Showing 156001 words to 159000 words out of 178317 words
girmamawar da idan sun kebe ne kawai yake samun daman nuna masa.
"Barkanka Maher" Ya amsawa Maher din a ataqaice wanda shima hankalinsa yake kan kayan da abdii keta dagawa.
"Obbo......zaka fita ne?" Maher yayi tambayar a nutse yana zama.
"Tambayeshi" Ya furta yana masa nuni da sashen da abdii din ke zaune ba tare da ya sake bi ta kansu ba,sai ya ture duka kayan gabansa yana miqewa gami da duba lokaci.
Gayyatar tazo masa a bazata,kuma tabbas inda abdii ya fadi masa zai basu haquri ne. Ba kasafai ya fiya son a jashi cikin wasu alaqoqi ko dangantaka masu zurfi ba.
Murmushi maher ya saki bayan abdii ya bashi amsar tambayarsa. Da gaske rashin sani duhu ne da bashi da kama,inda sultane yasan da waye yake tare,ko wannan apartment din daya ajiye haisam zaisan yayi babban kuskure. Girma qarfi da izzar masarauta baya jin akwai ya masarautar oromo koda cikin Ethiopia ballantana sauran qasashe,amma a iya sanin Maher,ba qaramin mutum bane sultane zaiwa gayyata irin wannan.
"Da gaske sultane ya baka babban matsayi da bana tunanin a tarihinsa akwai wanda ya samu kwatankwacin haka......karkace ba zaka halarta ba obbo......amma abdii wannan kayan duka daka dauko maidasu zakayi" Maher ya fada yana dariya.
Ya sani,sau da dama abdii din yana manta mission dinsu na shigowa agadez,girma da matsayin haisam yana bugar dashi ya manta da wannan.
Yana takawa zuwa dakinsa yana juya maganganun Maher. Dukka maganganunsa suna kan hanya,hanya daya ce kawai zata kawo masa komai cikin sauqi,tunda dukka wani bincike da kuma signals sun basu hasken wanda suke nema yana rayuwa ne cikin daya daga cikin masarautun qasar niger,masarautar agadez kuma nada girman da zarginsa yasa yafi rinjaye a kanta.
A nutse ya isa dakinsa ya tura ya shiga,idanunsa akan private patio din gaban ginin benen wanda baida wani wadataccen haske. Ma'abocin son zama ne shi a irin guraren nan,don suna bashi iska me kyau,suna kuma bashi damar warware tunanikan da suka sarqafe masa kwanya. Duqawa yayi ya dauki wani abu kaman Bluetooth ya,ya budeshi,sai ga wani abu ya bayyana kaman keyboard dan mitsitsi. Wasu number dake bada kalan sky blue ya danna jikin qaramin Keyboard din,sannna ya zari Bluetooth daya ya cusa cikin kunnensa,ya maida dan qaramin box din ya ajiye ya fara takawa a hankali zuwa private patios din,don bai samu shiga gurin ba sam tunda ya fara zagaya sassan nasa.
Fes gurin yake a tsare da wani irin tsaftar da ba zaka dauka saman bene bane. Lullube da wasu irin marbles masu daraja da sheqi. Glass ne ya zama kaman Katanga na gurin,wannan shine zai bawa wanda yake ciki cikakken daman ganin hagu da dama da kuma gaban komai dake zagaye da sassan nasa.
Straight idanunshi suka sauka ga qawataccen ginin dake gabansa. Wani madaidaicin gini da yafi kama da gidajen da aka dauko cancakat daga qasashen turawa akazo aka dasashi gaban nasa.
Daga yanayin color na paint din ginin,yawan deco na flower da ya hanga,da kuma tsarin private patios din dake kallon nasa ya tabbatar gurin mallakar macace.
Akwai qarancin hasken dake nuna ba kowacce fitila bace ta sashen a kunne,kaman yadda farfajiyarsa ma bata cika haske sosai ba.
