Showing 147001 words to 150000 words out of 178317 words

Chapter 50 - LU'ULU'U COMPLETE

dubanta tana sakin wani murmushi. Gyaran murya yalwa tayi wadda ke zaune a gefanta,abinda yaja hankalin mammina kenan ta maida dubanta ga yalwa,sai yalwa din ta sakar mata murmushi.

"Akwai wani sabon karatun hala uwar dakina?". Jinjina kai sosai mammina tayi tana dauke idonta daga kan yalwa.

"Wani lokaci kina da son jin gulma yalwa" Dariya yalwa ta saki tana sake yin qasa da kanta.

"Ba son gulma bane Allah ya baki dogon kwana....kawai dai na sani,a dukkanin motsinki.......a dukka wani abu da zaki aiwatar.....dukkan wani second qwaya tak na rayuwarki darasi ne ga duk wanda ya rabeki......tabbas a wannan motsin akwai wata maganar......akwai wata hikimar,akwai kuma sabon aiki....sabuwar kwangilar da na tabbatar ta sake shigowa da sabbin jerin sahun sunayen da babu su asali a cikin aikin" Murmushi sosai da yafi kama da dariya mammina tayi tana dunqule hannunta guri guda kaman wadda ta kama wani abu.

"Daya daga cikin abinda ya sanya na zabeki kenan,daya daga cikin abinda ya ya sanya nake kuma sonki kenan yalwa......kina da saurin kama abu da zaquloshi" Ta furta tana miqewa tsaye.

"Tabbas......wasu sun shigo tsarin......wasu kuma sunayensu sun fice.....akwai yuwuwar shigar wasu kuma a nan gaba,don suna tsakanin gaba ne......saidai ki sani yalwa,ita matsala daga sanda ta qunshi ciki kake rainonta.....kake kula da ita......daga sanda ka fahimci tana yunqurin haife wannan abinda yake cikin nata,hakan yana alamta maka sabbin rassa take shirin zubawa.......sai kayi dukkan me yuwuwa wajen murqushe wannan naqudar......" Saita waiwaya tana duban yalwa

"Idanma fa har kayi saken da matsalar taka ta qunso wani abu kenan" Ta qarashe maganar da wani yanayi a idanunta da kuma muryarta.

Kai yalwa ta jijjiga alamun fahimta ganewa da kuma gamsuwa. Tana kuma sake juya girman iya tsari iya yaku da iya tafi da komai cikin wani madaukakiyar basaja da bad da kamanni.


★★Magazine na qarshe ya rufe ya kuma dorata a hankali saman sauran magazines din da suke gefansa yana furzar da siririyar iska daga tsakiyar tausasan labbansa dake da wani irin launi da yanayi me jan hankali.

Tun sanda yazo agadez ya zame masa dabi'an duba jaridunsu. Da farko me kawowar ya tsaya mamakin me zaiyi da jaridu?,bayan a iya abinda ya sani bai iya yaren French ba ballantana ya fahimci abinda suke rubuta ba,saidai abdii ya datse wannan mamakin ta hanyar fadi masa.

"Abinda akace kayi kenan". Cikin ran abdii yana masa kyakkyawan uzuri.

Ko shi yasha mamakin yadda captain obbo ke iya sarrafa yaren English da French a harshensa,kai kace yana yara yaren oromo ne,hankali kwance da wani irin qwarewa da accent din da ko cikin mafarki zai qaryata cewa captain obbo dinne. A hankali yake karantar cewa aikinsa ya dace dashi,hakanan aikinsa ya dace da yanayinsa.....komai nasa yana da wani irin sirri,yana kuma da wani irin tsaro. Ba komai daya shafeshi yake bari a sani ba,sai abinda shi din ya aminta ko ya yarje maka ka gani ko kuma ka sani.

Sau da dama dabi'unsa na bala'in burge abdii din,harma yakan zauna ya dinga imagination na kanshi a matsayin muhammad haisam din.

