Showing 48001 words to 51000 words out of 178317 words
don shiryawa gabanin fitowarsu. Wata irin shiga data sake fidda ainihin kyanta,wanda hatta da aisa da Shehnaz zama sukayi suna kallonta.
Farin skinny trouser daya fidda shape na qugunta da sosai......wata irin jacket data dora samansa me dogon hannu bayan riga 'yar ciki data saka. Ta daure wannan dogon gashin nata cif a tsakiyar kanta,saita sake jelar tana lilo. Takalmin qafarta wani tsadadden boot ne da tayi cinikinsa da Europe ba dolla ba takanas ta saka aka kawo mata shi. Komai na jikinta fari ne qal,kamar yadda kalar thunder (dokinta) ya kasance fari tas.......me wani irin cikar zati da ban sha'awa ga duk mutumin daya kalleshi. Koda bakasan doki ba.......bakasan kuma darajarsa ba idan ka kalli thunder sai ya baka sha'awa qwarai. Qosashe kuma ingarman dokin data sayeshi daga United arab Emirates wato dubai da kudade masu nauyin gaske. Kulawa ta musamman take bawa dukkan dawakanta da kuma me duba lafiyarsu na daban data ajiye a Niamey da agadez. Akwai me musu regular check up da vaccination don tabbatar da lafiyarsu,hakanan abinsu na dabanne bayan abincin ana ciyar dasu fresh fruits da vegetables irinsu apple da carrots da sauran kayan marmari. Hatta da SULTANE yana sha'awar dokunanta......wani irin qauna ce tsakaninta dasu. A shekarun baya kafin ta zama busy akan kamfaninta har haka akwai ranaku na musamman da take warewa kawai don hawa ko zaman kallonsu ko lura da lafiyarsu.
"Amma dai.......ki rufa mana asiri kada kallon tseren doki ya koma kallon biftu....." Wani murmushi ta saki sanda take dauko wasu safar hannu guda biyu. Sai data fara zurawa sannan fa daga kyawawan idanunta da kwallin data zizara musu a yay ya qara musu kyau.
"Jikar muhammad agg nake......diyar muhammad hammud......akhnan.....biftu......don kawai na na shiga gasar tseren doki sai kuma jikina ya zama me abun banza ga kowanne kare da doki?......arahata batakai har haka ba" Ta qarasa fada tana zama saman wata ottoman sofa tana daidaita riding globes dinta cikin hannunta.
Murmushi aisa ta saki,akwai abu guda dake burgeta game da akhnan din......tana martaba jikinta.......tana tsananin kula da qaunar jikinta,tana bashi kima da daraja,amma kuma wani abun na daban.....wannan izzar ta akhnan tana burgeta......wannan izzar ta akhnan tana saka mata shakku.......anya kuwa ba da gaske bane kuwa?,anya a yadda izzarta da alfaharin kanta yake zata iya auren wani d'a namiji bare wataran ya ganta gayarta?,bare wataran su hada gado kamar yadda tasha fada?......anya kuwa akwai wanda zai samu nasarar sauke wannan izzar?,anya kuwa akwai wani qarfi na wata aba soyayya da zai sauke wannan ALFAHARIN?.....ya cillata duniyar matsananciyar soyayya da shauqi?. Da wanann tunanin da yabar murmushi saman fuskarta ya kaita nisan da har akhnan din ta gama qarasawa shiryawa hankalinta bai kai ba.