Maida dubansa yayi hannun hagunsa,daga can din wani guri ya hanga daban,wanda da alama kebantacce ne shima,ba gurine na mu'amalar mutane ba,a yadda ya nazarci gurin yafi masa kama da wani guri na ajiye ajiyen kayan da ba nan kusa ake tabasu ko ayi amfani dasu ba. Hannun damansa ya maida dubansa,daga can nesa shima wani muhallinne na daban,sai ya janye idonsa a nutse sanda muryar omari ta cika kunnensa da cikakkiyar sallamarss.
Ya motsa labbansa a nutse yana amsawa omari din sannan ya fara takawa yana dawowa bedroom dinsa gami da maida qofar da labulen daya raba tsakanin dakin da private patios din yana rufewa.
"Mr ilaalcha gadi buusuun.......ya kakeyi da 'yammatan masarauta?" Omari ya fadi da sigar tsokanar nan tasa. Ido haisam ya lumshe sannan ya bude duka lokaci guda.
(08187255862 lu'u lu'u paying)
"Ka adana yaren oromo omari.......ba yanzu ba,ka saka a kanka kuma,shi muhammad haisam idan aiki ya taso masa,baya gane kowa,baya kuma gane komai,har sai ranar daya kammala aikinsa.....koda ya kammala dinma,nanay kawai yake ganewa" Ya fada calmly,kuma har cikin zuciyarsa yana jin hakan. Aikinsa nada matuqar muhimmancin da yakejin bazai iya hadashi da kowa ba,bazai kuma iya badashi da komai ba.
Qaramin dariya omari ya saki,halayen haisam nada abun mamaki,sun jima a tare,amma har yanzu yana kan shan mamakinsa idan yayi wani sabon abu cikin halayensa da shi baisan dashi ba.
"Naga alama.......ka dole Menelik sai data kirani,sai data nemeni da tarin jin kunyarnan taka,tana cigiyarka,gidanka satittika da dama ba haske,bata ganin motsinka kona wani a cikin gidan........ba zaka duba ba haisam kuwa?,anya?"
"Omar" Ya kirashi cikin qosawa da maganganunsa.
"Kaji da ita mana?.......saamee Menelik dukka nabar maka,kaidain mijin mace hudu ne ko?".
"Haisam mana...." Omar ya fadi da zummar jan hankalinsa,da gaske tausayinsu yakeji,don shi kansa baisan ta hanyar da zamu cimma burinsu akanshi ba,daga ita har innocent saame.
"Look please........muna bakin aiki ne ka tuna.......duk wani kira da zaka sameshi daga gareni ta wannan device din me muhimmanci ne,baida alaqa da kowacce yarinya........my rules are as simple as ABC......ya kamata ka haddacesu haka" Yadda tone din muryarsa ya canza ya tabbatarwa da omari da gaske yana nufin abinda ya fada. Murmushi me sauti ya saki yana jinjina kai kaman haisam na gabanshi.
"Bana tunanin kana lafiya haisam......even little akayi magana akan abokiyar rayuwa
"Omaaarrrrr...." Ya kirashi yana jan sunansa da qarfi,don attention nasa kawai yake buqata,wannan zancan ya isheshi haka.
"I'm focusing on what matters most to me" Ya fada yana zuqar numfashi da yakejin kaman bazai kai masa ciki ba.
Shuru ne ya ratsa tsakaninsu,omar yana sauraren saukar numfashin haisam din,yayin da shi kuma haisam ke qoqarin daidaita nutsuwarsa.
"It's fine......idan lokaci yazo maka a qurace,zanga wadda zaka damqo,Allah ya rabaka da makahon zabe". Hannunsa ya aza saman kansa yana yamutsa lallausan gashinsa,da gaske dai dole omar wannan kafiyar tasa ba zata barshi ba.....dole sai ya qarasa zazzage masa abinda ke cikin ranshi?.
"Zan shiga gurin sultane yau" Ya fadi saqon kawai kai tsaye,don maganganun omari kawai yana kallonsu ne a wasu abubuwa da basu da muhimmanci ko amfani face bata lokacinsa kawai.
"That's good......da sauri haka?"
"Out of the blue........yanzun nan saqon ya sameni.....inaso ka zama a ankare,this could be our starting point".