A nutse ya miqa dogon hannunsa ya jawo wani dan littafi dake dauke da calendar din shekarar da muke ciki gaba daya. Watanni goma sha biyu ne a ciki,ba kaman calendar qasarsu Ethiopia ba,da su suke da watanni goma sha uku a shekara.

Duba kwanan watan yau yayi,wanda a kansa yayi cycling dinsa da maka,wannan ya tuna masa schedule dinsa na yau,sai ya maida calendar ya ajiye,ya zaro wayarsa ya soma kiran hussam.

Bugu daya ya dauka,cikin girmamawa da barkwancin nan nasa ya soma gaidashi.

"Barka da rana captain obbo". Numfashi yaja kadan yana lumshe idanunsa,ya rasa me yasa duk yadda yakai ga tsare gidansa sai hussam yayi wasa dashi?. Nanay kanyi dariya,duk da kasancewarta bame yawan magana ba,takance.

"Yana kallonka a matsayin sakonsa,ya manta cewa inda Allah ya qaddara amud yana raye shine sakonka". Zuwa yanzun ya soma sabawa da halin hussam,ba komai bane yake bashi muhimmanci ba......a haka yaci nasarar soma sauya masa halaye na maida abubuwa serious daga kasu ashirin zuwa kaso tamanin.

"Barka......ina fatan kowa yana lafiya?".

"Alhamdulillah......se kewarka da kowa keyi,nanay nata boyewa.....amma ni nasan hakan koda zata boye din kuwa" Boyayyen numfashi haisam ya sauke,ya sani nanay zatayi kewarsa akan kowa,daga ita kuma sai noorah daya tabbatar ita zata biyo bayan nanay din. Akwai shaquwa da qauna sosai tsakaninsa da 'yan uwansa.....hakanan ko a tsakanin junansu akwai wata soyayya me yawan gaske.

"Nan kusa in sha Allah.......yau nawa ga wata?" Haisam ya dora kai tsaye akan dalilin kiran.

"Sha takwas obbo" Kai ya jinjina a nutse.

"Dukka security din bangaren motii,dana bangaren nanay zasu bar bakin aiki a yau.......inaso su koma bakin babbar qofa,na babbar qofa dana kewayen gidan gaba daya aikinsu zai dakata.....za'a kawo wasu yau,bana buqatar ka sanar da kowa,zanyi magana daga headquarter,zasu zo su kwashesu su kuma kawo wasu" Yayi magana da calmness dinnan nasa dake nuna adadin rashin son hayaniyarsa.

Shuru hussam yayi,yanason tuna watannin da kwata kwata mutanen sukayi. Wannan wanne irin aiki ne da yake sanya obbo din rashin yarda da kowa,musamman akan motii da nanay?,idan zai iya tunawa cikin shekara biyu kacal an canza masu tsaron wadannan gurare sau uku kenan.

Yana ji a jikinsa akwai wani dalili daya sanya yake irin hakan. Wani irin tsaro yake bayarwa a dukka wani gilmawa tsakanin sassan motii dana nanay dama fadarsa da muhalli da guraben zamansu.

Irin wannan abun ya sanya masarautar jimma ta zama ta daya,kuma ta daban da sauran kowacce masarauta dake cikin Ethiopia,masarauta mafi girman izza da fadin mulki,tsananin tsaro da wani irin tsari daya sanya idanu da yawa suke kanta.

"Amma obbo......."

"Karka tambaya.....umarni nake baka,ba labari bane ko shawara".
(08187255862 lu'u lu'u paying)

" An gama" Ya fadi cikin girmamawar nan dake a tsakaninsu tun asali. Sai haisam ya zare wayar daya kunnensa kawai ya kasheta,sannan ya dorata a hankali saman table din dake kusa dashi.

