Showing 66001 words to 69000 words out of 178317 words
da kansa yana dafe hannunsa guda daya da kan nasa. Sai a yanzu da haisam yayi maganar da wannan yanayin ya tuna da abinda ya kamata ace ya tuna dashi din kafin wannan lokacin.
Tun suna da qananun shekaru mooti ya hana haisam shiga kowacce gasar tseren doki,saboda wani irin maita da yake dashi gurin qurewa doki gudu. Ya qware sosai irin qwarewar data sanya nanay ta yiwa mooti magana akan BAKI.
"Ina tsoron baki akan muhammad......baki gaskiya ne Allah ya taimakeka,a duk sanda zai shiga wata gasa shike zama na daya,kada baki ya kassara mana shi". Sosai mooti ya fahimceta,ya kuma fahimci inda ta sanya gaba,take kuma ya hana haisam shiga kowanne gasa bama ta doki kawai ba.
(Wannan din wani kariya ce data kamata kowanne iyaye su bawa yaransu,bawai kayita murna yarona ta daya yake zuwa ba....yarona ya iya kaza,ai yarona yayi mugun iya kaza.......baki baki masifa ne akan 'ya'yanmu,baiwar da Allah ya yiwa yaronka boyeta kakeyi,har sai sanda ya isa munzalin da duniya zata gani,baki gaskiya ne.....wani baisan kuma yana dashi ba,koda yaronka ne ka rage tankashi,don akwai da dama iyayen da suka cinye yaransu da bakinsu suka gusar da wata baiwa ta kyau yawan gashi ko farinjinin jama'a da yake dashi,dake da ubansa kansa ku rage tanka yaranki,Allah ya bamu kariya da tsari irin nasa ameen summa ameen).
"Na riga na shigar da komai.....sunyi approving kuma......yanzu mene abunyi?" Omari ya fada yana bawa haisam dukka hankalinsa.
Ajiyar zuciya ya sauke yana sauke hannayensa qasa
"Zan gani......zanyi dukkan qoqari wajen ganin komai ya tafi daidai ba tare da wata matsala ba" Ya fada yana miqewa hadi da zube hannayensa a aljihun wandonsa.
"Me gaminka da English ne?" Omari ya tambayi haisam din yana cire hular kanshi ya aza saman abun sallar da yake kai. Juyawa haisam din yayi a nutse,kaman bazai tanka masa ba,har sai da ya kai dab da qofa
"Idan baka da siffofi mabanbanta ka sani baka cika mizanin zama ma'aikacin NISS ba...........dole ka zama a duniyarka,dole kuma ka zama a wata duniya ta daban da taka". Shuru omari yayi yana bin hanyar da haisam ya fita da kallo,murmushi na fita kadan kadan daga fuskarsa.
Shi din shaida ne......kyakkyawar shaida kuma me cike da tabbacin muhammad haisam ya banbanta da mutane masu tarin yawa........idan maganar intelligence akeyi nashi na dabanne......komai nasa tamkar an zabar masa ne.....kamar haka yaso ya kasance.
★★*NANAY*
Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana gyara zamanta idanunta suna kan saami.
"Saamirah" Ta kira sunanta a tausashe,abinda ya sauke saukar da nauyi ga jiki da zuciyar sameera din kenan.
"Na'aam nanay" Ta amsa ba tare data iya daga idanu ta kalleta ba.
"Saamee......kada ki saka rai me yawa......kada kuma ki saka buri da yawa,amma kuma kada ki sare,kada kice kin gaza,kada kuma kice zaki daina har sai kin cimma burinki......". Wani faduwar gaba dukka maganganun nanay suka saukar mata dashi. Kunya da nauyi suka wani irin dabaibayeta,tana jin kamar ba zata iya motsawa daga inda take ba. Kada dai ace hatta da nanay ta fuskanci abinda ke zuciyarta?,dama kallonta kawai nanay keyi?.