"Ma sha Allah" Aisa ta furta can qasan ranta tana duban akhnan din. Wannan skinny trouser din daya bayyana shape dinta......ta batar da wannan surar tata ta hanyar dora wata irin riga me kama da alkyabba maras nauyi sam sam,sosai ta baje daga bayanta ta kuma rage fitar da shape dinta yayi kwata kwata,rigar tana hade da hula ne wadda zata aza saman Egyptian turban cap din kanta me azabar kyau da aka qawata da adon gold stones. Daga gaban rigar me kaman alkyabba akwai wata 'yar lanqwasa da aka yiwa ado da wani tattausan gashi tun daga fuskar hular dake saman kanta,ya sauko saman qirjinta ya rufe tudunsu daga sama,duk da hakan bai boye shape dinta ba....sannan ta dauki helmet dinta ta riqe a hannunta.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
Fadin irin kyan da tayi bata baki ne.......abu daya aisa ta sake tabbatarwa shine,da gaske akhnan din ta dabance......da gaske kuma tasha banbam da mata masu yawan gaske.
Wani irin cika gurin yayi wanda bai taba yin irinsa ba,su kansu masu saida ticket na shiga gurin.....jami'an tsaro da kuma masu kula da kai kawon jama'a a gurin yawan ya rikitasu. Mafi yawan mutanen da sukazo kallon wasan sunzo ne don PRINCESSES AKHNAN MUHAMMAD HAMMUD.......don fiye da rabinsu basu santa ba sani na ido da ido. Sunanta ba boyayye bane cikin nijer dama agazed gaba daya......amma sanin anihin fuskarta abune da ba kowa ne zaice maka ga kamanninta ba.
Kusan ita daya ta rage bata iso gurin ba cikin jerin 'yan wasan dake wajen......farin dokin qwaya daya dake tsaye ba maishi a kansa shima ya zama abu na daban daya tsonewa 'yan kallo ido. Ko cikin abokan wasan nata babu wanda dokin bai burgeba,duk da gabadayansu suna saman wasu irin qosassun dawakai da suka sha bamban da wadanda aka saba gani.
*ADDIS ABABA*
_national intelligence and security service(NISS)_
*_Washegari_*
Wani irin sabo da horo ya yiwa ruhinsa,tun daga sanda ilimi da hankali ya gama wadatarsa kawo yanzu. Duk daren duniya......duk inda qarfe uku na dare yayi muddin akwai cikakkiyar lafiya a tare dashi to yabar makwancinsa izuwa saman abun sallarsa.......a kowanne dare a kowanne guri,hakanan a kowanne yanayi. Daga sanda ya karanta ya kuma fahimci ma'anar ayar nan ta cikin suratus sajdah aya ta sha bakwai da Allah madaukakin sarki yake cewa
(Jukkunansu na nisanta da makwancinsu suna kiran ubangijinsu suna masu tsoron azabarsa.....suna kuma masu kwadayin rahamarsa......sannan suna ciyarwa daga abinda muka azurtasu). Tun daga wancan ranar zai wahala wani dare ya kubce masa ba tare da ya rayashi ba. Abinda yayi masa tasiri sosai cikin rayuwarsa......ba wata buqata da zai dorata saman abun sallar cikin irin wadannan dararen ba tare da yaga cikarta ba. Wani irin haske ne ke mamaye ruhi dama rayuwarsa gaba daya. Da gaske sallar dare na daga darajar bawa,ta sanya wani haske na musamman a ruhi zuciya dama fuskar me yinta,ga kuma tarin nishadi da walwala da zaka wayi gari cikinsa.
Kiran sallar farko da wasu mintuna yabar saman abun sallar,ya koma bandaki ya sake sabunta alwalarsa don samun qarin haske akan haske(alwala haske ce......kuma itace ranar qiyama zata dinga zame mana tamkar fitila,itace kuma zata rarrabe tsakaninmu da kafirai,so yana da kyau ki zama me yawaita yin alwala ko zama da ita.....tana bada kariya daga dukkan sharrin me sharri).
A nutse yasa dan qaramin lallausan towel dinsa dake fidda wani sirrintaccen qamshi daya samo asali daga turarukansa da yake amfani dasu ya goge lemar jikinsa,sannan yabi jikin nasa da wani sassanyan turarensa da mafi akasari shi yaf amfani dashi idan zai fita sallar asuba.
