Showing 42001 words to 45000 words out of 178317 words

Chapter 15 - LU'ULU'U COMPLETE

maka shakka ko d'ari d'ari game dasu......

Daya bayan daya take zagayawa tana duba lafiyar dawakan nata guda uku cikin dokunan hawa shida da take dasu.

Uku a agadez tare da raqumma uku da takan hau lokaci bayan lokaci,sai wadannan guda ukun da take dasu a nan Niamey.

Wasu irin qosassun fararen dawakai da take matuqar sonsu........ba ita kadai ba......duk wanda yasan sirrin kyan doki bazai kallesu sau daya tak yaji basu burgeshi ba.

Sanye take da yalwataccen wandon palazzo data dora masa wata blouse a sama long sleeve,sai ta kawo top data sauka har saman cinyoyinta me gajeran hannu ta dora a sama. Lallausan scarf ne a kanta data nannadeshi kamar tufkar igiya tayi wani irin dauri dashi daya bawa doguwar sumarta dake kwance a bayanta daman fitowa sosai,saidai ba zaka samu daman ganin tsahon sumar daya bazu a gadon bayanta ba sosai saboda wannan top din data dora a saman gashin nata.

Wani takalmi ne a qafarta,samansa kaman socks yake,qasansa ne takalmi. Jikinta a kowanne motsi idan tayi lallausan qamshinta ne yake kadawa.

Miqewa tayi daga tsugunnon da tayi tana duba qafar daya daga cikin dawakan nata,ta juya a nutse tana duban gabjejen mutumin dake tsaye a bayanta cikin son cika umarninta.

"Thunder zan hau(sunan daya daga cikin dawakan nata)"

"An gama ranki ya dade" Ya furta cikin rusunawa yana sakin murmushi. Da ita za'ayi wasan tseren dawakan.......amma ya fita qaguwa ranar tazo. Karon farko kenan data taba yin register kuma zata shiga wasan,duk da irin qwarewarta a sarrafa doki da kuma raqumi. Akwai kyakkyawar alaqa tsakaninta da dabbobin nan guda biyu,ta taso a cikinsu sosai,ta kuma koyi hawansu da sarrafasu. Tana da tarin raquma da ake kiwata mata,amma a ciki guda uku kacal take hawa da aka waresu musamman suka kuma saba da juna. Hakanan dawakanta guda shidan nan na Niamey da wadanda suke a agadez tana bala'in ji dasu. Sam sam yadda ta damu dasu bata damu da motocinta ba.....bata muhimmanci ba kamar nasu.

Wayarta ce dake cikin aljihun wandonta tayi qara,ta zura hannunta ta dauko tana duba me kiran,abinda ya saka murmushi subucewa daga fuskarta kenan,ta fara takawa tana fita a wajen hadi da sanya wayar a kunnenta.

Daga yadda take amsa wayar kawai zai shaida maka da wani me muhimmanci take magana.......hankalinta kwance take barin sashen dawakan zuwa parlor din gidan da wayar a kunnenta.

A nutse ta murza handle din parlor din ta wuce ciki,daga baki bakin qofa ta zare takalmin qafarta ta sauyashi da wani,sannan taci gaba da shigewa zuwa main parlor na farko.

Shehnaz kadai ta gani saman dining da alama lunch take. Don yau tun safe bataga gilmawarta ba,duk da kwana biyun nan ma ba wani magana sukeyi sosai ba. Haushinta takeji akan Jamaal shi yasa take shareta......tana ganin sam bai dace shehnaz ta ragi rayuwarta damarta kimarta da martabarta ba wajen auren jamaal din ba.....wayayyen namiji tafi dacewa dashi......wayayyen namiji take da buqata ba jamaal ba. Sai ita kuma shehnaz din tayi kamar bata gane abinda yake faruwa ba......sam taqi ta nuna wata alama na ta fahimci akwai wani abu.

