Showing 78001 words to 81000 words out of 178317 words
goma KACAL!โ๐ฝ*
*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*
*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*๐๐ฝ
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*
*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*
*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT da yardar Allah*
+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791
https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
____________________________
"Na shiga uku!" Ta furta a fili tana cusa yatsunta cikin gashin kanta dake hargitse tana maidashi baya. Ita kanta a yanzun data kalli gurin,ta kuma sakashi a mizanin hasashen gata ga sultane suke kalla......mene zai iya faruwa?".
"Biftu......Calme-toi! Uhmnn(ki kwantar da hankalinki uhmm)"
"Shehinaz......sultane ne fa da kanshi ya kirani......bana ji a jikina lafiya ko dadi ne suka sa hakan......kira da kuma umarni dukka na kai tsaye?" Tayi maganar idanunta na nuna tabata da abun yayi.
"Dรฉtends-toi!,(ki nutsu),Qu'est-ce qu'il a dit exactement?(me yace miki?)" Numfashi taja sosai,tana son tsoron da takeji yana task masa ya narke da kansa,a nutse ta motsa labbanta.
"Kome da nake na bari,alhamis tayimin a agadez,akwai abu me muhimmanci a ranar juma'a". Shuru shehinaz tayi,ita kanta tasan lallai tabbas akwai wani magana a qasa,banda hakan sultane bai taba yi musu ko yiwa akhnan zabin ranar zuwanta agadez ko ranar barinta ba.
"Calme-toi,il ne va rien se passer,khairan in sha Allah(ki kwantar da hankalinki......babu abinda zai faru,khairan in sha Allah". Shehinaz ta fada tana sake son gamsar da akhnan din cewa ba wani abu din bane.
*_AGADEZ_*
Batayi ajiyar komai cikin ranta ba saboda samun tabbacin ta kafawa sultane qusar da zai wahala akhnan ta cireta.....zai wahala wannan karon tarin soyayyar da yake mata......tarin qauna da riritawar yayi tasirin kasa daukar matakin daya dace cikin rayuwarta.
Don haka hankali kwance ta isa farfajiyar da takan zauna a duk yammaci irin wannan. Kusan idan tayi irin wannan zaman,zama ne na musamman saboda al'ummar agadez......takan zauna ne don sauraren koken al'umma,wanda asma'u mataimakiyarta ta musamman data ajiye saboda sauraren koke da damuwar jama'ar masarautar dama na wajenta.
Buqatu na mutane birjik da damuwoyinsu data maida nata. Cikin kudinta,cikin arziqin da Allah ya hore mata. Sam bata taba gajiyawa ko kuma kasawa ba koda sau daya.
Kunnuwanta suna kan asama'u dake lissafosu daki daki,yayin da take matsa carbin hannunta a nutse zuciyarta kuma tayi nisa karanta "subhanallahi wabi hamdihi,subhanallahil azeem" (Kalmomi ne da Allah yake sonsu,suke kuma nauyaya ma'aunin aikin bayi ranar awon ayyuka).
Muryar aeera ta jiyo daga inda take ita da Aafreen,kafin daga bisani ta hangi falaak na tahowa,hannunta dauke da qur'anin Aafreen.
Jikin momma aeera ta fada tana bata labarin ta haddace karatunta na jiya har an qara mata wani. Murmushin momma ta saki,a duk sanda ta gansu suna tafiya ko dawowa daga daukan karatun,tana jin wani nutsuwa gami da aminci har qasan ranta,tana jin wani kwanciyar hankali yana saukar mata.
"Momma.....malam yace yana buqatar magana dake idan an masa izini". Aafreen ta fada tana zama kan daya daga cikin tuntum din da aka qawata wajen dashi saboda hutawa. Sai data kalli falaak ta gyada mata kai alamun haka ne,sannan ta dakatar da asama'u.
"Ayi masa iso" Tace da asama'u tana gyara zamanta gami da sake lullube ilahirin jikinta da kyau.
Cikin qasa da mintuna goma ya bayyana a wajen. Cikin shigar manyan kaya na wani tattausan yadi babbar riga da 'yar ciki. Akwai kamala da nutsuwa sosai tare dashi,shekarunsa na haihuwa zasu kai aqalla arba'in da biyar zuwa da takwas.
