Showing 84001 words to 87000 words out of 178317 words

Chapter 29 - LU'ULU'U COMPLETE

riga tas yayi amfani da ita daga cikin rigar saman,sai dogon wando shima da yake mahadin kayan a jikinsa. Kyakkyawan nadi ne a kansa da yayi kamanceceniya dana buzaye,saidai akwai banbancin salon nadin da kuma yanayin yadin da baikai na buzaye kauri ba,saidai ya lullube ainihin kyakkyawan fuskar nan,sai zagayyayun manyan idanunsa da hancinsa me tudu daya bayyana ta cikinsu.

Da cikakkiyar sallama ya shigo gurin,sallamar data maida kowa cikin hankalinsa suna hada baki wajen amsawa,sannan suka tattara masa hankalinsu.

"Ku zauna" Ya fada yana nuna musu kujerun da hannunsa. Sai da kowannensu ya zauna sannan shima ya janye pillow din dake saman kujerar da tafi kusa dashi ya zauna. Wani irin zama daya sanya dukkaninsu kallonshi,kusan ya saba da zaman ba kuma don yana nufin izza ko iko ba,aah.....kawai ya zame mishi jiki kusan a dukkan wani yanayi da zaiyi magana me matuqar muhimmanci,a gida ne ko a office.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITAπŸ‘‘*

*HUGUMANKU CE*✍🏽


πŸ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*πŸ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 39
_________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*

*Assalamualaikum*

*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*

*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*πŸ‘˜πŸ₯»

*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin Aminci???*

*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*

*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana goma KACAL!✌🏽*

*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*

*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*πŸ™ŒπŸ½
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*

*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*

*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT da yardar Allah*

+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791

https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
___________________________





Salawi beeno da hambal suna cikin hadimansa mafi kusaci da mooti yace dole su kasance a tare dashi cikin tafiyar. Yace sam bai yarda ba,bazai kuma bari ya tafi gayarshi wata qasa da sunan aiki ba ba kowa a tare dashi. Duk da tsarin aikinsa,wani sirrintaccen aiki da ba kowa yasan yana yinsa ba.......da yawa suna masa kallon fitaccen kuma gawurtaccen yariman dake kawo duk wani nau'ikan turaruka masu tsananin tsada daga india da kuma daular larabawa wato dubai. A zahiri shine kasuwancinsa,wanda yayi matuqar karbarsa da wata irin nasara da bai taba kawota a kanshi ba. Ya zabi maida hankali a kanta ne saboda tsananin soyayyarsa da qamshi da kuma turare,abu na biyu kuma ya dauke hankulan mutane daga laluben meye aikinsa da sana'arsa?,sai gashi harkar ta maidashi wani boyayyen attajiri da da yawa mutane basusan waye mamallakin manyan kamfanunuwan turare 3stars guda uku daya mamaye Ethiopia da dukka qasashen africa ba.......hakanan basusan waye ainihin mamallakin gonakin nan masu Tsananin girman dake gigita manoma ba,wadanda suke noma ganyan turarukan da ake zuwa a siya a fiddasu qasashen qetare ba.

Takai ta kawo ganyayyakin nau'ikan turaruka da yawa ana nomasu cikin manya manyan gonakinsa guda goma sha biyar da yake dasu,saidai ya saida a kuma sarrafa masa zuwa turare da nau'in qamshin da kamfaninsa na 3star kawai ke da irin wannan qamshin.

Ba huruminsu bane susan abinda ya kawoshi agadez,amma yasan dole akwai sharuddan da zai gindaya musu su kiyaye karsu bata masa aiki,don haka bai soma dasu hamdii ba juniors dinsa a hukumar,sai ya fara dasu salawi.

"Ba kowacce tafiya bace take buqatar dogon bayani sharhi ko fashin baqi ba......munzo agadez kamar yadda kuke gani. Baquwar duniya ce a wajenmu,duniyar da ba tamu ba. Baqin mutane da kuma baqin al'adun daya zama dole kowa a cikinku yasan ya suke?,ya kuma zaiyi mu'amala dasu". Zamansa ya gyara yana soke yatsunsa cikin na juna.

"Kamar yadda nake yawan fada muku a jimma kuka kasa aiki da abinda nake fadi din,a yanzu ya zama tilas kuma wajib kuyi aiki da wannan......don nan din ba jimma bane......kuma a nan duk wani sabawa doka tawa hukunci zai iya hawa kan kowa a cikinku" Motsawa kowannensu yayi cikin mamakin furucin daya fada din. Mutum ne me tsananin uzuri,kauda kai da kuma sassauci sau da dama. Ba zasu iya tuna yaushe yayi hukunci a karan kanshi ba akan abinda ya zamana an masa laifi ne,ba abinda ya kasance cikin haqqin Allah da manzonsa ba.