(Turare kansa sunnah ce....sunnah me qarfi,cikin abinda aka sanyawa manzon Allah S A W sonsu akwai turare).
Qarshen layinsu masallacin yake,kuma kusan shike jagorantar sallar asuba din a yawancin lokuta,duk da wasu lokutan yanayin aiki ma baya barinsa kwana a gidan bare ga samu yayi musu limanci.
Cikin mintuna qalilan daddadar muryar nan tasa dake dauke da amon sautin karatu mafi daraja ya karade area din tasu,ya sake sanya nutsuwa sosai cikin zukatan duk wata halitta daka iya jiyo sautin nasa.
Sanda ya kammala jagorantar sallar yaso ya zauna a gurin kaman yadda yakeyi wasu lokutan ya jira fitowar hantsi sannan yayi salatudduha(wata garabasa ce me girma ayin haka,gwaggwaban lada ne ga bawa me yawan gaske,ladan hajji da umra cikakkiyar lada cikakkiyar lada cikakkiyar lada haka annabi S A W ya maimaita har sau uku,idan bakije hajji ko umra ba.....ga dama ta samu a sauqaqe na samun ladaddakinsu daga gida)".
Dole ya koma gida,don yana buqatar fita da wuri.....akwai abubuwan da yakeson dubawa kuma kafin ya isa headquarter dinsu.
A nutse yake takawa zuwa gidan.......qasa qasa yana motsa harshensa cikin tasbihi ga ubangijin halitta. Sassanyar iskar asubar dake busawa tana sake dauke duk wani nauyi dake qirjinsa,tana saukar da wani nutsuwa da nishadi sosai a ransa.
"Tsarki ya tabbata ga ubangiji" Ya fada qasan ransa,yana tuna yadda a alqur'ani ubangiji ke cewa a aya ta sha takwas cikin suratut takwiir
"Da asuba idan tayi numfashi(ma'anar wannan sassanyar iskar me dadi dake kadawa tsakanin sallar asuba,ki gwada shaqarta,tana saukarwa da zuciya nishadi sosai)".
"Ya akayi masu tsaronmu sukayi ganganci bar mana zakin qasarmu haka sasakai yana takawa zuwa gida haka gayansa?" Ya tsinci dattijuwar muryar daga bayansa.
Tun bai juya ba qaramin murmushin nan nasa dake alamta nutsuwar dake jikinsa ya subuce masa. Koda bai juya ba yasan ba kowa bane sai alhaji muntassir amari.
Dattijon da gidansa ke maqotaka da nasa ko nace yake kallon nasa. Dan asalin yankinsu garinsu na jimma,wannan hadakar garin ita ta kawo shaquwa da alaqa me qarfi tsakaninsa da alhja muntassir amari. Alhj muntassir tsohon ambassador din Ethiopia ne a Malaysia,wanda ya dauki shekaru masu yawa yana yiwa qasarshi hidima,bayan shekarunsa na retired sunyi ya dawo da zama cikin addis ababa da iyalinsa gaba daya.
Yana da matar aure guda daya da yara biyar,uku mata biyu maza,ya aurar da yaransa uku,mata biyu namiji daya,yanzun 'ya'ya uku ne suka rage masa a gabansa. Menelik da dan uwanta yonas su kadai suka rage masa. Wani irin girmama haisam yake saboda abubuwa biyu. Na farko kasancewarsa d'a ga sarkinsu da suke matuqar so da bashi girma.......na biyu nutsuwa da tarin ilimin da haisam ke dashi.
A aikace haisam din yaga alamu da abubuwa da yawa suka nuna yadda alhaji muntassir amari yakeson hada alaqa tsakanin haisam din da menelik.......menelik din da zuciyarta ta jima da narkewa haisam din......ta dade kuma tana addu'ar Allah ya kawo wani sanadi da alaqa zata qullu tsakaninta da haisam. Ta sani......ba wata hanya alaqa ko sanadin da hakan zata kasance,haisam din yayi mata tarin nisa......ya mata tazara me yawan gaske da take jin zata iya samun isa gareshi.
