Showing 171001 words to 174000 words out of 178317 words

Chapter 58 - LU'ULU'U COMPLETE


★***Da kallo birra ke binsa sanda taga fitowarsa daga shiyyar mammina. Tadan sake kallon sararin sama tana qiyasce nisan dare a wannan lokacin. Ko ba'a gaya mata ba tasan cewa dare ya soma shiga sosai,kuma doka ce a dukka fadin gidan na haramtawa kowanne jinsi shiga sashen da bana jinsinsa ba,daga sanda akayi kiran sallar magariba. Abu mafi ban mamaki ya fito ne daga sassan da sukafi kowanne tsaro,sukafi kowanne dokoki tsaurara,kuma a cikin dare irin wannan?.

"Gimbiya akhnan ce take kiranka" Ta fada tana rusunar da kanta ganin irin kallon da yake binta dashi,fuskar nan mai cike da qasumba a dinke tsaf.

Sosai yaji batun yazo masa banbarakwai,saboda wannan shine karo na farko da ya soma jin hakan,sai kawai ya gyara damarar jikinsa da baya rabo da ita kulli yaumin yace.

"Muje" Tayi gaba yana biye da ita a baya.

Sanda suka isa a farfajiya ta barshi,ya soma bin gurin da kallo,don kuwa wannan shine karon farko da qafafunsa suka fara taka sassanta. Sassanta yafi kowanne sashe tsananin doka tsaro da kuma qa'idojin da SULTANE kadai aka yarjewa aga qafarsa a cikin gurin. Da idanunsa yake bin ginin da kallo da mamakin yadda aka tsarashi cike da tsaro da kuma ado da qawa.

Zubewa tayi qasa tana shaida mata isowar tamim din,sai ta miqe tana gyara lullubin after dress dinta data rufe ko ina a jikinta tana fadin.

"Muje".

Da hanzari ya sauke kanshi daga nazarin da yakeyi yana maidawa inda ya jiyo takunsu,da sauri cikin tsananin girmamawa ya sauke kanshi,sannan ya karya gwiwarsa guda daya ya kaita qasa yayin daya cake tafin qafarsa a qasa da dayar qafar yana yin qasa da kanshi.

Wani girma takeji yana ratsata a duk sanda yayi hakan a gareta. Yana cikin mutane da suke lissafinta na gaba gaba da sukafi kowa iyawa da sanin yadda zasu girmamata.

"Tashi ka zauna" Tace masa bayan ta zauna,saiya tashi din amma ya tsugunna ne saman qafafuwansa.

"Muhimmin aiki nake tafe dashi......kuma nakeso idan ka fara shi ba dawowa saida cikakken amsa da bayanai masu gamsarwa".

"Umarninki kawai nake jira" Ya fadi kai tsaye,yana jin qarin samun wani matsayi daban yana tunkaroshi,yana jin cewa shi din me nasara ne da har gimbiya akhnan zata nnemeshi cikin dare irin wannan da buqatunta.

"Basai na tsaya tambaya ko tantama ba......tabbas kana da labarin tseren dokina na qarshe a hippodrome da wani baqon mutum dan wata qasa?". Kansa ya gyada a hankali yana sadda kanshi qasa,sanin halaye da dabi'unta,da kuma dokar tsanar kallo da tayi a rayuwarta.

Numfasawa tayi kadan ta kuma gyara zamanta,tana jin kamar komai zaizo da sauqi.

"Ba wani abu me yawa kome girma nake buqata ba illa sanin wayeshi?,inason samu cikakken sunanshi da kuma qasar daya fito,kamanninsa da wani abu nashi daban da zai kaini zuwa ga inda yake.......sauran ni zan qarasa aikina da kaina". Murmushi ya saki kadan.

"Aiki ne me sauqi qwarai wannan.......ki bani kwanaki bakwai kacal idan basuyi miki yawa ba" Kai ta jinjina.

"Sun isheka?"