"Munyi magana da mommonki morsa safiyya......." Daga daya bangaren wayar mata da suke kira da Nannie ta furta da muryarta me cike da nutsuwa. Lumshe idanunta akhnan tayi tana dawo da tunaninta kan wayar da sukeyi da Nannie din. Kiran sunan morsa safiyya kadai kuma ya dawo da nutsuwarta jikinta.

"Me matar nan taje ta fadawa Nannie a kaina ne?" Akhnan ta raya a ranta kafin ta sake jin maganar Nannie din.

"Na bawa shehnaz saqo......ina fatan ta gaya miki ko?". Sai data aza idanunta akan shehnaz dake kai abinci bakinta tana kuma danna waya da daya hannun kafin ta dauke idanun tana ansawa Nannie

" Aah Nannie.......batace komai dani ba".

"Don qaniyarta ban gaya mata ta gaya miki ba?" Nannie ta fada da alamun daukan zafi kadan a muryarta. Kai akhnan ta karyar gefe jin Nannie din zata dauki zafi da shehnaz,duk yadda sukakai ga fada da junansu basason wani yaga laifin dan uwansa,don haka a shagwabe tace.

"Fada mukayi Nannie.......batason kulani shi yasa bata gayamin ba......"

"Yoni ina ruwana da wannan shashancin naku da zata saka maganata a ciki?....."

"Nannieeeeee.....bada gangan bane ba" Akhnan ta sake fada a narke kaman zata sakewa Nannie din kuka.

"Sannu me 'yar uwa........ni naga gyada ma sarkin goyo" Nannie ta fadi tana jin haushin yadda ko laifi akayi tsakanin su ukun ake rasa gane waye me laifin waye me gaskiya.

"To abinda na gaya mata ta gaya muku......naji fes abinda ya faru zuwan yaroncan na garin tahoua........wannan shashancin ya ishemu hakanan......kuma tabbas don bana agadez wasu abubuwan ke faruwa,nace ta gaya miki keda aisa din gaba daya......Ku maida hankulanku jikinku......lokaci yayi da zamu miqaku dakunan aure.....don ba zamu zuba idanu ku dinga rayuwarku yadda duk kukaso ba". Duk wani walwala da nishadi da ta tashi dashi a yau Nannie ta warware mata shi tas,sai kawai tayi shuru tana sauraren sababin da Nannie din takeyi harta gama.

"Sai anjima" Nannie ta rufe da fada tana katse kiran.

Ba yau ko jiya ki shekaran jiya tasan Nannie ba.......tsayayyar mutum ce me wani irin kafaffen ra'ayi.......tana tsananin sonsu da qaunarsu.......to amma a hakan fa idan abunta ya motsa kowa ma bi take ta kanshi. Qanwa ce guda daya tal data ragewa sultane muhamma hamud a duniya,kuma itace mahaifiyar aisa.......mahaifiyar shehnaz ke bin Nannie,kuma shehnaz kawai ta Haifa ta rasu,don haka shehnaz Nannie kawai ta sani a mazaunin mahaifiya.

Sunan Nannie na asali bilkissou......Nannie ya samo asali ne daga bakunan shehnaz da aisa.

"Soni masoyi......soni ka sani ranka.....domin so da yardaaaaaa" Muryar aisa da akhnan batasan da zamanta a gefe ba ta soma motsawa cikin baitocin waqoqin fitacciyar mawaqiyar qasarsu.

A nutse ta juya tana duban aisa din,ta tabbatar da ita take......kuma da biyu tasan takeyi. Rasa me zatayi mata tayi,kawai saita jefeta da wayar hannunta.

Dukka idanunta aisa ta fidda bayan wayar tadan sameta a qafa kadan tana bin wayar da kallo kafin ta kalli akhnan.

