Showing 33001 words to 36000 words out of 178317 words

Chapter 12 - LU'ULU'U COMPLETE

taushi. Yau din ya fito a buzunsa kuma ba'adazensa sak,don kuwa riga ce 'yar shara a jikinsa ta wata dakakkiyar shadda da kum dogon wando,sai rawanin dake kansa wanda yayi masa nadi na cikakkun buzaye.

Shafukan qur'ani ne a hannunsa bugun warsh yake karantawa ciki ciki,amma shigowar safiyyan da kayan abincinta ya sakashi ajjiye qur'anin,ya kuma miqe ya zauna sosai yana murmushi.

Safiyya kenan iya rigima yake fada qasan ranshi. Ba tun yau ba yasan wannan,gwanar iya tunkarar duk wani nau'in rigima ne idan taso........idan kaso kuma komai zai wuce kamar bai faru ba.

"Marhaban lale" Ya fada yana miqa hannu zai karba mata kwandon. Janyewa tayi tana murmushi da accent dintan nan na yarensu tace.

"Bazan baka aiki ba.....kaida kake cikin lalura?". Murmushi kawai yayi. Kaman ba shekaran jiya aka gama hatsaniya da ita ba,ta birkita masa lissafi ta kuma birkitawa kowa.

Sosai ta zauna tana gaidashi cikin bashi girman da Allah ya bashin,ya amsa yana janta da tsokana,sai ta saki murmushi kawai ta jawo kwanukan abincin ta fara budewa.

"Me nassamu ni muhammadu?" Sosai maganar tasa ta sakata sakin murmushi,ta jima da sanin cewa tabbas shi din yasha banbam da sarakuna sosai......ya musu wata irin tazara me girma,yana mu'amala da iyalinsa da irin salon da zai nuna maka bai dauki kansa kowa ba a wajensu. Zakasha mamaki ida kaje ka sameshi cikin fadarsa.....ko ya fita wani taro ya cika wajen da wannan kwarjinin nasa,zaka tsinewa kanka ba shine a yanzun zaune ba.

"Tashi murmure na kawo maka". Tun bata gama zubawa ba yawunsa ya tsinke,ya sani bai taba yin matar da tasan martabar girki ba irin ta,tana da baiwa qarshe ta fannin iya abinci.......tana kuma bata lokutanta sosai wajen dafa masa abinci koda ba ko yaushe ba,girkinta a lokutanta yafi girkin hadimanta yawa.

"Wannan toshiyar baki ne halan?" Ya fada sanda yayi lomar farko,dadin abincin yana ratsashi.

Murmushi tayi tana sadda kanta qasa gami da murxa yatsunta kadan.

"Har ka gano ni?" Ta fada muryarta qasa qasa.

"Nafi kowa sanin halinki.......nafi kowa karantarki" Ya fada yana murmushi dadin abincin yana dibansa.

Kai kawai ta jinjina,bata musa ba......bata kuma yi jayayya ba. Mutum ce da bata iya boye abinda yake ranta ko yake cinta,ko yaya ne abu yake damunta sai ka fahimta,kota gaya maka,ko ka gani a fuskarta,ko ka gani a aikace. Bayan rasa imraan,bata qara tunani ko hasashen samu miji kamarsa ba,sai gashi Allah yayi mata kyauta da sultane din......wanda koda cikin mafarki bata taba kawowa zata mallakeshi ba koda wasa kuwa.

"Abincin cin hanci ne......cin hancin da na baka shine don ka tsaya ka fahimci zancan Allah da ma'aikinsa......zancan da yake da matuqar muhimmanci ba ga duniyarmu kadai ba......har lahirarmu" Tayi maganar a tausashe cikin qanqan da kai sanda ya kammala cin abincin yana miqe qafafunsa. Kallonta yakeyi sosai yana jin sautin muryarsa tana ratsashi,bazai ce ya maida gurbin safeena ba.......amma safiyya ta dabance.......daban take a zuciya da rayuwarsa.

"Wanne zance ne haka me muhimmanci har haka?".

"Batun amana ne.....magana akeyi akan amana" Ta fada yana sauke numfashinsa daga tambayarta da yayi.

"Amana?" Ya tambayeta yana jin kalmar tayi masa nauyi. Kai ta jinjina tana dubansa.

