Showing 60001 words to 63000 words out of 178317 words

Chapter 21 - LU'ULU'U COMPLETE

maqiyi dama koda ta takin qafa guda daya tak ne!......wannan matsoracin macijin dake fakewa daga raminsa ya sadado yayi muku b'arna ya koma.......ko ya sadado da zummar cutarwa........ba murna zakuyi saboda hargaginku yana sanyashi razana ya koma ba......a'ah.....tunkararsa zakuyi......ku bishi ku zaquloshi kuma kuma illata qarfinsa......ku maida jarumtarsa zuwa tsoro da kuma rauni". Ya qarasa maganar yana jin yaqininsa da qarfin gwiwarsa akan tafiyar tana ninkuwa.

A hankali omari ya dora hannunsa saman bayan hannun haisam,muryarsa a tsinke kuma can qasa yace.

"Na fahimta......na fahimceka haisam......wannan aikin bana qasar Ethiopia kawai bane.....aikin yiwa kaine.....aikin bawa mooti daya zama uba a garemu gaba dayanmu kariya.......na fahimta". Musayar kallo suka yiwa juna shida omari na wasu sakanni,kafin haisam din ya saki qaramin murmushi yana gyada kai,sannan ya juya yana ci gaba da tafiya.

"Sassauqar hanyar shiga kawai ta rage mana mu nema"

"Zamu samu!" Omari ya fada da qarfin gwiwa hadi da saki murmushi ya biyo bayan haisam din.


★Su biyu ne rak zaune cikin farfajiyar da aka qawata da nau'in shuke shuke dake sake bawa gurin wata nutsuwa da kuma wani yanayi na musamman. Tsaf gurin yake da wata irin tsafta da ba abinda ya cakuda da shukokin gurin balle ya jirkita nau'insu kyansu da kuma tsarin su.

Daga gurin daya zamana na musamman saboda xamanta kuwa.......shimfidu ne na alfarma na wasu lausasan carpet,bayan wasu manya da madaidaitan fililluka da aka yiwa ado da gashin dawisu,aka kuma rubucesu da sunan masarautar AGADEZ din.
(08187255862 lu'u lu'u novel)

Qaramin sharhin littafin iziyya ne a hannunta da take duba sharhin cikin wasu fasalai........ A zahiri karatun takeyi sosai,saidai kuma a bad'ini hankulanta ya kasu gurare da yawa.

Hankalinta na farko yana kan yaran dake sabgarsu daga gefanta. Tun sanda suka iso momma safiyya ta fahimci sakewa da walwala sosai daga yaran. Bata samu haihuwa me yawa ba.....kaman yadda sultane bai dasu da yawa.......amma Allah ya mallaka mata jikokin da suka share mata hawayen samun yara,ba ita kadai bama......harda sultane din.....duk kuwa da cewa dukkaninsu ba wanda ya haura shekara goma sha biyu.

Abu na biyu kuma hankalinta da tunaninta yana kan maganar da sukayi jiya da dare ita da falaak.

"Kin kira yayarki kuwa?" A nutse falaak din ta gyada kai

"Na kirata momma.......har sau biyu,amma bata daga ba bata kuma kirani ba" . Shuru momma tayi tana qoqarin boye bacin ranta. So take ta hadiye emotion dinta,don babu buqatar falaak ta fahimci komai,batason qara ciwo akan ciwo Tsakaninsu. Zuwa yanzun batasan falaak din ta sameta ko bata sameta ba?.

Daidai sanda take rufe littafin gami da fidda ajiyar zuciya falaak din ke takowa gurin. Doguwar matashiya wadda duka shekarunta ba zasu haura goma sha biyar ba. Sanye take da baqar yalwatacciyar abaya data lullube ilahirin jikinta gaba daya,banda saman qafafunta da hannayenta ba abinda kake iya gani. Wasu irin kamanni ne suke bayyana kansu......wasu irin kamanni dake nuna tsakanin qarfin jini nasaba da dangantaka tsakaninta da AKHNAN. Ba kamanni na fuska ba......kamannin da bahaushe yake cewa KAMANNIN JINI,wanda girman dangantaka da nasabar jini ke nuna kanta. Kamar jini ce kawai,amma kamanni na halitta tako ina sunsha bambam,kamar yadda suka yiwa juna nisa ta fannin halaye da kuma dabi'u.

Launin fatar falaak wankan tarwada ce.....amma irin me hasken nan da kadan ya rage a sanyata cikin sahun fararen mata. Tana da tsahon data dara akhnan,don idan ka kalli falaak zaka iya zaton ta haura shekarunta. Tana da sauqin kai,tana kuma da sauqin mu'amala......dukkan halaye da dabi'unta sun hau da mizanin da momma taso akhnan ce saman wannan dabi'un.