"Vous ne savez pas à quel point elle est coûteuse(bana tunanin kinsan tsadarta),kike jifa da ita haka?". Manyan almond shape eyes dinta ta ware ta watsawa aisa din,saidai kafin suce komai shehnaz dake can a zaune ta fara magana a nutse


"Vous êtes tous invités aux courses de chevaux spéciales, présentation du nouveau cavalier de la famille royale, Akhnan Muhammad Hammud".

Yadda tayi shuru bayan ta kammala karantawa haka falon ya dauki shuru,kowa a cikinsu ya rasa me zai fada. Tsam akhnan din ta miqe,don batason kowa a cikinsu ya maido mata tunaninta baya,da nutsatsiyar muryar nan tana da ta dace da innocent fuskarta da sam bata dace da attitude nata ba taurin kanta da kuma kafiyarta ba tace.

"Tous sont invités(eh.....dukkaninku ana gayyatarku" Sai ta fara wucewa hankali kwance.

"Biftu.......sanarwa ne fa na gasar tseren doki fa aka karanta miki.....da sunanki da na sultane a mazaunin babbar baquwa 'yar tsere......what if me martaba yaji?". Zagayayyun idanunta ta juyo ta zube musu.

"Idan ke kika gaya masa ba......ba wani gurin bane.....cikin Niamey ne......cikin Niamey din ma cikin hippodrome.....ba wani bangon duniya ba".

"Tare da maza ne fa biftu" Aisa ta sake fada fargaba na bayyana saman fuskarta.

"Et puis?(sai me?).....C'est mon rêve(mafarkina ne),zan kuma cikashi ko sau daya ne". Ta fadi hankalinta kwance,bata kuma qara ba taci gaba da takawa tana tafiya abinta.

"Laissez-la(ki qyaleta).....ki barmu muga wasannan s'ilvous plaît(please)" Shehnaz ta fada tana murmushi,don har ga Allah ita abun ya mata dadi. Tana ganin ba wani abu bane me muni tunda na dan lokaci ne,kuma tafi kowa sanin yadda akhnan ke mugun son tseren doki da yadda ta qware akai.

"Na qyaleku" Abinda aisa kawai ta fada kenan ta koma tana zama ba tare data sake cewa komai ba.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*

PAGE 19



Sanye yake da Moroccon jallabiyya ta maza,wadda ta sa haskashi sosai tayi masa wani irin kyau tana kuma sake haska fatarshi dake da wani irin launi,shi baiyi haske me yawan da zai kashe maka idanu ba,hakanan baiyi duhun fata ba,don kusan launin fatarsa yadan saba kadan data ainihin 'yan qabilae oromo.

Lallausar baqar sumarsa me santsi irin ta 'yan qabilar oromo din sai wani sheqi takeyi da walainiya,sumar da ta take kwance saman kansa zuwa gefe da gefen fuskarsa da kuma habarsa. Kansa wata qaramar hula ce irin ta larabawan morocco,wanda hakan bai hana bayyanuwar baqar sumar tasa ba data yiwa fuskarsa wani irin ado.

Shi daya ne cikin dakin,wanda kai tsaye ya amsa sunan library me wani irin tsari me daukan hankali da gasken gaske. Wani irin ma'ajiyar litattafai ne kewaye da ita,dauke da tarin litattafan da suka wuce ka iya qididdige yawansu,domin kuwa kowanne bango sune......bangon kuma tun daga samanshi har qasanshi. Akwai litattafan dake rubuce da yare kala kala......tun daga kan English......french.....oromo.......yayin da litattafan addini na larabci suka mamaye kaso mafi girma na library din.

Komai na library din ya bada wani irin yanayi da nature me kwantar da hankali da daukan hankali,gurine da yafi kowanne guri sama masa nutsuwa a duniya.........baya ji a jikinsa akwai wani abu daya mallaka da yakai wannan library din muhimmanci a wajensa.

