Showing 96001 words to 99000 words out of 178317 words

Chapter 33 - LU'ULU'U COMPLETE

daban.

Saman wata qawatacciyar shimfidar dake nuna asalin sarautar qasar agadez din yake zaune. Yasha ado da launin kayan da suka kasance koraye ne,irin launin koren dake da daukan hankali da idanun me kallo.

Daga hagunsa da kuma damarsa mutane ne zaune,mutanen da kana kallonsu kasan akwai kusanci tsakaninsu daya basu daman zama haka su dashi,sai kuma alamun dake nuna akwai magana me muhimmanci da suke tattaunawa.

Sarkin fada ne ya motsa,cikin tausasa harshe yake sanar da sultane isowar haisam din,abinda yaja hankalin sultane din a nutse ya daga idanunsa zuwa ga haisam wanda yake tattakowa cikin nutsuwarsa.


zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


PAGE 44

Gauraya idanunsu sukayi guri guda,,idanun sultane muhammad hammud a kansa,yayin da haisam ya janye kallonsa daga kan sultane,saboda dabu'antuwa da yayi na rashin girma ga sanya ido cikin idanun manya. Amma a qasan ransa yakejin wani nauyin mutumin,mutumin da yau ne karon farko daya soma ganinsa ido da ido,duk da baisan adadin iya hotunansa daya kalla ba a sanda bincike ya biyo dashi ta qasar a sanda yake shirye shiryen tahowa agadez din.

Daga inda sultane yake zaune yana nazartar tahowar haisam din,cikin jikinsa yake jin wani abu na daban game da yaron. Baiyi tsammanin ganinsa haka ba,matashin dake da qananun shekarun da duka duka basufi talatin ba zuwa da uku,ya dauka wani babban mutum ne zai dauki jagorancin karatunsu falaak din. A nasa son yafison me shekaru,to amma hakanan cikin jikinsa karon farko yakejin ya aminta da yaron.

Cloak robe dinsa yake qoqarin tattarewa don duqawa yakai gaisuwa ga sultane. Yadda yakeyi din kadai yasa sultane yakejin kamar ya dade cikin masarauta,sai ya daga hannu yana dakatar dashi daga qudawar da yake shirin masa,maimakon haka hannu ya bashi direct,haisam ma kuma ya miqa masa nasa sukayi musabaha,sannan sultane ya masa masauki kusa dashi.

Mamaki kadan ya d'arsu a zuciyar mutanen dake gurin,duk da cewa sultane din mutum ne me karamci qwarai,yana da girmama mutane sosai,babu ma kamar ace mutum masanin addini ne......kuma mahaddacin alqur'ani,wannan girman nasa yana ninkuwa a idanun sultane din.

Cikin nutsuwarsa yake bin tattaunawar da sukeyi akai,sai a sannan ya fahimci akan wasu dokoki ne na shari'a da akeson fiddasu,da wasu boyayyun qa'idoji na shari'a da za'a yisu a rubuce,ayi kuma seminar ta kwanaki ana wayarwa da malaman qasar agadez din kai.

Takardu aka raba a gurin,har tazo kan haisam. Idanun sultane a kansa sanda yasa hannu ya karba,ya bude ta a hankali yana duba maudu'an da suke ciki,da bayanan da ake buqatar warwaresu.

Murmushi kawai ya saki a nutse,ya maida takardar ya ajiye yana dora idanunsa akan sauran malaman da suke gurin.

"Ko zaka warware mana kowanne hukunci?" Muryar sultane ta sauka a kunnen haisam. A nutse ya waiwayo ya dubi sultane cikin girmamawa,a kallon farko kuma ya fahimci wani gwaji ne sultane yakeson masa.

"In fada tana da buqatar hakan sai nayi ranka ya dade" Ya furta da sasanyar nutsuwarsa cikin girmamawa.

Kai sultane ya gyada yana dauke idonsa daga kan haisam,murmushi kwance qasan zuciyar sultane din. 'Yan qananun mintunan da yayi da yaron ya fahimci yana da wata irin tarin nutsuwa da kuma kwarjinin da ba kasafai aka fiya samunsa jikin kowanne mutum ba,irin kwarjinin da yafi fita ne daga jikkunan ahalin sarauta.