"Eh amana......amanar da safeena tabar maka......amanar da safeena tabar min.....wadda ni kam duk yadda naso ban isa na sauketa ba saida hadin kanka da goyon bayanka". Kai ya sake jinjinawa,zuwa yanzu hankalinsa yakai inda take nufa. Ganin maganar zatayi mata daidai da yadda take so ya kasance saita gyara zamanta sosai tana sake qanqan da kanta.

"Nasani ka sani......manzan rahama da kansa yana cewa......namiji me kiwo ne a gidansa......kuma zaa tambayeshi gami da abinda aka bashi kiwon.....kiwonnan kuwa ya hada da mata da 'ya'ya.......Allah yana cewa......yaku wadanda kukayi imani ku tsare kawunanku da iyalinku daga wuta......wanda wannan wutar makamashinta sune mutane da duwatsu......safeena ta tafi tabar maka amanar biftu.....shin a ranar gobe kana da kowacce amsa da zaka bata akan khadeejah idan ta tambayeka game da ita ba tare da d'ar d'ar ko tunanin ka kuskuro ta wani fannin ba?" Ta qarashe maganar da tambaya. Tambayar data masa nauyi sosai,ta kuma tilasta masa yin shuru,idanunsa akanta har lokacin.

Kanta ta girgiza sannan taci gaba da magana.

"Musulunci ya bawa iyaye daman zabawa 'ya'yansu yammata mijin aure.....hakan daidai ne,saboda ya duba cewa qila hankulansu basu nuna ba bare su zabawa kansu mijin daya dace da rayuwarsu......akwai sakin hannu me yawa game da damar daka bawa biftu.......ba zata iya ba......ba abinda zatayi wataqila saici gaba da wulaqanta masu daraja.....wanda akwai tafkeken kuskure cikin hakan.....altaab shine na tara da taqi amsa a mazaunin mijin amre......kana lissafe?". Maganar tata ta ratsashi sosai. Don sam wannan lissafin bai taba zuwa kansa ba.

"Baka tsoron wani ya cutar da ita ta wannan hanyar?.....ko bada sihiri ba qullaci idanu da baki dukka suna iya zamewa rayuwar bawa masifa".

"A'uzubillahi min kulli ainin lammah......wamin kulli shaidanin hamma" Ya furta a nutse wanda ta tabbatar yana nemawa diyarsa tsari ne daga abinda ta fada.

"Neman tsarinnan ranka ya dade ya kamata ya zama a aikace......ta hanyar taimakar diyarka ka zaba mata miji ma'abocin addini da zai saita rayuwarta" Sosai yake dubanta da maganarta ta qarshe yana fassara hakan cikin kwanyarsa.

"Eh.........namiji me addini shine kadai wanda zai iya gyara rayuwar biftu.......namiji me cike da nutsuwa da hasken addini......shi kadai ne zai cike gibin da aka bar mata cikin rayuwarta.......shi kadai ne zai iya kula da ita......ya dinke kowacce kalar baraka dake tsakaninta da ibadunta da mahaliccinta dama mutanen da take rayuwa tare dasu.......namiji me addini ne kawai zai riqe hannunta daga duhu zuwa haske......shi kadai ne fitila cikin rayuwarta......akwai tarin gyare gyaren da shi kadai ne zai mata nuni dashi......muddin kana buqatar tsiron nagartattun jikoki da zasu iya riqe masarautar AGADEZ daga fita daga hannunka.....a nan kusa muddin kanaso kaci moriyar jikokinka.....idan hakan bata kasance ba kuwa zai zamana dukkan wata dama zata qarasa subucewa daha hannunka".

Wasu irin dunqulallun maganganune da suka jima cikin zuciyarta da ruhinta......wasu irin dunqulallun maganganu masu tarin yawa da yau ta samu ta warwarewa sultane su......wata dama da taketa fama taci gaba da samunta har abada......damar da take sanyan ran da ita kadai zata iya tsaiwa gaban safeena ta gaya mata NA BAWA KHADEEJA GUDUNMAWA IYAKACIN QARFI DA IKONA.

Maganganun da suka dauki tunaninsa suka maidasu saman saitin da yakejin ya kamata su kasance.

