Showing 150001 words to 153000 words out of 178317 words
janye qudurinsa ba,yaci gaba da qarfafa alaqar zumunci a tsakaninsa da haisam,a tsakaninsa da masarautar jimma ta dukkan hanyoyin da suka dace,yana sanya ran watarana alaqa me qarfi ta qullu tsakanin haisam din da haana.
*MOMMA*
Daga waccan ranar har kawo yanxun da take tsaye gaban closet dinta bayan ta ciro wata alkyabba da aka samar da ita daga wani silk material me tsadar gaske tana sakata a jikinta......hankalinta da tunaninta gaba daya bai sauka daga kan akhnan ba.
A kowanne rana tana sanyawa cikin sirri ana laluba mata halin da take ciki. Koda kebe kanta da tayi na wadannan kwanakin tana kwanciya ne ta kuma tashi da tunaninta ya take ciki?,me takeyi yanzu?,me yake gudana a kewayenta?.
Koda sau nawa akhnan zata aikata laifi.....koda meye zatayi batajin zuciyarta zatayi nesa da ita,zuciyarta zatayi nesa daga soyayyar da take mata,wanda wani bangarene kawai na soyayyar safeena da tayi fiffike ta sauka a kanta.
A nutse ta waiwaya tana duban falaak data shigo dakin da sallama gami da amsa mata sallamar,rungume take da litattafanta,wani kwantaccen murmushi yana fita saman fuskarta. Idanunta ta lumshe ta kuma budesu duka lokaci guda,a kwanakin nan wani nutsuwa da tarin walwala momma take hanga shimfide saman fuskar falaak din. Ga wata irin nutsuwa data sake fahimtar tana shigar falaak din,duk da dama ita din bame hayaniya bace ko zafi surutu ko rawan kai,saidai tana da kuzari sosai da hira ga duk wanda ta aminta ta kuma saki jiki dashi.
Sake duban falaak din tayi,dukka yanayin dressing dinta yana sake canzawa,duk da dama can ita ba ma'abociyar shigar bayyana tsiraici bace,wannan din tarbiyyar hairaan ce......hairaan kuma rainonta ce,duk kuwa da cewa suna rayuwa cikin masu jajayen kunne,to amma wannan yanayin dake tattare da falaak na dabanne.
Har a cikin ranta,har kuma zuciyarta tana jin cewa inama ace biftu ce ta samu dukkan wannan kamalar?,inama ace biftu ce ta samu wannan nutsuwar?,inama ace biftu ce ta samu wannan walwalar?.
"Momma" Falaak ta furta a shagwabe,tana waving hannunta saitin fuskar morsa safiyya.
"Momma wannan kallon kamar bakisanni ba?" Ta sake fada a narke. Murmushi morsa safiyya tayi,tana qoqarin maida hankalinta jikinta gami da soma gyara rigar jikinta.
"Meye ne haka yake sauyamin ke falaak?,ko dukka karatunne?" Wani qawataccen murmushi daya qara bayyana kyan falaak din ya qwace mata,wata 'yar qaramar kunya da batasan me ya haddasata ba ta taso ta rufeta,saita matsa tana taya morsa safiyya gyara rigar jikin nata.
"Ko dadin karatun sheikh muhammad dinne?" Morsa ta sake fadi tana fatan samun wani haske da zuciyarta ta jima tana haska mata shi.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
Irin murmushin dazu ta kuma saki tana fara sawa morsa safiyya maballan rigar.
"Nima ban sani ba momma.....kawai dai ya iya karatu gaskiya,yana da wani irin fasahar koyar da karatu,bani ba hatta badeea tace bata taba jin dadin karatu irin nasa ba.....momma ilimin dake kanshi da fasahar dake harshensa yafi qarfin koya karatu a gida......jami'a ya kamata ya tafi cikin dubannan dalibai.....momma har yanzu mamaki nake,jikina yaqi gamsuwa da cewa shi din gama garin malami ne kamar kowa". Shuru morsa safiyya tayi,tana jin yadda falaak din ta tsinke da surutu har fiye da bayaninma da momma din ta tambayeta.