Sam sam bashi cikin tsarinsa shiga shirgin mata,matan ma wadanda suke ba muharramansa ba irin menelik din. Yana da wani tarin kwarjini na musamman.......ya iya kuma iya tsare gida ta yadda zakayi tsammanin bai taba wani abu me kama da dariya ba.
A wani dare da abbii dinta ya gayyato haisam din don yaci abincin dare dasu a mazauninsa na babban mutum na musamman a wajen mahaifinta. A ranar ta dauka tana da qwarin gwiwar iya tunkarar haisam ko yin wani motsi da zai bashi haske a kanta.......don ta wuni tana rehearsal na yadda zata shigo da yadda zata gaidashi,sai gashi a kallo guda daya tak da tayi masa ya rusa komai......ya ware wannan tsarin nata. Duk kuwa da cewa idanunsa da hankalinsa suna kan mahaifinta suna wata magana data shafesu amma sai yayi bala'in cika mata idanu harta nema daburcewa,ba kuma wai don ya daga idanu ya kalleta ko sau daya ba,hasalima idonsa nakan yonas dake gefenta yana amsa gaisuwarsu,duk da ya amsa musu cikin nuna mutuntawa da karramawa.
Harta gama serving nasu komai ta juya zuwa ciki bai sake daga kanshi ko kallon sashen da take ba,don sosai ya bawa abbii dinta hankalinsa.
Hankalinta ya tashi ya kuma kwanta duk a ranar,saboda bayan tafiyarsu taji abbii dinta yana gayawa ummiinta ma'anar gayyato haisam gidan.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 24
____________________________
https://wa.link/l1gcz8
ASSALAMU ALAIKUM
Mutanen Zuzeam ventures
Ga wani sabon promo na bullo muku dashi don farin cikinku dajin dadinku
Kunsan promo na na dabanne namu ba irin nasu bane hajiya ta mai kike jira da 7500 dinki ki kwashi kayan 19k
1. Rabin kazar mallaka 4500
2. married femfresh wash 2k
3. garuka 7in1 masu wata 7 ajiki 2k
4. Gumbarmadaradanonon rakumi 1500
5. Tsimin mallaka 2500
6. maganin infection 1500
7. matsin mallaka ba aba mai kishiya 5k
Duka kayan 19k za a baki akan 7500
Kuma mutun 20 na farko sunada kyautar kayan 4k
Matsin maida tsohuwa yarinya 1k
Gumbar emergency 1k
Turaren mallaka 2k
Allah yaba mai rabo sa a Zuzeam ventures takuce 🥰👍🏼
Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin sa ni’ima da dandano Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi https://wa.link/l1gcz8 gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye ta WhatsApp 08144015291 muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
😁😁😁 https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki
___________________________
"Menelik nakewa sha'awarsa........banason tayi asara kota rasa miji irin muhammad haisam din......duk da ina tsoron kada mutane suyimin mummunar fassara,su dauka saboda sarauta mulki ko tarin arziqinsu nakewa". Daga ranar sai hankalinta yadan kwanta,ta samu yaqinin a ranta,ta kuma samu tabbas tunda ga abbinta nan zai tayata wannan yaqin,yaqin da har yau ba wani ci gaba a cikinsa,saima sake nisa da haisam din kewa idanunta,don koda ganin gilmawar motocinsa ta samu gani a ranar daga corridor din upstairs dinsu,to lallai ranar ta shiga cikin jerin ranakun sa'arta.
"To ya za'ayi?,barka da asuba" Haisam ya fadi yana bawa alhaji muntassir amari hannu sunayin musabaha. Tare suka jero bayan sun gama gaisawa suna dan tattaunawa kafin alhaji muntassir ya jefo maganar dake ransa.