"Yes" Omari ya fadi yana tashi daga kwancen da yake.
"Any update from beeno?" Kai omar ya girgiza.
"Munyi waya dazun,kowa dai yana bakin aikinsa........salawi ya tura wani information,ina cikin dubawa ne ma kiran Menelik ya shigo min". Tsaki yakeso ya jawa omari,amma ba abu bane me kyau,don haka yayi banza dashi kaman baiji ba.
" Ka turamin ta office email dina.....ka kula gurin tura komai"
"Wrapped up" Ya amsa masa,sai ya sanya hannu ya zare Bluetooth din yana katseshi gudun kada omari din ya sake jefo masa wani maganan.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer ๐ณ๐ช*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA๐*
*HUGUMANKU CE*โ๐ฝ
๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
PAGE 74
___________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________
A nutse ya matsa zuwa inda towels dinsa suke maqale,ya zari babba guda daya me tsananin laushi ya ajiye saman dressing table,ya soma zare rigar jikinsa,wanda hakan ya bawa faffadan qirjinsa dake dauke da lallausar gargasa daman bayyana. Wani irin baiwar suma Allah yayi masa,tun daga saman kansa zuwa kumatunsa habarsa girarsa,hannu da qafansa da kuma qirjinsa wanda ya hade har qasan cibiyarsa.
Ba kowa ke fahimta ko sanin hakan ba,kasancewarsa ma'abocin sanya long sleeve shirts da kuma jubah masu dogon hannu da kuma rufaffen wuya. Daura towel yayi a qugunsa,yana shirin wucewa toilet still wayarsa ta tsaidashi.
Ringing ne na musamman,wanda ya sakawa nanay. Sautin da ko bacci yakeyi idan ya jishi sai ya farka,don kirane na musamman daba kiran daya kaishi muhimmanci a gurinsa.
Zame towel din dake fadarsa yayi sannan ya dauki waya ya jawo stool ya zauna,don indai kaga ya amsa wayar nanay ko motii a tsaye tabbatar hakan shine option din kadai daya rage masa.
Cikin cikakkiyar nutsuwar nan tasa ya yiwa nanay sallama.
"Wa'alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu" Ta amsa da cikakken sallama,wani sanyi na sauka qasan ranta,yayin data aza idanunta saman fuskar saame wadda ke takowa a hankali zuwa ciki tana dauke da wata irin royal burner da turaren wuta ke fita a hankali.
"Barka da dare nanay" Ya fadi yana rusunar da kansa cikin yaren oromo kamar yana gabanta cikin tausasa harshe irin na 'ya'yan da sukasan tsantsar darajar mahaifiya.
"Barkanka da wannan lokaci muhammad......"
"Kina lafiya?......"
"Alhmdlh muhammadu"
"Motii fa?,na gaza samun wayarshi tun jiya,nayi magana da hussam nace ya hadani dashi". Murmushi kadan nanay ta saki,tasan akwai daru yanzun nan.
"Motii baya masarauta,yayi wata 'yar tafiya" Idanunsa yadan qarawa girma kadan kamar nanay na kallonshi.
"Nanay?,zuwa ina?,ina kuma yaje?". Ya furta calmly,saidai kuma muryarsa tana nuna labarin bai masa ba sam.
"Ba wani guri yaje ba,umara ya tafi,sati biyu kacal zaiyi ya dawo,shi ya hana a gaya maka saboda yasan zakace ya jiraka,zaka baro aikinka ne ka dawo kuje kuyi tare ku dawo tare,yace zuwa yanzun ya kamata kaima ka huta,ya kamata ka tattara hankalinka gaba daya akan aikinka.....iyali zaka ajiye nan gaba kadan,bazaiyiwu ka hada hidimarsu da tamu ba". Wani sassanyan ajiyar zuciya ya sauke,wanda duk yadda yakai ga boyewa nanay ta jita cikin jikinta. Yana daya daga cikin dalilan da ya sanya yaji har yanzu batun maida hankali yayi aure sam bai zauna masa ba,baya qaunar abinda zai nesantashi daga hidimar kula da lafiya da duk wani motsin motii ko nanay.