Yanayin yadda saami din ta takura cikin tsangwamar kanta ya sanya nanay sakin boyayyen murmushi.
"Koda ban haifeki ba saame ina iya fuskantar wasu al'amura daga yaran da suma ba nice na haifesu ba,ke din amana ce a hannunmu saami,dole mu sanya idanu a duk wani motsi naki kaman yadda zamu sanya akan na yaranmu........haisam......yaro ne da ban taba hasashen samun kyautar Allah kamarshi ba,yana da wasu nagartattun halaye da nayi imanin ba zaki wulaqanta ba,ba kuma zai wulaqantaki ba saboda kina sonshi.......amma yana da kebantattun halaye da suka sha banbam dana sauran abokan rayuwarsa.....yana da zabi.......yana da kuma irin nashi yanayin.....ko bayan haka ma gaba daya,zanso ko wacece zata shiga rayuwar haisam ta fara samun soyayyarsa tukunna......ta nemi soyayyarsa da kanta kafin ta kutsa kai cikin rayuwarsa,wannan ne kadai zai sanya ta fahimceshi,ta bashi uzuri,ta bashi cikakkiyar kariya a kowanne irin yanayi,irin kariya da nutsuwar da kowacce mace ta gari take bawa mijinta......" Sai tayi shuru tana maida numfashi,tana ganin yadda maganar ke samun kyakkyawan matsugunni a zuciya da kuma hankalin saame din.
"Zanso a sanda zaki shiga rayuwar haisam ki shiga da dukkan daraja da martabarki ta diya mace,kaman yadda zan sowa yaran da na haifesu a ciki na.....zanso ki samu wannan martabar da mutuntawar.......kin cancanta saami,kina da kowanne irin quality da namiji ke buqata a gurin mace,bana haufin watan watarana zaki samu wannan gurbin......zaki samu wannan muhallin......za kuma ki samu wannan darajar......wannan matsayin da kuma wannan matakin". Har tsakiyar zuciyarta takejin wani abu me sanyi yana kwarara mata da kalaman nanay,bata tana zaton haka abun zaizo da sauqi ba daga bangaren Nanay,duk da ita din me sauqi ce.......sai gashi yazo mata da sauqin fiye da yadda ta zata ko tayi hasashe ma.
"Na gode nanay.....na gode" Ta fada cikin matsananciyar kunyar data sanya takejin ba zata iya tashi tayi tafiya a gaban nanay ba.
★banda Dim light din da dakin yake bayarwa,ba wani sauran haske ko fitila data rage idan ka cire ta system din dake gabanta.
Su ukune cikin dakin,tsakanin qarfe goma zuwa goma da rabi na daren ranar.
Aisa akhnan da kuma shehinaz......kusan dukkansu su ukun,duk da suna zaune ne a mabanbamtan kujeru amma hankulansu yana kan system din dake gabansu wadda ta nuna maballai biyu. ACCEPT da kuma REJECT.
A yadda suke zaunen da yadda dakin ya dauki wani irin shuru saika rantse da Allah suna tsoron suyi qwaqwaran motsi kada wani abu me matuqar firgici ya dirar musu.
Blue eyes dinta da hasken system din ya qarawa wani irin haske me qyalli kawai take rabawa tsakanin fuskokin aisa da shehinaz wadanda suma junansu take kallo.
Tashi tayi ta zauna sosai tana sake fuskantar system din,sannan ta miqa hannu a nutse ta dannan maballin ACCEPT din,abinda ya sanya aisa fidda dukka idanunta waje tana dubanta.
"Biftu......kinsan me kikayi kuwa?" Zagayayyun idanunta ta daga a nutse hankali kwance ta zubewa aisa su,ta lumshesu sannan ta budesu,wanda iya hakan ya sanarwa da aisa tana nufin eh......nasan me nayi.
"Akhnan........wancan lokacin fa.......alfarma....."