Gurare kadan kadan sukayi tarayya a halayensu. Falaak nada yawan shuru shuru kaman yadda akhnan miskilanci ya zame mata cikin jini da zuciyarta. Saidai falaak nada sakewa da mutum idan ta aminta dashi ko kuma ta saba dashi har kuyi hira. Falaak nada kyauta.....girmamawa da mutunta dan adam......yayin da ba lallai ka fahimci wadannan daga gurin akhnan nan ba......don bata jibanci kowa ba......batayi mu'amala da kowa ba ballantana ka fahimci inda tasa gaba. Komai na AKHNAN din ta tsarawa kanta iya ita daya,sai wanda taso sai wanda ta gayyato sai kuma wanda ta yiwa ALFARMAR YAYI TARAYYA DA ITA.

Aeeda ce ta watsar da kayan wasan hannunta,ta rugo da gudu tana nufar falaak din. Tsoro yadan shigi falaak ganin gudun da Aeeda takeyi,ta tabbatar kuma daneta zatayi idan tazo,batajin kuma tana da sauran qarfin da zata riqesu ba tare da sun fadi ba,don haka kafin Aeeda ta qaraso falaak ta durqushe a wajen tana cusa kanta tsakanin qafafunta.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


PAGE 29
__________________________
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500 dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. ⁠married femfresh wash 2k
3. ⁠garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. ⁠Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. ⁠Tsimin mallaka 2500
6. ⁠maganin infection 1500
7. ⁠matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
____________________________



Cikin dariya Armelle da qarasowarta gurin kenan ta daga Aeeda cak tana dariyar da momma dake zaune daga nesa tana kallonsu itama ita takeyi. Aeeda qarfi falaak tsoro,cikin sati guda kacal da zuwan yaran sun bata wani farinciki......sun bata wani nishadi da nutsuwa,taji a jikinta tamkar tana hadewa da kammale ahalinta guri guda da wani irin kyakkyawan fata da kuma saka ran su zama wasu ababen alfaharin qasar niger da masarautar agadez din gaba daya.

Falaak dake durqushe batasan me ya hana Aeeda qarasowa ba,tadaiji muryar armelle tana cewa.

"Matsoraciyar uwa......ki miqe hakanan,aeeda ta barki da tsoronki". Kanta ta daga idanunta suka sauka kan armelle dake dauke da aeeda,saita saki wani gauron numfashi ta miqe tana gyara yafen mayafin abayarta da sulbin gashinta ya sakashi sulalewa ya fadi.

"Kwanan nan zan fara raba hanya dake aeeda.....ke bakisan kalar qarfin da kike dashi bane?". Sosai aeeda ta riqe wuyan armelle tana dariya abinta. A shekarunta guda hudu rak da take dasu,itakam ba komai bane ma take fahimta ba,ko yanzun ma hargagin falaak dariya ya bata,ta riqe armelle da kyau wadda take nufar momma don isar mata da saqon da take dauke dashi.

"Sauketa armelle......wannan inajin anya ba noma zamu koya mata ba?" Momma ta fada muryarta a washe. Dariya armelle ta saki,ta tsugunna tana sauke aeeda,wadda kaman jira takeyi ta fella ta koma wasanta abinta.

Gefen momma falaak ta zauna tana mitar qarfin aeeda,momma ta kalleta kadan

"Kin sake kiran yayarki?" Dakatawa da maganar falaak tayi sannan ta girgiza kanta a nutse.

"Na manta momma ban sake kira ba". Dauke dubanta tayi ta mayar kan armelle.

"Dauko wayata ki kiramin biftu"

"In sha Allah" Armelle ta fada tana matsawa daga gefe kadan ta dawo da wayar.

Shuru ne ya ratsa wajen sanda wayar ke bugawa tana ringing tare da tafiya kai tsaye zuwa wayar wanda aka kira din.


*AKHNAN*


Duk da cewa ranar tana cikin ranakun fitarta aiki.......amma saita soke fitarta aiki a ranar. Ta tabbatar kusan d'ai d'aikun mutane ne cikin ma'aikatan company dinta,manyan da qananan wadanda basu kalli wasan ba,ta kuma tabbatar da yawansu jiran isowarta company sukeyi. Duk da basu da wata fuska ko kuma damar da zasu iya fuskantarta da magana makamanciyar wannan......don kuwa baqon abune ganin fuskarta koda kuwa kai din dan halalin kamfanin ne. Samun damar ganinta yana ga d'ai d'aikun mutane,su dinma sai abinda ya zama dole,so ba wanda yake da cikakken access da office dinta ballantana ya samu ganinta kai tsaye.