Lallausan farin tafin hannunsa ya miqa me dauke da zara zata yatsu yana kalla. Wani irin abu yaji ya tsarga masa tun daga cikin tafin hannun nasa zuwa sassan jikinsa,wanda sai daya tilasta masa lumshe idonsa kana ya budesu yana jin wani abu na bin jikinsa.

"Astgafirullah" Ya maimaita har sau biyu. Besan me yasa abun yaqi bacewa daga jikinsa dama idanunsa ba,tun daga ranar shudewar awannin da kwanakin basu sauya komai ba. A duk bayan wucewar wasu lokuta sai yaji komai ya dawo masa kaman a sannan hakan ta faru. Tafin hannunsa tsakiyar nata tafin hannun me wani irin dumi da laushi. Hannun nasa ya maida ya dunqule yana mutstsukashi a hankali wai ko zai daina jin abinda yakeji din,ranshi na baci a hankali,siririn tsaki yana kubce masa.

Itace mace ta farko da hakan ya fara faruwa a tsakaninsu. A hankali tunaninsa ya koma baya,yana tuna wancan ranar a hippodrome,kalamanta cikin gidansu na ranar juma'a dana washegari asabar. Wani tsakin yasake fusga daga harshensa yana jin wani bacin ran yana sake d'iga saman zuciyarsa. Yana jin nauyin zunubin data jawo masa ya dauka,girman zunubin taba jikin macen da ba taka ba,wadda annabi muhammad S A W yace ya fiwa mumini sauqi ya zauna a samu qusa a kafa a saman kansa bugata da guduma ya lume tsakiyar kansa.

Numfashi yaja me wani irin nauyi yana sake ambatar astagfirullah,daidai lokacin da yake bude idanunsa a hankali sai suka sauka kan fuskar omari dake tsaye cikin gurin wanda sam baisan sadda ya shigo ba.

"Kada kacemin banyi sallama ba......don bansan jazabar daka shiga ba data hanaka jin kyawawan sallamata har guda uku" Ya fada yana daukan apple guda daya dake saman tray sannan ya koma ya zauna saman kujera gami da yin bismillah ya gatsa ya fara ci.

Idanunsan nan ya zubewa omari yana maimaita abinda omari din ya fada. Banda babu 'yar qarya a tsakaninsu da kai tsaye zai qaryata omari din. Baiji wani sound ko daya na sallama ba ballantana motsinsa,kuma bayajin tunanin da yakeyi din yakai nisan da zai hanashi jin hakan.

"Kana da baqo......na dakatar dashi ne akan saina shaida maka zuwansa in kana da interest na ganawa dashi" Omari ya fadi yana sake kai apple din bakinsa.

Idanun nasa kawai ya watsawa omari da body language dinnan nasa dake nuna tambaya ga omari din.

"Kaaiii" Omari ya fadi yana gotar da nasa idanun daga cikin na haisam.

"Am telling you ka daina tsare mutum da wannan idanun naka idan ba qarya yayi maka ba,idan ba haka ba one day zaka saka mutum ma yayi qaryar,abdii yasha gaya maka hakan". Sassauta kallon nasa yayi kadan,can qasan ransa yana mamakin meye haka a idanunsa da suke yawan complain?. Shi kam zai iya cewa bai ganin komai koda ya tsaya ya kalla cikin mirror,abu daya ya sani,suna da girma,girman kuma daba me yawa bane can can,sannan wani lokaci sukan koma su rusuna kamar name jin bacci,musamman idan ranshi na bace ko kuma ya gaji sosai ko da gaske baccin yakeji.

Bai cewa omari komai ba,ya miqe tsam yana ware hannun long sleeve black shirt din jikinsa dake nade tun dazun. Da kallo omari ya bishi sannan ya sake magantuwa.

"Bansan a ciki wanne kaya bane sukafi maka kyau.....jubah?.....shirts da trousers?.....ko suit?" Yayi maganar da dukkan gaskiyarsa yana tallafe kanshi da tafin hannunsa guda daya.