Cikin qwarewa da tarin baiwar fasaha da zalaqar zance haisam din ya soma bayani da sharhi,bayanin da yaja hankalin duk wani wanda yake gurin,ya kuma sanya sultane maida hankalinsa kacokam kan haisam.

"Bari mu fara da hukunce hukuncen dake kan bayi mata......baiwa a daraja da martaba ba kamar d'iya take ba.......idan 'ya zatayi idda wata hudu da kwana goma,to baiwa wata biyu zatayi da kwana biyar shine iddarta.......,idan baiwa tayi zina,istibara'inta zai kasance haila daya ne wato jini daya,idan aka saki baiwa zatayi idda na wata biyu ne,ba kamar 'ya da zatayi wata uku ba,idan me baiwa ya siyar da ita ga wani,jini daya nan ma zatayi kafin ta zama mallakin wancan,sauran abinda ya shafi 'ya shine kamar haka. Duk wanda yayi zina da mace,sannan aka daura musu aure kafin tayi istibra'i to wannan auren batacce ne ba halastacce ba,dole a raba wannan auren,idan kuma har ya kebe da ita to taci sadaki,dole ya biya sadakinta,bayan ta gama istibra'i bayan rabuwarsu yana da ikon sake aurarta halal ne......"

"Amma kuma duk wanda ya daura aure da mace tana cikin idda,sannan ya tare da ita,to aurensu ya haramta har abada,koda ita dashi ne kawai suka rage a duniya,kwatankwacin hukuncin ma'auratan da sukayi li'ani(tsinenenuwa),ya rantse d'an data haifa ba nashi bane,itama ta rantse d'anshi ne,to bayan sunyi haka a kotu a gaban alqali wannan aure ya rabu har abada,kuma sun haramta ga juna har abada" Numfasawa yayi a hankali sannan yace.

"Iddar qaramar yarinyar daka saki,wadda bata fara al'ada ba,watanni uku zatayi kaman yadda babbar mace zatayi,sannan iddar me kwantaccen ciki.......". Sake daukan shuru masallacin yayi,yayin da dukka fuskokinsu ke gaya masa yadda bayanin nasa yake shiga.

"Mace me kwantaccen ciki shekara hudu ne,zatayi shekara hudu sannan ta sake wani auren"

"Allahu akhbar" Sultane ya fada a hankali yana girmama lamarin shari'a,tabbas ita din sabanin hankali ce.

"Wadda ta debe tsammani da ganin haila,saboda shekaru itama watanni uku ne iddarta.....kaman wadda take shayarwa,wadda bata haila sanadiyyar shayarwar,to iddarta zata kasance shekara guda,hakanan macen da bata da cikakkiyar lafiya,itama shekara daya ne iddarta.....macen da take cikin jinin cuta wato istihadha,itama iddarta shekar daya ce". Ya qarasa fada a nutse yana sauke muryarsa qasa.

"Ma sha Allah.......ma sha Allah" Sultane ya samu kanta da furtawa. Duk wanda yake gurin saida bayanan nasa sukayi masa dadi. Shugaban malamai ya motsa kadan yana duban sultane.

"Allah ya taimakeka,dukka ya tattara bayanin ya gama yinsu,abinda kawai ya rage shine rubutasu a tsare,aka rarrabasu zuwa guraren da suka dace".

" Zaka iya tsarasu a rubuce?" Sultane ya maido dubansa ga haisam. Nutsatsen murmushi ya saki,a duniya baya ga bincike da rubuce rubucen addini ba wani abu da yakeso yake kuma masa dadi gami da qawata lokutansa,sai kuma aikinsa na intelligence da yakeyi.