Kai ya jinjina musu a nutse,alamun yana nufin abinda ya fada din.

"Ordinary mutum nake kaman kuwa koda a jimma ne......inason kusa a ranku a yanzun da muke agadez. Zan iya ganinku na wuceku kamar ban sanku ba,kamar yadda kuma zaku wuce ni kamar baku sanni ba idan ba ni na buqace ku ba. Ba batun obbo......ba batun prinsii.......a agadez sheik haisam zallah nake......idan kunso ma kuce haisam sak". Duban junansu sukayi su dukka shidan,bawai iya su salawi kadai ba,hatta dasu hamdii maganar ya musu nauyi.

Sosai ya tsaresu da kaifafan idanun nan nasa,yana sake tabbatar musu da abinda ya fada din haka yake nufi.

"Zakuyi rayuwarku da duk kalar 'yancin da kukeso.......saidai bazan lamunci sabawa dokar Allah ba,a duk sanda nake buqatar ku zan sanar daku hakan" Shuru sukayi dukkaninsu suna juya maganganunsa. Wacce irin rayuwa zasuyi haka cikin agadez din?,ta yaya zasu iya kiran sunansa haka gatsal?,ta yaya zasu rayu dashi a gurabe daban daban ba tare da bashi kariya ba kaman yadda mooti ya buqata?,ya zasu iya banzatar da wofantar da amanar mooti?,ya zasu iya yin nesa da baya baya da prinsii din nasu.....wanda ya kasance abu mafi soyuwa a zukatansu?,abu me girman daraja sosai a idanunsu dama qasarsu?.

"Kowacce kalmata guda daya tana da gurbi da muhalli.....kowacce kalmata guda daya rubutacciya ce kuma me amfani.....ya kamata ku kiyayesu da kyau,idan akwai buqatar wani abun kuma kuna iya sanar da abdii.....zaku iya tafiya" Ya furta yana nuna musu hanya.

Jikinsu a sanyaye suka miqe suna nufar qofa har suka kammala ficewa.

"Don Allah obbo kada ka kafamin kalar sharadin daka kafa musu.......na rantse bazan iya kiyayewa ba" Abdii ya soma fada tun kafin haisam yakai ga cewa komai.

Wani lallausan murmushi da haisam bai shirya yinsa bane ya subuce masa. Yayi qasa da kansa yana dan jan hancinsa kadan kafin ya daga kansa yana duban abdii da kyawawan idanunsa.

"Da gaske karaya nake gani cikin idanunka abdii" Ya fada yana dage cikakkun girarsa dukka biyun. Narai narai abdii yayi yana dubansa.

"Ai nace maka bazan iya ba obbo.....don Allah karka sakani cikin sharuddansu" Kai kawai ya girgiza sannan ya maida dubansa kansu hamdii.

"A cikin gidannan ko a masaukinku ne kawai na sanku a yayin da muka kebe......amma a waje baku sanni ba ban sanku ba....."

"Baku sanshi ba bai sanku ba" Abdii ya furta yana gyara maganar gudun kada ayi jam'i dashi. Idanunsa haisam ya watsa masa,saidai still har yanzu yana ganin wannan tsoron tattare da abdii.

"Will you keep quite?" Ya fada a nutse,sai abdii ya kama bakinsa,ya kuma koma gefe yana jin yadda haisam ke tsara komai tsakaninsa dasu hamdii cikin salo da cikakkiyar qwarewar aiki har suka kammala.

"Kowa ya zaman kusa da na'urarsa,a kowanne lokaci xan iya buqatar wani abu daga gurin dayanku.....ku sauka lafiya" Ya sallamesu sukayi saluting nasa suka fice.

Shuru dakin ya dauka,sai haisam din ya miqe a nutse yana takawa da nutsuwar nan tasa.

"Inason naga yadda garin yake.......inason insan wani abu ko ba yawa game da gidan sarautar agadez" Wani farinciki ya kama abdii,ya miqe da sauri yana jin dadi yana ratsashi. Koda haisam bai fadi a fili cewa zai zamana na hannun damansa ba,bawai boyayyen amini ko majibancin lamarinsa ba......yadda ya zabeshi a yanzun a matsayin wanda zai rakashi zuwa cikin gari kadai ya bashi amsarsa.

Kallon haisam kawai yakeyi,yadda yayi shiga ta cikakkun buzaye,tun daga tufafi zuwa rawanin kansa. Satar kallonshi kawai yakeyi,har sai da haisam ya gaji da kallon ya damqi wuyansa sanda suka miqe sosai kan titinsu.

"Wannan kallon is too much fa,ba mace bane kai,namiji ne" Cikin boye dariyarsa abdii yace.