Kaman baijishi ba haka yayi,sai ya duqa kadan kaman yana dauko wayarsa,ya faki idon omari din ya hado da wata babbar apple guda daya,ya dago cikin hanzari ya jefi omari din da ita yana cewa.

"Ban sani ba......wannan ta baka amsa dan neman rashin zaman lafiya,zan gayawa nanay,duk ranar da akace mayu sun kamani to tabbas cikinku ne kai da su amjad" Sosa qirjinsa inda apple din ta sauka omari keyi yana dariya bayan ya dauketa daga saman cinyoyinsa inda ta fado.


zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽


💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


Page 70
____________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
__________________________





"Ka tunamin da masoya......yau ya kamata mu hadu mu sada zumunci koda ta video call ne........amma dai gaskiya ce ba zamu daina fadi ba,ka rufa mana asiri ka fidda mata ko za'a samu kaifin kyan nan da abinda ke diban mutane ya ragu".

"Saika aurar dani din ai" Ya amsa masa qasa qasa yana sauka da stairs din cike da karsashin nan nasa da cikakken kuzari irin ta lafiyayyen namiji.

"Saura qiris.....menelik na nan,ga kuma saamee,auren gata,mata biyu a rana daya.....motii yafi daukan jikokinsa da yawa kuma da wurwuri.......don wallahi a idanunka naga duk matar daka aura zai wahala ta cika shekara daya babu d'a". Wannan maganar ta omari ta qarshe ta sakashi sakin murmushin da baiyi niyya ba. Omari yafi kowa shige masa hanci da qudundune,bai sani ba tsananin shaquwarsu ne ya kawo haka?. Yafi kowa gaya masa maganganu ire iren wannan gaba gadi,ba kunya ba shayi ko nauyin abinda zai fito daga bakinsa. Tabbas banda yanzun yana da abunyi me muhimmanci sai ya koma ya samu omari ya gaya masa wanne irin kalar sharri ne yayi masa haka?,amma ya saka maganan a mala,tabbas sai omari yayi bayaninta.

Bedroom dinsa ya koma ya daura alwala,sannan ya tsane ruwan da towel,don yasan zai wahala kafin su gama ganawa lokacin sallah bai shigo ba. Babban minister ne harkokin tsaro na cikin gida,yasan da zuwansa,amma bai bashi daman zuwa din ba,bai kuma zaci zaizo koda bai samu izini daga gurin haisam din ba. Tunda ya riga yazo bazai qi ganinsa ba,don mutuntawa da martabawa suna daya daga cikin kyawawan halayen haisam din.

Kafin ya fita ya dauki personal waya ya kira security kan su bashi masauki gashinan fitowa.

Da wannan kwarjinin cikar haiba da kamala yake takawa zuwa inda ya bada umarnin a saukeshi. Tsam ya miqe wani irin kwarjinin haisam din yana cikashi tun kafin ya qaraso. Wani gefen na zuciyarsa kuma mamaki ne yake kamashi,a qalla ba aksar ba,ya haifi haisam din,bai taba zaton ganinsa yaro qarami irin haka da wannan babban muqamin ba. A shekarunsa ba'a taka matsayin dashi yake dashi cikin national security intelligence agency.

Kai tsaye haisam ya bashi hannu shima ya miqa masa suka gaisa.

"Bismillah" Haisam ya fadi yana masa nuni da mazauni cikin nuna alamun girmamawa. Abun ya burge minister sosai,akwai alamun tarbiyya da kuma ilimi me zurfi a tare dashi. Sai da minister ya zauna sannan shima ya zauna suka sake gaisawa kafin su fara tattaunawa akan dalilin zaman.

Kusan duka tattaunawar tasu da harshen French ne......abinda yayi matuqar bawa minister houdu mainassara mamaki. Yadda yake sarrafa yaren saman harshensa zaka rantse haihuwar qasar French ne,harma yana so ya fishi qwarewa wajen furta yaren kaman shine da kuma haifaffe ga yaren.