"Ba zaya gagara ba in sha Allah,hukunce hukunce ne daya kamata a sansu a kowanne gida,kowacce mace da kowanne magidanci susan dasu,saboda wadannan sune hukunce hukuncen da suke tsaftace aure,kowa ya sani daga aure ake samar da zuri'a,zuri'ar nan me kyau ko maras kyau?. Yadda za'a tsaftace mahaifa don samun 'ya'ya daga bayyanannen tsatso kuwa yana da nasaba da samar da 'ya'ya na gari,da yawa an haifi yaran da nasabarsu ta cakuda data wasu......an haifi yara cikin iddar auren wani,an daura aure cikin sauran haqqin wani mijin,wannan sai yake zama sanadin haifar yaran da suke gagarar al'umma,su gagari iyayensu,harma kaji d'a ya dauki abun kaifi ya kashe mahaifi ko mahaifiyarsa ko 'yan uwansa,da yawa wadannan kurakuren dake cikin idda ko saki suke jawo hakan".

"Tabbas......ko shakka babu" Sultane ya fadi yana jin wata irin gamsuwa da dukka bayanan haisam,yana jin wata cikakkiyar nutsuwa dashi.

Kalar burikan da kowanne uba kanji akan haisam yaji ya saukar masa. Sai yakejin inama ace d'ansa ne?,inama ace mallakinsa ne?.

"Koda bai zama d'anka ba,zai iya zama mafi kusanci sosai da kai......kana buqatar irinsa,sosai kana buqata" Ya gayawa kansa da kansa. Ya sani mulki abune dake buqatar mashawarta na qwarai,aqilan mutane masu nisan zangon hankali da fahimta,tsayayyu masu tsoron Allah.

Yanaji a jikinsa kamar Allah ya aiko haisam ne cikin rayuwarsa,haka kawai yakejin wannan feeling din da baisan dalilin jinsanba,baisan kuma daga ina ya taso ba.

Sanda lokacin sallah ya cika tuni masallacin ya soma samun dafifi na al'ummar agadez,masallata da suke halarta sallah a masallacin duk wunin juma'a,tun daga sallar asuba har isha'i,wanda daga nan sai kuma wani satin za'a sake budewa da bada daman shiga cikinsa,wannan ya sanya da yawansu a dukka wunin juma'ar a masallacin suke duka sallolinsu.

"Bismillah" Sultane dake gefe ya fada yana nunawa haisam shimfidar da aka tanada saboda liman. Kansa ya saukar qasa,ba kasafai ya fiya son a bashi limanci ba daga zuwansa guri,saboda kaucewa fitina da susa cikin zukatan al'ummar gurin dama wanda yake da ikon jan sallar

"Shiga mana ya sheikh......bismillah,umarnin sultane ne" Limamin da shike da haqqin jagoranta ya fadi fuskarsa dauke da murmushi.

A nutse ya wuce gaba,ya kuma tsaya yana daidaita tsaiwar tasa,ya miqan hannu ya dauko qaramin mic din yana maqalashi gaban rigarsa,kafin ya furta.

"Sawwu sufufakum(ku daidaita sawunku)" Muryar tasa ta bada amsa kuwwa daga kowanne nahiya na unguwar gaba daya saboda qarfi da nisan amsa kuwwar,yayi kabbara da husky voice dinsa cikin cikakkiyar nutsuwa.

Sautin kabbarar daya isa har cikin kunnuwan akhnan dake tsaye tsakiyar dakin nata. Sautin ya bata wani irin baqon yanayin da batasan meye shi ba. Karon farko da kabbarar sallah daga masallacin ya taba fusgar hankalinta,har kuma takejin kamar baquwar murya ce wannan din. Kafin tace komai taji buhaina qasa qasa na cewa da birra,birran dake qoqarin gyara zip din zubabbiyar doguwar rigar da akhnan din ta sanya.

"An nada sabon limanne ko sabon malami?". Kai birra ta girgiza

"Banaji gaskiya,amma nima baquwar murya nakeji". A nutse akhnan ta daga kanta daga sunkuyar dashi da tayi saboda taje mata doguwar sumar da bushira keyi.

" Aikin kula da lamuran da suka shafi masallaci dama aka baku?" Akhnan ta furta maganar da alamun bacin rai sosai cikin muryarta.