Cikin karramawa tasa aka tarbeshi,kafin su fara magana.
"Da dadewa na cike foam na ummul_quraa a madeena......shekara guda kenan sai wannan satin Allah yayi na samu sanarwar samun gurbin karatu acan din,wannan dalilin ya sanya nace bari na sanar miki.....ina me bada haquri mun fara karatu da yara kuma zai yanke". Sosai momma taji zuwan maganar a wani abu na ba zata,har cikin ranta taji sam labarin bai mata dadi ba,to amma ci gaba ne ya samu malam Ousmane haris din,koda akan kanta ne ko yaranta kuma hakan zata kalleshi a abun alkhairi.
"Ma sha Allah malam.....na tayaka murna sosai.....ci gaba ne da qaruwa ai,ba kuma akanmu kawai ba.....har qasarmu gaba daya,Allah yasa albarka".
"Ameen,godiya nake".
"Ma sha Allah.....in sha Allahu zan aika da tawa gudunmawar tafiyar". Murmushi ya danyi
"To Allah ya saka da alkhairi"
"Ameen ameen......saidai kuma wani hanzari ba gudu ba......karatun yaran nan,banaso ya tsaya malam......don Allah idan ba damuwa.....ko zaka duban wani amintacce cikin amintattunka?". Shuru kadan yayi na wasu daqiqu kafin ya nisa.
"Mutum daya ne na amince dashi,nasan kuma zai iya fiye ma da abinda zanyi,don iliminsa ya zarga nawa nesa ba kusa ba.....saidai kuma shi din mutum ne me wuyar sha'ani,hasalima bani da tabbas din zaiyi,kinga kuwa baima kamata na bada sunansa ba". Tashin farko momma taji maganganun malam Ousmane haris ya zauna a ranta,karon farko kuma hankalinta taji ya zauna daidai kan wanda taji yana yiwa yabon da kuma tabbacin samun karatu sama da wanda shi yake bawa yaran.
"Don Allah malam.....ko za'a roqa mana ALFARMARSA?......ko nawa ne zan biyashi......ya daure yaci gaba da dukan nauyin karatun yarannan". Shuru malam Ousmane haris yayi,kafin daga bisani ya sauke ajiyar zuciya.
" Abinda za'a biyashi ba shine damuwar ba,ku din da yaran,na tabbatar sai ya saka ya kuma kafa musu wasu qa'idoji da dokoki muddin zai daukesu karatu,ban sani ba ko zaku iya jure hakan Allah ya taimakeki". Qaramin murmushi momma ta saki tana daidaita zamanta.
"Banda abun malam Ousmane......ai nafison irin wannan tsarin koyarwar......kuma ina son mu'amala da irin wadannan mutanen,don nasan cewa komai nasu in sha Allah zai zamana a nutse ne bisa tsari......wannan aikin za'a yimin malam.....ya fadi duka tsare tsarensa.....in sha Allah zasu kiyaye". Qasa malam Ousmane haris yayi da kansa. Yana jin nauyin matar qwarai,saboda tarin alkhairanta da sanin ya kamata da take dashi.
"In sha Allah komai zai zo da sauqi".
"Momma" Falaak ta kirata sanda take shirin maida hankalinta ga asama'u bayan sun kammala da Ousmane haris. Duban falaak din tayi,ta bata fuska sosai
"Gani nakeyi ba malamin da zaizo da yafi malam iya koyarwa.....na dauka zaki hana mishi tafiyar ne saboda karatunmu". Murmushi kadan momma tayi,sai ta ajiye takardar da asama'u ta miqa mata zata duba tana kallon falaak din.
"Bakisan duk me hankali yana mu'amalantar malami tamkar sarki ba saboda girman qur'ani da tarin alfamar littatafan da suke kanshi ba......abune da bai dace ba kayi karantsaye cikin al'umaransu ba........suna da daraja da martaba sama da wadda sarakuna da masu mulki suke da ita......baka da hurumin amfani da qarfin iko ko na mulkinka na sanyasu yin abinda basuji amincinsa a zuciyarsu ba.....tsakaninka dasu biyayya girmamawa da tausasawa". Kai falaak ke gyadawa tana sake samum gamsuwa da dukka bayanan momma din.