Yana iya rayuwarsa shi kadai a wajen.......zai iya qarar maka da awanninsa na rana duka a wajen ya kebance kansa. Karatun addini ruhinsa ne......fatarsa ne.....kuma rayuwarsa ne,ya kuma sameshi,don babu wani abu da yake sanyashi nishadi kamar lokaci irin wannan. Lokacin da zai kebanta cikin yanayi na shuru da wata irin kyakkyawar nutsuwa cikin dakin karatun,yana yin bincike da zaqulo mas'aloli masu yawa daga mazhabobi da malamai iri daban daban.

Ya tsara wajen daidai da yadda zai dace da tsarinsa da kuma yanayinsa da abinda yafiso. Wasu irin kujeru da lausasan carpet aka yiwa gurin ado dasu,sai wani sashe na daban na library din da aka sake zuba wasu rukunin kujerun da kuma teburansa,yadda zai dace da zaman me bincike.

Daga gaban kadan dan qwarya qwaryan table ne me dauke da wasu qananun cabinet,wanda ba komai a ciki sai nau'in coffee kala kala.....coffee makers har biyu da wasu irin mugs da trays masu daukan hankali.

Yankin jimma dama qabilar oromo gaba daya coffee yana daya daga cikin manyan al'adunsu.......sukan ware babban fili me girman Hector me yawa suyi noman coffee zallah. Su kullum ranar shan coffee ce a wajensu bayan rana ta musamman da suka ware mata,ba abinda yake da muhimmanci a gurinsu irin coffee. Wannan jinin da wannan al'adar ta gudana a jikinsa sosai,don ko cikin masu son shan coffee din shi na daban ne.

Sake miqe dogayen qafafunsa yayi saman ottoman sofa dake gabansa yana fidda wani sassanyan numfashi. Sosai yake jin dadin zaman nasa a nan safiyar lahadin,duk da rabin hankalinsa yana kan wata 'yar qaramar danja dake gefansa.

Green light da yayi blinking shi ya sakashi daga kansa a hankali,lumsassun idanun nan nasa suna sake rusunawa da wata irin nutsuwa yana duban light din don tabbatar da motsawar da yayi. Ya sake bada green color kuwa......don haka ya sauke qafafunsa a hankali yana rufe littafin bayan ya sanya alama,ya miqe da cikakkiyar nutsuwarsa yana zare hular kansa ya ajiyeta saman ottoman din,sannan ya dauki wani irin nau'in Bluetooth ya latsashi ya sakashi a kunnensa yana nufar wata bookshelf data banbamta da nau'in da yanayin kowacce daya dake wajen,labbansa masu sulbi dake da wani irin color suka motsa a hankali suna bada sautin husky voice dinsa da ta rage boldness yana fadin.

"Assalamu alaikum warahmatullah" Daidai sanda ya latsa wani abu jikin bookshelf din take ya juya kansa ya canza siffa daga bookshelf zuwa qofa,sai ya murza handle din ya shiga sannan ya maidata yadda take bookshelf a dazu.

"Wa'alaikumussalam.........mun tashi lafiya haisam?". Babban mutumin da muryarsa kadai ta bayyana nutsuwarsa da dattijankarsa ta bayyana sosai ya fada.

"Alhamdulillah babbo". Ya amsa yana kunna switch na dakin,take haske ya mamaye ko ina.

Wani lafiyayyen daki ne da tun daga gininsa zaka tabbatar ya samu ingantaccen tsari da wannan irin sirri na musamman,don hatta da windows din dakin suna da wani irin yanayi ne,ba normal winduna na yau da kullum bane. Cike yake da tarkacen kayan wuta iri daban daban......wayoyi tsayayyu alluna na zane.......da sauran wasu abubuwan da ko sunansu ba lallai ka sani ba. Saidai duk da wannan kayan komai yana ajjiye a muhallinsa a kuma tsare,don a kallon farko ma abinda zai fara zuwa kanka shine wani office ne na musamman dake koyar da harkar na'ura me qwaqwalwa.

"Nayita qoqarin samunka a jiya......sai omari na barwa saqo.......ka duba email naka yanzu yanzu".

