Showing 114001 words to 117000 words out of 178317 words
wannan,idan kaga an cinyeta to d'ai d'aikun wasan da bata iyasu ba,a nan ma sakar musu take,bata fiya yarda a buga wasan da ita ba ballantana a cinyeta.
Ta saba koda yaushe nasara tana bangarenta,ba kowanne lokaci bane take daukan rashin nasara tayi haquri dashi ba.
"Nanniee tace tunda tazo bata ganki ba......tanata kuma aiken kizo,ko saqo bai sameki ba?" Shehnaz ta fadi idanunta akan akhnan tana zama kujerar dake facing dinta.
Sai data sha kusan rabin ruwan kafin ta miqawa barratu,tasa hannu da sauri ta karba tana rufe bottle din.
Blue eyes dinta ta zubewa shehnaz kafin ta janyesu tana rage musu girma.
"Zuwa kukayi daukan gawata kenan?,an gaya muku sultane yayi layya da nama na ne?" Ta fadi da wani irin taushi saidai a tsakiyar muryarta da zancanta zaka fahimci da yanayi na jin haushi take maganar.
A nutse shehnaz ta dauke dubanta daga kan akhnan din. Bata shirya gaya mata komai ba a yanzun,don zai zamana kamar qarin rikita mata lissafi ne kawai. Duk da akwai buqatar su zauna da ita,akwai buqatar sanin da saninta komai yake tafiya a sahel couture ko kuwa?.
"Me kuma yanzu akayi miki?" Shehnaz ta fadi duk cikin neman hanyar da zata gusar da fadin ainihin dalilin rashin tahowarsu akan lokaci ita da aisa din.
Kaman akhnan din ba zata daina kallonta ba,sai kuma ta zare idonta daga kanta tana jin bata da lokacin bawa shehnaz amsar komai.
Duk da cewa tare suke takawa suna kuma komawa zuwa cikin gidan amma ba wanda yace da dan uwansa komai,daga qarshe suka rabu a mararraba,akhnan tana wucewa sashenta gami da bawa buhaina saqon ta aikawa nannie tace mata zata shigo.
Kafin ta gama hutawa a rest room dinta tuni barratu ta hada mata lafiyayyen ruwan wanka kaman yadda suka saba. Ruwan wankan da kullum ake shiryashi hawa biyu. Na farko ruwan ganyan gwanda ne daya zame mata abokin rayuwa dana ganyen lalle,wanda akayi packaging dinsa ake mata order dinsa tun daga qasar china. Kowacce safiya ganyen gwanda shine abu na farko da ake dafa mata ta shashi a matsayin tea(anti aging ne,indai bakison tsufa ki gwada shansa kullum da safe,yana hana tsufa da gyara fata sosai).
Mayukanta na amfani dukkaninsu organic ne daga mayuka na asali irinsu man kwakwa da sukanzo a mazubi me kyau da tsada,a kuma batar masa da kamannin da zaka kasa tantance wanne irin mai take amfani dashi?.
Wani irin kyau na musamman fatarta take dashi,kaman yadda glowing din skin dinta yasha banban dana mutane da yawa,zaka tara mutane sosai baka samu me fata me sulbi da jan hankali irin nata ba,wannan yana daya daga cikin abubuwan da yasa take alfahari da kanta,take kuma sake kula da jikinta tare da bashi wani irin tattali da muhimmanci.
Mintuna talatin ta dauka kafin ta fito,ta zarce zuwa spa room dinta,dakin da aka ware na musamman da dukkan wasu nau'ikan gyaran kayan jiki da 'ya mace zata buqata dan qarawa fuskarta da fatarta kyau dama jikinta gaba daya.
Idan ka kalli dakin zaka dauka an wareshi ne don yiwa hamshaqan mata gyaran jiki,irin tsadajjen gyaran jikinnan me aji da kuma tsada da daraja saboda yanayin kayan aikin da aka ajjiye a gurin.
Wani abu ne daya zame mata jiki duk qarshen kowanne wata,tana ware rana irin wannan ta shiga body steamer machine ta tsuma jikinta sosai da sassanyan turarukan da batasan daga ina aka samar dasu ba.
(Asalin turarukan INCENSE BY KABO DAUGHTER,masu tsananin kama jiki da muhalli da wani irin tattausan qamshi,tasted and trusted,ba tallan molanka bane +234 803 211 9803).