Akwai wata lullubabbiyar qura cikin rayuwarsu,qurar daya tabbatar har yanxu ba'ayi ruwan da zai daketa yadda ya kamata ya kwantar da ita katitir ba. Yayi imanin wannan qurar tana kwance......zataci gaba da kwanciya ne har zuwa ranar da zai damqo makashin ajani......ranar da duk wani da yake da hannu cikin mutuwar ajani zai bayyana,yana tunanin daga wannan lokacinne kadai yake da cikakken sukuni cikin rayuwarsa. Har yanzu basusan siradin da suke ciki ba,motii ma da ya fuskanci kadan daga ciki har yanzu bai dauki abun da girman daya kamata ya daukeshi ba,yana yaiwata gaya masa.
"Muhammad..... Mutuwa da rayuwa dukkaninsu a hannun Allah suke,ba me rayawa sai shi,kaman yadda ba wanda ya isa ya kashe saishi". Ya sani,kamar yadda shima motii ya sani. Yana da dukkan wannan........amma hakan bazai zama hujjan da zai saki jiki ga kulawa da bada dukkan kariyar da zai iya ga halittu guda biyu mafiya daraja da kima a tattare da rayuwanshi ba.
"Muhammadu?" Nanay ta kira sunansa a hankali,sanda saame ta qaraso gefanta ta tsugunna tana ajiye kaskon hannunta,ta kuma motsa zuciyarta na tsananta bugawa da zummar tashi tabar gurin. A tausashe nanay ta riqe hannuwan samee cikin nata tana kuma sauraren qorafin haisam.
"Don Allah nanay......ki fadi masa,kada ya sake zuwa ko ina shi daya,yayi haquri har sai na dawo,idan ya zama dalili ne kuma na gaggawa,zan bar duk abinda nakeyi,zanyi booking flight nazo na daukeshi muje mu dawo" Murmushi maras sauti ya subuce mata. A duniya idan tace bata taba sani ko ganin iyaye 'yan gatan 'ya'yansu ba ita da motii batayi qarya ba. Bakinta harshenta dama zuciyarta gaba daya basa gajiya da nanata addu'a a kanshi da 'yan uwanshi,ba shakka tana cikin jerin sahun mata da sukayi dacen samun 'ya'ya a duniya.
"Zan shaida masa in sha Allah.........nayi nayi da hussam yayi magana dakai akai kudaden daka saka ya sanya a account dina?". Sai daya sauke ajiyar zuciya kadan,har yanzu hankalinsa yana tare da mootii sannan ya amsa mata calmly.
"Naki ne nanay,kiyi duk yadda kikaga dama dashi". Ba wani abu bane sabo a gurin nanay,amma yawan nauyin kudaden suna sanyata jin kamar tana shiga haqqinsa da yawa.
" Jinan Muhammadu......kasan nawa ya saka?". Kai ya gyada a nutse yana lumshe idanunsa.
"Na sani nanay.....ko kaina na saka aka narka aka saka miki a account dinki ban biyaki da komai ba......ba abinda na mallaka ba,ni kaina sai yadda kikayi dani" Ya fada da wata irin cikakkiyar nutsuwa dake saka masa wani irin kwarjini a fuska da nutsuwa a maganganunsa.
Shuru nanay tayi na dan lokaci,tana jin kamar a duniya babu wani aiki data taba yi wanda ta cancanci ubangiji ya bata yaro irin muhammad haisam din,kawai baiwa ce da falala daga ubangijinta.
"Allah ya farantawa rayuwarka,ya sanya haske daga farkonta har qarshenta,ya sanyaka cikin mafiya alkhairi kuma mafiya rinjaye a rayuwa".
"Allahumma ameen" Ya fadi yana jin a duniya yau dai duka baiji wani lafazi mai dadi sama da wannan ba.
"Shi da waye da waye suka tafi?" Ya dawo da zancan motii,abinda ya sake haifar da murmushinta tana jin hannuwan saame dake cikin nata har yanzu yadda sukayi sanyi qalau.