"Okay bobbo". Ya amsa masa a girmame yana danne makunnin Bluetooth din nasa sannan ya isa a hankali gaban wata qaramar system yaja kujerar dake gabanta ya zauna.

Waving hannunsa kawai yayi a fuskarta ta kunna kanta da kanta,ya matsa gaba sosai ya fara sarrafata. Wasu irin tarin password ya saka mata kafin ya budeta,password din da zakayi mamakin yadda akayi suka zauna daram cikin kwanyarsa.

Wata irin nutsuwa ya bawa na'urar yana bin kowanne saqo daya bayan daya da idanu da kuma hankalinsa,nutsuwar da zata gaya maka muhimmancin aikinsa a wajensa da yadda komai na aikinsa yayi masa ya dace da tsarinsa da muradinsa. Hasken screen din ya sake haska fararen idanunsa da suke juyawa a hankali cikin screen din,har zuwa sanda ya kammala duba saqon. Bayansa ya jinginar jikin kujerar yana yin relaxing sosai,still bai dauke fararen idanunsa daha kan allon computer din ba. Yatuntsa guda uku cikin sumar dake kwance saman habarsa yana dan yamutsasu a hankali.

Paragraph din qarshe na saqon da bobbo ya rubauta masa da kalmar turanci ya motsa labbansa a hankali ya karanta *_operation into AGADEZ_*

Ya kafe kalmomin da idanu yana maido tunaninsa baya. Duk tsahon wadannan lokutan?,duka tsahon shekarun?,me yasa tunaninsu da bincikensu baikai can ba sai yanzu?.

Idan zai iya tunawa shine ya fara kawo wannan idea na baza komarsu zuwa ga qasashen dake cikin fadin africa gaba daya. Bai manta osama yana daya daga cikin mutanen da sukayi Challenging nasa a lokacin......saboda dalilai na ganin cewa duka duka yaushe ya shigo hukumar tsaro ta sirri?......bai wuce watanni da fara aiki dasu ba amma ya samu nasarar shigowa babban team irin nasu na goggaggun ma'aikatan sirri.......ya tsinci kuma case din kisan gillar Abban ajani Ahmed......duk da akwai abota me qarfi da girma tsakaninsa da mahaifinsa me martaba abba jifar,amma osama yana ganin wannan daban da wannan. Ya raina tunaninsa a wancan lokacin,yana kallonsa a wanda baisan komai ba akan aikin........taka haye ne shi. Ran osama yayi fari qal a sanda aka soma fadada binciken zuwa wasu qasashen Africa din.......kuma basu samo komai a kai ba.......sai matsala ma da yaso jawowa ta alaqar diplomacy tsakanin Ethiopia din da maqwabtanta.

Daga qarshe bobbo yace a haqura a ajjiye binciken......aci gaba da taba case din lokaci bayan lokaci. Yana da wani abu guda daya a rayuwarsa daya zame masa silar nasararsa.........JAJIRCEWA DA TSAIWA akan dukkan abinda yasa a gaba,ya kuma samu gamsuwa cewa eh zaiyi. Baya tunkarar komai da ka,sai ya gabatar da ISTIKHARA irin wadda ma'aiki ya koyar da sahabbansa......sannan ya dora da addu'o'i. Wasu lokutan harda azumi,muddin ya gama wadannan ya samu nutsuwa da gamsuwa akan komai.....to ko meye wannan abun,komai girman hatsarinsa baya jin fargaba ko digo akai,domin yasan Allah ya bawa zabi......kuma ya gama zabar masa koma meye..........so bashi da wani sauran haufi tsoro shayi ko shakka.

Tun daga wancan shekarun bai qara bari zuciyarsa da jikinsa sun huta ba akan case din ajani Ahmed.......musamman daya zama aboki sosai ga mooti abba jifar........wannan sai yake sake motsa zuciyarsa a duk sanda hira ta hadashi da me martaba zancan ajani Ahmed ya fado ciki.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login