Wasu awanni biyun ta sake batawa wajen maintaining jikinta da gyara,bayan ta shafe kanta da kwababben lalle shima da wasu sinadarai na musamman.
Dukka wadannan din sun zame mata jiki,ta tashi dasu tun batasan darajar abun ba a gurin mammina.......asali daga wajen morsa safiyya aka fara mata,saidai rashin sakewarta da morsa safiyyan ya sanya ta miqa komai ga hadimanta da kusan dukka rayuwarta da kulawarta ta lura a hannunsu take,su kuma suna rayuwa da ita ne cikin sassan mammina din.
Sosai mammina ta riqi bada umarnin yi mata gyaran hannu bibbiyu,har ta girma yazo ya zame mata jiki. Wannan ya sanya ta zama wata ta daban........koda cikin mata dubu nawa zata shiga zaka hangeta ta fita daban a cikinsu.
Glowing dinta,qyallinta da kyan fatarta daya cakuda da wannan sirritaccen kyan na asalin buzuwa ya sake zama wani abu na daban a gurinta,kwarjinin data debo daga jinin sultane shima ya qara zama ado a komai nata.
Tsaf birra ta tayata ta shirya cikin wata sassauqar doguwar riga ta wani irin nau'in material da aka saqashi daga auduga da zare me daraja da tsada. Ko yaushe shirinta yakan zama me jan lokaci,tamkar shirin amaryar da ake kan hidimar aurar da ita,ahi yasa har yau har gobe tafiyarsu office dasu aisa bai taba zama daidai ba,har gwara ma lokacin dawowarsu.
Sha biyu saura na rana,don haka ta qarasa dining room,buhaina ta ja mata kujera ta dora mata falin yanki ta zauna,sannan ta bara'atu ta matso tana dora mata wani yankin na musamman saman jikinta don kada wani sashe na jikinta ya baci,a lokacin tana duba kiran da yake shigowa wayarta.
Daya daga cikin directors dinta na kamfani ne,saidai a yanzun bata cikin mode na wani magana daya shafi kamfanin,tana jiran ta gama settling wannan issue din dake gabanta tukunna,don haka ta maida wayar ta kife tana miqa hannu ta karbi spoon din da bara'atun keta miqo mata.
Sama sama ta taba breakfast din,so samu tayi zamanta a kebantaccen balcony dinta,to amma kuma nannie ce.......tun jiya tasan da dawowarta,ta kuma aiko still an shaida mata,amma ta gaza zuwa,wata fuskar ai tafi gaban mari.
Kawai dai bataso ta yiwa zuciyarta fami ne,tasan kuma halin nannie qwarai,bata tsoron ta mutu balle tayi rai muddin akan gaskiya ne.
Sultane yana matuqar ji da ita,ita kadai ta rage masa cikin 'yan uwanshi hudi da yake dasu,su kadai suka rage a raye a duniya......don haka dukkaninsu da idanun matsayi irin na sultane suke kallonta.
Miqewarta kawai ya gayawa birra me take nufi,don haka da sassarfa ta koma ciki,ta kuma dauko mata sassauqar alkyabbar da bata da wani nauyi ta daidaita mata ita saman kafadunta,sai tafara takawa kawai idanunta akan wayarta ba tare da tace komai kota dubi kowa ba.
Yau din a cikin jininta takejin izza da kuma miskilancinta yana motsawa,don haka duk inda zata wuce,dukkan wanda Allah yayi yaga gilmawarta zubewa yake yana kwasar gaisuwa,duk kuwa da cewa basa samun damar ganin fuskarta,bara'atu da birra dake biye da ita suke amsa musu da sautin GODIYA TAKE.
Daidai lokacin da aisa ke cikin katafaren parlour din nannie din,wani irin parlour da wanzuwarka ta farko a cikinsa zai gaya maka zallar sarautar da mamallakiyarsa take da jibi dashi.
Bai cika kayan alatu ba,amma komai na cikinsa me daraja ne da janye hankali
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 55
___________________________
Bononza bononza https://wa.link/l1gcz8
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 6k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba pills shaki matse masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 11k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, da maganin sanyi wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne
Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 4k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka
Karku manta promo kwana 3 ne an kare insha Allah
Dukkaninsu suna zaune a qasan tattausan carpet din saqar hannu dake mamaye da parlour din,aisan na kashingide gefan nannie din,dankwalin kanta a qasa,yayin da waya ke riqe a hannun nannie da alama amsa wayar takeyi.
