Showing 144001 words to 147000 words out of 178317 words

Chapter 49 - LU'ULU'U COMPLETE

dace da d'iyarki?" Ta fada tana jin cewa matsalarta tazo qarshe. Ko kowa bai fahimceta ba mammina tana fahimtarta,ko kowa bai kawo mata mafita cikin matsalolinta ba mammina tana kawo mata,ko kowa bai goyi bayanta ba mammina tana goya,tsanani.....wahala ko dadi basa sanyawa mammina ta janye mata ko ta daina goyuwa da bayanta.

Wannan karon ga mamakinta sai taji mammina na zameta daga jikinta,abinda ya tilasta mata daga kanta a hankali tana duban mammina din cikin zallar mamaki.

Mamakin ya sake ninkuwa yadda taga mammina na dubanta da wani irin kallo,wannan tausayin.....wannan tausasawar.....wannan laushin dukka babu su. A hankali mammina ta soma girgiza mata kai.

"Wannan karon.....idan har kin bijirewa maganan sultane,idan har kin kasa biyayya wa umarnin sultane,to tabbas bana tare dake......". Mamaki ya tsayar da kukan akhnan gami da wani dan siririn firgici daya ratsata.

"Mammina......ke kikamin alqawari fa". Kai ta daga a hankali tana takawa da baya.

"Nice akhnan......saidai akwai abubuwa da dama da suka tilastamin tunanin janye wannan alqawarin........morsa safiyya,nice mutum ta farko da zata kalla wadda ta zigaki ta kuma doraki akan turbar bijirewa maganan sultane....."

"Morsa safiyya!......morsa safiyya!......har yau har yanzun dai ita!......ita kadai ce matsalata a dukka wani cikar muradina?,itace damuwata a dukka burikana?!......qanwar uwata ce amma BA UWATA BACE!......ba itace ta haifeni ba,kin yarda mammina WATA MACE CAN ta shiga tsakaninki da tausayin dake zuciyarki game da 'yarki?" Ta fadi da wani irin zafi bacin rai da kuma tarin gungun tsanar morsa safiyya sabo daya bude shafinsa cikin kwanyarta.

Wani abu ne me girma ya motsa can qasan zuciyar mammina. Ta samu nasarar dasa DASHE na farko,wani sabon babin sabon aikin da zai zame mata sharar fage a dukkan komai da zai biyo baya.

"Akhnan......ko kinaso ko bakiso morsa safiyya wani bangarene me girma na rayuwarki.......tana da matuqar muhimmanci a rayuwarki......ita din jininki ce........wata sashe ce ta rayuwarki,jini iri daya ne yake yawo a jikinku......ko baya ga wannan SULTANE zai iya shiga sahun mutanen dake zargin akwai sanya hannuna kan dukkan wani abu da kikeyi,akwai sa hannuna akan duk wani abu da kike aiwatarwa.......musamman idan hasashe na ya tabbata yi masa tunani akeyi.......ba shine yake tunanin ba,bazanso bata wannan alaqar ba......bazanso rasa wannan yardar da amincin da yayimin akanki ba,akan zan iya kula dake.....akan zan baki kalar rayuwar da MAHAIFIYA zata bawa 'YARTA,wannan karon dole ki biyayyawa umarnin sultane" Tana kaiwa fuskarta na nuna wani irin narkakken qauna da tausayin akhnan saman fuskarta. Sai ta juya tana ficewa a dakin.

