Showing 126001 words to 129000 words out of 178317 words

Chapter 43 - LU'ULU'U COMPLETE

suke zame masa......amma kaima kaji tsoron Allah,ka manta ma'eesha?.....ka manta khansaa?,ka manta batul......"

"Qyaleni haka" Omari ya fada da sauri yana boye dariyarsa,sai kawai haisam din ya dauke kai yana qyale Omari din kamar yadda ya buqata.

Ba wai shi kadai ba,ba kuma Omari kadai ba,kusan dukkaninsu su bakwai dinnan wani baiwa garesu na musamman. Sun hada wani irin qualities ne da ba kowa Allah yake baiwa shi ba,wannan dalilin ya sanya suka zama masu nuna godiyarsu ga Allah ta hanyar kame kansu da kuma kare mutuncinsu da mutuncin iyayensu dama na addininsu gaba daya.

"Duba nan" Omari ya fada yana jiye system din a tsakiyarsu.

A hankali haisam ke duban bayanan daya fitar masa din yana saurarensa.

"Wadannan guraren,suna daya daga cikin guraren da na samu information gurine na haduwar jama'a masu yawa kuma mabanbanta a qasar nan da garin nan,sannan a nan ne kadai a bincike na za'a iya samun wani da yasan yaren oromo,ko yake yarawa ko kuma ya taba jinsa. Koda taba jinsa yayi zai samar mana haske gurin kusantar samun inda TURAAD ya boye a qasar nan". Shuru haisam yayi yana ci gaba da duban bayanan,kafin a hankali ya janye idanunsa.

"Ka hada dukka bayanan ka turamin ta e-mail,sannna ka turawa abba muhammad dawud.......amma ban gamsu da hakan ba". Ido omari yadan zuba masa. Ya iya magana a dunququne da qananun jimloli,mai hankali yana iya faffasata yayi dogon sharhi a cikinta. Duk abinda ya fadi yana da hujja,kuma akwai dalilin da yasa ya fadi haka.

"Me yasa kace baka gamsu ba?".

" A nan unguwa ko nan garin da muke tabbas akwai yaren oromo" Ya fadi cikin harshen turanci. Idanu Omari ya fidda sanda motar ke gangarawa don tsaiwa a gurin da haisam din yace duka satinnan a nan zasu dinga tsaiwa su jirashi,idan akwai yuwuwar sauya guri cikin satin zai fadi musu.

"Ka bari na dawo......ka jira abeer.......ka gaya masa yau su sauya unguwa,su matso maqotan unguwannin da suke kusa da nan,a yau dinnan basai gobe ba......idan na dawo zamu qarasa magana" Ya qarasa fada yana bude murfin motar gami da sanyo qafafunsa waje bayan ya tabbatar ba gilmawar kowa.

Da kallo Omari da yayi zaune cikin motar yake binsa dashi. Qaramin murmushi ya subuce masa a hankali.
(08187255862 lu'u lu'u)

Komai nasa yana nuna sarautar dake zagayawa a jininsa,tsananin nutsuwarsa da kamun kansa,takunsa kadai yasha banban dana maza da yawa,gashi kuma cikin gidan sarautar wasu. Muddin akwai mutane irinsa cikin gidan,muddin akwai mutane masu kaifin hange da dogon nazari irinsa,to babu abinda zai hana su kasa gasgata zukatansu akan cewa shi din malami ne kawai......malamin da zai koyar da yara kawai a biyashi.

A nutse yake karantar kowanne sauyawar motsi da yanayi na gidan. Yana wuce kowacce qofa....kowanne shinge yana fahimtar kamanceceniyar yanayin jiya dana yau.

"Shalelen sultane.......akhnan yau zata sake baqon da zai zama final choice dinta dana mahaifinta". Maher ya furta qasa qasa wanda yake biye da haisam a nutse. A qofar shiga gidan suka hade da Maher din.

Sarai yaji abinda Maher din yake fada amma kuma baiko waiwayo ba bare ya alamta ya jishin.

Abinda ya faru jiya sai yaji ya dawo masa fes cikin kanshi. Baya ko shakka yarinyar jiya ce,baya kokwanto ita din ce wani mara sanin ciwo da darajar kan zai sake taka qafarshi muhallinta. Tsaki yakeso yaja,amma yana ganin ba wani dalili na yin hakan,matsalar wasu ce.....matsalar cikin gidan.....matsalar mutanen dake zuwa gurinta.

A iya saninshi,babban abu guda daya dake janye hankalin nutsatsen namiji zuwa ga mace shine nutsuwa da kuma tarbiyyarta. Bai ganta a ido ba ballantana yasan nutsuwarta,amma kuma duk inda nutsuwa take tana damfare da tarbiyya.......tarbiyya da bayajin akwai sauran b'urbushinta a gurin.