"Har yanzun dai kaqi sake amsa gayyatar cin abincin dare tare damu Muhammad?" Dan murmusawa yayi,wanda wannan karon kawai iya labbansa ne suka motsa. Yana jin nauyin yadda alhaji muntassir ke yawaita masa tayin zuwa cin abincin da a gurinsa baida ma'ana,ya rasa yadda zai masa bayani cikin girmamawa yadda zai gane.
Ba zuwa cin abinci ko zuwa gidansa bane matsalar..... Matsalar tana ga yadda wancan karon ya bashi dama ya shiga har ainihin parlor din iyalinsa. A nashi tsarin bayan yayi aure........a duniya baiga wata qwaqwarar hujja da zaa bashi ba da zai sanya ya bawa wani baqo damar keta koda qofar farko ta gidansa wato gate dinsa ba har kuma ya kutsa zuwa ciki. Ko bayan haka ma shi abun bai burgeshi sam,uwa uba kuma ba wani sassauci ko hutu daya samu daga hukumarsu da zai samu lokacin zuwa ziyarar cin abinci,don haka ya hanke bashi uzurin qarshe kawai
"Rashin lokaci ne kawai......ina fata kuma zaayi mana afuwa?". Murmushi alhaji muntassir ya saki,y fahimci bai iya wani boye boye ba,kai tsaye yakeyin maganarsa da dukka gaskiyarsa a yawancin lokuta.
"Karka damu....qanwarka ke yawan tambaya dama,tana ganin kamar mun wareka,baka kusa da gida". Sai ya bashi hannu suka sake gaisawa ya taka a hankali zuwa qofarsa.
A parlor dinsa yayi zamansa,zaman da kaman jira akeyi saqo ya shigo wayarsa,abinda kuma ya janye masa hankali kenan
Tunda ya samu saqo daga abba muhammad dawuud da wasu taqaitattun kalmomin da su kadai suke gane ma'anarsu ya fahimci yanason ya rigashi isa office ne......na biyu yau ya tsara suyi zaman da zasu tattauna yadda tafiyarshi zata kasance......don haka yau din yana son yayi monitoring shige da ficen hukumar gaba daya bisa tsari na sirri yadda suka saba. A cikin ma'aikatansu waye ya shigo?,waye ya fita?,qarfe nawa ya shigo kuma qarfe nawa ya fita?.
Tafiya ce me tarin muhimmanci ga hukumar tasu,saboda kasancewarta wani tsohon case da aka dauki shekaru ba tare da gano hasken komai ba a kai sai yanzu.
Yau hatta da omari raba tafiya sukayi. Ya gama komai nasa akan lokaci ba tare da sanin dukka hadimansa bama,don ko breakfast bai tsaya beruk shugaba cooks dinsa ya kammala shiryawa ba ya fice.
Shi daya ya zai motar da yake jin fita yau a cikinta ya fice abinsa. Sai yake jinsa yau sakayau.......ba guards ba hadimai.......daga shi sai shi sai kuma qira'ar qur'anin daya kunna a motar yana bi sannu a hankali yana tuqi cikin cikakkiyar nutsuwa da matsakaicin gudu.
Yadda yake bin karatun kawai zai gaya maka yadda qur'ani ya zauna a zuciyarsa da rayuwarsa. Mutane na shiga nishadi da wani irin shauqi a sanda suke sauraron waqoqi......nashi akasin hakanne......yana jin dukka wannan nishadin......wannan shauqin da wannan jin dadin a sanda sautin qur'ani ke shiga kunnuwansa.
Yayi wani irin kyau cikin ire iren kayan da yafi amfani dasu a ranakun aiki irin wannan Kurta pyjamas da sukayi masa bala'in kyau. Tattausan yadin da akayi kayan dashi da yadda yanayinsu yake ya sanya