"Tabbas" Ya fadi yana me bata tabbaci. Kai ta jinjina.

"Yayi.......saidai akwai sharuda guda biyu cikin aikina,wanda idan ka kiyayesu nan gaba zaka iya samun damar da tafi wannan daga gurina". Wani irin dadi yaji yana ratsashi,wannan aikin aikine da zaiyishi koda babu ko sisi da zai rabauta dashi,aikine da yakejin zai iya kiyaye dukkan sharuddansa komai tsaurinsu.....wannan MATSAYIN da kusancin kawai yake buqata.

"Na farko,banason kowa yasan da aikin nan.....na biyu kuma,inason ka gabatarmin da kowacce hujja shaida da kuma sakamakon bincike,ni zan fara dubawa da kaina.....ko idanunka ban lamunce suga komai ba" Ta fadi da dukkan yanayin da yake nuna da gaske take. Ta dauki wannan hukuncin ne saboda tanason zama ta farko da zataga waye din,idan har ya zamana wani wulaqantacce ne da darajarsa batakai tata ba,zai zamana babbana abun kunya wani ya san ta tsaya bata lokutanta masu tsada wajen yin tsere da wulaqantaccen mutum irinsa. Idan ita tafara gani,zatasan yadda zata lulluba komai ta kuma dauki matakin da zai gamsar da ita a sirrance.

"An gama Allah ya qara miki daukaka" Ya fada yana dunqule hannunsa a qirji alamun dake nuna girmamawa da sallamawa.

"Jeka.......zan sa ayi maka aike a safiyar gobe".

"Godiya nake bisa wannan tarin girmamawa da karramawa da kikayimin na sakani cikin kebantattun al'amuranki" Ya fadi yana miqewa ya juya ya fice.

Ajiyar zuciya ta sauke,tana wassafa irin yadda zata ladabtar da kuma hukunta mutumin. Ita daya tasan a ukun da zata sakashi,wanda saiya qare rayuwarsa yana dana sanin jaa da ita.


★★★Akwai wani sassanyan yanayi a tattare da ita wanda hatta da badee'a ta karanci hakan.

Tana da hira wasu lokutan,duk da hirarta bata zama me tsaho da yawa,amma bata fiya zaman shuru ba musamman ga mutanen da sabo kadan ya shiga tsakaninsu irin ta da suke tare kusan mafi yawan awannin wuninta.

Numfashi taja kadan,tana rufe shafin alqur'aninta. Ta juya agogon hannunta ta kalla sannan ta dora idanunta da sukayi wani irin laushi akan badee'a

"Anya yau ma zaizo?". Dubanta badee'a tayi,yadda damuwa ke son yin tasiri cikin idanunta.

" Ina kyautata zaton zaizo,a jiya da bazai zauna ba ya sanar......yauma inda bazai zauna din ba zai sanar,kaman yana cikin mutane masu tsari sosai da kuma girmama lokaci" Boyayyen numfashi ta sauke tana buda tafukan hannayenta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)


So take ta lalubo maqasudi kuma gurbin damuwar da takeji a ranta na rashin zuwansa karatu a jiya,yauma kuma kaman gashi hakan tana shirin faruwa,qarin mintuna ashirin,abinda bai taba yi ba tunda suka fara karatu.

Ba zata iya tuna sanda ya qara mintuna biyar bama,yau kuma ga mintuna ashirin suna shirin salwanta.

"Gashinan" Taji badee'a ta fada mata saitin kunnenta ta sigar rada.

Wani matsanancin faduwa taji gabanta yayi,zuciyarta ta fara qara yawan bugunta. Tanason daga kai ta tabbatar,amma kuna tana tsoron wannan kwarjinin nasa.

Gaza jurewa tayi,a hankali ta daga idanun nata da zummar koda a sace ne ta kalleshi,idanun nata suka sauka a kansa daidai sanda yake takowa cikin ginshira da qasaitar da baisan tana bayyana kanta da kanta a tattare dashi ba.