"Tuba muke ranki ya dade" Buhaina tayi saurin furtawa. Batace komai ba,kaman yadda bata bada kanta bushira taci gaba da gyarawa ba,har kaman ba zatayi magana ba sannan tace.

"Ya zama na farko kuma na qarshe da kunnuwaku zasu dinga damuwa da rayuwar wasu,harma ya zame muku abun tattaunawa.....wannandin dokata ce"

"Bazai sake faruwa ba,ki mana afuwa" Birra ta fadi cikin duqar dakai. Siririn tsaki taja sannan ta maida kanta yadda yake tana fadin.

"Banason wani dogon fi'ili,ribbon daya zaki saka ki hademin shi yadda bazai dameni ba"

"An gama,in sha Allah" Bushira ta fadi tana ajiye kayan adon data debo a gefe.

Shuru dakin ya dauka,kafin qarar wayarta ta katse shurun. A ladabce barra'u ta dauko wayar takai qasa saman gwiwarta tana miqa mata.

Sunan kawai ta kalla ba tare da ta taba koda wayar ba. Shehnaz ce,sai ta bawa barra'u umarnin daga kiran ta saka a handfree ta riqe mata da hannunta.

Hakan akayi,barra'u ta dora ma akhnan wayar saman tafukan hannuwanta,ta kuma matsa mata dasu daidai yadda zataji dukka abinda shehnaz zata fada.

"Saluuut ma sœur(hello sister)" Ta fada cikin nuna kulawa da kuma yanayin sabo dake tsakaninsu.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽


💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


PAGE 45


"Salut toi shehnaz....." Ta fada da nutsatsiyar muryarta dake sirkin qasaita a ciki,kai ba zakace can cikin qasan zuciyarta zallar tashin hankali bane.

"Zuwa dare muna agadez in sha Allah,hankalinmu ya kasa kwanciya......fatan dai ba wani abu mara kyau ko?". Idanunta fa lumshe,tana kuma qoqarin zuqar numfashi,don so take ta daidaita kanta,ta kuma rage zafin da zuciyarta take mata.

"Akwai matsala shehnaz......amma kafin kuzo ya zama tarihi.....zai shafe tarihin nasa ma gaba daya". Shuru shehnaz tayi tana juya maganar akhnan,idan tace akwai matsala eh tabbas akwai matsalar........ Sau tari tana da wani irin qarfin zuciya da ya gauraya da kafiyarta da yake sanyawa take iya tunkarar matsala komai girmanta,bata da shakka kuma bata da saurin tsoro. Ba komai ne yake girgizata ba,ba komai bane yake daga mata hankali ba. Matsala indai ba daga sultane ko mammina ba,basa taba gigita nutsuwa ko tunaninta,shi yasa a yanzun dukka rauninta ya nuna kansa,saboda sultane ne.....daga gareshi abun yake.

Kafin shehnaz ta sake cewa komai akhnan ta bada umarnin gimtse wayar,ta dauke idanunta tana maidawa ga madubin dake ajiye a gabanta tana duban fuskarta.

A nutse take duban yanayinta,taci alwashi ko waye wannan daya nemi gigita duniyarta saita shayar dashi mamaki,saita nuna masa illa da kuskuren abinda ya aikata din,ba zata taba qyleshi ba cikin kawo mata tsaiko da yayi na kwanakin nan a dukka al'amuranta,ba zata daga masa qafa ba......yadda ya kawo sabani tsakaninta da sultane,abinda ta jima rabon da ya faru a tsakaninta dashi.

Kira na biyu ne ya sake shigowa,a nata zaton shehnaz ce still. A yanzu kam bata da wani juriyar sauraren dogon zance daga shehnaz din ko aisa ma gaba daya,inda zata qyaleta to tabbas zasu iso ne a daidai sanda shirinta zai kammala,maganar ma sai yafi dadi,amma kuma ga tarin mamakinta sai buhaina tace mata

"Nannie ce". Manyan blue eyes dinta tadan bude kadan. Ba kasafai Nannie ke kiranta haka kai tsaye ba. A wasu lokutan dabi'unta suna kamanceceniya dana morsa safiyya,wani lokacin kuma tana diban kamannin halayyar mammina. Kai ya juya a hankalin dake alamtawa buhaina cewa ta daga kiran,ta daga din,ta sake dawowa ta duqa cikin girmamawa da wayar a hannunta.