"Alfarma?" Akhnan ta fada a nutse tana dauke hannunta daga saman system din tana zubewa aisa su a karo na biyu.
"Alfarma aisa?......" Ta sake maimaitawa tana maida bayanta jikin kujerar tayi relaxing tana fidda manyan idanunta waje.
"Akwai wani abu dama da za'a yiwa akhnan alfarmarsa a duk duniyar nan?" Ta qarashe maganar da sigar mamaki cikin muryarta. Duban juna suke ita da aisa na wasu sakanni,kafin aisa din ta dauke kallonta daga kanta
"Alfarma ko ba alfarma ba.....koma meye biftu,last time nayi kawaici ne kawai,kina tunanin idan sultane yaji kina shiga irin wadannan abubuwan ko mu zamu kubuta daga laifi a gurinsa?" Ta qarashe maganar tana dubanta sosai itama.
Yatsunta kawai akhnan take muzawa,ko meye aisa zata fada....ko meye aisa zata ce ta fadi din......daidai da ita ne,amma ta janye kalmar alfarma a maganarta,shine kadai abinda zai sanya ta fahimceta.
"Alfarma aisa....." Ta sake fada tana duban tafin hannunta da rashin hasken dakin yasa bata iya ganinsa sosai.
"Yes" Aisa ta fada kanta tsaye. Shuru ya kuma wanzuwa tsakaninsu,cikin qasa da minti daya ta yunquro da wani irin zafi zafi a muryarta.
"Yayi daidai.....kici gaba da alfarma din ko kada kici gaba.....ki zabi duk abinda kika zaba......koda wannan shine tsere na qarshe da zanyi sai na yishi" Akhnan ta fada tana soma sarrafa system din da zafi zafi tana cike duk wani abu daya kamata ta cike tayi submitting.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
Ita kanta tasan cikin murna da alfaharin sake amsar gayyatarta suke,saboda ta tabbatar wani abu ne da bazasu taba tunanin zai yuwu ba.
"Haka kika ce?" Aisa ta fada ranta a bace sosai.
"Haba aisa mana......mubi komai a hankali don Allah" Shehinaz ta fada karon farko tana duban aisa din.
Tsam Aisa ta miqe tana dubansu,kafin ta ajiye kallonta na qarshe akan shehinaz.
"Ko meye zai faru......kada sunana ya fito a ciki gurin sultane ko nannie......babu Aisa a ciki sam". Daga haka tayi gaba abinta ba tare data ko waiwaye su ba.
Shehinaz ta wannan bangaren,duk da irin sabaninsu a abubuwa da dama ita da akhnan.......amma ta wasu fannonin a ra'ayinsu da kawunansu yafi zuwa daya. Kamar a wannan bangaren......shehinaz mutum ce mesonh abubuwan da zasu bata nishadi gami da sakata walwala,don haka tseren ke nishadantar da ita itama,to amma ita kanta ba zataso sunanta ya fita wajen sultane da nannie ba.......ga morsa a gefe data tabbatar azabarta zata iya shafe ta kowa.
"Akhnan" Shehinaz ta kirata da nufin gwada kwatanta mata bayanin tabar wannan race din.
"Kada kice komai.......na gama cike komai na tura musu......damuwata daya shine......bansan abokin kara wasan ba......bansan wanne me gangancin bane yakeson sai munyi wannan wasan ba......na tabbatar nayi kuma imanin yayi hakanne don ya zubar dani,ya kuma ramawa wadanda na zubar haushinsu a kaina" Akhnan ta fada a nutse tana sake duba bayanai a kansa,saidai kuma blank take gani,don babu koda cikakken sunansa ma bare wani abu daya shafu tarihin wasannin daya taba yi,wanda wannan shine ita kuma zai bata nata hasken..