Ita din shaida ce,taga wasu irin mabanbantan dabi'u masu kyau da nagarta gami da burgewa tattare da malam Ousmane haris da bata zaci akwai sauran mutane dake da wannan dattakon da kamalar ba har haka. Mutum daya ta sani haka....SULTANE dinsu.
(08187255862 luu luu paying)
โ
Cikin nutsuwar nan tasa wadda ta zame masa tambari yake takawa a hankali zuwa saman stairs na gidan. Abdii omari da kuma addisaleem suke biye dashi a baya. Omari ne a bayansa....abdii a bayan omari,sai addisaleem dake biye dasu a baya cikin matuqar girmamawa.
A nutse yake duban saman,wanda ke dauke da wani irin qawataccen parlor na zamani. Yalwatacce da aka yiwa wani irin tsarin gini aka kuma zuba masa furniture masu wani irin mahaukacin tsada da daukan hankali. Kai ya jinjina a hankali,komai na gidan yayi masa,tsarinsa da komai nasa. Idan iya qasan gidan ka zauna ba zakayi tsammanin zaka taras da wani qawataccen upstairs da yakai kyau tsari da haduwar wannan ba. Ba zakayi zaton samun aljanna duniya irin wannan a upstairs din ba sam,haka ya tsara.....kuma haka yaso tsarin gidan ya kasance.
"Ta wanne bangare kuka ajiye library din gidan?" Yayi tambayar yana zubewa abdii idanunshi. Qaramar dariya omari ya saki yana takawa gami da zubewa cikin lausasan qawatattun sofas din da aka qawata parlorn dashi 'yan asalin qasar china hand crafted da suka qawatu qwarai da gaske.
"Ka nuna masa daidai inda ruhinsa zai dinga samun sakeena(nutsuwa?" Yana dan boye dariyarsa. Murmushi abdii yayi shima yana shafa sassalkar sumarsa.
"Bayan ka sauka qasa,hannun hagu da qofar shigowa" Abdii ya fada yana kwatanta masa da hannu. Kai haisan ya kada a nutse
"Yayi....." Hannunsa ya miqa yana cire jakarsa dake kafadar abdii din.
"Komai yayi....zan shiga na huta......ka fadawa musu kowa ya wuce mazauninsa......sai gobe idan Allah ya kaimu zamu zauna gaba daya......."
"Amma Ousmane haris na buqatar ganinka obbo". Dakatawa yayi da tafiyar da yakeyi ya waiwayo yana duban abdii,har ga Allah ya gaji tubus,tafiya ce ba 'yar kadan ba tsakani Niamey da agadez. Tsananin yadda tafiye tafiye take cikin wasu abubuwa da yake matuqar so ya sanya baiga nisa ba.....bai kuma gaji ba har sai yanzun daya tabbatar ya kawo inda zai huta. Tafiyar awanni goma sha biyun nan a wajensa wani sabon aji ne kuma mabudin ilimi.
"Kace ya bani zuwa goben injini" Ya furta a nutse tamkar ba wani gajiya a tare dashi yana kallon yadda abdii din yadan diririce.
Zare kallonsa yayi daga kan abdii din.....wani lokaci can baya yana gaza gamsuwa da maganganunsu amjad a kansa.
"Idanunka nada wani irin kaifi da nauyi......basan wacce budurwa ce nan gaba zata iya dauke nauyinsu ba har ta tsaya ta fuskanceka da soyayya ko a mu'amala ba......don Allah ka rage magana da idanunka da kake yawan yi........daukemin idanunka haisam......bazan juresu ba". Kadan kenan daga muryoyi da kuma maganganun mutallab game da idanunsa,bai kuma fahinta ba,hakanan bai qara gasgata maganarsu ba sai da qara shekaru saman wadanda yake dasu,shekarun da suka fara fusgar hankulan 'yammata cikin rayuwarsa.
"Am.....obbo" Abdii ya sake kiransa sanda ya sanya hannu zai murda handle din qawatacciyar qofar dakin.
"Kuma?" Ya fada yana juyawa kadan amma bai kalli abdii ba.