Ko ya zama dole ka ganta,to sai ka shallake wadansu mutane kafin ka samu izini da daman hakan,cikinsu harda aisa da shehnaz.

Haka kawai take jinta cikin nishadi,musamman da gidan ya zamana ba 'yan takurarta aisa da shehnaz,don dukansu sun fita office ita daya ta rage.

Ko da buhaina ta hada mata breakfast ma kadan taci ta koma ta kwanta abinta. Bacci tayi sosai,don da qyar ta tashi tayi sallar azahar,sannan ta zauna tana duba ayyukan dake office ta cikin system dinta. Awa biyu ta shafe kafin ta janyo waya tayi kiran barra'u.

"Hadamin ruwan wanka" Ta fadi ba tare data kalleta ba tana qoqarin concluding wani report data gama summary dinsa.

Cikin girmamawa ta wuce,ta kuma shirya mata toilet din,hatta da towel ta ajjiyeshi a inda ya dace,ta kuma saisaita yanayin dakin yadda zai dace da jikinta yadda takeso,sannan ta fito tana shaida mata ta kammala.

Batace komai da ita ba,itama bata wani damu da hakan ba ta taka ta fice don ta turo birra ta qarasa aikinta. Da sallama birran ta shigo,ko kafin tace wani abu akhnan ta daga mata yatsunta,abinda ya alamta mata bataso tace komai.....ta wuce kawai tayi aikinta,sai ta wuce zuwa cikin.

Sashen kayan sawarta ta isa,ta kuma zabi sutura kala biyar kamar kullum,ta duba bangaren undies ta ciro mata,sannan ta fito dasu ta jera mata su saman gadon. Kusan a kowacce rana hakan ce take kasancewa,birra buhaina bushira da barra'u sune duk wani motsi nata,sune komai nata. Ida akwai wani abu da akhnan ta sani shine ta zare tufafin dake jikinta ta watsar ta shiga ta wanke fatarta ta dauro jikinta da towel,sai sanya under wears dinta kawai. Wani lokacin hatta da kayan nata sai sun taimaka mata wajen sanyawa,musamman idan suka kasance ba simple dressing zatayi a ranar ba. Kamar ta fannin abinci,abinda kawai ta sani shine........ta duba me aka dafa,idan yayi mata tace su zuba mata ta tsakura ta tashi tabar gurin,idan baiyi mata ba ta saka order na wani abun a kawo mata,musamman idan 'yan sarautar suna kusa,bata sha'awar fita. Wani lokaci ma ciye ciyenta zatayi kadan taci gaba da harkarta,kasancewar sam abincin bai dameta ba. Koda taci abincin dan abinda takeci din bai kai ya kawo ba,amma hakan bai hanata jikinta da fatarta wani irin kyau murjewa da kuma daukan hankali ba,kasancewar tana ta'ammali da madara shanu data raqumi tatacciya.

Ko a yanzu ma data gama system din nata kawai ta iya dauka saboda muhimmancinta tana wucewa ciki da ita. Bayan ta wuce toilet birra ta dawo ta kwashe komai ta killace,ta kuma dauke inner wears dinta ta wuce dasu zuwa laundry room don tsaftacesu kaman yadda suka saba.

Da dogon towel nannade saman kanta ta fito,wanda da alama wankeshi tayi saboda yadda qananun gaban goshinta suka kwanta sosai a goshinta. Da idanu takebin kayan daya bayan daya tana son gane wanne ne ya dace da yanayinta.

Qaramin tsaki taja tana ware towel din gami da zareshi daga kanta ta wurgar dashi a gefe,wannan ya bawa dogon gashinta da tsahonsa yakai har saman mazaunanta kadan bai qarasa kansu ba damar warewa. Hannu tasa ta sake daga kayan,batasan sai yaushe birra zata daina debo mata kayan da basu dace da yanayin ba.

Watsar dasu tayi ta koma bakin gado ta zauna,ta jawo wayarta tana qoqarin kiran birra kan tazo ta maida kayan ta debo mata wasu kiran momma din ya shigo.

Idanu ta zubawa screen din wayarta daketa motsa numbers din dake kai kawo saman screen din. Ko sau daya bata taba sha'awa ko marmarin saving number wayar matar ba. Har yanzu ta kasa jin akwai alaqa a tsakaninsu kamar yadda sultane da mammin suke fada. Zuciyarta empty take akan matar.......ko kwatar kwatar kwatar kwatar abinda takeji akan mammina babu shi ko digo a zuciyarta a kanta.