Abinda ya dauki hankalin shehinaz kenan itama,ta manta ma da batun bawa akhnan shawarar ta haqura din,suka shiga bincike akan komai daya shafi abokin wasan,saidai har suka gaji da ita da itan ba wanda ya samu komai a kansa.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
PAGE 32
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
_____________________________
"Na tabbatar akwai manufarsa........bawai hakanan komai ya tsara kanshi ba.......amma na yiwa kaina alqawarin saina bashi kunya kamar yadda sauran na bayanshi suka kunyata" Ta fadi tana rufe system din cikin cin matsanancin alwashi. Alwashin da ko a wancan wasan bataji tana da sha'awar ta cishi ba,tunda wancan wasan wasane kawai da ita a karan kanta ta yishi ne kawai saboda nishadi,sabanin wannan da taji yana neman canza salo.
★Cikin kwanakin ta rufe duk wani hanya ko dalili da zai sanya a nemeta a agadez........ta kuma maida hankalinta wajen gwaji da qara qwarara kanta a babban filin dake cikin gidanta. Sam bata kawo aisa a matsalarta ba,bata ma sake bi ta kanta ba. Ba wannan ne karon farko da suke samun sabani irin haka ba,kuma suzo su shirya kansu kaman bai taba faruwa ba.
Duk yadda aisa takai ga cika baki tasan ba zata iya komai ba,ba zata iya tona mata asiri ba. Ba kuma aisa kadai ba,a tsakaninsu su ukunñ babu wani wanda yake iya tonawa asirin dan uwansa,kowanne irin laifi daya kuwa yayi,wannan ya sanya nannie ke kiransu da MUNAFUKAN 'YAN UWA.
Sunan yana bawa sultane dariya,ya sani gaskiya anne ta fada,kuma sunan ya dace dasu,amma yakance
"Ayi musu haquri,a canza musu suna".
★★★ *HIPPODROME NIAMEY*★★★
Duk girma fadi da tsahon gurin amma hakan bai hana mutane cike gurin cif cif ba. Wani irin cika gurin yayi,irin cikar da bai taba yin irinta ba a tarihin gurin.
Gurin kuwa baiyi cikar banza ba,don kuwa wasan ya zama wani na musamman,fiye da ma da wasan da akayi wancan satin. Ninkin mutanen da sukazo wancan wasanne suka halasci wannan wasan,don da yawa gulma ta fita game da wacece 'yar wasan......sunanta da sunan mahaifinta,harda tambarinta a matsayinta na mamallakiyar katafaren kamfanin suturun mata masu aji.....mata masu abun hannu wato SAHEL COUTURE.
Mintina talatin din farko kawai akayi aka tafi hutun farko,amma sai mintunan suka zama wasu na musamman a zukata da idanun 'yan kallo. Kamar yadda suka zama na musamman a wajen akhnan da wani madaukakin farinciki ganin score din data samu tun a zagayen farko.
Wani irin wasa daya zama baqo a idanun masu kallo......su biyu ne rak mahayan......wadanda gaba dayansu ba wanda kake iya ganin fuskarsa saboda helmet din dake kawunansu. Mahayin doki na farko kana dubansa zaka fahimci namiji ne,saboda qira da zubin jikinsa daya bayyana a kayan hawan dokin dake jikinsa.....yayin da ta biyu ta fita a suffar mace sak......tun daga yanayin qirarta da kuma launin suturar jikinta.
Yana sane yake bada dukkan wata dama ga abokin karawarsa.......ba tare daya tantance macace ko namiji ba......yana sane yake dage qafa saboda ba nasarar tseran dawakai bace ta shigo dashi niger........nasarar aikin hukumar binciken sirri ne ya kawoshi.
Cikin muhallin da aka basu saboda hutun mintunan,hakeem ne ya miqa masa bottle na ruwa,cikin murya qasa qasa yace.
"Sun saka hope da yawa akan dan wasansu......ban tantance sunan na mace bane ko na namiji.......amma da alama yana da cika baki da yawa......kayi wani abu mana akai" Hakeem ya qarasa fada qasa qasa yana ranqwafa kanshi saitin haisam.