Sulalewa tayi kawai ta zauna gefan sofa,tana jin komai tana kuma ganin komai kamar wata almara,kamar komai ba gaske bane. Yau ita mammina ta kwarewa baya?. To amma still idanuwanta suna iya hangen raunin mammina cikin dukka maganganunta,idanunta suna iya hangen wani abu me kama da qauna da kuma tausayinta cikin ranta......wannan kawai ya isa ya tabbatar mata da gaske mammina zata tilastata ne kawai tabi sultane saboda tsoron hukuncinsa......zata tilastata ne tabi sultane saboda gudun xamowarsu masu laifuka dukkaninsu a gurinsa.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

*HUGUMANKU CE*โœ๐Ÿฝ


๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 68
___________________________
Bononza bononza https://wa.link/l1gcz8
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 6k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba pills shaki matse masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 11k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, da maganin sanyi wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne
Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 4k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka
Karku manta promo kwana 3 ne an kare insha Allah
___________________________



"Bazan iya ba wallahi......bazan iya auren hakeem ba......ban shirya rayuwa qarqashin ikon kowa ba,gashin kaina zanci gaba daci.....halastaccen 'yanci da babu takurawa ko kuma qunci a ciki" Ta fada tana girgiza kanta..


โ˜…โ˜…โ˜…Kwanaki biyun da suka biyo baya sun zamo wasu irin kwanaki ne da suka sauya launi da kalar rayuwar wasu cikin gidan. A kwanakin komai na gidan yana nuna akwai wani kwantaccen abu dake faruwa cikin gidan,kwanaki ne dake sake bawa ko tabbacin da gaske akhnan itace zuciya kuma hasken gidan. Sai komai ya zama wani iri,kowa cikin takatsantsan da walwalarsa yakeyi kada taci karo da yanayin da ake ciki a wannan lokacin.

Kwana biyunnan cur ba wanda ta bari ya ganta,kaman yadda bata bari taga kowa ba,koda aisa shehnaz ma.

Koda sultane baiyi wani yunqurin nemanta ko neman sake ji daga gareta ba,ya riga ya gama yanke hukuncinsa a wannan karon,ya kuma tsayarwa da ransa ba abinda zai sanyashi janyewa. Baya son ya bata kowacce irin dama da zata sakata jin cewa akwai yuwuwar ya janye nufinsa ko ra'ayinsa,don haka hatta da mammina ko morsa safiyya baima zauna yayi zancan da kowa ba,shirinsa kawai ya farayi na yadda komai zai kasance.

Nannie kawai ya saurara har suka tattauna ta nemi ganinsa akan batun,ranta a matuqar bace,hankalinta kuma dukka a dagule,cikin tsananin bacin rai tana fadin.

"A wannan karon ka barni,sai naci mutuncin biftu......wai shinma dame aka halicceta ne?,da qarfen lu'u lu'u ko na gold da zata dinga wulaqanta mutane masu daraja?,masu darajanma irin hakeem......malamai magada annabawa?,masanin ilimin da zai kaika tudun muntsira?.....fatan kuma kowanne musulmin kirki kenan?" Ta qarasa maganan a sanyaye. Murmushi kadan sultane ya saki,irin murmushin dake cike da nutsuwa da sanin ciwon kai.

"Duk maganan nan da kikeyi fatima bata baki ne.......karki cewa khadeejatu komai,kulawa ma ai yabawa ce,tayi duk abinda zatayi,ban gani ba,bansan kuma abinda zai saukeni daga wannan hukuncin dana yanke ba". Kai Nannie ta jinjina,hakan daya fada da kuma tsaiwarsa akan hukuncinsa wannan karon ya mata dadi,amma can qasan ranta tana jin wani dan rashin dadi kadan,kaman hakan zai zama takura da auren dole ga akhnan din kenan?,bayan Shehnaz da aisa kowaccensu an bata dama ta fidda wanda takeso?.

"Amma yaaya.......tun jiya aisa tacemin tana sassanta,taqi yarda ta fito taqi kuma yarda taga kowa".

"Shirme kenan,tayita zama,idan ta gama zata gaji ya fito" Ya fada cikin rashin bawa maganar wani cikakken muhimmanci.

"Yaaya" Nannie ta sake fada. A nutse sultane ya aza dubanshi a kanta,da alama dukkan wannan qwarin ran da fadan da takeyi akan akhnan raunin nan irin na diya mace yana tattare da ita.