Har qasan ransa yakejin idan ya fadi hakan baiyi laifi ba,don ba tarbiyya a muhallin da d'iya mace zata iya daga hannunta ta mari d'a namiji.....baligi. Ya jima baiga wani abu da bai shafeshi ba wanda yazo yayi masa tsaye a rai irin wannan ba. Besan dalilin da yasa wannan din ya zame masa karan tsaye ba,ya tsaye masa a rai,ya kasa cireshi.

"Ya isa" Ya tsawatarwa da zuciyarsa cikin don zare abinda bai shafeshi ba daga ransa. Ya dinga takawa a nutse cikin kebantaccen masallacin da zummar bada faralin sallar la'asar kamar kullum,kafin yakai ga qarasawa cikin makarantar.

Ya lura da yadda shiga ainihin cikin masallacin yau ya zama wani kebantaccen abu ga wasu kebantattun mutane,amma hakan bai hanashi takawa a nutse ba yana wucewa ciki abinsa,ba tare da jiran izini ko dama daga bakin kowa ba.

Su kansu basusan dalilin da ya sanya suketa dage masa kowanne shinge yana shigewa ba. A cikin jikinsu ba wani me zarrar dakatar dashi ko masa bayanin yau dinma sultane zaiyi sallah ne cikin masallacin tare da surukinsa.

Akwai ragowar mintuna da suka rage,wannna ya sanya ya zauna cikin sahu a nutse,ya sanya hannunsa yana fidda wani dan qaramin littafin daya soma dubawa daren jiya bai kammala ba,ya bude ya fara dubawa a nutse,wannna ya sanya kusan duka abinda ke faruwa cikin masallacin bai sani ba.

Rufe littafin yayi a hankali sanda yaji alamun fara daidaita sahun sallah,ya miqe a nutse yana gyara cloak robe dinsa.

Satar kallonshu Maher yayi,har qasan zuciyarsa burgeshi haisam yake sakeyi. Yayi imanin inda wani ne Allah ya bashi mulki kudi da qarfin iko irin haka,bazai taba aiki da hukumar national intelligence ba,saidai su suyi masa aiki. Inda wani ne....bazai taba yarda a jashi ko a jagoranceshi sallah ba......saidai shi yaja. Yana da tarin ilimin da iya zamansu na kwanakin nan Maher ya fahimta. Baya daukan kansa da nisa,shi yasa da yawa wadanda ke tare dashi basusan irin ilimin da Allah ya hore masa ba.

Ranar daya fahimci yarukan da yakeji ya jima yana juya abun. Tabbas rayuwa kowa da irin nashi nasibin. Ya iya French ya iya English,ga amheric ga oromo ga larabci,sai hausa da bata kama bakinsa sosai ba,don bashi da sabga me yawa da ita. Bai bari ya gane yasan ya iya duka yarukan ba,don ya fahimci kamar yana sirranta hakanne.


zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽


💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


PAGE 60


"Salamu alaikum" Yaji sautin sallama daga gefan damansa. Idanunsa da suka rusuna kadan ya daga yana dubansa na wasu sakanni sanda yake sakar masa murmushi,shima sanye cikin cloak robe da zaunennan rawanin da kana dubanshi kasan qwararru ne suka zauna suka masa wani nadin burgewa saman kansa.

"HAKEEM" Sunan yazo kansa lokaci guda,sai yayi qoqarin daidaita fuskarsa yana rage mata daurewar da take dashi tun a dazun,daidai sanda hakeem din ke qoqarin masa bayanin yana tunanin bai ganeshi bane,don ya fahimci kadan daga halayensa na rashin son shiga sabgogin da basu shafeshi ba,saidai shikam ya jima yana burgeshi,tun daga wancan ranar a Riyad har yau ya kasa mancewa da fuskar sheikh din.

Musabaha sukayi da juna,haisam ya zame hannunsa,don babu dogon magana kasancewar an fara tayar da iqama.

Cikin mintuna bakwai suka kammala sallar. Hakeem na gefansa bai tashi ba yana nashi azkar din na bayan sallah.

Ya gane hakeem,a wata musabaqa da suka gabatar a Riyad akan wasu kebantattun litattafan addini daga dukkan qasashen duniya. Kwanaki uku sukayi a wani kebantaccen hotel,wanda kusan duka haisam dinne ya dauki nauyin komai,amma kasancewarsa mutum wanda baison asan yayi wani aiki na alkhairi gudun shigar riya ayyukansa,sai bai bada dama ga kowa yasan shi ya dauki nauyin komai ba.