Haisam din baice komai ba illa karbar ruwan da yayi. Sam wasan ba shine a gabansa ba,ba wanda kuma zai fahimci hakan a cikin su,bayaso kuma su fahimta din,faduwa ko nasarar bashi yake hange ba,yadda a yau zasu fice daga Niamey,subi jirgin da zai sauka a agadez kai tsaye ne damuwarsa.
"Hakeem" Ya kira sunansa a nutse.
"I beg you" Hakeem ya fada da yaren turanci yana hadewa haisam hannuwansa guri guda.
Cikin wani irin nishadi ta sauke helmet din nata tana ajiyeta a gefe. Gashinta ta kama ta tattarashi da kyau tana daureshi,fuskarta washe da wata irin fara'a da take jinta har tsokar zuciyarta.
Dukka kunnenta suna sauraren bayanan Shehinaz dake kwatanta mata yadda take sarrafa thunder da wani irin qwarewa gami da miqa mata ruwa.
Sai data saki miskilin murmurshin da iya sakin da fuskarta kadai tayi shine kawai zai alamta maka murmurshi tayi.
Ita kanta basai an gaya mata ba.......wasan yayi mata ba zata,saboda yazo mata da wani irin sauqi da bata taba zata ba. Ta zaci abun zai zame mata me tsananin wahala walagigi dashi,sai gashi cikin sauqi tanata samun damarmakin wuceshi. Da farko sanda yake fitowa don hawa nashi dokin sanye da helmet data hana mata ganin fuskarsa ta tsorata,sosai gabanta ya fadi,wata irin baquwar faduwar gaba da bata san da ita ba.
Ba yau ta saba ganin maza giant ba,Giant ne kuma ingarman da tsaiwarsa kawai zata baka labarin jarumtar dake gangar jikinsa da zuciyarsa,batasan me yasa take jin wani irin kwarjini yana hudata ba,wani irin yanayi da ya sanya tun a farko ta dinga jin faduw warwas a gasar.
Faduwarta kuma daidai yake da kafawa kanta da kanta tarihin abun kunya......kamar ita zai zamana wani babban abun Allah wadai ace wani da batasan ko wayeshi ya cinyeta a wasan da wancan satin ta zamana cikin tafin hannunta.
Izzarta da qasaitarta tana tare da ita,tana kuma zagayawa a jininta,wannan ya sanya taqi maida hankalinta ko idanunta ta sake kallonsa koda sau daya ne kuwa. Sai a yanzun cikin maganganun Shehinaz ta samu amsar
"Ko sau daya bai kalleki ba bare har ya damu da yadda kike tsere masa.......wallahi wannan ko waye shu'umi ne......kuma bansan me yasa bai dauki hankalinsa ya dora akan race din ba" Kai ta jinjina,ranta kuma ya fara mata saqe saqe.
Ko yaya ne bata son taci nasara cikin sauqi......ko yaya ne tana son su gwabza......tana sha'awar su fafata ta finciki nasararta koda tsiya ne a hannunsa. Abu na biyu ta sanya masa qatotuwar ayar tambaya......anya ba wani shiri a qasa?. Bata da wani zabi illa ta san yadda zata tona koma meye a zuciyarsa a wannan zagayen qarshen.
Saidai kuma akwai wani abu daya da tayi noticing.......ta fahimci kamar akwai wani sirrintaccen sirri tattare dashi......sirrin da ya zuba masa wani irin kwarjini na musamman. Bata iya ganin komai nashi,koda kuwa hannuwansa ne dake lullube da safar hannu irin ta masu hawan dawakai......hakanan qafafunsa ballantana fuskarshi,amma tana jin wani abu me nauyi game dashi
"Matso kiji Shehinaz" Akhnan ta fada tana murmushi gami da yafito Shehinaz din.