Showing 81001 words to 84000 words out of 178317 words

Chapter 28 - LU'ULU'U COMPLETE

yake dirkawa cikinta,duk wani hanya da zata samu gutsiren dalilin da ya sanya sultane mata irin wannan kiran gaggawar ta kasa samun kowanne labari,koda daga gurin mammina kuwa,don hatta mammina dinma bata da labarin kiran saida akhnan din da kanta ta gaya mata.

Bacin ran taji yana neman mata yawa,don haka ta miqa hannunta ta dauki headphone dinta dake maqale ta dora saman kanta,ta kuma lalubo waqar best artists dinta cikin mawaqan dake waqa da French wato indila.....

Waqar love story ta kunna,ta qara volume din daidai yadda zai ratsata,ta maida idanunta ta lumshe. Tanason waqar sosai,batasan kuma iya adadin sau nawa ta taba saurarenta ba,har wasu baitukan sun zauna a kanta. Amma kuma duk da haka sau daya tak ta taba kallon video din waqar.......tana against duk abinda ke cikin waqar idan ka cire waqar kawai,sautin yana mata dadi sosai,ya kuma bata nutsuwa a ranta.....amma sam video din bai mata ba. Bataga wani dalili bane......bataga kuma wacce irin qaddara ce zata sakata dakon son wanda ya mutu ba.......ko rayayyen ma bata fata qaddararta ta zana mata haka. Bata hangi komai ba cikin so sai qasqantar da mutum......ta sanya duk qarfi da izzarka kayi qasa,itakam duk wani abu da zai sanya kima da martabarta da kuma izza da ikonta su tabu to babu ita a cikinsa.

Yadda ta saka volume din ya sanya sam bataji sallamar da barratu ke yi ba,har zuwa sanda waqar ta qare,ta zare headphone din a kunnenta. Haka kawai taji yana sha'awar maimaita kallon film din the umbrella of Cherbourg.

Batayi zaton ganin barratu a gurin ba,wannan ya tsoratata sosai.

"Afuwa ranki ya dade.....inata sallama amma baki jini ba" Sosai ta shaqi iska ta kuma fesar,ta lumshe idanunta ta budesu sosai a kanta.

"Shine me?.....shine zaki tsayamin a guri?.....da izinin wa?" Qasa ta sakeyi da kanta,don ta fahimci cikin kwanakin izzar tata ce ta motsa

"Tuba nake" Ta fada a sanyaye.

"Karki kuskura ki sakemin wannan haukan.....bacemin da gani kafin raina ya qarasa baci". Da hanzari barratu ta juya tana barin gurin. Ba wani baqon abu bane a wajensu,dama kura ce tayi lafiya ai......lafiyar tata kuma sanadin dauki ba dadin da suka dinga yo ne da morsa safiyya.

A duk sanda zatayi musu wani abu na rashin martabawa ko girmamawa......muddin ya fada idanu ko kunnuwan morsa safiyyan saita dakatar da akhnan din.....tun abun yana mata zafi,tana ganin yarfata take,wulaqantata take gaban bayinta kuma hadimanta,har ta fahimci morsa safiyyan ba zata fasa mata gyara ba ko a gaban waye,dole wasu abubuwan da yawa suka ragu.

Ta gama saita system din tayi playing film din kiran mammina ya shigo. Iska sosai taja,ta yiwa birra dake tsugunne tana zuba mata lemon inibi sign na ta bata wayar,ta dakatar da zuba lemon ta dauki wayar ta miqa mata da dukka hannuwanta biyu.

Sai data janye qafafunta ta maida saman kujera sannan ta daga kiran tana rungume pillow a qirjinta.
(08187255862 luu luu paying)

"Hi..." Ta furta da siririyar muryartannan maras hayaniya ko kadan.

"Sai yaushe zaki girma ne akhnan?" Mammina tayi maganar tana gyara zamanta hadi da miqa hannu ta karbi yankakken apple daga hannun yalwa dake durqushe a gabanta.