"Mun lamunce da zamanku......kuma zamu baku dukkan wata gudunmawa wajen kama wanda kuke nema,muma din zai bamu cikakken tsaro ai da kwanciyar hankali cikin qasarmu". Kai haisam yake gyadawa cike da nutsuwa.

"Ma sha Allah.....a madadin gwamnatin qasar Ethiopia da shugabannin NISS muna miqa godiya a gareku da gwamnatin qasarsu,kuma in sha Allah zanyi qoqari a yau dinnan zanyi magana da His Excellency mr President,zan shaida masa goyon bayan da muka samu daga gareku" Murmushi houdu mainassara ya saki,haisam din yana sake burgeshi ya miqa masa hannu suka sake musabaha. Confidence dinsa da irin qwarewarsa,fasahar zance da yadda yake kowacce magana cike da nutsuwa suna sake kama hankalin mainassara.

"Ina fatan zumunci bawai zai tsaya bane iya batun daya shafi aiki kawai" Minister ya fadi sanda haisam ya masa tattakin rakiya zuwa bakin motarsa guda daya da yazo da ita saboda kauda hankalin jama'a daga kansa.

Murmushi haisam din ya saki,bai fahimci me mainassara yake fadi kai tsaye ba,amma with time yasan zai fahimta.

"In sha Allah.....saidai kada ka sanyani alqawarin yin ziyara a tsakaninmu saboda yanayin aiki" Dariya kadan mainassara ya saki yana jinjina kai

"Bazan sanyaka ba,har sai sanda ka gamsu da kanka,ko ni aka bani dama nazo" Kai haisam ya jinjina,ya kuma ja da baya da kansa yana rufewa mainassara qofar motar.

Tare suka taka da omari suna komawa ciki yana gayawa omari din wasu daga cikin abubuwan da omari xai iya sani.

"Mun kama hanya,inaji a jikina" Omari ya fadi,sai haisam ya gyada kanshi.

"In sha Allah,komai zai tafi daidai".

Lokaci ya duba sanda yake komawa daki,akwai sauran mintuna kafin ya fita agadez palace,don haka ya zauna ya soma lalubar number president na Ethiopia don bashi bayanan da suka dace,kafin nan kuma ya kira bobbo muhammad daud shima.

President Amaan Mikel andom wanda haisam yayi saving number dinsa da Mr amaan. Daya daga cikin tsayayyun shugannin qasa a tarihin Ethiopia da qasar ta samu,jajirtattu da sukayi tsaiwar daka a kanta.

Kasancewar masarautar jimma daya daga cikin masarautun dake da girma da qarfin iko.....kyakkyawan tsari na aiwatar da mulki da samarwa mutanenta ci gaba ya haifar ya kuma samar da kyakkyawan alaqa tsakanin gwamnatin qasar Ethiopia da masarautar. Uwa uba tsirowa da kuma samuwar jajirtaccen dan kishin qasa,qwararren ma'aikacin national intelligence and security service prinsii muhammad haisam cikin masarautar jimma,wannan ya qara zurfafa alaqa a tsakaninsu.

Samun irin haisam cikin hukumar abune me wahala,matashi me ji da gata fikira kyau uwa uba ga sarauta a gefe,amma hakan bai hanashi jin sha'awar taimakaw qasarsa da dukkan fikirar da Allah ya bashi ba.

Muhammad haisam din yayi ayyuka masu tarin yawa.....ayyuka masu zafi wadanda ba'a taba yin irin su a tarihin hukumar ba,wannan ya sanya sosai mr President Aamani yake ji dashi.

Tun ba'a wani jima ba yaso hadashi da d'iyarsa,shalelensa wadda ita daya ce 'ya mace daya haifa wato HAANA amma a hankali da kanshi ya fahimci hankalinsa baya ta gurin. Duk da hakan bai sanya ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login