Sallamarta ta sanya dukkaninsu suka daga kai suna dubanta,aisa ce ta amsa tana tashi ta zauna sosai,suka hada idanu,sai akhnan din ta janye dubanta daga kan aisa din.
Ko batayi magana ba ta gama fahimtar abinda akhnan ke nufi......fushin takeyi da gaske,haushinta takeji,to amma a irin wannan lokacin da idan ta hau wannan qadamin fahimtar da ita yake zama abu me wahala,sai itama ta share kaman bata fahimci me take nufi ba.
A hankali ta tako zuwa gaban nannie a qasa kamar yadda ta samesu,ta zauna sosai tana tattare rigarta yadda zataji dadin zama,ta jingina da daya daga cikin kujerun alfarma da aka qawata parlour din,wanda sam sam basu ci guri ba.
Qamshin daya motsa daga jikinta bayan zamanta ya sanya aisa dubanta. Ko bata tambayeta tasan daga gyaran jikinta na wata wata ta fito,duk kuwa da cewa ita din gwanar qamshi ce,bata tunanin akwai wani company na turare da suka qware wajen fidda nau'ikan turaruka masu tsada da kama jiki da basusan da zaman akhnan din ba,amma wannan qamshin nasu khumras da lab lab din incense by kabo daughter daban yake. Wani qamshi ne da zai dinga saukar miki da nishadi,kaji zuciyarka tana wani irin sanyi da saukar da cikakken nutsuwa.
Har kullum kuma a koda yaushe,a duk kowanne wucewar daqiqa idan ta kalli akhnan mamaki take qara bata.
Da gaske ne.....kamar yadda take fada,kamar kuma yadda ta saba fadi.....bata rasa komai ba.......Allah ya bata dukkan wata cika da siffa da kowacce diya mace zataso ta mallaka......Allah ya bata wasu irin qualities da kebantattun abubuwa masu yawan gaske.....a zahiri a iya abinda idanu ke gani bata da wani sauran naqasu ko buqata........amma ta kowace fuska da kowa ke iya hange mata tana da buqatuwa zuwa AURE......abu dayan nan da har yanzu bata gamsu da cewa haka yake ba.
Har yau har kwanan gobe,har jiya da yanzu babu wani dalili guda daya da take basu ko zata basu kan haka,abinda kuma har a yanzun yake bawa aisa mamaki kenan da daure mata kai.
Wannan dalilin guda daya bai kai mizani ba.....QASAITARTA DA IZZARTA da kuma surki na GIRMAN KAI a wasu lokuta,basu gaya mata daidai din cewa......su kadai sun isa su mallake su kuma mamaye gami da ci gaba da riqe mata rayuwa ba har izuwa ga bigiren da ya dace da ita.
Hankalinta yana a kan waya,amma kunnuwanta na wajen nannie. Sai data zauna din sosai sannan ta fuskanci da HAIRAAN take wayar.
Sau da dama takan manta da hairaan din shaf cikin mutanen dake existing a rayuwarsu. Tana mantawa da ita kwata kwata cikin babin rayuwarsu. Duk da kasancewar hairan din mutum me wani irin zuciyar zumunci......son duk mutumin daya rabi rayuwarta,da kuma girmama babba,wannan yayi sanadin da ta maida nannie qanwar mahaifinta kuma kaka a wajen ta ta halak malak.
Idan hairaan tana nan,ba zaka taba banbance wata haifa ba tsakanin aisa da ita,idan hairaan tana nan,zaiyi wahala ka dauka morsa safiyya ce mamanta ba nannie ba,idan kaga sabanin hakan,nannie din bata nan ko kuma tayi wani balaguro.
"To Allah ya kaimu......ya nuna mana cikin amincinsa da yardarsa......ma sha Allah......ga biftu" Ta fada tana miqawa akhnan wayar kai tsaye.
Wani abu ne da batayi tsammaninsa ba,ba wani magana ko waya suke da Tante ba(kamar yadda falaak ke kiranta dashi),duk da hairaan din tana da wani irin kirki da jan 'yan uwanta a jikinta.