"Afwan obbo......saqo ne aka bani......kuma tamkar amana ce da bai kamata ce ban idar da amanarta ba" Shuru parlor din yayi,don tuni omari ya wuce nashi dakin,addisaleem kuma ya sauka yana komawa don tabbatar da shigowar kayansu ciki.
Ta baya ya miqawa abdii hannu,cikin farinciki ya matsa ya dora masa a saman hannunsa ya juya da sauri sauri ya lalubi hanyar fita,tun kafin yakai ga duba sunan me saqon,saidai cikin sa'a gajiyar dake taba jikinsa ta hanashi dubawa ya wuce dakinsa da ita a ransa yana raya qila wani sabon shirmene na abdii din kawai.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer ๐ณ๐ช*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA๐*
*HUGUMANKU CE*โ๐ฝ
๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
PAGE 37
_________________________
*_M&A EGYPTIAN ABAYAS_*
*Assalamualaikum*
*_Ina dandazon tawagar gayyar MATA 'YAN QWALISA?_*
*_WADANDA SUKAYI AMANNA DA ADO SUNE MUTUNCIN D'IYA MACE?_*๐๐ฅป
*Ina masu son sari ko siyan daya na Egyptian abaya masu quality su iso garesu cikin Aminci???*
*M&A EGYPTIAN ABAYA itace zabinku NA FARKO*
*kuse ABAYAS takanas kuma kai tsaye DAGA EGYPT su iso gareku cikin kasa da kwana goma KACAL!โ๐ฝ*
*_Ina masu son siyan abaya Amma Kuma basuda halin siya lokaci daya?_*
*_zaki iya ringa biya ahankali har ki kammala abaki abayarki cikin aminci_*๐๐ฝ
*Sannan gamasu San siyan airfreshener a farashi mai sauki muna dasu*
*muna turo da mayukan kitso original AMLA da VATIKA*
*Idan kana da wani personal shopping dakakesan ayi ma duk munayi CIKIN QASAR EGYPT da yardar Allah*
+20 114 341 0873 ko kuma
0810 959 7791
https://chat.whatsapp.com/Hm9HBCXeyfjFDwi3OPSFqP?mode=wwt
____________________________
"Rabbi anzilni munzalan mubarakan wa'anta khairul munzileen" Ya furta da nutsuwar nan tasa dake qara masa kwarjini,take kuma qarawa kyansa kyau,sannna ya taka a hankali ya ajiye jakar tasa saman wani zagayayyar sofa ta hutawa dake wani corner daban na dakin.
Da idanu shima dakin ya gama observing dinsa. Da gaske abdii yasan komai a kansa.....da gaske abdii yasan abinda yakeso da wanda bayaso,yasan abinda yake burgeshi dama wanda baya cikin tsarinsa,sai kawai ya furta.
"Bismillahillazi la'ilaha illa huu" Ya soma zare kayan jikinsa,don a yanzun wanka kawai yake buqata ko zai warware gajiyar jikinsa.
(Ba'a cire kaya haka kai tsaye,saboda idanun shaidanun da suke a muhallinmu,idan kikayi wannan addu'ar Allah xai sanya hijabi a tsakaninku ba zasu ga tsiraicinki ba).
Sanda ya fito ya shirya tsaf cikin farar short sleeve shirt fara qal,ya sanya joggers pant shima daya kasance fari. Shigar kaya farare da shigar kaya green wani dabi'a ce tasa da kusan duk wanda ya sanshi ya sanshi da ita. Wayoyinsa ya debo don sanya charge a parlor,yana fita akayi knocking. Daya tambaya sai yaji muryar addisaleem.
"Nine obbo"
"Shigo" Ya bashi dama kai tsaye yana zama saman wata ottoman dake kusa da socket.
Rusunawa yayi kadan sannan yace.
"An kammala abinci......bansan ko kana buqata ba". Manyan zagayayyun idanunsa ya daga ya kalli agogon bangon dake manne,dare ya soma yi,ba kasafai kuma yake cin abinci me nauyi ya kwanta ba,don haka ya girgiza masa kai.
"Coffee kawai.....gahwa,kar kasa sugar,narkakken ruwan rake ya isa" Ya fada da wani irin yanayi dake dake bayyana qasaitarsa da tabi jikinsa. Kai addisaleem ya gyada sannna ya juya yana ficewa.