"Mammina......indai ina dake......indai kina tare dani bazan taba girma ba" Ta fada a narke tana jin kamar ta koma cikin mammina din ta sake haifarta a matsayin d'iyar cikinta ta halali. Tabbas inda haka zata iya kasancewa lallai ba shakka da tafi kowa sa'ar samun uwa.....irin uwar da zata lullubeka da soyayyar da ba zata baka daman kokawa ba ko kadan.

"Gaskiya ne biftu na.......ina fatan kina lafiya ko?,baki sanya wannan damuwar a ranki ba?". Sosai ta sake narkewa cikin pillow din kamar wata 'yar mage.....muryarta a karye tace.

" Dole na damu mammina......banason na bata da sultane......banaso nayi masa abinda ranshi bayaso". Shuru kadan mammina tayi tana jujjuya dukka maganganunta a ranta. Akwai abubuwan da ya kamata tayi magana da akhnan akai......amma ba zatace mata komai ba,zata jira har zuwa lokacin da ta yanke gaya mata.

"Bana jin akwai wani abu da zakiwa sultane da zaiyi muni har irin yadda kike zato ko zargi ba biftu.....na jima banga soyayya tsakanin uba da 'yarsa ba irin taku.....soyayyarki da sultane daban take a zuciyarsa" Sosai maganganun mammina suka bata wani irin relief data gaza samu tunda sukayi magana da sultane. Ta sauke ajiyar zuciya me nauyi,yana daya daga cikin abubuwan da suka sanya take matuqar son mammina din,take kuma ji da ita a rayuwarta sama da kowa da ya rabeta ko ya jibanceta.

Tana bata relief qwarin gwiwa da kuma tabbaci akan duk wani abu da zai tunkareta. Tana nuna dukkanin damuwarta da kulawarta akan kome da zai shafeta...... Wannan shine cikakken banbanci da tazara me nisan gaske data yiwa morsa safiyya.......kuma irin wannan tazarar ko mafiyiyarta ta yiwa morsa safiyyan a cikin rayuwarta.

"Me yake faruwa a sahel couture?" Mammina tayi furucin cikin tausa murya.

Kiran sahel couture din da tayi ya sanya akhnan bude zara zaran idanunta gaba daya da suka rusuna a dazu.

"A sahel.......bazan iya tunawa ba mammina". Wani ajiyar zuciya me nauyi mammina ta sauke da tazarar sakanni sannan tayi magana.

" Tabbacin ba cikin nutsuwarki kike ba biftu......shin kin manta muhimmancin da kamfanin yake dashi a tare dake?.....me yasa zaki bari damuwa ta shiga cikin muhimmam al'amuranki?". Numfashi ta jawo tana gyara zamanta sosai cikin sofa din. Da jiya da shekaran jiya dama yau duka dai sunan ta shiga company dinne kawai......amma ba wani aiki da tayi daya shafeshi,ba kuma wanda ta bawa daman ganinta idan ka dauke aisa da Shehinaz,suma kuma bata bari sun mata maganar komai ba.

"Mammina.......Je ne suis pas dans le ton(bana cikin yanayin)" Tayi maganar kamar qanqanuwar yarinyar data rasa mafita.

Wani murmushi ne ya subuce mata,wanda daga ita sai zuciyarta ne kawai sukasan da fitarsa.....koda yalwa dake zaune gabanta ba zatace ta ganshi ba bare akhnan da bata tare dasu.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITAπŸ‘‘*

*HUGUMANKU CE*✍🏽


πŸ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*πŸ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 38
_________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*

*Assalamualaikum*

*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*

*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*πŸ‘˜πŸ₯»

*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin Aminci???*

*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*

*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana goma KACAL!✌🏽*

*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*

*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*πŸ™ŒπŸ½
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*

*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*

*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT da yardar Allah*

+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791

https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
____________________________




"Har yanzu baki gama fuskantar matsayinki ba akhnan.......kinsan girman matsayinki da martabarki a qasar agadez?.......ina kikai jarumtarki?.....me yasa zaki bar qaramar damuwa ta mamayeki har haka?.....ba haka na sanki ba.....ba kuma haka nakeso naci gaba da ganinki ba" Ta furta cikin kambamata da kuma motsa mata matsayinta.