"Ina saurarenki" Sultane ya fada yana tattarawa Nannie hankalinsa.

"Nace anya ba jinnu ba sihiri a al'amarin biftu?" Tayi maganar qwayar idanunta suna nuna da dukka gaskiyarta take maganan. Shuru ya ratsa a tsakani na wasu sakanni,kafin daga bisani sultane ya saki wani murmushi.

"To......gida dai irin namu ba za'a ce bamu da mutanen boye na gado ba,mutanen boye na ainihin kan gidan ba,amma ba masu cutarwa ba,ba wandada zasu dinge bige mana d'iyoyi suna faduwa ba suna sakasu fagamniya ba......sihiri kuwa ba wani a waje daya isa ya jefi daya daga cikin zuri'armu ya kamashi.......saina cikin gidan,a cikinmu kuwa bana zaton akwai wanda zaiwa biftu wani mummunan aiki.....ko akwai?" Sultane ya qarashe tambayar yana duban nannie.

Kai ta girgiza a hankali,dukka maganganunsa tasan haka suke,ko ita kanta shaida ne,ta taba rayuwa da kishiyar da tace nata aikin asiri da jifa ne,qarshe ya koma mata da wani irin zazzafan haukan data dinga yinsa har ya zame mata ajali. Tabbas ga dan waje cinsu da asiri bame yuwuwa bane,cikin gida kuwa tsakanin ahalin sultane,takun saqa da sabani irin na harshe da haqori dole akwaishi......amma bata tunanin asiri a ciki.

To shin ma idan akace da asirin waye zaiwa biftu?. Morsa safiyya duk duniya bayan sultane tafi kowa kusanci na jini da akhnan.....ba yadda za'ayi uwa ta jefi diyarta da asiri. Mammina kuwa......wani abu ne da sam hankali bazai dauka ba......sam tunani da sharrin me sharri ma bazai biyo ta gurin ba. Matar data zame mata uwa tun tana da shekaru hudu a duniya?......ta zame mata wata irin garkuwa abar misali. Tabata zaifi zuwanma mutum da sauqi akan taba akhnan. Dukka tunaninta da damuwarta kan yadda akhnan zata rayu cikin 'yanci da walwala ne,to waye zai aikata wani mugun abu a kanta cikin mutum biyun???. Qatuwar tambayar data sanya ta bawa kanta amsar yin tambayar ma ba abu bane me ma'ana.

"Ki rabu da ita kawai,zatayi dukka ta gama,munyi aure da safiyya kuma mun zauna shigen wannan zaman,amma yanxun bai zama tarihi ba?" Ya fadi yana duban nannie. Murmushi ya subucewa nannie din harma sultane din yana tayata. Ta sani shima ya sani,kowannensu ya tuna wani abu ne daya shude da zamewarsa tarihi ya zame musu wani abun tunawa da sanya dariya.


*KWANA NA UKU*


Yammaci ne dake dauke da wani irin lullumi da ya bada wani sassanyan hadari daya wanzar da canzawar launin sarararin samiya zuwa ruwan toka toka. A dukka sasannin qasashe da suka samu irin wannan yanayin daya kasance tamkar wani sassauci ko rahama daga ubangiji na zafin daya dinga koda mutane a kwana biyun da suka shude,irin zafin damina dake tayar da hankali ga duk mutumin da bayason zafi. Daidai lokacin da mammina ke zaune farfajiyarta ta musamman,tana kuma ganawa da baqin data zabi iya wadanda take buqatar ganawar dasu.

Su uku ne a yanzun a gurin,Shehnaz aisa mammina din sai kuma yalwa data kasancd mutum ta hudun.

Dukkaninsu saman qawatattun kujerun gurin suke,hakanan akwai yawaitar kayan marmari dana maqulashe aka zube a gurin da duk me buqata ya dauka yayi amfani dasu.