Hakeem yana daya daga cikin wadanda suka tsaya takara......a lokacin haisam ya shiga sahun alqalai na gasar. Tabbas a lokacin yaga matuqar qoqarin hakeem,ya kuma yaba sosai da irin hazaqarsa da yadda ya iya fadin kowacce amsar tambaya daga masu tambayar,duk da daga qarshe ya samu zuwa na biyu ne maimakon na daya,saidai a wajen yin jawabinsa abun ya qayatar da haisam,har ya sanyashi yadan murmusa kadan. Yadda Hakeem din ya bayyana shigarsa qasar kawai nasara ce basai an ayyanashi ba,ya kuma miqa kyautarsa da girmamawarsa dukka ga mahaifinsa,ya kuma ware guda daya yana sake karbar abun magana.

"Inaso a bani dama na miqa wannan kyautar guda daya data rage,zuwa ga wani mutum daya da daga yau nakejin ya zamemin wani abun kwaikwayo koda daga nan ba zamu sake haduwa ba SHEIKH MUHAMMAD HAISAM" Iya sunan da haisam din yayi amfani kawai dashi kenan,gudun bayyanuwar identity dinsa. Yana jin dadi idan ya shiga guri yayi mu'amalolinsa da rayuwarsa cikin privacy ba tare da an fahimci waye shi ba. A rayuwa yana jin ba kowanne lokaci bane......ba kuma a kowanne guri bane ya kamata asan wayeshi ba. Wannan kyautar ta Hakeem taxo masa a bazata,saidai abinda yayi masan bazai manta dashi ba.

Sosai Hakeem yaso karbar number haisam,saidai hadimansa basu bawa hakeem wannan damar ba,sun rabu yana yawan tuna haisam din,har yau daya ganshi cikin ba zata.

Sanda haisam ya kammala addu'o'insa ya shafa a nutse,hakeem ya sake miqa masa hannu cikin sakakkiyar fuskar nan tasa,cikin tataccen larabci ya soma magana da haisam din,don bazai iya tantance wanne yare yakeji ba,kasancewar ko a wancan lokacin da larabci sukayi dukka kwanakinsu da mu'amalolinsu.

"Naji dadin sake ganinka sheikh.......ban tsammaci ganinka a agadez qasarmu ba,da nasan kana kusa damu da na jima da nemanka" Murmushi yadan saki masa,baisan me ya hada jininsu haka da hakeem din ba.

"Nazo ne ganawa da d'iyar sultane,amma ban sani ba ko zan iya samun damar sake ganinka?" A nutse haisam ya daga kanshi.

"Indai baiyi sama da mintuna arba'in ba"

"In sha Allah zan qoqarta na kammala a qasa da hakan"


*AKHNAN*


A zaune take daga gaban dressing mirror din saman stool cikin shigar atamfa embellished holland golden sea blue da ratsin blue black. Wani irin colors ne a jikin atamfda masu wani irin daukan hankali da suka dace da kalar fatarta na cikakkiyar buzuwa. Wannan fatar dake da wani irin glowing da sparkle masu daukan hankali dake nuna zallar kulawa da hutu gami da jin dadi da cikakken sukunin rayuwa da take samu.

Wani irin dinki ne na buba akayi mata,kusan zata iya cewa karon farko da zata iya tuna ta sanya atamfa a rayuwarta,don itakam tafi ganewa ready made gown da exclusive abayas,sai designers materials da take bada umarnin zaba mata dinkuna ta hannun LAARA dake kula da closet dinta tana bincika me ya kamata a zuba mata,me kuma ya kamata a cire. Dinkuna dari uku da sittin da biyar duka shekara,domin kuwa sau daya tak take sanya kaya,bata kuma sake maimaita sakasu saidai a sakasu a kayan bayarwa. Shadda kam tana dasu,su dimma bawai sakasu takeyi ba,don kwata kwata iya adadin sanyawarta da shadda zata iya qididdige lokutan.

Ko wannan atamfar ma laara ce ta dinkota,ta kuma bawa birra ta gabatar mata da ita,tana ganin zata dace da shigar ta ta yau.

Ba wannan bane a kanta a yau,don tana kallon lamarin baqonta na yau shine zai zame mata matsalar qarshe,kuma namiji na qarshe da zata sake bari ya samu daman ganin xagayen fuskarta da furucin bakinta da tsadarsa yafi qarfin kowanne namiji ya jishi.

Dinkin ya zauna mata a jiki sosai,ya kuma sake fidda sigar kyanta,qirar jikinta da kuma qara mata wani irin zaunennan kwarjini. Shehnaz na kallonta tana sake gasgata da gaske suturar bahaushe na daya daga cikin suturu da tufafin dake qarawa mutum kyau da kuma kwarjini.

Birra ke taje mata doguwar sumarta tana kuma shafeta da tsadaddun mayukan da take kula dasu,saidai duk wannan abun da yake faruwa hankalinta ba'a nan yake ba.