Idanunta ta lumshe ta kuma budesu a sarauce.

"Ina nan yadda nake mammina.....ban canza ba,bana jin kuma zan canza din.....saidai sultane daban yake a raina....dole damuwarsa dama komai nasa ya zama daban a raina......koda sahel couture a bayanshi take.......da girman qarfinki na amince kiyi abinda ya kamata na dan lokaci kafin komai ya daidaita". Shuru sukayi dukkaninsu,wani abu yana bugawa a tsakiyar qirji da zuciyar mammina.......ta tsuke idanunta daga inda take zaune,tunaninta kuma yana harbawa da nisa fiye da nisan dake tsakaninta da akhnan.

"Indai kina da uwa irina har abada ba zakiyi kuka ba.......ki dauki lokacinki.....kiyi amfani dashi har iya yadda kikeso.....mammina dinki zata kula miki da komai.....zata kuma ji miki da komai".

" Na gode" Ta furta da wata lanqwasashiyar murya,kuma bata qara cewa mammina din komai ba ta yanke kiran,ta ajiye wayar a gefanta ta zame tana kwanciya.

Da sauri yalwa ta miqa hannu ta karbi wayar daga hannunta tana duban yanayin fuskar uwar dakin nata. A nutse ta maida dubanta kan yalwa.

"A jikina ina jin akwai wani baqon abu......akwai wani abu na daban ba irin abu ba yau da kullum ba.......bansan me yake faruwa tsakanin sultane da akhnan ba......banga alamun komai tattare dashi ba,kamar yadda baiyi niyyar gayamin ba.....daren jiya mun kasance tsahon daren tare dashi muna hira......amma baicemin komai ba a kanta,bana buqatar tambayarsa komai,kaman yadda baiyi niyyar na sani ba......amma ina buqatar sanin komai din.....yalwa" Ta sake kiranta a karo na biyu.

"Allah ya taimakeki" Ta furta cikin girmamawa.

"Inason nasan meye wannan?......wanne laifi ne akhnan ke zaton ta yiwa sultane daya hanata nutsuwa......inason insan dalilin kiranta da sultane yayi zuwa agadez a satin nan". Kai yalwa ta jinjina sosai.

"An gama ranki ya dade......komai zai kasance a gabanki a bude". Yalwa ta furta cikin bata tabbaci,kamar yadda take da tabbacin a kanta.

"Sahel couture.......ina ganin kamar ya kamata a lura da kamfanin nan......sannan ayi amfani da dukka wata dama data samu a wannan taqin......wannan tsukin da kuma wannan lokacin.....lokaci ne me kyau daya dace a kula da sahel couture!" Ta qarashe da fadin sunan da wani harshe wani sauti daya tabbatarwa yalwa dukkana abinda ta fada tana nufin hakanne,abinda ya sanya yalwa komawa ta zauna sosai,tana bawa mammina hankalinta dama awannin rayuwarta gaba daya.


β˜…β˜…β˜…β˜…Ni'imtaccen qamshi ne me wani irin sanyi da laushi kawai ke fita daga ilahirin parlor din dama gidan gaba daya a safiyar ranar,daidai da qarfe sha daya na safe agogon qasar garin agadez dama niger gaba daya.

Su biyu ne rak zaune saman qawataccen dining din nasa da aka qawata da kalolin abincin da dan adam ka buqata kowacce safiya,wanda kusan komai da yake kai irin zabin abincinsa ne. Ba wani abinci da aka dafa me yawa,kowanne dan kadanne da bazai zama asara ba koda bai cinye gaba daya.

Wata sky blue din kurta ce a jikinsa me daukan idanu sosai,wadda aka yiwa adon zare a wuyanta da hannun rigar da wani kalar zare blue black. Iyakar tsahon rigar gwiwa sai wandonta da a wuyan qafan wandon shima aka yiwa ado da blue black din zaren.