A gajiye yake,irin gajiyar da hutu kawai yake buqata. Tun goma na safe ya fita,suka hadu da omari dasu beeno,har kuma qarfe uku suna tare suna duba abubuwa masu yawan da suka bawa kowa a cikin su tabbaci tare da yaqinin NASARAR AIKINSU tana rataye masarautar agadez,amma hakan baya nufin kuma su saki sauran masarautun da kowannensu ya saje da ita yana rayuwa a cikinta.

So samu yayi zamansa cikin sassansa,ko gidansa dake waje,amma kuma bayason ko yaya yabar wata shaida ko digo ko wata alama komai qanqantarta da zata bar sahun zargi. Iya haduwarsu dasu a jiya kawai yana jin cewa dole ya sake matse kowanne motsi nasa. Indai abinda yake zargi akai ya tabbata to ya sani zai zama ana binciken bincike ne.......kallon kallo,idanu kan wasu idanun,wannan ya tilasta masa watsa ruwa me dumin gaske,sukayi jam'i shida abdii daya zube a nan saboda gajiya yana fadin bacci zaiyi,ya duba closet dinsa ya shirya cikin Moroccan jallabiyya maroon color da aka yiwa adon milk din zare.

Hula dara ya dora saman kansa ja data dace da kalar rigar sak da sak,wannan ya sanya sassalkan gashinsa ya samu yadan fita kadan ta qasan hular,abinda ya qara masa wani irin ajiyayyen kyau da kuma kwarjini na musamman. Kusan yau duk inda ya gifta cikin gidan sai idanu sun bishi da kallo,kallon da baisan mafarinsa,tun daga cikin gida abdii ya soma,bakinsa ya lura taf yake da magana yanason kuma tankawa amma yayi masa birki,dole abdii ya hadiye yana satar kallon yadda kayan suka zauna masa,yaso ya bashi fuska ya fadi abinda idanunsa suka gani,amma rashin samun fuskar ya tilasta masa kama bakinsa.

Taji wani irin kunya da nauyi sun saukar mata sanda idanunta suka fada cikin nashi.

"Innalillahi" Ta fadi cikin jin kunya na hada idanu da sukayi,da yadda kyan da shigar yayi ta wafci idanunta da hankalinta,sai tayi qasa da idanunta tana maidashi saman qur'anin hannunta.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽


💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


PAGE 81
____________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________



Shima idonsa ya dauke yana karantar wani abu tattare da yanayinta. Akwai abubuwa da yawa idan tayi da suke kasa kama da dabi'u da kuma yanayin saamee,abinda sam baya son tunawa ko hadawa kenan guri guda,don sam baya mata fatan ta fada yanayin da saame din ta fada.

Ya karanci tasirin nutsuwa da kunya sosai tattare da ita,baisan me yake neman fusgar hankalinta ba?,tunanin daya sanya yaji zuciyarsa ta quntace guri daya,yana neman amsa da laluben dalilin da yasa irin hakan ke faruwa,duk da yadda yake yawan kaucewa duk wasu abubuwa,dukkan wasu dalilai da zasu sanya mace tayi falling a kansa.

Wannan dalilin ya sanya me yawan daure fuska.......mara fara'a me fusataccen yanayi. Mutum me mugun nesa da dukkan al'amuran mata,don ya sani a yanzu bai shirya aure ba,dole ya kiyaye duk wani abu da zai sanya a shiga soyayyarshi.

Yanaso yayi aure a sanda yake da cikakken lokacin kansa......don dausayin aljanna yake son ginawa......tattausar shimfidar soyayya qauna da rahama a cikin gidan sa kwatankwacin yadda annabi muhamamd S A W ya koyar. Bayaso yayi aure a sanda baida lokacin matar......bayason yayi auren da matar zata yita sadaukar masa.......zata yita haquri dashi da irin busy dinsa alhalin kuma ita tana cutuwa.

