Showing 138001 words to 141000 words out of 178317 words
yake miqewa tsaye,sanye da wata fara qal din shirt cotton sosai me gajeran hannu da round neck,abinda ya bayyana cikakkun muscles dinsa da suke gayawa duk wanda ya kalla yanayin qarfi da yawan motsa jikin da yake dashi. Hannunsa zube a aljihun wandonsa da bai sauka har qasa ba.
๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
PAGE 65
Daga kai omari yayi yana dubansa yana kuma d'an jin mamakin tambayar,don ko a wancan karon haisam din baima tsaya sauraren kowanne bayani akan race din ba,abinda yafi maida hankali kawai shine yadda wasan zai qare,su kuma samu daman shigewa cikin agadez a sirrance.
"Princess akhnan muhammad hammud.......qasaitacciyar d'iyar sarki muhammad hammud......bansan ya zata kasance ba duk ranar da tasan cewa kaine silar faduwar nasararta" Omari yayi maganar yana sakin murmushi idanunsa akan haisam. Ya san halin haisam din,yana da sauqin kai ta bangarori da dama.... Yana da bala'in bada girma daraja da martabawa ga dukkan wanda yake sama da shekarunsa........amma fa bashi da dadi a wasu lokutan......yana da wata irin zuciya da muddin aka tabota......sauketa yana zama abu me wahala......ba kowanne irin hali da dabi'u yake tolerating daga waninsa ba......akwai wasu halaye da dabi'u da muddin kana dasu kada kayi kuskuren sha'awar yin rayuwa dashi. Yana da girmamawa don haka bayason raini,bai fiya daukan kansa da girma ba......amma kuma baya daukan raini wulaqanci ko qasqanci. Yana da dokoki......yana da iyakoki.......yana da layuka da yakam shata akan kowanne mutum da zaiyi rayuwa dashi.
RESPECT wani abu ne muhimmanci a tare dashi........baya wasa dashi baya yiwa wani wasa da mutuncinsa. Miskili ne irin miskilancin da idan ya motsa masa zaka jima kana rayuwa dashi baka gama fahimtar ya sound na muryarsa yake ba. Zai iya wuni guda kuna hira yana maqale da littafi abinsa,ko kunnensa ba zaku samu ba ballantana hankalinsa. Murmushi yafi zame masa amsa akan ya furta da bakinsa,dariyarsa tana da qaranci qwarai da ba kowa yasan launinta ba.......saidai duk da wadannan yana da zuciya me taushi......yana da wani irin kyakyawar zuciya me cike da dimbin alkhairi..... Irin alkhairin nan me sanyi da saka zuciya a mamakin mallakin zuciya me tarin alkhairi irin wannan.
"Na fahimci abubuwa da dama a tattare da ita a fitata da nakeyi cikin mutanen ta" Omari ya dora da fadi ganin ya samu daman hiran da yakeso yayi da haisam din. Taku biyu haisam din ya qarayi gaba,abinda ya tabbatarwa omari idan bai hanzarta ba haisam yana iya tafiya abinsa.
"Bata yana faduwa ba a dukkan komai.......itace gaba a kowanne abu da zai taso,ta tsani faduwa.......tana da wata irin izza da take rayuwa sama da izzar da sultane mahaifinta yake da ita. Ba kowa bane yasan fuskarta,ba kowa bane yasan muryarta,ba kuma kowa bane yasan ainihin kamanninta koda kuwa wadanda suke rayuwa cikin gidan.......a cewarsu har yanzu ba'a halicci mijinta.....su a karan kansu sunsan babu wata halitta data dace da princess akhnan hammud..........kaima kuma tana neman dukkan wata hanya da zata sake tsere da kai.....hakan kuma nasan baya rasa nasaba da faduwarta daka zama sila" Omari yakai qarshe yana miqa masa wayarsa bayan ya bude wani abu yana miqa masa.
