Showing 123001 words to 126000 words out of 178317 words

Chapter 42 - LU'ULU'U COMPLETE

biyun sanin wayeshi?......waye wannan daya bata dukkan wani record na rayuwarta,ya bata mata kyakkyawan tarihin da take dashi na tabbatuwar NASARA cikin kowanne taku motsi da gasa. Alwashi taci......sai kuma ta cikashi,ko waye shi sai ta bincikashi,sai ta yaye duvet din a hankali tana jan jikinta zuwa bakin gadon ta sauke qafafunta.

"Kada ki dinga wani abu kamar kin damu dani......kamar kuma kin damu da halin da nake ciki" Akhnan ta fadi cikin nuna halin ko in kula,tana kuma qin duban koda sashen da aisa take ne.

Idanu kadan aisa ta zuba mata,ta fahimci a birkice take,a kuma wannan yanayin da take ciki bata buqatar suyi rigima ko kadan. Ta karanci wani abu,duk sanda zai ziyarci mafarkinta,da dukkan zuciya da kuma feelings dinta takejin komai da zai faru a mafarkin kaman a gaske ne.

Bata fiya daukan FADUWA ba.......amma kuma zuciyarta bata da riqo irin wannan. Kafiya da taurin kai tabbas wannan cikin halayenta ne,amma riqo kam idan ta sakashi a cikin dabi'unta tasan da gaske ta mata qazafi.

"Biftu" Aisa ta kira sunanta,sai tayi kamar bata jita ba,ta qarasa gaban masaqalin da lausasan towel dinta ke a jere ta dauki dan madaidaicin ciki tana wucewa toilet.



*HAISAM*


Cikin nutsuwa ya zube dukka idanunsa saman system din gabansa,wadda a qalla kusan awa biyu ya kwashe a zaune din.

Sun gama tattaunawa dasu beena,wanda kowannensu yake wani sashe na daban cikin niger din don baza komarsu yadda ya dace. A yanzu da hussam yake waya,wanda kusan duka tattaunawar akan kamfanin turarensa ne da a yanzun suka samu labarin fitar wani qamshi dake shige da nasu a kasuwa.

Numfashi yaja yana lumshe kyawawan idanunsa masu yawan eye lashes,ya sakeyin relaxing yana ci gaba da duban hussam.

Ya fara gajiya da wannan tarin complain din da tun dazun yaketa abu daya,baisan me yakeso ba kuma.

"Hussam" Ya kirashi da wannan coolness din nasa.

"Obbo.....Allah obbo ka..."

"Ya isa.....,magananka yayi tsaho da yawa haka,da nazari nakeyi zuwa yanzu na karanta fuula(pages) masu yawa......maimakon hakan ka bata duka wannan lokacin mana wajen binciken sabon scent mana?" Ya qarasa maganar da sigar tambaya wanda kai tsaye hussam yasan umarni ne.

Kai hussam din ya jinjina,yana nufin cewa wani abu sallamarta da muryarta ya sauka a kunnensa.

Ci gaba da kallon screen din haisam yayi ba tare daya ware yatsunsa dake cikin na juna ba. A hankali taci gaba da takowa tana jin yadda sautin bugun zuciyarta yake qaruwa.

Tunda ta iso dab da gurin taji sassanyar muryarsa na fita ta system din radau kaman yana a wajen. Wannan sautin da take kwana ta kuma tashi da kewarsa. Ba'a maganar kyakkyawar fuskarsa data mata wani irin nisan da ba wanda yasan me takeji?,ya kuma takeji?,daga ita sai Allahnta kawai.

"Ani dagadheera saamee(na manta samee)" Hussam ya fadi yana waiwaya kadan ya dubeta,abinda ya bawa haisam daman hangota kenan.

Kamar kullum cikin jilbab dinta da yake yawaita dacewa da fatarta da kuma doguwar fuskarta,ma'abociyar siririn hanci,sak kamannin kyawawan 'yammatan qabilar oromo. Kanta a qasa,saidai hakan ya qaryatata. Ga duk me zuzzurfa da dogon nazari irin haisam din,kai tsaye zai fuskanci hankalinta yana fusguwa ga son kallon screen din system din hussam din,saidai tana qoqarin hana kanta faruwar hakan.

"Daqiiqaa tokko naaf kenni(bani minti daya),zamuyi sallama da captain obbo" Ya fadi tare da waiwayowa gaba daya yana duban haisam din.

"Obbo......ina ganin zan siya ticket kawai,zan wuce addis ababa gobe da safen.....zamu tura wasu sample na hadin sabon scent zuwa china.......akwai yuwuwar na tafi china din da kaina,akwai yiwuwar mu tura". Kansa yake gyada masa a nutse,kafin yace.

