Showing 177001 words to 178317 words out of 178317 words
ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 83
___________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________
"Wallahi bazan aureshi ba....zanje na sake jaddadawa sultane......bazan aureshi ba!.....bana sonshi!.....a rabu dani mana haka!"
"Bita aisa......bita" Shehnaz da abun yazo mata a matuqar bazata da wani irin tarin mamaki ta fadi,sai aisa ta saketa ta kuma fita zuwa parlor din da sassarfa,inda dukka hadimanta sukayi tsaye cak cikin razana da tsoron fusataccen fushin da suke gani tattare da uwar gijiyar tasu.
Tana dab da qofar farko,amma ba wanda ya isa ya kamota a cikin su,sai zallar tashin hankalin daya bayyana a idanunsu saboda maganganun da take fadi cikin bacin rai.
Cafko hannunta aisa tayi,wadda ta qaraso gurin da gudu,sai akhnan din ta waiwayo tana dubanta gami da watsa mata wani irin kallo
"Sakeni!" Ta fada a fusace. Duban tsakiyar idanunta aisa takeyi. Wannan fusatacciyar zuciyar data jima bata yunquro ba ayau ta ballo kenan.
"Biftu?,baki da hankali?,a cikin hayyacinki kike?,sultane din zaki je ki tara gaban baqi ki gaya masa bakyason auren hakeem!"
"Eh!......haka nake shirin aiwatarwa,don suma su sani bazan auri dansu ba.....banaso!....ki sakeni aisa!" Ta fada a tsawace da lallausar muryar nan da ayau ta zama wata me kaushi.
"Bazan sakeki ba.....bazan kuma barki kije kiyi abinda xai zubda kimarki ba,ya zubda kimar masarauta,ya taba mutuncin sultane ba" Wani kallo me cike da tsananin bacin rai take jefawa aisa.
"Idan ma baki sakeni ba naje.....bazan zauna baqinciki ya kasheni ba,zanyi abinda yafi haka.....guba zansha!.....guba zan sha na mutu kowa ya huta!.....naga wanda za'a yiwa auren ko?!" Akhnan din ta furta da madaukakiyar muryar da sautinta ya karade dukka falon da wajensa.
Kasa cewa komai aisa tayi,sai idanu data zubawa akhnan a tsorace. Tasan fushinta.....wani irin fushine me girman tasiri da idan ya motsa tana yin kamar me aljanu,tanayin kamar ta rasa hankalinta ñe......amma na yau din kamar yana neman zarta hankali,yanxu qiyayyar aure a zuciyar akhnan har yakai haka?.
Batasan sanda shehnaz ta iso guri ba,sai ganinta tayi ta rungume akhnan din ta baya kuka yana balle mata.
"Ki daina irin haka biftu....meye haka?,kinsan girma da munin abinda kike fada?,da kanki kike cewa zakisha abinda zaki kashe kanki?......biftu ki dawo hayyacinki mana" Ta qarasa fada tana zagayowa gaban akhnan din gami da riqe dukka fuskarta cikin tafukan hannunta.
Wasu irin hawaye ne suka cika blue eyes dinta da suke nuna koda wanne lokaci zasu gangaro,labbanta suka motsa,motsawar da aisa ta fahimci ta furta.
"Astgafirullah ne" Wadda bata da sauti ko kadan.
"Kowa ya wuce zuwa aikin gabansa" Aisa ta bawa duk wanda ke tsaye a parlor din umarni,yayin da yalwa ta qarasa korar kowa.
Hannun shehnaz da akhnan din aisa ta kama da sauran dakakkiyar zuciyarta,ta kuma jasu kai tsaye zuwa daya daga cikin bedrooms din akhnan din suka shige ciki sannan ta maida qofar ta kulle ta kuma murza key.
Tunda ta hango tahowar yalwa ta miqe tsam tana fuskantarta gami da jiran isowarta.
Zubewa zatayi kaman yadda ta saba,saidai ayau hannu mammina ta saka ta riqe kafadar yalwa.
"Me ya faru?" Ta mata tambayar da dukkan zaquwarta nason jin abinda ya biyo baya.
Tamkar a gaban mammina din akayi komai haka yalwa ta tsara mata,sannan tayi qasa da kanta a yau din tana jin nauyi tsaiwa gaban mammina a maimakon durqushewa a gabanta suyi magana yadda ta saba.
Kamar saukar ruwa da daukewarsa gurin ya dauki shuru,sai kuma sautin siririyar dariyar mammina ta ratsa gurin.
"Zatasha guba?" Ta sake tambayar yalwa. Kai ta jinjina mata.
"Qwarai haka tace". Kai ta kuma jinjinawa.
"A gaban aqalla jama'ar da sukakai adadi nawa?".
"Hadimanta da yawa.....ciki harda ranta ya dade aisa da shehnaz". Kai ta sake jinjinawa.