Taku biyu haisam yayi ya dawo baya,ya kalli wayar da lumsassun manyan idanunsa kafin ya miqa hannu ya karba yana dubawa. Har yanzu murmushi ne shimfide saman fuskar omari,ya dade yana neman wannan damar da zaiwa haisam magana........yanason yaga dambarwar ya zata kaya. Yana ganin yawan saqonni daga hippodrome suna neman cikakken bayanai a kansa,da kuma yawan adadin request da suke sake turawa na shirya sabon race da zai zama globally gaba daya.
Zayaso yaga yadda nasu prince din zai sake nunawa wannan qaramar gimbiyar TAZARA da bambamcin dake tsakanin MAZAN ETHIOPIA da matan AGADEZ. Yayi imanin cewa koda sau million nawa ne zata sake gwabza tsere da haisam,abune me wahalan gaske taci nasara a kansa. Baisan gaibu ba......amma ta bangaren sarrafa dawakai da raqumma baya tunanin har yau akwai mutumin da yakai haisam fasahar sarrafasu. Bai manta dalilin hanashi wasan tseren da akan shiryawa 'ya'yan sarakai da 'yan sarauta na cikin yankin jimma gaba daya ba....... Qwarewarsa da zarrarsa tafi ta kowa,shi kadai yake zuwa na daya a dukka shekara ko watannin da za'a shirya wasan,dole nanay ta sanya aka janyeshi daga komai gudan bakin al'umma.
Email din farko kawai ya karanta......tun sakannin da suka gilma tsakaninsa da ita a jiya yaji a jikinsa itace. Yana da wani kaifin basira da fikirar laqantar abu. Second biyar din kacal suka dawo masa da abinda ya faru a wandancan mintunan na satittikan baya. Wannan abun da yaji ya tsarga jikinsa ya gauraya da jininsa me kama da jan wutar lantarki still shi ya sake ji a dukka jijiyoyin jikinsa dake aika jini.
Idan ka dauke mahaifiyarsa nanay......rumaisa noory da Anani da suke shaqiqansa.......ba wata mace a kaf rayuwarsa da tafukan hannunsu suka taba gauraya da juna. Ita ta fara kafa wannan tarihin da hakan ya faru a tsakaninsu har sau biyu,wanda yakejin nauyin zunubin haka saman kowanne tafi na hannunsa har yanzu.
Sanda suke makaranta.......rayuwar makaranta rayuwa ce dake cakude da tarin nau'ikan mutane mabanbanta. Duk kuwa da cewa sunyi karatu ne cikin larabawa,sai suke ganin larabawan zamani,ba asalin balaraben mutum me tsananin kamun kai da sanin addini ba. Shagalallu da har shagalarsu takan basu mamaki.
Yana da wani irin haiba da daukan hankali,wanda sassanyan kyau da wasu kebantattun halitta da Allah ya bashi ya qara yawan adadin matan dake da muradi a kansa. Daure fuskarsa......janye jikinsa daga shiga dukkan wasu huldodi da mu'amaloli da suka shafi Mata a ciki basu sanya hakan matan sun janye jikinsu daga neman alaqa dashi ba......saima qara neman shiga da sukeyi. Kamun kannasa sai ya sake zame masa wani irin ado me fusgar hankuls,ba ga ashararan 'yammata ba,harda kamammu masu kunya da kintsi......a lokacin da gaba daya baisan wani abun burgewa tattare da d'iya mace ba,bai tantance wani abun jan hankali ba akan diya mace ballantana yaja hankalinsa.
Abu daya ya sani.....mace me suturce jikinta,mace me kunya yana ganin martabarta kima da mutuncinta fiye da me bayyana tsiraicinta. Karatu yayi masa wani irin mugun kamun da bayajin zai iya hada space dinsa dana tunanin wata diya mace......ya samu wani babban gurbi a rayuwarsa da baya tunanin akwai sauran gurbin wata mace. Duk da cewa yana cikin shekarun da jini ke harbawa a jikinsa da sauri,yake kuma aika saqo izuwa zuciya kwanya da ruhi.