Yanason yayi auren da MAWADDA da RAHAMA zasu zama shimfidar cikin gidan sa. Yanaso ya bawa matar da duk zata zama macen aurensa wani kebantaccen gata da zata sha banbam da kowacce mace a DUNIYA. Yana da tarin tsari da buri me yawa a gidan aurensa. Gidan SOYAYYA yakeson ya gina,ba gidan ZAMAN HAQURI ba.

Kamar ko yaushe,tana jin yadda Aeera ke riqeshi da kyau tamkar taga mahaifinta,surutunta da bakinta cakwai tana iya jiyota. Abu daya dake sake zama ado a gareshi.....duk yadda Aaera takai ga zaqin surutunnan nata ba zaka taba jin nashi muryar ba. Wata irin cikakkiyar nutsuwa da kamalar zance gareshi,yana biye mata yana kuma amsa ta,amma sautinsa daga Aaera sai Aafreen dake kusa dashi sosai sukejin abinda yake fadi.

Akwai ranar da badee'a ta matso saitin kunnen falaak da itama fiye da rabin hankalinta yana kansu,duk da littafi ne a hannunta a bude take dubawa.

"Idan ina ganin mutumin nan,saina dinga raina ajin duk wata mace me aji.......jan ajinsa yayi yawa.......gaskiyarki fa uwar dakina,komai nasa cikin sarauta yakeyi......sai naga kamar mu ba mata bane,yadda namiji keda aji irin wannan,anya akwai macen da zata burge wannan?" Idanu qasa qasa falaak ta juya ta watsawa badee'a harara.

"Dama ba karatu kike zama dauka ba?,yanayinsa kike karancewa?". Ta qarasa fada tana jin wani abu yana taba zuciyarta. Dan murmushi badee'a ta saki tana janye jikinta.

"Afuwa nake bid'a,na tuba bazan qara ba,na gagara yin shuru ne wallahi".

" Banason irin haka"

"Ba za'a sake ba" Ta fada tana komawa ta zauna sosai.

To amma sai maganar badee'a ta tsaya mata a rai. Maganganun badee'a suna shige da abinda ya jima yana kai kawo cikin ranta. Ta tashi gidan sarauta,cikakkiyar d'iyar gata gaba da baya,wadda ta mallaki dukkanin siffofin kyau da aji irin na cikakkiyar mace me tarin quruciya,cikin shekarun da duka duka suke sha shida zuwa sha bakwai. Tun a yanzun akwai masu kamun qafa da momma da kuma sultane a kanta,mutane masu yawan da batasan adadi ba,amma a duk sanda suka wanzu a muhalli daya ita dashi sai taji ta raina komai data mallaka.

Kyan,quruciyar.....mulkin......sarautar dama ajin gaba daya.

Ko a yanzun daya nutsu yana musu qarin qur'ani cikin muryar nan tasa dake shigen kama data sheikh afif muhammad taj,sai takejin a duniya ba wani sauti da yakai wannan dadi. A hankali ta zama aminiyar sauraron karatun qur'ani a yawan lokutanta na rayuwa,da kuma qira'ar sheikh afif din,kafin ta fara fitowa da wayarta tana recording karatun daya zame mata abokin fira. Abin yana yiwa momma dadi,nutsuwa ta sake shigar falaak din saboda abotar data qulla da sauraren qur'ani,tana sake samun tabbaci da yaqinin halayenta zasuyi kyau fiye da yadda take mafarki,domin shi qur'ani waraka ne daga dukkanin cututtukan jiki zuciya dama ruhi gaba daya. Ta dinga godewa Allah daya shigo da sheikh muhammad haisam cikin rayuwarsu a sanda take fafutukar inganta rayuwar 'yarta da jikokin da Allah ya azurtata dasu.

Wani abu da falaak ta lura dashi shine,muryarsa tana qara daguwa ne da qara kaifi a duk sanda yake rera karatun qur'ani. Ta lura sautin yana kaiwa nesa kadan da inda suke,sai taji kaman komai na gurin ya sake nutsuwa ne da rerawar karatunsa cikin gwanancewa da hikimar sarrafa harshe dake kan harshensa dama wadda ke cikin littafin me tsarki.