"Bansan yaushe kasan al'adar mutanen nan ba,har ka iya nadinsu da shigarsu obbo......" Kai ya girgiza

"Ina mamakin yadda kuke daukan aikinku bada muhimmanci ba......a lokacin da kake wata sana'a,ya kamata ka zama qwararre a kanta......ka birkida zuwa dukka launi da kalar da akeso ake kuma buqatar ka zama" Kai abdii ke gyadawa cike da gamsuwa,don sosai ya fahimci abinda haisam din ke nufi.

"Kuma shigar tayi maka mugun kyau obbo....."

"Kama bakinka abdii" Ya fadi masa yana duban hanya sosai sanda yake hango wasu baqaqen motoci masu tsananin sheqi suna wulwula gudu saman titin.

Kyawawan motoci ne guda hudu da dukkaninsu suke kama da juna,saidai guda daya a cikinsu tafi Kowacce kyau da girma da kuma alamun tsada.

Sosai haisam ke qoqarin nazartar motocin,har zuwa sanda suka zo suka gilmasu da wani irin gudu.

Kadan ya waiwaya yana kallon plate number din dake manne a bayan motar,wanda ya fuskanci dukka iri daya ce.

PRINCESS AKHANAN shine abinda ke rubuce a kowacce mota,sai lambobi daga daya zuwa hudu.

Kansa ya dauke a hankali,yana duban abdii daya matso da zummar kade masa 'yar qurar da ta hau jikin kayansa. Da idanunnan nasa masu nauyi ya dubi abdii,magana kuma yayi masa da idanu wadda ta sanya abdii din janyewa baya da sauri,sai ya miqa nasa hannun yana kade qurar.

"Khadeeja Muhammad hammud" Maheer ya fadi yana duban titin da motocin suka wuce,wanda haisam ya fahimci ba wata mota data biyo bayan tasu har sai bayan da suka wuce din,abinda yake alamta masa kamar wani tsararren abune da dukka masu ababen hawa a garin agadez suka saba dashi lokaci irin wannan.

"Zuciyar sultane ce.....diya qwara daya da sultane yake ji da ita,diyar kuma data zama wani abu mafi girman daraja da tsada da sultane yake dashi a duniya" Idanu haisam ya lumshe sannan kuma ya budesu,yana jin maganganun Maher din a wani muhalli da sam bai gane masa ba.
(08187255862 lu'u lu'u paying)

"Idan kace ita daya ya mallaka bakayi laifi ba.....duk da a zahiri diyoyinshi guda biyu ne.......sangartacciyar 'yar gatar da ake tattalinta da dukka abinda takeso.......da kuma dukka abinda taga dama takeso ya wanzu a yadda take muradi. Tana hukunci tana alfarma,tana kuma zartarwa dukka a qarqashin nata ikon,saidai wani abun mamakin kuma.......ba wani wanda zai iya baka cikakken siffa da kamanninta,don ganinta ido da ido a gurin jama'ar yankin nan bai zama abu me sauqi ba".

Wani abu haisam ya hadiye a hankali yana qoqarin faffasa kalaman Maher,yanason kawo daidaito tsakanin maganganunsa dana Ousmane.

"Akwai maganganu da yawa a kanta ga wadanda ke rayuwa kusa dasu.......tana da wata irin izza girman kai da alfaharin daya zarta na mahaifinta.......tana da tsare tsare da dokokin da muddin zaka rayu tare da ita dole ka kiyayesu.......har ila yau......ita daya ce tilon macen da take iqirarin har a yanxu ba'a haifi nau'in namijin da zai dace da rayuwarta ba.......har yanzu babu namiji irin nau'in ajinta....." Idanu abdii ya waro yana duban haisam da gabansa kawai yake kalla,hankulansu suna rarrabuwa kashi kashi. Yanayin unguwar da suke tafiya a cikin ta,yanayin mutanen dake kai kawo jifa jifa,sai wani dan qaramin kaso na hankalin nasa daya miqa akan maganganun Maher. Dukkan alamu sun tabbatarwa abdii hankalin haisam baya kai dari bisa dari,sai ya janye idonsa daga kan haisam din ya mayar kan Maher yana mamakin me ya hana wannan baqon labarin da yasha banban da labaran da suka saba ji da gani su dauki hankalinsa?.

"Amma ita din wacce irin halitta ce ita?......yaya take?......wani irin launi gareta da dukka mazan duniya basu tsaya a mataki da cancantar samun aurenta ba?".

Sosai shima Maher yake da nutsuwa,irin nutsuwar da zai wahala ka fuskanci shi din daya daga cikin ma'aikatan NISS Ethiopia ne.

"Mutum ce kamar kowa......amma nasha jin hirarta a bakunan mutane a guri daban daban da lokuta daban daban.....mutum ce amma tasha banban da tarin Mata........tana da wani kyau kwarjini da kebantattun abubuwa da naji suns cewa ta cancanci zaben duk kalar mijin da takeso.....ko waye ko wanne iri ne......"