Yana ganin yadda a hankali su mutallab wannan feeling din nason yin budurwa.......wannan feeling din na nemewa zuciya abokiyar hadi kuma abokiyar tarayya sannan abokiyar rayuwa ya fara tasiri a kansu. Ko kadan bai zargesu ba,don yasan sunkai wadannan shekarun,don shi bai tasirantu da wannan ba ba lallai ma kowa ya zama haka ba,bugu da qari dukkaninsu kamar guri daya aka musu tarbiyya. SARAUTA sunan da aka bawa 'yan team dinsu cikin makarantar kenan da harshen hausa. Kyau kwanya da gata dukkaninsu Allah ya musu baiwa,saidai wani yafi wani. Su biyu ne 'ya'yan da suka fita daga gidan sarauta cikin team din nasu,wannan ya sanya sukayi representing sunan team din,don shi da maleek din yanayin gadon sarauta da sukayi sai suka sake zama yanayinsu daban,ba kuma wai don sun qirqiri hakan bane a karan kansu....a'ah,wani yanayi ne dake bibiyar jini.
Dukka bayanan omari yake saurara sanda yake qoqarin maida email din kan nashi wayar,ya kuma saukeshi daga wayar omari din sannan ya miqa masa wayarsa,bai kuma tsaya qarasa jin qarshen labarin ba ya soma takawa yana fita a parlor din.
Wanka yakeso yayi da ruwa me zafi kafin ya kwanta,sannan kuma ya kira nanay da yakejin kewarta. Kewarta dukka da kewar gida yakeji,kaman yadda yasan zuwa yanzu qannensa dukkaninsu sunyi kewarsa,idan ma akwai wanda yakejin ko a jikinsa hussam ne,zaima ji dadi me matsa mishi ya kauce ya bashi guri,zaici karensa babu babbaka.
Sanda ruwan me dumi sosai ya soma ratsa gabbansa sai ya saki wata ajiyar zuciya yana nutsewa cikin bathtub din sosai. Haka kawai komai nata yake dawo masa,wanda duk yadda yakai ga ture tunanin sai daya mamaye ilahirin kwanyarsa.
Abinda ya faru akan kunnensa.......maganganun omari da bayanansa.....email din da aketa turawa da komai da komai,take yaji wani bacin rai yana sauka saman zuciyarsa a hankali.
Tana da izza tana kuma buqatarta.......tana son girmamawa daukaka da martabawa amma bata iya aiwatar da ita akan kowanne d'an adam. Ta iya duban idanun dukka wanda taso ta tozartashi da kalaman da dukka sukazo bakinta,batasan me ake nufi da MUTUNTAWA da KARRAMA DAN ADAM ba.......
Masanan ilimi sune halittar da tafi RAINAWA tafi TSANA mafiya kuma qasqanci a idanunta......while kuma sultane mahaifinta ya kasance mutum me karrama wannan nau'in mutanen da ita kuma suka kasance wulaqa tattu a idanunta......garin yaya RAYAYYE ya haifo MATACCE?. Daga ina ta samu dukkan wadannan baqaqen halayen da suke kishiyoyin juna da halayen mahaifinta?.......mahaifiya?. Ya tambayi kansa tunaninsa yana tsayawa cak!.
Qin aminta da hakan yaji zuciyarsa tayi,indai wannan mahaifiyar ce.......wannan dai mahaifiyar data yi aike cikin girmamawa da karramawa.......tayi aike cikin bashi dukkan cikakkiyar dama......cikin neman alfarma da qasqantar da kai daga dukkan girman da sarauta ya bata take neman ya zamewa yaranta malami.........indai itace zuciyarsa da ruhinsa basu gamsu ta dauki kowanne dabi'a nata ba!.
"Dole akwai daga inda damuwan yake!" Ya fadi a hankali yana bude idanunsa gami da motsa labbansa.