"Ka sallameta tukunna". Yayi maganar yana masa nuni da idanunsa

"Obbo.....wani littafi take nema......ina zaton kuma saina masa duba me kyau,kalleta ka gani ba sauri take ba a zaune take" Yayi maganar yana juyar da fuskar system din inda saamee ke zaune.

Idanunsa haisam din ya janye,daidai sanda ta daga kanta zuwa ga allon system din. Tana jin duk wata juriyarta ta qare,koda ta cikin allon computer din tana muradin ganin fuskarsa.

"Nagaan waaree booda obbo(barka da yamma obbo)" Ta fada a hankali tana sauke idanunta akan fuskarsa.

"Barka kade saamee......ya dalibai?" Yayi maganar yana qoqarin jawo wayarsa dake bada haske,abinda ya sanya sam idanunsa da hankalinsa basa kan system din kenan.

"Alhamdulillah" Ta fada a hankali tana jin wasu abubuwa biyu suna saukar mata.

Na farko wani yanayi da kai tsaye zata iya kiransa da qarfin izzar so irin tashi,wata qauna da ta cakuda da kewar abinda zuciya keso din. Ya mata wani fresh,ya mata wani irin kyau me daukan hankali,irin kyan da a kowacce rana ta daga idanunta take sake ganin sabuntarsa a idanunta.

Na biyu tayi burin ya kalleta......ko yaya itama ya kalleta kaman yadda ta kalleshi,sai kuma akayi rashin sa'a sam idanunsa basa kanta.

"Zamu sake magana anjima hussam,of eeggadhu(ka kula)" Ya qarasa fada yana aza idanunsa akan saamee da tuni ta maida kanta qasa tana wasa da yatsun hannunta kana ya katse kiran gaba daya.

System dinma gaba daya ya soma kashewa yana dan aza idanunsa akan agogon dake jikin system din kafin takai ga yin shutting down. Siririn tsaki yaja yana jin kamar kada yau ya sake fita ko ina. Saidai cikin qasa da second guda abinda ya faru jiya ya gilma a idanunsa.

Yaren oromo da ya fita da wani irin harshe da accent da yafi kama da irin nasu sak!. Irin karin harshen dake nuna duk wanda yayi yaren idan ba haifefaffen jimma bane yankin oromia,to lallai akwai wani dogon zama da kuma doguwar rayuwa da yayi a qasar.

Gilmawar kayan da ya gani dake bashi tabbacin na gidan sarautar agadez ne......sai ya miqa hannu ya dauki daya wayar tasa.

Notepad dinsa ya bude,yana sake duba documents din da yayi saving plate number din jiya yana sake duban numbers din da idanu,sai yayi minimizing ya koma contact nashi yana laluben wata number.

Bugu daya tak aka daga. Daga daya sashen ya soma gaidashi cikin girmamawa da yaren oromo irin na bakinsa sak.

"Aiki nakeso ayimin,amma bana buqatar gaggawa......take your time,inason respond din da zan samu ya zama me ma'ana....."

"In sha Allah sir" Ya kirashi da laqabin girmamawa na yaren turanci. Bai katse kiran ba yayi copying numbers din ya tura masa sannan a nutse yace.

"Have you seen it?".

"Yes sir" Ya fada da qwarin gwiwa.

"Fingers crossed" Ya fadi a taqaice.

"Thanks" Shima ya amsa masa,sai ya zame wayar daga kunnensa yana miqewa riqe da dukka wayoyin saboda knocking da yaji an masa kadan,yasan kuma zai wahala idan bai kasance maher bane.

Ya canka daidai,maher dinne rungume da litattafai a hannunsa.

"Minti arba'in yayi saura lokaci ya cika".

" Ka jirani" Kawai yace dashi yana takawa a nutse gami da nufar hanyar da zata sadashi da sassan dakunansa yana karbar towel daga hannun salaana,abinda ke alamta masa ya kammala hada masa ruwan wanka kenan.

Baisan me yake faruwa dashi ba,ba kuma zaice gashi ba......amma haka kawai yake loosing interest akan aikin. Aikin da shi ya nema gudanar dashi,amma haka kawai yakejin yana barin kansa,wanda baisan dalili ba.

Dukkanin yaransa da suke aiwatar da aikin tare sun fishi zama serious. Baisani ba ko saboda sanin da sukayi masa shi din bame wasa da ayyuka bane yasa kowannensu yake cikin hayyacinsa akan aikin ba tare da sunsan shi din ya rasa interest ba.