"Shi da Musayyib da Hezbollah,akwai security da NISS suka aiko daga muhammad Dawood". Kai ya jinjina yana jin ya samu 'yar qaramar nutsuwa. Abba Dawood din yasan komai da zai sakashi nutsuwa a aikinsa,ya tabbatar shi yasa ya hada motii da security team.
"Ga samee" Ya tsinci muryar Nanay cikin kunnuwansa. Ko kafin yace wani abu,ta cire wayar daga kunnenta tana miqawa samee idanunta akan yarinyar.
A daren sam batayi niyyar kiran haisam ba,sai gobe kaman yadda suka saba. Amma hakanan take lura da motsin yarinyar ya sauya,ta zama so silent,bata da wani karsashi.
Ta sani,tana kewarsa ne wanda alkunyarta ya sanya ba zata iya fadi ba,tsaron kima da martabarta kuma ba zata bari ta kirashi ki tsaye ba,saita miqe a nutse bayan ta damqa mata wayar,don sam bata da wani ciwon qafa ko nauyi jiki irin na wanda shekarunsa suka fara tafiya,ta taka a nutse tana bar mata dakin hutawar zuwa ainihin nata dakin kwanar.
Daskarewa jinin jikinta yayi na wucin gadi kafin ya narke yaci gaba da kwaranyawa cikin jikinta da wani irin matsanancin bugun zuciya,ta maqala wayar a kunnenta tana jin kamar zuciyarta zata fito ta bakinta.
Da wani irin sanyi da tsoro tayi sallama,yana jin yadda zuciyarta ke bugawa a qirjinta saboda tsananin kewarsa da tayi.
Sanda ya amsa sallamarta kuwa saida numfashinta ya tsaya na wucin gadi,ta kuma gaza cewa komai,har sai da taji yace.
"Kina lafiya?".
" Alhmdlh obbo.... Ya aiki?,Allah ya taimaka yayi jagora".
"Ameen ameen" Ya amsa mata a taqaice,don yana jin kamar tana cinye masa lokacinsa.
Shurun data sakeyi sai yaji kaman bai kyauta ba. Yasan meye a zuciyarta,yasan kuma me take yaqi doshi,ko yaya tana buqatar abinda zaiyi calming nata down,koda bame yawa bane,don haka cikin qarfin hali ya tattara kalaman.
"Komai lafiya ko?"
"Lafiya qalau alhmdlh"
"Ma sha Allah......ki kula da kanki,Allah ya taimaka". Saura qiris garin jan numfashi ta hada harda zuciyar dake qirjinta. Karo na farko da irin wannan kalmar ta fita a bakinsa zuwa gareta.
Ta sani,he was a caring person......yana da tausayi musamman ga mace,amma bai taba gwada gaya mata kalma irin haka ba,sai kawai ta kifa fuskarta saman cinyoyinta zuciyarta na wani irin bugu,ko kalaman NA GODE da zuciyarta ke bata shawaran gaya masa bata samu damar fadi ba,don dama yana gama fadin hakan ya yanke kiran.
"Har kun gama wayar?" Muryar Anani ta ratsa kunnuwanta. Kanta ta daga da sauri suka hada idanu da Anani din,sai ta kashe ma saame idanu tana dariya qasa qasa.
"Muddin kikace zaki fara narkewa da soyayyar captain obbo......na rantse nan gaba zaki koma tamkar ruwa ne.......ni nasan irin su captain sheikh..........saamee...." Sai kawai Anani ta gaza qarasawa tahau girgiza kai.
Ranar data fara duba daya daga cikin rubuce rubucensa akan soyayya,cikin wani irin tsari na a addinance yadda zaka kama zuciyar mace tabbas banda yayanta ne uwa daya uba daya tayi imanin ba abinda zai hanata fadawa soyayyarsa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Wasu irin kalamai da aka shiryasu da harshen larabci,sannan akayi translating nasu da yare biyu English da oromo,sai da tayi kwana uku tana duba littafi daya,daga qarshe data fuskanci idan batai wasa ba littafin zai iya sauketa daga karatunta daga