Ko yaushe fuskarta shimfide take da fara'a,kamar yadda lokaci lokaci takan duban akhnan din koda ta watsapp ne,ita dince bata damu da duba hakan ba. Idan ta nemeta shikenan,idan bata nemeta ba koda tsahon shekaru nawa ne ita din bame damuwa ta nemeta bace.
"Biftu na" Hairaan din ta fadi da salon kirkinta da kulawarta kwatankwacin wadda take nunawa falaak,saidai har yanzun ita din ta kasa jin haka har zuciyarta. Kamanni da kuma murya na hairaan dukkaninsu ta debo na morsa safiyya ne,wannan dalilin ya sanya kowanne qoqari na kawo kusanci tsakaninsu yake wargajewa a zuciyar akhnan.
"Bonjour" Ta fada a taqaice da muryarta da tayi wani sanyi a yau da yake nuna batason magana.
"Bonjour,comment ça va?" Ta maidata mata muryarta cike da nishadi.
"Alhamdulillah" Ta sake amsa mata bata wani jin armashi a gaisuwar.
"Fatan komai lafiya......ya sahel couture"
"Alhmdlh" Ta sake amsa mata,don tana jin bata da amsar data wuce wannan.
"Allah yayi jagora........muna kusa da zuwa gida in sha Allah,kafin qarshen shekarar nan". Idanunta ta lumshe ta kuma budesu,tana jin bata da wani hadi sam da wannan labarin.
"C'est bon" Ta sake fadi a taqaice.
"Ma sha Allah,Nous nous reparlerons bientôt in sha Allah(zamu sake magana nan kusa in sha Allah).
Zare wayar tayi kawai daga kunnenta tana ajiyeta kuda Nannie.
A nutse nannie ta kalleta tana qoqarin karantarta,sai ta janye idanunta,cikin nutsuwar nan dake cakude da qasaita tace.
"Barka da warhaka......" Sai da nannie din ta gyara zamanta,tana kuma karantar yanayin boyayyar damuwa qasan ran akhnan din sannan ta amsa.
"Barkanki dai......."
"An dawo lafiya?,Allah ya karbi ibada"
"Ameen summa ameen" Nannie ta amsa can qasan ranta cike fal da maganganu,saidai yanayin da take karanta tattare da akhnan din yana nuna mata abubuwa da yawa. Da yawan yawan abubuwan da take karanta din mamaki suke bata. Wanne irin mugun tunani ne a ranta har haka da fidda mijin aure yake zame mata babban abun tashin hankali ko kuma damuwa a tattare da ita?.
"Abubuwa da yawa sun faru sanda bana nan biftu.......mene damuwarki ne?,akwai wani abu ne daya kamata a sani wanda baki fadeshi ba a zahiri?" Ta furta da sigar lallashi,tana tunanin ta wannan hanyar zata samu kamo bakin zaren damuwar akhnan din.
Blue eyes din nan nata ta juya kadan tana janyesu cikin jin gajiya da yi mata maganar kowanne d'a namiji. Tana ganin basu kai matsayin da rayuwarta zata fuskanci takura irin wannan har haka ba......tana da 'yancin da zatayi rayuwarta ita kadai,don bataga ta inda hakan ya sabawa addini ba muddin tana da qarfin zuciya dana gwiwar rayuwa ita daya.
"Ina saurarenki" Nannie ta sake fada tana bata dukka hankalinta. Tsam aisa ta miqe da zummar basu guri,amma sai Nannie din ta zube mata idanunta.
"Dawo ki zauna......kunfi kusa da ita akan kowa,qilan akwai wani abun da bamu san dashi ba,ku zaku fimu sani......qilan akwai wani abun da ita ba zata iya fada ba,ku zaku fada" Tayi maganar cikin maida hankalin nan nata akan komai.
Wuya ta karyar tana duban Nannie din,idanunta na nuna dukka gajiyawarta.
"Nannie.......dama dai baki sani a wannan batun ba,don Allah kice na tafi" Ta fada tana burin hakan,don daga ita har shehnaz bata tunanin akwai wanda ya yiwa akhnan fahimta ta haqiqa akan wadannan tsare tsare nata.
"Aisa!.....zama nace