Ya dan jima gaban closet dinsa yana duban kayansa dake tsare a saqale jikin hanger. Mafi akasarinsu jubah ne masu tsananin kyau sulbi da kuma daukan hankalin dake bayyana tsadarsu da darajar zaren da aka samar dasu. Kusan yawancinsu qasar qasar saudiyya ne....qatar oman da morocco. Sai kuma cloak robe da suma bangarensu yake daban,nau'ika da kaloli mabanbanta da suka dace sosai da kowacce jubah da jallabiyya dake cikin closet din. Akwai kurta da kuftas masu kyau,wanda ba kasafau ya fiya sanya kufta ba,yazo ya samesu ne an jeresu cikin closet din,wanda ya tabbatar aikin abdii ne,kuma tafiyayyu ne daga qasar nigeria,bayan wani dare da abdii din ya kashe yana searching qasa da kuma yankin da yafi ko ina iya dinkasu,bincikensa ya sauka a garin kano dake qasaf nigeria din. Sun burgeshi,sun bashi sha'awa sosai,kowacce kusan da hularta 'yar Maiduguri me daukan idanu,amma har yau bai sanya ba,yana ganin kamar bazai zama comfortable ba idan yayi shigar.



zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*


*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261


*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

*HUGUMANKU CE*โœ๐Ÿฝ

๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž


*H U G U M A*


PAGE 59
___________________________
Bononza bononza https://wa.link/l1gcz8
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 6k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba pills shaki matse masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 11k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, da maganin sanyi wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne
Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 4k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka
Karku manta promo kwana 3 ne an kare insha Allah
_____________________________



Sake bin kayan yayi da kallo,a qalla sun kusa set d'ari. A hakan kuma kadan aka tsakura daga suturunsa dake tsakanin addis ababa da kuma jimma,don idan yace yasan adadin suturarshi tabbas yayi qaryar da baisan ta inda zaiyi kaffararta ba.

Wani irin ni'imtaccen qamshi cikin closet din kanshi yake bayarwa,ballantana kuma suturun dake ciki,masu abu da abunsu....... Gidan turare ne shi din.....sai ya zamana kuma masoyin turaren,kyautuka guda biyu mafiya girma da tsada da daraja da zaka masa shine. Turare da littafi,sai kuma dabino daya zame masa kusan abincinsa. A kowacce shekara qwararrun masu sarrafa turare daga dukkan kamfaninsa ne suke zama su fidda masa qamshinsa na musamman,irin qamshin da komai kudi dukiya ko mulkinka basa taba fiddashi ko su saidashi,wani unique qamshi ne da babu inda zaka sameshi sai jikin SHEIK HAISAM din.

Sun fara haka ne da zummar tukuicin kyautatawa da yakewa dukkan wani ma'aikaci dake qarqashinsa,basusan dame zasu saka masa ba,shi yasa suka maida hakan a mazaunin hanyar rama alkhairansa a kansu. Hakan yana masa dadi,dukkan wani turare da zasu fidda masa yana jin kamar yafi na baya dadi,da wannan ya kasance.......yadda komai na sheik HAISAM yake na daban.......na musamman,haka ma qamshinsa. Wannan qamshin ya nasaka zukatan 'yan mata da yawa......qamshin da muddin kika jishi sau daya ba zaki sake jin makamancinsa ba har abada.

Masu kudi da masu mulki da dama daga sassan duniya,sun saka kudade masu nauyi saboda samun irin wannan scent din,amma dukka ma'aikatan,duk da ya basu dama sunqi aminta su bawa kowa wannan TAMBARIN wannan TAG din,wannan alamar ta SHEIK MUHAMMAD HAISAM ce.

Wata dark grey colour jubah hannunsa yakai kai. Lafiyayyen dinki aka mata da wani irin yadi me yauqi. Hannu da wuyanta dukka na musamman ne da wani irin button na musamman.

Cloak robe ya zaro me hasken kala da zata dace da rigar ya taka yana matsawa a gurin. Tsaf ya kammala shiryawa,yayi tsaye gaban mirror yana daura agogo a tsintsiyar hannunsa. Tun daga nesa idan ka kalleshi zaka ga wani irin kwantaccen kwarjini saman fuskarsa,duk da yau fuskar haisam din adan dinke take,wanda yake da nasaba da yanayin da yakejin zuciyarsa. Haka kawai yakejin ranshi ba dadi,kaman an masa wani abu daya taba ranshi. Ya sani,ba wani wanda ya bata masa rai,hakan wataqila yana da nasaba da shaidan,wanda a kullum burinsa shine ya zunguri zuciyar dan adam,don haka ya daga idanunsa a hankali ya sauke akan fuskarsa data fita sosai da wani irin annuri. Kwantacciyar sumar kansa data habarsa zuwa kuncinsa tayi luf da wani irin baqi me qyalli da daukan hankali,ya lumshe almond eyes dinsa yana furta.