Murmushi ta saka me dan sauti,a hankali ta soma takawa.
"Nagartacce ne kenan?" Momma din ta fadi ba tare data waiwaya ta dubi falaak ba,don batason ta bata haske akan wani abu take zargi. Tasan falaak sarai,tana da wani irin alkunya,tsaf zata tsinke zaren zancan ba tare kuma da ita takai ga gaci ba.
Idanu falaak ta fidda waje tana qaramar dariya.
"Momma......idan nace miki har yau sau daya tak ya taba kallona zaki yarda?" Har cikin ranta momma din taji mamakin abun,amma sai tace
"Kaman yaya?,shi baya kallon mutane ne?".
" Momma.....bama kallo kawai ba,ko magana sau daya zuwa biyu take hadamu har a gama karatun,idan kinga yana sake fuska to da aaera ne,don ko da Aafreen ba sosai ba.....na fuskanci yana da tausasawa da tausayawa ga yara,yadda yakewa aeera karatu daban da yadda yakewa Aafreen,nima yadda yakemin daban da yadda yakewa Aafreen,wani irin qasaitaccen murmushi yakeyi momma,saika lura sosai kake iya banbancewa.......me kyau dashi momma".
"Halan ke tsira masa idanu kikeyi ko?,bayan shi kame ganinsa yake?" Maganan momma din kenan data dawo da ita hayyacinta.
Bakinta ta rufe tana dariya gami da girgiza kai,sai a sannan taga kaman maganganun data saka sunyi yawa.
"Aah fa momma.....idan zanyi tambaya ne ko shi ya tambaya wani abun,ko idan yana yiwa su Aaera karatu......"
"Sai kita qare masa kallo kafin azo kanki kenan ko?". Wata qaramar tsawar kunya ce ta buga cikin kan falaak,kaman zata nutse a wajen. Ya akayi momma ta gano ainihin gaskiyar qarshen zancan?.....da gaske ne,tana yawan satar kallonsa idan suna karatu dasu Aafreen kafin ya sallamesu yazo kansu,amma daga nan bata iya sake kallonsa,saboda wani mugun mahaukacin kwarjini yakeyi mata,idan yazo musu karatu duk sai taji ya cika gurin da kwarjininsa,wannan qamshin da bata taba jin makamancinsa ba,hannunta har rawa yakanyi wasu lokutan,tana samun lalubo nutsuwar ta ne da zarar ta gama biya karatun jiya baice komai akai ba,alamun ta iya ba gyara ba kuskure.
"Saura awa daya ku shiga aji,kinsan dokarsa ai ko?" Momma ta fada tana takawa don ficewa daga dakin,ganin falaak ta daskare a wajen ta kasa cewa komai.
Saida tayi nisa sosai da gurin sannan murmushi ya kubcewa momma din. Ta soma tariyo maganganun falaak da kuma yanayinta. Tun daga sanda taga irin yabon da sultane yayi masa,da kuma daukansa a mazaunin mashawarcinsa na musamman taji dari bisa dari ta yarda dashi. Ballantan Aeera da kowanne lokaci cikin hirarsa take?.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer ๐ณ๐ช*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA๐*
*HUGUMANKU CE*โ๐ฝ
๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
Page 71
_____________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________
Ajiyar zuciya ta sauke me nauyi,fatanta da mafarkinta a kullum shine,Falaak da akhnan suyi auren isa da qasaita.......idan tace hakan bawai tana nufin qasaitaccen namiji me kudi ba.....aah qasaitaccen namiji tsayayye isashe ma'abocin sanin haqqoqin matarsa akansa. Wanda zai tausayawa ainihin rauninsu na diya mace......zai riqesu bisa gaskiya da tsantsar amana.....koda rayuwa tazo da juyin da duk wani abu me daraja a tare dasu zai tafi ya barsu,kyau ne mulki nasaba ko dukiya?. Wanda bazai wulaqantasu ba bayan sun rasa dukkan wadannan abubuwan,wanda zai zame musu mijin HUCE HAUSHI......namijin kerewa sa'a da nunawa duniya gurin samun kulawa kariya da kuma riritawa.