"Na gode sosai safiyya......ina alfahari da samunki......saidai alqawari ne na yiwa kaina.....muddin raina ko yara million nawa na haifa bazan taba musu auren dole ba.....kowacce cikin yarana tana da damar farko......saidai idan ta gaza a damar farkon.....wala'alla a dama ta biyu ta rasa damarta" Dan murmushi ta saki,don iya wannan kadai daya fadi ya bata nutsuwa da tabbaci.

"Bashi da alfanu.....saidai sau tari idan har an kaucewa son rai,ita kadai ce take zamewa iyaye damar fidda yaransu zuwa turbar tsira......na aminta da alqawarin daka daukarwa kanka.......na yarda dakai kuma kan zaka canza komai.........." Kai kawai yake jinjinawa,saita rage masa tsahon tunanin daya jefa kansa ta hanyar gyara zamanta sannan tace.

"Dazun da safe munyi waya da hairaan......mun jima muna tattaunawa da ita.......daga qarshe dai ranka ya dade......raina da hankalina bai aminta da ci gaba da zaman yaran nan ba a qasar nan......mun yanke shawarar zasu dawo nan suci gaba da karatunsu......zan nema musu malamin da zai dinga koyar dasu qur'ani da litattafan addini......domin duk rayuwar da babu karatun addini a cikinta rudu ce da fagabniya zallah......ruhin da ba qur'ani a cikinsa Allah ya taimakeka fanko ne" . Kai yake jinjinawa yana sake aminta da hankali da nutsuwar morsa din. Tana da zafi da gaske ne tana da fada.......amma kusan komai tana yinsa ne bisa gaskiya da hangen nesa.

"Hakan yayi.....amma ko acan din nasan hairaan ba zata qyalesu haka ba ba karatun addini".

"Allah ya baka yawan rai ayimin afuwa.... Duk yadda zaa basu na addinin nan baikai na boko yawa ba.....har abada yaro yaro ne......akwai kuma quruciya dukkaninsu a jikinsu......suna manta shi ilimin addini tamkar dan jagora ko sandan jagora ce ga makaho......shike saita kowanne ruhi da gangar jiki.....shine yake saita ruhi rayuka da rayuwa gaba daya".

"Allah yayi miki albarka.....dawa dawa zaa taho?". Ya tambaya yana murmushi,don shi kansa kawai yana yin kara ne don kada ya shiga rayuwar yaran nasa..... Amma yan tsananin kewar jikokin nasa

"Dukkansu me martaba,falaak din......sai aafreen da aeeda,shi Aaroon nace su barshi can gurinta ya zauna da Anwar dan uwansa,kafin lokaci yakai suma na tattarosu".

" Ma sha Allah.....Allah ya kula mana da rayuwar su " Ya fada yana jin dadin hakan har cikin ransa. Duk da cewa falaak ce kawai jininsa.......amma yana jin hairaan a matsayin diyarsa halak malak........don daga jikin safiyya ta fito.....'ya'yan safiyya kuwa jinin safeena yana jin nasa ne. Idan ahalin suka hadu......yana manta cewa bashi da wani magaji tsayayye guda daya......yana manta cewa a yanzun ida ya fadi ya mutu sarautar qasar AGADEZ tana iya barin cikin gidansu ta fada zuwa hannun yaran gidan baffanninsa.....yasan komai na Allah ne.....muddin kuma akwai yiwuwar zaman sarautar hannunsu ba wanda ya isa ya karba,ballantana ma shi bai dauki gadon da wani zafi ba.... Don ko a baya zamanin kakanninsu ta taba barin hannun kakansa sai daga baya ta dawo musu.

"Ranka ya dade.....bawai zakayi sabbin amare ba fa kuma a juya mana baya" Ta fada cikin sigar tsokanar data sakashi murmusawa har kyakkyawar wushiryarsa ta fito.

★★★★

Qarfe shida da rabi na yammacin ranar motar qirar Lamborghini ta ajiyeta a sashen ajiyar motoci na musamman dake gidan.

Bude murfin motar akayi,daga gaba wani kakkauran matashi dake da komai baqi ya fito yana bude seat din baya.

Iska ta furzar daga bakinta tana jefo qafafunta waje.......gaba daya jikinta yayi laushi saboda dadewar da tayi a zaune a office.