*_DAIDAI LOKACIN_*


Da take zaune cikin balcony dinta,zama ne na jiran tsammani.......zama ne na jiran isowar mammina da ta shaida mata ta sake shiga gurin sultane a karo na biyu don karbo mata sassauci. Ta zabi ta kebe kanta a nan,ta kuma qona dukkan lokacinta ta jirayi mammina,don shine kawai abinda ya rage mata.

A hankali sautin ya fara kai mata har inda take zaune,ya kuma fara shiga mata kunnuwa. Idonta ta lumshe sannan ta bude,sautin ya danyi nesa daga inda take jiyoshi,amma yana da wani irin kaifin tasiri daya soma sauka kai tsaye cikin zuciyarta. Inda ace inda take zaunen akwai hayaniya da ba yadda za'ayi ma ta iya jiyoshi.

A hankali take bin kowanne harafi dake fita,tana kuma qoqarin zaqulo surar da ake karantawa,amma sai taji kwanyarta ta gaji gaba daya,ta kuma gaza gano komai.

"Biftu" Muryar mammina ta haye saman sautin karatun,ta kuma fusgi hankalinta,saita waiwaya da sauri tana duban mammina dake tsaye.

A hankali a sanyaye kuma ta miqe tana dubanta,jikinta ya bata,hakanan alamun rashin samun nasararsu ya bayyana saman fuskar mammina din.

Hannuwanta ta sanya ta kamo mammina tana duban idanunta dake cike da tashin hankali.

"Bai janye ba ko?" Ta tambayeta a sanyaye. A qa'ida yayi tayi maganan ya kamata taji tausayinta ko yaya,duk da cewa itama tana cikin tashin hankalin samun tasgaro kan hanyar data shareta fetal take kuma hangen babu wani sauran datti ko tsiro da yayi saura da zai bata matsala,sai gashi sultane yana neman zame mata BABBAN DALILIN DAMUWAR.

Wannan tashin hankalin da take gani saman fuskar Akhnan shine garkuwarta......wannan tashin hankalin dake gauraye da fusata shine nata makamin guda d'aya daya rage.....amma hakan bazai hanata daidaita takunta ba,don haka ta kama dukka kafadunta ta maidata tana zaunar da ita.

"Rashin samun nasara a kanshi yau ba shine yake nufin gobenmu ta saraya ba......idan bamu amintar dashi a yau ba gobe ko jibi tabbas zata sauya mana shi......amma dai....." Saita dakata sannan itama ta zauna tana fuskantarta.

"Sultane ya kafe da irin nau'in kafiyar da ban tana ganinta a tattare dashi ba.....kici gaba da haquri,zanci gaba da qoqarina muddin mumfashina". Jijiyoyin kanta dana idanunta tuni suka motsa,ta kama hannun mammina din tana jin duk wata qwarin gwiwa da nasararta ta dogara a kanta.

"Yayi abinda bai taba yi ba,bawai saboda rad'in kansa ba.....yayi ne saboda an sakashi,an dorashi a hanya an nuna masa.......bazan taba yafe mata b......"

"Akhnan mana" Mammina ta kirata da yanayin dake nuna bata qaunar qarasa fadin abinda zata fadi din,yanayin da yasha banbam ainun da abinda ke qasan zuciyarta.

"Ko ban fada ba a nan a gabanki.....zan fadi watarana.....watarana a gabanta,watarana a gaban kowa da kowa.....ta rusamin mafarkaina.......ta maida farincikina zuwa baqinciki na.....indai ni halastacciyar d'iya ce,kuma haifaffiya ga MUHAMMAD HAMMUD.....wannan zuciyar ba zata taba sonta ba".

"Ba wannan keda muhimmanci a yanzu ba......abinda ya fishi muhimmanci shine ki.maida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login