Sau da dama ma tana mancewa da ita cikin rayuwarta,tana mancewa da komai daya shafeta,ciki kuwa harda falaak din. Duk da cewa yarinyar bata cikakken sati bata tabata ba,kota watsapp din da take jimawa batabi ta kansa ba,ko ta email da sauran hanyoyin tura saqonni,saboda abune me wahalan gaske ta kirata,kamar yadda itama ba zata iya tuna lokaci na qarshe data kirata din ba.
(08187255862 Lu'u lu'u novel paying)

Ganin kiran ya sake shigowa a karo na biyu ya sakata sakin qaramin tsaki,tana jin kamar ta dameta ne,tana da tabbacin kafin su kammala wayar saita gaya mata wani abu da zai sanya ranta ya baci. Batasan me yasa ba kullum wani irin kallo take mata,tana ganin kallon da take mata ma kaman bata aminta da zamanta a Niamey bane,tasha fadi kuma yasha shiga kunnuwanta,don matar macace da bata shakka ko shayin fadin maganar data dace da ra'ayinta,koda akan waye kuma koda a gaban waye.

Muryar falaak da taji tana sallama ta sassauta mata abinda takeji a ranta. Ta amsa sallamar cikin qasaitarnan tata.

"Bonsoir sœur chérié(barka da yamma lovely sister)" Falaak ta fada da wannan sanyin nata.

"Chérié?(abar so?)" Akhnan ta fadi qasa qasa tana juya kalmar. So take ta fadi wani abu da zai hambarar da kalmar ko yaya ne,amma sai bakinta ya gaza furta komai. Tadan nisa kadan muryarta a nutse ta amsa mata.

"Bonsoir"

"Kina lafiya yaaya?.......inata kiranki ban sameki ba" Falaak ta sake fadi can qasan ranta tana jin wani abu yana motsawa game da akhnan. Duk duniya zata iya cewa ita daya ce......tana jin wannan kadaicin har cikin jininta.......duk duniya akhnan kawai zata kalla a mazaunin shaqiqiyar 'yar uwa,wadda ba wani dama komai qanqatarta da zata iya yanke ko rarrabe jinin da yake gudana jikin akhnan da irin jinin da take gudana a nata jikin. Hairaan ce ta biyu....hairaan din ce kuma tayi qoqari matuqa wajen cike mata dukkan wani gibi da takejin tana dashi,saidai akwai wannan gurbin,har yanzu akwai wannan space din da babu abinda ya cikeshi.

"Je suis accupé(nayi busy)" Ta fadi a taqaice tana duban birra data shigo dakin a sannan ta kuma duqe tana jiran umarninta,sai tayi mata nuni da hannu akan ta kwashe kayan ta maidasu inda ta debo,daidai sanda falaak ke gaya mata.

"Na kira mu gaisa......na gaya miki mun dawo agadez.....ni da aeeda da Aafreen". Shuru tayi tana son tuna yaran su waye?. Tasan hairaan.....tasan kuma itace mamarsu......amma sukam yaran ko cikakken kamanninsu ba zata iya tunawa ba,hasalima sunayen nasu banda yanzun falaak data fadi babu guda daya data riqe. Ta taso a matsayin 'YA GUDA.....ta taso a sansanin da babu wani yaro da ake gani......ba wani yaro da ake bawa kula gata da tarairaya.......ba wani yaro daya isa ya gilma ya gaban shugabancinta,ta gaban qaunarta.....ta gaban iko da sangartarta,da haka zuciyarta ta ginu ta wani sha'awar yaro burgewa ko qauna. Ita daya take kalla a matsayin yarinya a wancan lokacin,a yanzun kuma ita daya take kalla a mazaunin wadda ta samu dukkan soyayya.

"Yayi" Ta sake amsawa a taqaice,qasan ranta tana jin meye hadinta da dukka wannan labarin?,meye alfanun da zata samu da falaak ke bata lokacinta haka?.

"Yaushe zaki shigo agadez?......II y a longtemps que nous ne nous sommes pas rencountrés(mun dade bamu hadu ba)"

"Pas pour le moment(ba yanzu ba).....Appelle-moi plus tard,merci(kya sake kirana wani lokacin.....na gode)" Sai ta yanke kiran tana jan siririn tsaki gami da kangarar da wayar a gefe tana matse yatsunta guri daya.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login