacciyar madara me zafi tayi sipping a hankali.

Qasa tayi da kanta,tana jin qirjinta yana bugawa.

"Naso nayi miki bayani ranki shi dade.......wannan jumma'ar ba'a samu damar gudanar da sadakar ba,ganin a gaggauce kike da kiran da sultane yayi miki" Har takai spoon bakinta ta maida ta ajiye tana duban buhaina din da wani irin kallo.

"Me kika ce?" Ta tambayeta tana ritsata da idanu,saita sake yin qasa da kanta.

"Kiyi haquri ranki shi dade" Akwai bacin rai sosai cikin idanunta take duban buhaina dasu. Sadakar juma'ar ta zame mata tamkar wani bangare na ayyukanta na duk sati. Sau tari ita da kanta take shirya kayan abincin cin wani kyakkyawan wando babba sosai na kaba,a fita dashi gidajen da basu da hali a ajiye maka a qofar gidanka ba tare da kasan daga ina yake ba.

Wani alqawari ne data daukarwa kanta muddin numfashinta.......wani sashe ne na abinda yake faranta mata rai a duk sanda tayi hakan,ba tare kuma da tasan abinda yake sakata wannan farincikin da nishadin ba.

"Kinsan muhimmancin aikinki kuwa?.....menene hadin kiran sultane da wannan aikin buhaina!?" Ta jefa tambayar tana dan buga cokalin hannunta kadan.

"Ki gafarceni uwar gijiyata.........nayi kuskure......"

"Ba kuskure bane wannan ganganci ne!" Ta sake fada cikin fadan da yake damfare da yadda zuciyarta ke a bace tun jiya.

"Ammm.......buhaina......a samu a maida madadin ta juma'ar da bayi ba wannan lahadin.......nan gaba kuma kome akeyi ko meye ya faru ki dinga qoqarin ganin anyin.......idan ya kama da akwai qaqqarfan dalilin da zai hana ayin saiki sanar tunda wuri". Aisa ta karbe maganar don bataso tayi tsaho,ta fuskanci idan tayi tsahon kowa ma sai ranshi ya baci.

Dogon tsaki taja ta miqe tana daukan tissue,ta tura kujerar baya tana fita daga tsakanin table din.

Jakarta birra ta dauka tabi bayanta,yayin da aisa ta girgiza kai kawai taja wata kujerar ta zauna tana cewa buhaina ta hada mata abincin dan kadan,don tasan zata samu lokacin da zata gama cin abincin harta rusketa,don tasan tabbas ne saita shiga ta yiwa sultane da mammina sallama.

Kai tsaye sultane ta fara gani,yayi mata addu'o'i sosai sannan ya rufe da cewa.

"Ina buqatar zuri'a me yawa wadda bayanta bazai yanke ba.......zuri'arta ba zata samu dogon zango da kuma dogon tarihi ba saita tsatsonki da tsatson suhaana,kece babba,kece bake da fata a kanki sama da suhaana........kece burina yafi zurfi a kanki biftu,kiyi qoqarin zama magajiyata ta wannan fannin ma......kamar yadda kika sharen hawayen rashin d'a namiji ta fannoni da bangarori da dama.....nagartaccen suruki akhnan.......nagartaccen lu'u lu'u nake buqata.......wanda zai maye min gurbin da na rasa.......kafin ki sake shiga ko ina......ki shiga wajen mommanki kiyi mata sallama". Ya qare maganar yana tuna yadda safiyya ta kasa zama,ta ratso tsananin duhun daren jiya ta iskoshi a sassansa. Sunyi maganganun da suka tsaye masa a rai,maganganun da suketa yaqi tsakanin zuciya da kwanyarsa,suna son zaqulo masa ainihin inda matsalar da damuwar suke......sunason bashi tabbacin akwai kuskure ko babu?.

Sosai maganganun sultane suke mata yawo saman kanta lokacin da take takawa zuwa sassanin morsa safiyya.

A nutse take kurbar dafaffiyar madarar dake cike da wani mug dake iya baka damar ganin abinda yake cikinsa. Cikin wannan tsaren gidan da kamalarta ta qara masa kaifi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login