"Ina jinku 'yammatan sultane" Mammina data ajiye wayar data gama amsawa ta fada cikin mayalwacin murmushi gami da nuna tsantsar kulawa a kansu.

Aisa ce ta ajiye wayarta a gefe,sannan ta jawo wani file ta tura gaban mammina.

"Mammina.......game da sabbin muqamai da ma'aikatan da aka dora ne a sahel couture......munso muyi maganan da biftu amma har yanzu hankalinta bai jikinta,ba wanda yake samun damar ganinta ma". Ido ta zubawa file din kafin ta dubi aisa cikin mamaki.

"Wani abunne yake faruwa a sahel din?". Tayi tambayar da yanayin dake nuna zallar kulawa.
(08187255862 lu'u lu'u paying)

"A zahiri ba wani damuwa bace ta fili" Shehnaz ta fadi kai tsaye.

"To me ya kawo qorafin 'yammata?" Mammina ta fadi tana sanya yalwa bude mata file din tana bibiyar rubutun ciki.

Dukkaninsu duban mamminan suke suna jiran ta kammala,cikin qasa da mintuna ta gama,yalwa ta maida ta rufe.

"Ban gano wani damuwa ba a ciki 'yammata" Ta sake fadi da wannan shimfidadden murmushin kan fuskarta.

"Akwai abubuwa da yawa muke buqatar qarin haske mammina.....nidai bazanyi qarya ba,ta bangaren office dina kusan komai a makance yake tafiya,ba komai na fiya fahimta ba,akwai muqaman da aka bayar kuma da suna buqatar dogon nazari kafin a bawa wadanda aka bawa din,ko kuma a jira dawowar CEO ta rattaba hannun amincewa da hannunta". Shigar mammina maganar tayi da wani sauti da tajishi ba'a daidai ba,amma saita tsaurara kallonta akan fuskar aisa din tana sake fadada fara'arta.

"Ina kyautata zaton baku samu kunyi kowacce magana da akhnan din ba?......banda abun aisa,ai ba akhnan ba,ko ke ina da ikon zartarwa ina da ta cewa a rayuwarki ballantana akhnan......" Yadda tayi maganan sai aisa taji kaman tayi maganana muhallin da bai dace tayi maganan ba,kaman tayi rashin kyautawa a ciki,kamar kuma mammina taso fahimtarta baibai.

"Ayimin afuwa......tambayata bawai tana nufin wani abu na daban bane,inaso ki fahimceni da kyau,da akhnan da sahel couture dukkaninsu amanarki ne dana sultane a hannunmu,bazan manta wannan maganan naki ba,gata nan na baku amanarta.....ku kulamin da ita kowanne qarshen sati idan baki gayawa shehnaz hakan ba ni zaki gayamin,amana ba abar wasa bace......sahel couture shine zuciyar dukiyar akhnan,zuciyar dukiyar masarautar agadez,dukkaninmu mun aminta zamuyi aiki cikinsa ne bawai don bamu da tamu dukiyar ba......muna aiki cikinsa ne don kawai sadaukarwar da zamu iya yiwa kowa a cikinmu idan buqatar hakan ya taso.....yin wasarere da irin wadannan abubuwan zai iya zama cin amana ne,zai kuma iya haifar da matsalar da bamusan qarshenta ba a gaba".

"Well done" Mammina ta fada cikin salon burgewa tana dan tafa hannuwanta.

"Ashe muna da talented girl har haka ban sani ba......ma sha Allah aisa" Mammina ta fadi tana sauke qafafunta qasa cike da tsananin nuna jin dadin dukkan bayanan aisa din.

"Na sake samun nutsuwa,na kuma sake samun tabbacin akhnan tana tare da sisters din da babu irinsu.......yanzu gayamin kanki tsaye me kike buqatar ayi?". Ta fada tana miqawa aisa takarda da abun rubutu.