"A'uzubillahi minashshaidanir rajeem.....subhanallahi wabi hamdih......subhanallahil azeem". Ya maida qwayar idanunsa akan agogonsa.

Tsaiwa yayi cak yana karanta brand din agogon. Yayi kudi da yawa,yayi tsadar da duk wanda yasan kudin agogo yana kalla zai dora zargi a kansa,ya jawo jewelry organizer din dake saman dressing mirror din yana neman me sassauqan kudi,saidai har ya gama lalubensa bai samu daidai da wanda yakeso ba,dole ya dauki qaramin ciki ya daura ya koma neman takalmi.

Shima still kaman agogon dai,duk ciki ba wani me qaramin kudi,ya gama lalubensa shima dole hakanan ya dauka ya saka,a ransa yana mita akan abdii.

Baisan me ya samu abdii ba,shi ya shirya masa komai na amfaninsa,me yasa yake manta dalilan shigowarsu agadez ne?. Dole komai nasa ya zama moderate,idan ba haka ba da taqi kadan zamansu zai kasa tsaho,duk da yace baisan inda zai sama masa sutura masu qaramin kudi ba sama da wadannan,amma dole ya canza masa wasu abubuwan nashi.

Cikin girmamawa drive dinsa ya bude masa BMW din. Yana shirin shiga muryar omari ta tsaidashi.

"Captain sheikh" Ya fadi yana takowa a nutse. Baice komai ba sai daya shiga ya zauna,ya daga idonsa yana duban Omari. Gira kawai ya dagewa Omari din,a karon farki kuma Omari ya fahimci yau 'yan miskilancinne a kusa.

Maganan da zasuyin me muhimmanci ce,banda hakan zai qyaleshi ne ya tafi,yasan idan 'yan mode din nasa suka sauka zaya nemeshi da kansa.

Screen din system dinsa dake hannunsa ya juya ya nuna masa,sai baice masa komai ba bayan ya kalla ya masa nuni da hannu yana matsawa ciki omari din ya samu gurbin shiga.

Ba wanda yace da kowa komai,omari na qoqarin qarasa saita bayanan da zaiwa haisam din,yayin da haisam din ya maida hankalinsa ga qari'ar dake fita can qasa cikin motar. Sanda Omari ya yunqura zaiyi magana sai ya dauki remote din dake gefansa ya kashe karatun.

"Captain sheikh.......mr Ilaalcha gadi buusuun" Ya fadi yana murmushi ba tare daya kalli haisam din ba.

"No more oromo dialogue here mr man......ka kiyaye" Ya fadi yana maida mode dinsa na senior oga kaman yadda yakeyi wani lokacin.

Murmushi me kama da dariya sosai Omari ya saki,yayi saluting nasa yana cewa.

"Yes sir......but am sorry,Allah saina fadi,mr lowering gaze.......amma komai naka ya zama me daukan hankali.......ta yaya su matan zasu iya kame idanunsa daga kanka?......ka kalli kanka yau kuwa?,kasan Allah?......am very serious,duk yarinyar da tayi falling a kanka saina tayata yaqin samunka?". Ido kawai haisam ya zubawa omari,ganin yadda yake maganar da dukka gaskiyarsa. Sai ya janye idanun ganin Omari shima ya dauke dubansa ya mayar ga system dinsa yana qananun mitoci qasa qasa.

"Haka kawai,rashin adalci ne ka dinga tunanin 'yammata ba zasu soka ba,......suma da laifinsu.......mu su somu su gani mana".

Bai shirya yin dariya ba sam,duk da dama ba al'adarsa bace,amma duk da haka sai da omari yayi sanadin fitar murmushi a fuskarsa,ya kuma kaiwa Omari dind duka,sai shima ya saki dariya yana wani mazewa.

"Allah,da gaske......inajin akwai wani laqanin da kake karantawa a kansu"

"Inda akwai Omari saika riga kowa sani......inda kuma akwai da tuni na dade da baka omari,kaje kayi kaji yadda nakeji......banaso omari,sau da dama yawaitar mata a rayuwa mutum irin haka idan baiyi takatsantsan ba,idan kuma baiyi da gaske ba sharri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login