"Matan sultane nawa?" Tambayar data tsaye masa a ka kenan,yake jin ya kamata ya sani. Tasiri aikinsa yayi masa sosai cikin rayuwarsa da yakan saurin harbo wasu abubuwan a sanda yake ganin tafiyarsu ba daidai ba. Ya qarasa wankansa a nutse,ya kuma nade jikinsa da babban towel,ya nade sumarsa da wani,sai fuskarshi tayi kyau,kaman wanda yayi hakanne da manufar ado. Kusan komai ya sanya kyau yake masa,duk da shigarsa me sauqi ce amma kuma sutura ce da kowacce zaman kanta takeyi. Tsadarta kadai idan kaji xaka sake kallanta ka qara. Dukka jallabiyarsa daga asalin factory din da mafi yawa suke saqa jubah,cloak robe da jallabiyyar gidan sarautar saudiyya ne.
Wata mitsisiyar waya da duka duka batafi tafin hannun qaramin yaro ba ya jawo,ya danna wasu lambobi dake haddace a kansa ya soma kira.
Bugu uku aka dauka,muryar maher ta bayyana cikin girmamawa.
"Matan aure nawa ne cikin gidan sarautar agadez?".
"Biyu ne obbo" Ya amsa masa,saidai kafin ya qara cewa wani abu maher yace.
"Morsa safiyya.....da mammina zaituna......morsa itace ta saka oustaz Ousmane ya kawoka a madadinsa,mammina zaituna itace uwargidansa,kuma ita ke riqon shalelensa akhnan,wannan ya sanya matsayinta yake na daban cikin gidan".
"Is okay" Ya fadi yana katse maher,don ba wai dogon bayani yake buqata ba. Koda yana da buqatar yana ji zai bincika ne da kansa.........yana sake jin buqatar zama da wanzuwa cikin gidan tun daga sanda zuciyarsa ta ayyana masa wanda yayi yaren oromo yana da alaqa da cikin gidan.
Wayar ya janye gefe yana daukan hand drayer don tsane kansa da ita. Basai ya tsawaita tunaninsa ba.......zaiyi wahala daukan dabi'u da ra'ayiyyikanta ta samosu ne daga UWAR RIQONTA?.
"zai iya kasancewa" Ya bawa kanshi amsa yana qoqarin cillar da tunanin. Ya gaji da tuna komai da ya shafi gidan sarautar,yana buqatar tuntubar nasa ahalin,yana buqatar jin muryar nanay dinsa,wadda ita daya ke debe masa duk wani gajiya da xaiji daga can cikin kwanyarsa akan aikinsa.
โ
๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
PAGE 66
__________________________
Bononza bononza https://wa.link/l1gcz8
Assalamu alaikum yan uwa mata masu albarka
Zuzeam ventures zatayi promo karshen wannan watan har zuwa cikin watan nan me kamawa insha allah
-Da 6k kachal zaa baki kaza da ciccibi da gari da tsumi da gumba pills shaki matse masu kyau da ingancin dazai sakaki dawowa ki qara harma ki kawo wani,
-Da 11k zaa baki kaza full da ciccibi da gari da tsumi da gumba, da maganin sanyi wannan promo ne akan murnar cika shekara 10 cif da fara sanaa a online Dan haka duk wadda take bukatar shiga cikin wannan promo Dan samun wannan garabasa to tayi sauri kafin ta kare
Kuma ku sani tsakani da Allah zaayi wannan promo komi me inganci ne
Kyau sosai zaa baku tsakani da Allah Idan kinada 4k ma zaa baki ciccibi kawai sai gari da tsumi masu kyau da ingancin suma,
Dan haka duk wadda take da bukata kofa a bude take
Idan kinada Yan uwa da abokan arziki zaki iya tallata masu idan kin kawo mutun goma suka shiga na 10k kinada package din 5k
Idan kin kawo mutun goma suka
Karku manta promo kwana 3 ne an kare insha Allah
__________________________
Kadan kadan murmushi ke fita saman fuskarta ba tare da tasan hakan tana kasancewa ba. Cikin sukuni da saituwar al'murabta take jin kanta,tana hango wasu kwanaki kadan masu zuwa yadda komai zai zo mata da irin tsari da burin da take muradi. Ta sani ta jima tana shan wahala ta zuciya da gangar jiki,tana jin wannan kadai ya isa ubangiji yayi mata alfarmar bude mata kowacce qofa don isa ga sauran muradanta na duniya da suka rage mata.