GARKUWA take nema musu a sanda duniya zata iya harar rayuwarsu.......DIRKA take nema musu a sanda duniya ke neman ruftowa saman kawunansu.......MAFAKA a sanda rayuwa zata iya kadasu kota hargitsa su.
Indai ya zamana wani al'amari ya darsu a zuciyar falaak game da sheikh muhammad haisam.......lallai zatayu bacci cikin nutsuwa cikin rayuwarta,zatayi bacci harda minshari bisa samun tabbaci da yaqinin kyakkyawan zabin da falaak ta yiwa rayuwarta,saidai fatan ta samu kwatankwacin abinda take tare dashi daga gareshi.
Amma can qasan zuciyarta zataso ace dukkan hakan ta kasance da akhnan. Hakeem kusan yana da wasu daga cikin qualities din daya sanya taji ta aminta da hadinta dame martaba......amma akwai abu daya da har yanzu yake tantama a kansa. Hakeem bashi da ZAFI bashi da ZARRA baida TSAIWAR DAKAN da take tunanin ita kadai ce zata bashi daman juya akhnan......ita daya ce zata bashi daman tafi da ita a sunan matar aurensa. Har a qasan ranta takejin kamar shi din BA JAJIRTACCE BANE.....irin jajircewar da take buqata take fatan ta kasance cikin jini halayya da dabi'un dukka mijin da zai zama mallakin akhnan din,domin sune abokan tafiyar iya zama da wannan TAURIN KAN nata,sune abokan tafiyar wannan KAFIYAR TATA.
A wannan yammacin tana jin dukka dauriyarta ta qare,tana buqatar riskar akhnan din a inda take,ta zauna da ita,tayi maganan fahimta da ita,irin maganan da UWA zatayi da DIYARTA.
Ta kusa da parlor din qarshe ta samu buhaina tana faman goge gogen falon da sassanyan turaren daya kama sassan,wanda anihinsa an samar dashi ne daga companyn INCENSE BY KABO DAUGHTER +234 803 211 9803. Wani turare ne na dindindin daya kama komai na parlor din. Tana tsananin son qamshin,amma ita kanta batasan daga inda ake samo turaren ba.
"Ta fito dazun,ta zagaya ta wancan shiyyar qarshen sassanta" Buhaina ta fadi kanta a duqe da girmamawa. Kai morsa safiyya ta jinjina.
"Buhaina" Ta kirata a sanyaye
"Allah ya baki yawan rai".
"Kuyi qoqarin riqe amana da kyau......ku kula da akhnan kaman yadda masarautar agadez ta yarda daku ta dauki amanar abu mafi soyuwa a ranta ta baku".
"In sha Allahu......in sha Allah da dukkanin iyawarmu,sai inda qarfinmu ya qare" Ta fada cikin girmamawa tare da jin qarin qaunar matar da ganin darajarta me tarin yawa a idanunta.
Awa daya saura lokacin karatu ya shiga ya qaraso cikin masarautar,ya kuma samu jagorancin me wada cikin girmamawa zuwa ga sashen guda da me martaba ya mallaka masa a duk sanda yake da buqatar zama.
"Allah ya qara kusanci.....dukkanin gurin nan mallakinka ne halak malak muddin rayuwarka......ga osama nan......" Ya fada yanayin nuni da wani nutsatsen saurayi.