Fuskarsa tayi wani fresh kaman yadda hasken qwayar idanunsa tayi wani irin tarwai. Sumarsa dake a kwance luf da wadda ke habarsa da kumatunsa sun sake fidda kwarjininsa sosai da kuma sigar kyansa.

Sosai yakejin zuciyarsa fresh......kaman yadda yanayin garin a safiyar farko da ya wayeta a qasar tayi masa,don wata iska me damshi damshi ke kadawa wadda ta sake tabbatarwa da kowanne me rai damina tana tafe,daminar da zata jiqa rayuka da tsirrai da sauran halittu da ni'imomi daga ubangijinsa.

Coffee ne a gabansa da aka zuba cikin wani qwataccen cup dake dauke da dan qaramin tray dinsa a qasa. Ba wai coffee din yake sha ko yake kallo ba,dukkan hankalinsa ya tattarasu ne akan malam Ousmane,yayin daya sanya coffee din a tsakiyar hannunwansa,ya zagayeshi yana soke yatsunsa a cikin na juna.

Bayanan malam Ousmane haris yake saurara,lokaci lokaci yana lumshe kyawawan idanunsa dake da brown din qwayar idanu wadda bata cika duhu ba sosai.

"Finally an samu hanyar shiga sultane palace......kuma wannan itace hanya guda daya da zaka zama ahalin masarautar,don muddin ka zama malami ga d'iyar sultane,suna mu'amalantarka ne tamkar d'ansu......musamman morsa safiyya.......tana da karrama dan adam sosai" Malam Ousmane ya qarasa fada cikin bawa haisan tabbaci.

Wata sassanyar ajiyar zuciya ya saki kana ya lumshe idanunsa ya kuma budesu duka lokaci guda akan Ousmane din.

"Akwai wani option dinne bayan wannan?" Ya furta a nutse,labbansa masu daukan hankali suna motsawa a hankali. Dan kadan malam Ousmane ya zuba masa idanu sannan ya girgiza kai yana cewa.

"A'ah" Can qasan ransa ya gama fahimtar abinda haisam ke nufi. Shigarsa gidan a mazaunin malami ne sam tsarin bai masa ba......to amma kuma ba wata hanyar da tafi haka sauqi.

"Kana da wata hanyar da tafi wannan ne sauqi?" Ousmane ya tambayi haisam din yana qoqarin tsareshi da ido. Kai kawai haisam ya girgiza ba tare daya dubi Ousmane din ba,yaja cup din coffee dinsa a nutse yana kurba gami da zubawa wani canister dake gabansa ido.

Kurba kusan biyar yayi,shuru yana sake ratsa wajen,Ousmane yayi qarfin halin ajiye ajiyar zuciya. Akwai buqatar ya fahimtar da haisam din,don wanann din wata dama ce babba a gurinsu,wucewarta kuma zai zaman kamar rasa gwaggwabar dama ne.

"Shiga agadez palace yana da muhimmancin haisam ka fahim......"

"......na fahimta Ousmane......." Ya katseshi yana mai bashi amsa. Can qasan zuciyarsa wani kishin tashi masarautar tana kamashi. Ba inda zaije a duniya sarautar jimma ta sauka daga jikinsa ko kuma zuciyarsa,wata sarauta ce da aka haifeta a asalin cikin jininsa,ta yaya zai iya rayuwa qarqashin wata sarautar?,qarqashin wani tsare tsaren da ba na mooti abba jifar ba?.

"Shiga gidan yana nufin sanin mutane da yawa dake rayuwa cikin gidan......mutanen dake rayuwa qarqashin kariya da alfarmar masarautar.......shiga gidan zai zama hanya mafi sauqi ta sanin mutane da dama da cudanya dasu........haka abun yake ba kuma laifi......amma zama malamin d'iyarsa da jikokinsa fa?.......banajin abune me yuwuwa". Haisam din ya fadi yana jin har cikin zuciyarsa abun be gamsheshi ba.