Kadan aisa taji zuciyarta ta saki daga tarin saqe saqen da takeyi,tadan rusunawa mammina din

"Basai na fadi ba,kaman zaki fimu sanin abinda ya dace mammina". Kai mammina ta girgiza.

" Yadda kika gano dukka wadannan abunuwan na tabbatar idan nabar kwanyarki tayi aiki yadda ya dace za'a samu result me kyau". Kai aisa ta jinjina,tabbas daga farkon wancan watan zuwa yanxu tana ganin abubuwa da yawa a kamfanin da bata gane musu ba,take kuma ganinsu kamar ba'a daidai suke ba,tunda har mammina din ta bata cikakkiyar damar yin magana zatayi maganan.

"Ina ganin a dakatar da daukan ma'aikata da kuma rarraba muqamai da ake tayi a yanzu,ayi limiting fitar kudi da siyo wasu kayayyaki da kamfani ke da buqata.....wadanda aka Riga aka dauka kuma yana da kyau a auna amanarsu da ingancinsu kafin a sakar musu komai......saina qarshe,ina ganin a rufe office din biftu......a barshi a rufe,a dakatar da dukka ayyukan da suka shafi office din har sai bayan ta dawo".

"Ke zaki karbi office din ciki gaba da gudanar dashi" Mammina ta fadi kai tsaye hankali kwance cikin confidence idanunta cikin na aisa.


zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

*HUGUMANKU CE*โœ๐Ÿฝ


๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 69
__________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________




Dubanta itama aisa din takeyi,haka kawai cikin kanta takejin wani abu daban yana amsa kuwwa da maganar mammina.

Wani abu ne da bata taba tunani ba,wani abu ne da bata taba kawoshi kanta ba,kuma wani abu ne da ita din bata taba sha'awarsa ba. Jagorancin office din akhnan wani abu ne daban da tayi imani ba kowanne mutum bane zai iyashi. Dari bisa dari dukkaninsu sun aminta da akhnan din ta musamman ce,tana da wani irin fikira da hazaqar tsara abubuwa da sanyasu a guraben da suka dace,lissafinta daban yake kaman yadda kwanyarta take daban......baya ga haka ma kuma tana ganin babu tsaro sam sam gurin bude office din CEO guda aci gaba kuma da tafi dashi,tana ganin akwai hatsari cikin hakan,ba kuma tsari akai.

Wadannan lissafin ya sanya aisa din sakin murmushi,ta kuma girgiza kai.

"Mammina......tu n'as aucune ร  quel point ta fille est incroyable(bakisan wacce irin d'iya gareki me ban mamaki ba).....ba wanda zai iya tafi da l'enterprise sai akhnan din". Yanayin fuskar mammina ne ya sauya,tadan tsuke fuska tana duban aisa.

"Aisa?.....yanzun ace akhnan babu ita,ko dalili ya sanya ba zata iya ci gaba da gudanar da aikin ba,shikenan komai ya tsaya?." Kai aisa ta girgiza a hankali.

"Hakan bazai faru ba......"

"Daga yau na hukunta kece a mazaunin CEO.....ina fatan zaki riqe amana da jajircewa har akai lokacin da 'yar uwarku zata dawo daidai". Tayi magana tana yin rubutu saman wata takarda,sannan ta turata gaban aisa,da alama tana buqatar sanya hannunta.

Kai aisa ta daga tana duban shehnaz,itama shehnaz din ita take kalla,sai tayi mata sign da idanu na ta karba din,amma sai aisan ta zare dubanta daga kan shehnaz,ta maida kan mammina tana dan sakin murmushi.

"Zanje da takardan tukunna kafin saka hannu,idan na saka din zan dawo miki da ita". Kai ta gyada a nutse.

"Baki da damuwa,Allah yayi muku albarka ya qara hada kanku" Ta fadi tana nuna tsananin kulawa da taushinta.

Da idanu take bin bayansu da kallo sanda suke ficewa suna barin gurin,har sai da suka kammala ficewa sannan ta dauke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login