Yau din harta gota lokacin tashinta saboda alwashin da taci tabbas sati me zuwa sabbin design na kamfaninsu zai fara zaga kasuwannin duniya.

Duk da a jigace take,amma hakan bai hana bayyanuwar kwantaccen kyan da take dashi ba. Jikinta yana busa lallausan qamshin nan nata a kowanne motsi da zatayi,iska kuma na dada zaqulo qamshin nata sanda take kada tattausar lafayar data nade jikinta da ita,lafayar data yafata iyakar kafada,kanta zaune das da daurin dankwalin wani veil baqi me taushi daya zauna mata kamar hula.

"Birra" Ta kira sunanta a gajiye..... Gajiyar data sake zame mata ado,don sai suka qara adadin yauqin halitta da yangar data zame mata ta asalin halittarta. Sign kawai tayi mata na ta karbi tarkacen office dinta dake hannun saaleem ta fara takawa zuwa gaba tana furta.

"Wash Allah na". Gami da yarfar da hannu.

Taku goma kacal tayi idanunta suka sauka kan Shehinaz ita da baqonta dake zaune suna facing juna..... Da alama magana ne sukayi me matuqar muhimmancin da har basa sanin meke faruwa daura dasu.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*MY NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽


💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎


*H U G U M A*


PAGE 14


Idanu akhnan ta fiddo tana kuma rage dan saurin data aro daaa don isa ciki ta watsar da gajiyarta. Mamaki da tsoro suna cikata tana kuma sake ware idanunta akan baqon Shehinaz din,wanda bata sani ba,kaifin idanunta ne suka sanya yaji kallon a jikinsa ya maido dubansa sashen da take?,abinda ya dauko hankalin Shehinaz kenan itama ta maido dubanta inda taga yana kalla.

Hannu ta dagawa akhnan cikin sakin murmushi,tashin farko taji ba zata iya maida mata koda da daga hannun ba bare murmushi ballantana akai ga takawarta zuwa inda suke,sai kawai ta dauke kai ta maida hankalinta zuwa hanyar da zata sadata da ainihin gidan zuciyarta na wani irin bugawa,bugawar da batasan meye dalilinta ba.....bacin rai ne?,ko kuma mamaki ne?,ba zata iya tantancewa ba.

Da kallo dukkansu sukabi bayanta har ta bacewa ganinsu,sai Shehinaz ta dauke dubanta ta mayar kan Jamaal tana maye mamakin dake saman fuskarta da murmushi.

Duk yadda taso wucewa daki kamar yadda ta tsara kafin ta iso gidan amma sai ta yada zango a parlor,abinda kusan ya bawa duka hadimanta mamaki. Saboda wani baqon abune da bata saba yinsa ba. Lokuta da dama ma idan ta dawo ta wuce ciki ba lallai bane ka sake ganinta ba sai washegari.

Hannatou keda hidima da ita tana kai kawon bata abunsha da tasan takan sha idan ta dawo gidan. Buhaina na qoqarin tattare kayan office din data cire a nan,takalminta laffayarta dan kwalinta da jewelry dinta duka data zare. Ta saba komai tana ajjiyeshi ne a inda yayi mata,akwai masu kula da komai din su tattalashi. Xasu kwashe jewelry dinta a gogeshi kowanne a maidashi cikin box dinsa. A sake goge takalmanta ayi musu feshi a maidasu cikin qawatacciyar ma'ajiyar takalman dake cikin dressing room dinta. Wannan ya sanya komai nata idan ka kalla zakace ba'a sakashi ko ba'a taba sakashi ba,don hatta da qasan takalmanta babu wani datti da zai alamta maka haka. Tana da mugun qyanqyami.......sai Allah ya hadata da hadimai na amana dake iyayi mata komai kamar ko fiye ma da yadda takeso. Ganin hankalinta ba'a gurin yake ba sai Hannatou ta janye hirar da take dan sako mata.

Agogo ta kalla dake bango don tuni ta cire na hannunta an wuce mata dashi. Ta soma gajiya da zaman jiran shigowar Shehinaz,kuma alamu sun nuna bata da niyya ko yunqurin shigowa a yanzu,dole ta miqe don wucewa ciki ranta na sake sosuwa. Taso qwarai Shehinaz ta shigo da zafi zafinta kafin ta sauya ra'ayin yi mata magana.