"Haka zaka shiga muhammad.......ka sanya a ranka daga yau kaine malami na gaba da zaici gaba da koyar da diyoyinsa........chapter closed,komai ya kammala.......fara gudanar aiki kawai muke jira,don duk wani jan qafa da zai biyo baya,tamkar qarin kwanakin da zakayine cikin aikin" Ya tsinci muryar bobbo muhammad dawud da baisan daga ina take ba. Sai daya daga qwayar idanunsa a nutse sannan ya lura video call ne Ousmane ya daga a wayarsa,fuskar abba muhammad dawud din kuwa ta fito tarwai a wayar,furfurar nan tasa dake nuna shekarunsa da kamalarsa dukka sun fita sosai.

Idanu suka hada da haisam din,sai ya jinjinawa haisam kai,ya kuma dunqule hannayensa dukka biyun cikin na juna yana jijjigawa. A hankali shima haisam din ya hada hannunsa hakan,wannan din wani salon alwashi ne da suke ciwa juna muddin zasu fara aiki me wahala da hatsari irin hakan,wani alqawari ne na cika aiki da suke yiwa junansu.

Daukewar kiran dif ya sanya haisam maida kallonsa kan Ousmane,suna hada ido ya saukar da nasa idon qasa yana fadin.
(08187255862 lu'u lu'u paying)

"Afuwa......bansan shine ya kira ba,bansan kuma na daga kiran kai tsaye ba,duk da already tun jiya mun gama maganar dashi,ya kuma tabbatar ba wata hanyar data wuce wannan......ko ina ya kamata bincikenmu yakai......muna da hadin kan hukumar tsaro har uku dake riqe da qasar nan" Kai haisam ya jinjina kawai baice komai ba,ya jawo wani kyakkyawan mazubi da ake zube dabino a ciki masu laushi da zaqi ya soma barewa,don dasu yakeson yasha tea din. Yana da zabi da madadi ashan sugar,mazarqwaila ko zuma ko dabino,sune abokan zaqinsa.

"Akwai yiwuwar sanar da shugaban qasarsu" Haisam ya fada kansa tsaye ba tare daya dubi Ousmane ba daya soma yin hanyar fita. Cak ya tsaya sannan ya dawo da baya da sauri.

"Amma akwai hatsari fa ayin hakan......" Dogayen yatsunsa ya daga masa alamun dakatarwa.

"Wannan kasadar tawa ce ba taku bace....idan ka fita ka turomin addisaleem". Wani yawu me tauri Ousmane ya hadiye. Yasan halin haisam din,kaifi daya ne......idan yace zaiyi ba abinda yake saukar dashi daga wannan bigiren. Ba lamari bane daya shafi addini ballantana ya jawo masa aya ko hadisin da sune kadai makaman dake iya saukeshi dama.......dabara ce da kuma fahimtarwa,ya kuma fuskanci bashi da buqatar wannan,sai kawai ya juya ya sauka yana kiran mass addisaleem kamar yadda ya buqata.

"Dukkan wadanda muka taho dasu daga addis ababa nakeso ka sanar musu,ina buqatar ganinsu nan da awa daya......ka saka abdii a ciki" Ya bawa addisaleem umarni kai tsaye.

"An gama" Ya fada yana rusunawa sannan ya juya yana fita a gaggauce.

Yana da kiyaye lokaci,yana kuma mutuntashi da martabashi qwarai. Idan shi yayi zabin lokaci don gudanar da wani abun,baya wuce adadin mintuna da awannin daya ware,idan shi aka bawa lokacin,zaiyi komai kaman yadda lokacin yace......idan abune kuma ya saka awa nawa zai dauka......baya shallake wadannan awannin yake qoqarin kammala komai.

Cikin kamala ya sauko zuwa dakin da ya gama wareshi a mazanin dakin da zai kasance wajen ganawarsa ta sirri da dukka wanda yakeso. Kaman yanzu dai da mutum shida harda abdii na bakwai suke jiransa.

Sosai yayi wani irin kyau da kwarjini cikin shigar wani kyakkyawan yadi da aka yiwa budadden dinki kamar rigar fulanin Nigeria,saidai ita din tafi tasu fadi sosai ta kuma sauka har gwiwarsa. Farar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login