"Assalamu alaikum" Nannie ta fadi da kamilar muryar dinnan da yanayin jinyar da take ciki bai gaurayata ba.

"Wa'alaikumussalam......Bonsoir nanniee(barka da yamma nannie)".

" Bonsoir,comment allez-vous?(barka da yamma,kina lafiya?)"

"Alhmdlh" Ta fadi tana hadiye wani abu a wuyanta.

"Munyi magana da bappinki.....ya gayamin kina da baqo yau ma kaman yadda aka saba ko?" Tayi maganar da sautin da shi kadai ya fadarwa da akhnan gaba.

Shuru ta yiwa Nannie din bata amsa mata ba,hakan kuma bai hana Nannie magana ba.

"Biftu....."

"Na'am Nannie" Ta amsata tana qoqarin tattala qwarin gwiwarta.

"Yana da kyau ki dakatar da wannan wasan kwaikwayon haka nan.....lokaci yayi,muna da buqatar kawar daku daga gabanmu". Lumshe idanunta tayi sosai kaman ba zata bude ba,wani bacin rai ne yake taso mata.

"Bana buqatar haka Nannie silvous plaît.......bana buqatar wannan hadakar.....zan iya rayuwata ni kadai na,hadin baya burgeni,rayuwar bata burgeni itama" Ta fada a sanyaye duk da akwai zafi me nauyi cikin kalamanta.

"Biftu!" Ta kirata tana tsaurara kiran wannan karan.

"Aure dole ne wuyan kowacce mace.....komai qasaitarki baki cika ba saida aure.......kina da zabi guda biyu.....wannan sune adalci na qarshe da zamu iyayi miki" Nannie ta fadi cikin nata zafin da akhnan din ta jima bata jita cikinsa ba.

Wuta tsaf akhnan din ta dauke kafin ta janye jikinta daga kusa da wayar,sannan ta sulale ta zauna gefan gadon tana qoqarin gaya musu su fita a dakin su bata guri.

Dukkaninsu sun fahimta,don hatta da buhaina da wayar ke a hannunta,wayar da tana iya jiyo Nannie na maimaita fadin.

"Hello......hello" Haka ta fice da ita a hannunta. Bata da ikon katse kiran Nannie,don aikata hakan babban laifi ne,dole ta ajiye wayar a gefe har Nannie din ta gaji ta gimtse kiran da kanta.

Ta gama fahimta ta kuma gama gane komai,wannan karon al'amarin yafi kama da taron dangi akayi mata,momma......Nannie uwa uba sultane dinma.

Zata tsammaci hakan daga momma,harma sama da hakan,amma daga sultane kuma ko Nannie dukka baqon abu ne a wajenta.

Wai wanne dalili ne zai sanya ba zata tsani morsa safiyya ba?.......me yasa ba zataji bata qaunarta ba?. Tana da cikkakken imani da yaqinin komai ita ta assasashi,komai kuma ita ta shiryashi,in fact ma jikinta yana bata ita ta jawo komai ta hadashi daidai da muradinta da cikar burinta.

Tsam ta miqe tana zare ribbon din kanta,ta kuma daure gashinta tsakiyar kanta da wani irin zafi,jelar ta sauka gadon bayanta tana lilo. Banda umarnin daga sultane ya fito......bata tunanin yau duk duniya akwai wani wanda ya isa ya sanyata ta fuskanci wannan baqon. Umarnin sultane ne......zata cikashi,amma kuma ta hanyar da takeso,ta kuma hanyar da taga dama itama.


*FALAAK*

Sallamar morsa safiyya ya sanyata daga kanta daga duba shafin littafin dake hannunta,wanda kusan ta zauna ne kawai tana duba littafin saboda ragewa kanta lokaci da kuma dogon zama,amma sam ba wai don tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login