A nutse motar dake lullube da baqaqen glass tinted ta sauka daga hannunta,ta kuma fara kutsawa cikin wani qaramar gona da yafi girman lambu ba tare da damuwa da adadin shukokin da take takewa ba,don dama bawai anyi shukokin bane don su amfani kansu kosu amfani wasu ba,ba kuma an dasa su sun kuma girma bane don suci gaba da rayuwa irin rayuwar da kowacce shuka keyi don isa ga wani mataki ko kuma muradi.
Tafiyar mintuna goma kacal motar ta fita daga cikin shukokin,wani dan madadaicin fili ya bayyana a gabanta,wanda wani plate house ne daga tsakiyar filin,qawatacce da wata irin qofa me kyan gaske.
Matuqin baiyi koda horna ba gate din ya bude qaramar farfajiyar gidan ta bayyana,motar kuma ta kutsa kai zuwa cikin gidan,ta tsaya daga tsakiya,sannan mutum daya cikin mutane ukun dake tsaye a gurin suka qaraso da sassarfa da kuma tsananin girmamawa suka bude hannun da mammina ke zaune.
A qasaice ta sauko,wanda kafin qafafunta su qarasa direwa a qasa ta saki tamabayar.
"Ina tamim yake?".
"Bai qaraso ba" Suka amsa mata cikin matsanancin girmamawa suna sauke kawunansu a qasa.
"Muje na ganshi" Ta basu umarni na kai tsaye,wanda tana sauke maganar sukayi gaba da hanzari suna mata jagora.
Qawataccen parlor ne da aka zuba wadansu irin kayan alatu da sam bana qasar bane ba,wasu irin kayan alatu masu daukan hankali da nuna asalin tsadarsu da nauyin kudin da aka kashe domin siyansu.
Gaba daya daga cikinsu yayi zuwa daya daga cikin rufaffun qofofun da suke kulle,mammmina ta bishi a baya,har zuwa sanda ya murda dakin ya tura ya budewa mammina yana tsayawa daga gefe alamun bata daman shiga.
"Bacci yakeyi?" Ta jefa tambaya ga mutumin da yake tsaye din kansa a qasa. Tambayar tata da alama baiso ta fada a kansa ba,ko kuma baiso ta ruskeshi ba,don hannunsa ya aza saman kansa yana shafawa a nutse.
"A'ah......yadan sha......"
"Sake bashi kukayi?!" Ta furta a tsawace cikin wata irin fusatacciyar murya data haifar da shuru cikin falon. Ba wanda ya iya motsawa ko ya amsa a cikin su,sai sadda kawunansu da sukayi a qasa.
"Sau nawa zan gaya muku?.......sau nawa zan maimaita muku?" Ta sake musu tambayar da duk cikinsu ba wanda keda amsarta. Itama ta fahimci babu me iya bata amsa,don haka ta taka da hanzari tana cusa kai cikin dakin.
Yalwataccen daki ne da aka zuba masa set ma kayan gado masu tsananin tsada da daukan hankali,gami da dauke hankalinka daga ainihin duniyar da kake zuwa wani ni'imtaccen guri na daban.
Daga can saman yalwataccen gadon da aka qawatashi da wani tsadajjen bedsheets da comforter gami da pillows da aqalla sun kusa shida. Mutum ne kwance,wata irin birkitacciya kuma hargitstsiyar kwanciya da kana mata duba daya zakasan ba cikin nutsuwa akayita ba. Domin komai na gadon a yamutse yake,kaman yadda qafafunsa suke zube a qasa wadanda ke sanye da snickers din da ko samun daman ciresu ba'ayi ba.
Idanu ta zuba masa ranta tana jin yana wani irin baci. A duniya idan akwai wani abu qwaya daya daya kasance rashin sa'arta na duniya zata iya cewa almaz ne......yana daya daga cikin miyagun qaddarorinta.......yana daya daga cikin qaddarorin data gaza sarrafasu har sai da sukaso yin wasan kura da rayuwarta.
"Tasheshi"