"Me martaba yace abaka shi don yi maka dukkan wata hidima ta cikin gidan nan,kome kake da buqata kuma kana iya sanar dani,in sha Allah za'a samar maka dashi da gaggawa". Me wada ya fadi bayan ya gabatarwa da haisam kansa a mazaunin babban bawan dake da alhakin kula da hadiman dake da alhakin kula da sassannin iyalai name martaba,wanda a yanzun haisam ya shiga qarqashinsu. Koshi me wada yayi mamakin kawo haisam din kusa da villas din iyalin me martaba haka har kusa kusa,amma bayan kallon farko da ya yiwa haisam din,kwarjininsa ya cikashi ya kuma ga dacewa da cancantar hakan.
Cikin nutsuwa ya gyada kai
"Ina godiya,zan sanar idan akwai buqatar wani abu"
"Na barka lafiya" Me wada ya furta yana juyawa gami da barin wajen.
A nutse abdii wanda a yau ya samu nasara haisam ya taho dashi yake qarewa sashen kallo. Babban bangare ne da aka wadatashi da dukkan nau'in kayan alatu......saidai bai ko kama koda kwata kwata kwatar gidansu na nan cikin agadez ba.....ballantana har ya taka ya tsallaka ya kuma kai kimar sassan da prinsii haisam din yake mallakinsa cikin masarautar jimma. Kallon abun abdii yakeyi yana dariya qasa qasa,wannan shine daidai da karin maganar da yakan ji lokaci lokaci,ana cewa wai a rashin sani kaza ta kwana kan dami. Baisan adadin gidaje irin wadannan dama wadanda suka bigeshi a girma kyau da daraja ba da muhammad haisam ya badasu kyauta ga mutanen da basu da muhallin rayuwa ba,yana kuma kan bayarwa,don ko a tahowar nan tasu ana gab da kammala ginin estate guda me dauke da gidaje dubu da zai rarrabawa mutanen da basu da matsugunni,da kuma 'yan gudun hijirar da gwamnati ta yarda da zamansu. A yanzun aka saka masa bindiga baisan adadin gidajen da obbo din nasa ya gina ya bayar ba,gidaje kuma complete gida da furniture da komai,bawai kangon gida ba.
"Gaskiya ne.....nan fa babban karramawa aka yi maka ko?......da gaske ne da akace qaramin sani qunqumi" Abdii ya qarasa fadi yana sakin dariya sosai,har yana fadawa saman daya daga cikin sofas din parlor din.
"Abdii' ya kira sunanshi da wani irin tone da yaja hankalin abdii din,sai ya miqe ya zauna daga dariyar da yake qyaqyatawa.
"Ka manta da rules dina?" Ya sake tambayarsa calmly yana shawagi cikin parlor din. Gaban wani window ya isa,yasa hannu ya yaye labulen ya kuma buda window din,take sassanyar iska ta fara shigowa ciki.
"Afwan obbo.....bazan sake ba". Abdii ya fada cikin d'ari d'ari. Burinsa su zauna a nan din tare da haisam din,to ya tabbatar indai baiyi wasa ba kadan daga aikin haisam ya maidashi gida. Wannan ne kuma sam bazai iya haqura ko lamuncewa ba,qafarsa qafar haisam din,don bazai bar komai da zai cutar dashi ya rabeshi ba,zai zame masa kaman garkuwa ne koda obbo din baya son haka,zai riqe wannan amanar ta motii da nanay.
Idanunsa ya sauke ta gurin,wani irin guri ne me kyau yake fuskantar gurin,wanda da ya duba da kyau sai ya fuskanci ginin benensa na sama akwai balcony na musamman da aka fiddata tana fuskantar gurin. Wani sirrintaccen murmushin qasaita ha kubce masa,kawai ya hango gurin da zai zauna ne yayi karatunsa cikin nutsuwa,sai ya maida window din ya rufe yana dawowa da baya.
"Kana iya tafiya sai na nemeka" Yace da abdii kai tsaye.