Dab da zata wuce hanyar da zata sadaka da dakunan baccinsu taji shigowar aisa. Ta biya ta wani guri ne bayan sun tashi daga office,don haka yau tafiyar tasu daban daban take.

"Kinga Shehinaz?" Ta tambayeta da muryarta a sanyaye. Bude idanu aisa tayi tana kallonta.

"Eh na ganta ita da jamaal.......so masha Allah wallahi......Il a une maturité étonnante,II a une apparence trés religieuse(akwai alamun kamala sosai tare dashi,da alamun addini sosai tare dashi)" Ta fada kanta tsaye fuskarta na gasgata abinda ta fada har cikin zuciyarta yake fitowa.

Baki da idanu kawai akhnan ta saki tana duban aisa,maqogoranta taji kamar ya bushe duk da bata jima da shan ruwa ba.......ta tattaro ragowar yawun bakinta ta hadiya sannan tace.

"Aisa.....Êtes-vouse conscient de ce que vous dites(kina sane da abinda kike fada?)......kina tunanin mace irin Shehinaz ta dace da kidahuman mazan da babu wayewa a tare dasu?"

"Qidahumai?" Aisa na maimaita kalmar cike da mamaki.

"Biftu?.....wai me kika dauki ma'anar KIDAHUMIN NAMIJI?.....Namijin da baiyi karatun boko ba?......namijin da ilimin arabiyya kawai yake dashi?,shine kidahumi?.....kinsan kura kuren dake cikin wannan tunanika naki guda biyu?".

"Ehnnnn........ki gayamin,Vouse lui lavez le cerveau(ke kike wanke mata tunani).......wannan mummunar hanya ce......hanya ce mara bullewa.......a ajin da darajar rayuwarta?........namiji me wannan suffar II n'était pas qualifié(bai cancanci) ya zama mijinta ba.......ba wani guri da mataki na rayuwa da zai iya tsaya miki........ba wani abu me muhimmanci da zai iya tunkararsa saidai ya tsaya a bayanki ki zame masa garkuwa.......banason irin wannan namijin......koda yaushe nafison NAMIJI ZAKI NAMIJI GARKUWA.......wayewarsa da iliminsa basu isa su tsaya a kowanne mataki da me ilimin boko zai tsaya ba.......mu gaya ma kanmu gaskiya kuma itama ki gaya mata gaskiya...." Ta qarashe maganan cikin fada da bacin ran da aisa ta jima bata ga ta yishi ba,sai kuma tayi gaba fuuuu da dan guntun saurinta ta wuce dakinta har aisa na jiyo qarar rufe qofar duk da qofofine da sam saika qaraci zamanka dasu bakaji qarar koda motsinsu ba.

"Mon dieu du ciel(oh Allah na)" Aisa ta fada tana komawa ta zauna saman kujerar dake daura da ita. Ba zafi abun yayi mata ba......mamakin dauka zafin da akhnan din tayi ne yake daure mata kai. Tabbas a dukka su ukun suna iya shawara akan rayuwar daya su tsaida matsaya ko si zartar. Tun asali tasan burace buracen akhnan akan iri mijin da ya cancanci ta aureshi masu yawan gaske ne.......tun asali tasan akhnan din burinta babba a wajen namiji ya zama me cikakkiyar wayewa.......me zuzzurfan matakin karatu a duniya gaba daya.......namiji me zarra sosai......tsayayye jarumi maras tsoro ko shakka......bata da burin namiji me ilimin addini muddin yana da ilimin da zai kiyaye ibadarsa daidai........abu na qarshe data tsana tafi kuma raina ajawalinsa shine.......namijin da zaiyu karatun arabiyya. Takan fadi wani lokaci idan magana ta tashi.

"Banga hikima ba......banga basira da wayo a karanta arabic ba.......a matsayinka na namiji da aka sani da zallar gwagwarmaya.......ina wani gwagwarmaya a karatun da iyakacinsa ka zama malami me koyarwa ko karantarwa?.

A sannan zata iya cewa bata fiya ganin aibu ko rashin dabara a maganganun akhnan nan ba.......amma sannu a hankali da girma ya ratsasu.......rayuwa ta rarrabasu zuwa wasu qasashe......cikin jinsina da yare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login