"Meye alaqar koya karatuna da yaran sarki da ita?" Yayi tambayar ta kai tsaye ba tare daya kalli Maher ba,don yanason banbamce wasu abubuwa da baiso su zama cikin qurataccen lokaci. Uwa uba ya gaji da jin soki burutsun bayanai a kanta......abu guda yakeson tantancewa shine.......ta kasance bata cikin mutanen da zasu fado hanya ko gonarshi.

Girman kai......izza da raina mutane,wasu dabi'u ne da yanzu yanzu suke raba tsakaninsa da kai. Wasu dabi'u ne da ya tsana yayi matuqar yin hannun riga dasu.

"Tana Niamey tana gudanar da kasuwancinta.......itace CEO na SAHEL COUTURE" A nutse haisam ya maimaita sunan kamfanin can qasan ransa.

Kalman CEO babbar muqami ne ko matsayi a kamfani. CEO yana tsaiwa akan komai da komai daya shafi cikin kamfanin dama wajensa......to amma ta yaya tana da wannan matsayin fuskarta ta zama wata boyayyar aba?.

"Zanso naga wannan......." Abdii ya soma fadi,saidai baikai ga qarasawa ba haisam din ya tari numfashinsa

"Abdii" Ya kirashi still idanunsa yana kan hanya.

"Obbo" Ya furta yana maida hankalinsa jikinsa.

Daga yanayin haisam Maher ya fuskanci baya buqatar hirar......hirar kuma bata dace da mode dinsa ba,don haka bai sake cewa komai akai ba,har zuwa sanda sukayi doguwar tafiya sosai.

"Ina buqatar qarin sani akan komai daya shafi cikin gidan......sauran zan bincika da kaina" Ya fadi yana tattara hankalinsa guri daya.


β˜…β˜…β˜…Cikin girmamawa kowacce qofa ta gidan da masu tsaronta mataki mataki take motsawa tare da budewa don samun damar shigar motocin dake dauke da akhnan din cikin ainihin ginin gidan.

Basu tsaya ba har sai da sukakai gurin ajiyar motoci na musamman na cikin gidan,wanda ke dauke da tarin motocin sultane dana mammina da ragowar na akhnan din,harma dana morsa safiyya wanda ba kasafai ta fiya hawansu ba.

Tun kafin motocin su kammala tsaiwa take iya hangen mammina din. Tsaye cikin adon nan nata da kowanne lokaci yake qara nuna ita din matar sarki ce.....matar babban mutum me alfarma ta daya sultane muhammad hammud. Iya suturar dake jikinta kawai wani babban jarinne a gurin dubbunnan mutane,daga bayanta kuma hadimanta ne su biyar,ciki harda yalwa ta hannun damanta.


zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITAπŸ‘‘*

*HUGUMANKU CE*✍🏽


πŸ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*πŸ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 40
___________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*

*Assalamualaikum*

*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*

*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*πŸ‘˜πŸ₯»

*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin Aminci???*

*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*

*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana goma KACAL!✌🏽*

*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*

*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*πŸ™ŒπŸ½
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*

*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*

*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT da yardar Allah*

+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791

https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
____________________________



Dauke idonta tayi tana sauke ajiyar zuciya,jikinta duka a mace yake kuma a sanyaye,saboda har yanzu bata da tabbaci ko tartibin abinda zai faru da ita.

Alamun bude mata murfin motar ne ya dawo da hankalinta jikinta,ta fidda numfashi me nauyi tana jin yadda zagin gidan yaketa wasata

"Gaba salamun baya salamun......barka da isowa zuciyar sultane.....tauraruwar qasar agadez......me alfarma 'yar masu alfarma,wallahi ganinki kadai ya ishi bawa alkhairi,zamanki tare da mutum alfarma ce,qarin daraja a wajensa,sukari me farin alkhairi,bango majinginar bayi........me kyauta da hannun damanta hagunta bata sani ba,me darajar da babu ta biyunta.....ga khadijatul kubra". Sau tari yadda zagin ya iya tsara da jero kalamai a kanta abun yana matuqar burgeta,uwa uba kuma ba wanda yakewa sai ita daya,koda sultane kuwa baya yiwa,ita kadai ya tsayawa yake yiwa,shi yasa sosai take sakar masa kudi.

Mutum ce ita me amana,meson kuma mutum me amana. Wannan ya sanya zai wahala kayi magana da ita ma ka jita a gurin koda su aisa ne,amanarta da zallar miskilanci da izzarta ma ba zasu bari ba. Amma a yau din sai takejin kirarin nata yana damunta har cikin kanta. Ta daga ido tana duban wanda ya bude mata motar,mammina ce da kanta,ta miqa mata hannu kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login