"Hakan yayi kowa ya shiga lissafi.....ZATA SHA GUBA" Ta fadi kai tsaye tana sakin kafadar yalwa gami da yin taku uku baya don bada tazara tsakaninta da yalwa din.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Kai yalwa ta daga da sauri tana duban mammina din,abinda ya jawo hankalinta ta sake maida dubanta ga yalwa,da wannan murmushin da a idanu da yawa yake bayyana zallar kirkinta da karamcinta......saidai a wasu lokutan kebantattu,a wasu idanun a wasu yanayiyyikan yake zama baqin murmushi,kuma mafi munin murmushi.
"Zata sha guba kamar yadda tace.....nayi laifi?,ita ta zabawa kanta ko?" Ta qarasa maganar tana duban yalwa. Da sauri yalwa ta girgiza kai
"Ba shakka......zabinta kenan.....furucinta na qarshe kuma kenan". Dage dukka kafadunta biyu tayi tana takawa hankalinta kwance.
" Tamim za'a nemo?" Yalwa ta fada tana duban bayan mammina. Maganan yalwar taja hankalinta,ta tsaya can na wasu mintuna kafin ta waiwayo tana dubanta.
"Yaushe kika fara min hasashe da kutsa kai cikin wasu abubuwan da ba'a gayyaceki ko an nemi tajin ta bakinki ba?" Da hanzari tayi qasa da kanta,jikinta ya soma rawa a hankali,tana kuma tuna LAURATU a shekarun baya da suka shude......a shekarun daba ITACE AKAN WANNAN MATSAYIN BA LAURATU CE
"Afuwa nake nema.....kaina bisa wuyana.......ayimin aikin gafara" Ta fadi tana hade hannayenta guri daya,hannayen da rawa kawai sukeyi.
Ido sosai mammina ta zuba mata,tana karance da yanayin razanin data shiga. Iya wannan kawai ya gamsar da ita,saita juya a nutse ta fice ba tare data sake cewa yalwa komai ba.
Wani irin razanannen numfashi ta saki bayan ta tabbatar da fitarta,ta koma ta zauna dab'as saman mazaunanta tana sauke wani irin numfashi dake gauraye da tsoro.
Ba zata sake gangancin aikata abinda ta aikata a yanxun ba.....ba zatayi gangancin da abinda ya samu LAURE ya sameta ba,tanason LAFIYARTA tana son RAYUWARTA.
*Tofa!!!!.....ME KARATU?.....shin kana hasashen abinda nake HASASHE KUWA?.....kana iya hangen abinda nake HANGE KUWA?.....TUNANINKA YANA KAIWA INDA NAWA YAKAI?*
*SU WAYE ZASU MUTU?*
*WA ZA'A RASA?*
*WAYE ZAI TSIRA DA RAYUWARSA?*
*WAZAI TSALLAKE?*
*WAYE KUMA ZAI AFKA?*
*Kasan irin GIRMA da adadin TUGGU da MAKIRCIN DAKE DAURE da wannan masarauta kuwa?*
*Akwai wata BABBAR ALAQA dake tsakanin masarautun biyu......ETHIOPIA da AGADEZ*
*Akwai wani LULLUBABBEN SIRRI......akwai wata irin BAHAGUWAR SOYAYYA ME WAHALAR GASKE cikin labarin LU'U LU'U*
*WACECE MAMMINA NE?*
*WACECE SAFEENA?*
*WACECE MORSA SAFIYYA?*
*_NEMANSA TAKE CIKIN DUHU SAIDAI BATASAN YANA DAB DA ITA BA_*
*_GANI YAKE BA HURUMINSA BACE......BA DON ITA YA SHIGO MASARAUTAR AGADEZ BA......saidai bai san cewa itace RUBUTACCIYAR QADDARAR DATA SANYASHI SHIGOWA QASAR BA_*
*_BATA DAUKESHI A BAKIN KOMAI BA CIKIN RASHIN SANI TAKE MASA KALLON QASQANTACCE......SAIDAI BATASAN TARIN NAGARTAR DAKE LULLUBE DA WANNAN LU'U LU'UN BA.......WANI SIRR DAKE ZAMEWA ALFARMAR RAYUWARTA A GABA_*
*_TA YAYA SIRRIKA MASU TSANANIN NAUYI ZASU FARA FASHEWA?_*
*_TA YAYA ZUKATAN ZASU KAMU DA SOYAYYAR DA ZATA KAISU GA SADAUKARWA?_*
*_WACCE ALAQA CE TSAKANIN WADANNAN MASARAUTUN BIYU DA DUKKA BASUSAN DA ITA BA?_*
*_idan har kace a nan zaka dakata.....to tabbas zan maka jaje.......wannan itace shimfidaddiya kuma miqaqqiyar hanyar da zata kaimu ga wani SHINGE DAKE DAUKE DA WATA IRIN RIKITACCIYAR SOYAYYA DA WARWARAR MAQULLAN ASIRAI DAKE BINNE A QARQASHIN QASA_*
*KU KASANCE DANI A KASHI NA BIYU NA LABARIN*
*ina fata baku manta da ALMAZ ba???*
*NA GODE*
08187255862