Idanu abdii ya fiddo waje yana duban haisam din.
"Amma obbo......"
"Shshshsh" Ya fadi yana dora yatsansa akan lips dinsa gami da zubewa abdii din idanunsa.
Janye kallonsa yayi daga kan haisam din,ya karyar da wuya kalar abun tausayi sannna ya juya ya soma takawa. Har yakai qofa ya tsaya.
"Ko kace na yafi zan dawo obbo.....Allah bazan iya zama can gidan ni kadai ba.....zan dawo,Allah obbo zan dawo" Ya qarasa fada da sauri yana fita a sassan don kada ma haisam din ya fadi abinda zai karya tsarinsa.
Murmushi kawai yabi bayan abdii dashi,ya sani dama indai abdii ne saidai kawai yayi haquri ya qyaleshi,to amma dole ya kiyaye wasu abubuwa muddin zamansu yana so ya yiwu,dole ya ajiyewa abdii wani jadawalin tsare tsare.
A nutse yaci gaba da bincike dukkan wani loko da saqo na sassan,yana kuma nazartar komai. Saboda qwarewa da yadda aikin sarrafa tsaro yabi jikinsa......ba wani guri da yake sauka hakanan ba tare daya karanci kimiyyar yanayi da kuma tsarin gini dana tsaron gurin ba.
Kusan komai yayi masa,ba wani abu da yaji zuciyarsa bata gamsu dashi ba,don haka ya soma takawa yans fitowa da nufin karantar dukka farfajiyar dake kewaye da ginin kafin ya wuce zuwa makaranta.
*AKHNAN*
A qalla ta kusa mintuna goma Idanunta a runtse,tana kuma jin yadda iska ke wasa da gashinta daga hagunta zuwa damanta.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
A yau cikin rad'in kanta taji buqatar fitowa daga sassanta zuwa wannan kebantaccen gurin,wani guri da yake daga baya kuma daga qarshen sassanta wanda yayi linking da sashen dake maqwaftaka da nata,sashen daya zamana ba kowa a ciki iya saninta tsahon sanda aka ginashi,don haka take matuqar son zaman gurin a lokuta da dama saboda akwai privacy sosai a gurin.
Kowanne zaren tunani da kuma tarin lissafe lissafen mafita ne suke kai kawo cikin kanta. Mammina din dai,ita kadai lissafinta yake bata duk inda taje ta bugashi ta dawo.......ita daya ce mafitarta dake tafin hannunta. Hatta da mamminan an sanar mata zuwanta kusan sau hudu,amma taqi yarda a barta ta shigo ballantana ta samu damar ganinta,amma a yanzu zuciyarta na jaddada mata ita kadai ce dai zata isar da ita ga muradinta........MORSA ce kawai keda wannan matsayin,amma bata fatan abinda zai sanya ta roqi kowacce alfarma daga gurin morsa safiyyan har abada.
Tun daga nesa data zuba mata idanu sosai,sai take ganin wani sashe na kamanceceniya tsakaninta da safeena dinta,abinda ya karyar mata da zuciya kenan,ya taso da wani irin yanayi me qarfi ya azashi saman zuciyarta.
A nutse ta iso gabanta,duk da akhnan din taji alamun taku amma hakan bai sanyata ta bude idanunta ba,saboda ta sani,koma waye yake shigowa gurin cikin mutum biyu ne mafiya muhimmanci a rayuwarta,mammina ko sultane,wanda bata sanya ran zai tako inda take a cikin irin yanayi da suke ciki ita dashi yanxu.
Tsaiwar takun ya sakata bude idanun nata a hankali,saidai kuma wadda ta gani din bata taba tsammanin ganin nata ba.
Abinda tafi hasashe da tunanin zata iya aikatawa shine,ta miqe kawai ta matsa daga gurbin da matar ke tsaye,don ba wani dalili ko hujja na hada muhalli da