Idanu hankali tunaninta dama nutsuwarta gaba daya ta azasu saman ipad din data kafeta saman dressing table din da yake gabanta. Wannan wasan dai......wannan tseren na Hippodrome Niamey shi take bi da kallo cikin kowanne gilmawar second.

Har a yau har kuma a kwanan gobe bata da nutsuwa akan faruwar abun. Tunda abun ya faru har zuwa yanxun yana jin sunan MARASA NASARA yana bibiyarta a duk harbawar daqiqa,bata jin kuma zata samu nutsuwar har sai ranar data lalubo WAYE SHI?....Har sai ranar data san meye manufarsa?,me yasa ya zabi ya shirya wasan,ya qirqireshi,ya kuma gabatar dashi?.

Meye dalilin bata mata LAMBARTA da ita kadai keda mallakinta tsahon shekaru?,me ya yiwa thunder data kasa controlling dinsa?,har dai shine yayi controlling dokin da kaf cikin dawakanta tafi ji dashi?,dokin da suke communicating ita dashi da tsananin sabo tamkar dan adam?.

A hankali aisa ta tura qofar tana shigowa da sallama,saidai shehnaz kadai dake kwance rub da ciki saman gado ce ta amsa,don akhnan din ko motsawa batayi ba bare tayi yunqurin amsawar. Abinda ya ja hankalin aisa din,ta taka a nutse zuwa inda take,sai tayi tsaye a bayanta tana duban abinda take kalla,wanda clip din yazo daidai inda take fadowa ya kuma tallafeta da hannunsa guda daya.

Ita da aisa din lokaci guda hannuwansu yakai kan ipad din,kaman aisan tasan niyyar akhnan nayin wurgi da ipad din ta samu nasarar rigata dauketa tana kasheta ta wurgawa shehnaz ita.

Idanunta ta aza kan akhnan,duk wani mode nata yana nuna fushi da bacin rai,wanda aisa din takejin sam baima dace ta doshi baqonta a haka ba. Muddin haka zata kasance komai zai iya faruwa.....kunyar da dukka aka tattaru ana fatan kada yau a jita zai wahala ba'a shata ba.

"Meye amfanin kallon abinda ya riga ya faru......banda yiwa kai tanadin bacin rai?" Aisa ta furta tana duban akhnan da fuskarta tayi wani irin kyau tsakanin surfanin dake wuyan atamfar bayan gama daure mata gashin da birra tayi.

Hannu ta sanya tana ture dankwalin da birra ta aza mata a kai da nufin daura mata,ta dubi aisa din tana juyo da kujerar gaba daya tana fuskantarta.

"Kina zaton wannan tarihin zai tafi ne a banza?......kina tsammanin xan qyaleshi ne?,yayimin abinda,ya kuma bace ba tare da yabar wani alama ko guda da zata bayyana wayeshi din ba......kina zaton duka hakan ya faru ne bada wani shiri ko manufa ba?......na rantse saina laluboshi a duk inda ya shiga......na kuma rantse sai na sanyashi ya kwashi kashinsa a hannu......diyar SULTANE MUHAMMAD HAMMUD NAKE FA". Idanu aisa ta janye a hankali tana sauke ajiyar zuciya. A yau ne ta sake yadda da akhnan din baudadden halinta na halitta ne......kafiyarta kuma a jininta take,bata tunanin akwai wani yanayi ko wani dan adam da zai iya canzata

"Est-ce que c'est la seule chose qui vous dérange?(wannan ce kadai damuwarki?" Ta tambayeta tana riqe da qugunta tana dubanta.

Sai data daga fararen idanunta masu surkin blue ta watsawa aisa,sannan a nutse itama tace

"Est-ce qu'il y a autre chose?(akwai wani abunne daban?)" Idanu aisa ta bita dashi,ta fuskanci da gaske idan ta biye mata zasuyi rigima ne,sai taja tsaki kawai tana matsawa inda shehnaz ke kwance.

Harara ta watsawa shehnaz din tana dubanta.

"Ba wani sauran abinda zakiyi ne?" Ta furta cikin gatse,don ta fuskanci wani lokaci plan din akhnan yana zuwa daidai dana shehnaz.

"Ques veux-tu que je fasse?(me kikeso nayi?)" Ta fada cikin rashin ko in kula. Ta sani,ita ko aisa basu isa canza ra'ayin akhnan ba.

Mayafinta ta zara wanda birra ta ajiyeshi daga gefe da nufin idan ta kammala shiryata ta bata tayi amfani dashi. Lullubawa tayi kawai saman kanta ba tare data damu da d'aura dankwali ba ta soma takawa tana fita a dakin,sai su dukka suka bita da kallo cike da mamaki.


*FALAAK*


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login