Kadan kadan sautin karatun hadisai da ake karantawa daga channel din saudi sunnah daga littafin sahihul bukhari ke fita daga tafkekiyar TV din dake zaune dafa'an cikin parlor din,yayin da hannunsa ke dauke da daddadan coffee din,yana kurba yana ratsawa har cikin zuciyarsa. Ya yadda shan coffee da gahwa wani rubutaccen abune cikin jikin oromia......uwa uba ma kuma cikin jinin sarauta,nanaya yakeson kira,muryarta yakeson ji,amma koda ya kalli agogo yanzun goma na dare ne cikin agadez,a jimma kuma yasan sha biyu na dare ne. Idan ya kirata zai tada ne kawai,zai kuma lalata mata tsarin baccinta,don tana kwanciya ne akan lokaci don ta samu ta riski sallar darenta ta kuma sukwane har asuba. Dole ya haqura da kiran nata ya tattara ya wuce bedroom din nasa.
A daddade yayi shafa'i da wuturi,wanda komai tsanani baya taba bari su wuceshi,ya cire kayan jikinsa ya saka pajamas,ya tsaya gaban mirror yana feshe jikinsa da night scents dinsa masu lallausan qamshi.
Yana tsaka da feshe kyakkyawar qasumbarsa idanunsa ya sauka akan envelope din. Har ya janyesu ya ajiye kwalban turaren ya juya,sai kuma ya dawo a hankali ya dauki envelope din ya budeta ya zaro farar takardar ciki.
Rose flower ne qwara daya ta biyo bayan takardar ta fado,ya bita da kallo ba tare daya tsugunna ya dauka ba,sai ya dawo da dubansa kan takardar ya farketa a nutse,
Kwantaccen rubutune cikin yaren oromo,ya soma bin rubutun da idanu yana karantawa.
_Sallama me cike da aminci da kuma fatan alkhairi,godiya a bisa amsa gayyatar abba na zuwa cin abincin dare tun a wancan lokacin,a wannan karon ni da kaina nake roqon wannan alfarmar don sada zumunci da kuma samun lada.......Menelik ce_
Sai number wayarta har guda biyu a rubuce daga qarshen takardar. Kansa ya daga a nuts,ya cukuikuye takardar yayi cilli da ita a inda baisan inane ba,ya daga qafarsa yana qarasawa bakin gadon. Hannu ya saka ya zuge net din dake kewaye da gadon,sannan a hankali ya shige ciki yana yaba tsarin da aka yiwa gadon kansa.
"Allahumma innaka kalaqta nafsi,wa'anta tawaffaha,laka mamataha wa mahyaha,in ahyaytaha fahfazha,wa in amattaha fagfir laha,allahumma inni as'alukal afwa wal'afiyah" Lafuzzansa kuma addu'arsa ta qarshe kenan a kowanne dare idan ya kwanta,yau dinma da ita ya rufe,ya lullube idanunsa yana fatan kasancewa cikin wadanda Allah zaiwa alfarmar ganin washegari.
โ
โ
โ
โ
Sau uku tana duba tickets ko zata samu jirgin da zai tashi daga Niamey zuwa agadez koda ranar laraba ne amma sam sam babu. Wani abu daya sake quntata ta,ya kuma sake sanya ranta yayi matuqar baci.
Kamar yau dai,duk data kasance litinin ce,tana cikin ranakun da takan jima a company ba tare data dawo gida ba,amma litinin din yau din ta zama ta daban. Don tun break din da ake fita da azahar ta umarci driver dinta ya maidata gida.
A kebantaccen balcony dinta ta zauna bayan ta canza kayanta,tayi zaton zata iya sake rage wasu ayyukan a system dinta amma saita kasa,ta koma laluben ticket din da zai dace da ranakunta amma ta rasa.
Tsaye kawai tayi goye da hannayenta jikin qarfen balcony din,iskar dake kadawa daga hagu zuwa dama suna wasa da gashin kanta da muddin tana gida basu fiya shiri da dan kwali ba. Dogon wando ne a jikinta sakakke,sai shirt me gajeran hannu rounded neck data fidda qirar qirjinta da kuma shafe din shafaffen cikinta da ya bawa mazaunata suma damar fidda nasu shape din.
Banda lemo ba abinda