Showing 27001 words to 30000 words out of 144990 words
a lokacin da ya ga dama ya kuma kar
ɓ
e ta a lokacin da yake so don wanke zunubanmu, saboda hak
a ba kaifinka bane, ba laifin kowa bane, don kowan bai wuce ya wayi gari shima an karbi tasa ta wata sigar ba.
Insha Allah abinda ya same ka kaffara ne ga wasu abubuwan da ba lallai ka san dasu ba ma. Don haka daga kai har mu ba abinda zamu yi da ya wuce a
ddu'a kamar yadda kowa da ya taru anan yayi tayi maka..."
Tayi shiru tana kallonsa kafin ta karasa a hankali.
"... abinda kake bukata kenan."
Taji hannayensa sun sake rike ta sosai kafin ya karadso da fuskarsa a hankali ya dora goshinsa akan nata.
"Ban san
me zan ce miki ba Amina, duk abinda kike yi, duk kike fada yana wuce dukkan tunanina, bana jin a duniyar na bayan Mami akwai wanda yake fahimtata yanzu sama dake."
Ambatar sunan Hajiya Kilishi da yayi yasa numfashinta yin rawa kafin ta rufe idanunta a ha
nkali, tana jin nasa numfashin shima na sauka akan fatarta, sai kawai ta tatraro dukkan dauriyarta tace.
"Nima bana son kowa yafi ni fahimtarka, nafi son na zama mutum ta farko da zaka nema a kowanne lokaci walau na
ɓ
acin rai ko farin ciki."
Bata sani ba k
o kallonta yake yi amma taji sanda ya kara rike ta a jikinsa yana gaya mata dukkan wasu kalaman godiya, sai kawai ta ture dukkan wani tunanin a cikin kanta a lokacin ta mika hannunta daga saman kirjinsa zuwa bayan wuyansa, ta rike shi kwatankwacin yadda sh
ima ya rike ta. Wani abu da ya bashi mamaki don taji sanda ya dantsaya a cikin hannayen nata kafin ya kira wannan sunan nata a hankali.
"Doll..."
Kafin tama yi tunanin amsawar yace.
"Wannan ma yana daya daga cikin amsata na ranar?"
Ya rufe bakinsa daidai s
anda ta daga kanta alamun amsa, taji yayi wani murmushin mai sauti sannan ya matsar da fuskar sa kadan daidai saitin kunnenta ya rada abinda a lokaci guda ya sata dunƙule yatsun kafarta akan tiles din dakin.
"I want to kiss you again dan Allah..."
Ya fa
ɗ
i
hakan sannan ya janye fuskarta daga tata, yayi baya sosai yana kallonta. Amina taji lebbenta ya shiga rawa tare da hannayenta sai kawai ta ƙara tsawon kafarta a lokaci guda, ta kai fuskarta daidai gefen tasa kuma ba tare da jiran komai ba tayi pecking gefe
n kumatunsa.
Ta sake jin sautin murmushinsa kafin ya kara sunkuyowa cikin fuskar tata ya kwaikwayi sak abinda tayi yayin da take jin murmushinsa akan fatarta, kuma sai da ya matso dab da bakinta sannan ya tsaya, wani abu da yasa a lokaci guda ta bu
ɗ
e idanu
nta tana kallonsa.
"I want to ask you something? (So nake in tambaye ki wani abu.)
Kafin ta amsa yace.
"Naga kin fara kwarewa a wannan karatun, shekarar ki nawa? 'Cox I don't want us to stop, bana so mu tsaya kuma bana so a kama ni da laifin child abuse."
Amina bata san lokacin da bakinta ya subuce da wata irin dariya ba, ta rufe idanunta gaba
ɗ
aya sautin dariyar na fitowa tare da tsananin kunyar da maganganun dake lullu
ɓ
e ta.
****
_
Wani abu yana shirin konewa anan.
😅🥰🤩
_
_Ina kuke tunanin Hajiya Kilishi ta
tafi ne?_
_Me suka shirya ita da Awwalu?_
_Ruƙayya da mahaifiyarta sun samu nasara, Hamida ta koma wajensu, kun tuna mataki na biyu a tsarinsu?_
_Yaya kuka ga kokarin Amina na farko wajen hada kan gidan Alhaji Muhammad Mansour Bakori?_
Sai naji dukkan sha
rhinku..
🥰😍🙏
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
°°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'E
E*
*PAID BOOK*
*05*
~~~~~~~
_If it's not you, it's not anyone._ _- Unknown_
***
*Abuja.*
*No. 1146 C west, Maitama.*
*Ƙarfe tara da rabi na safe.*
A cikin harabar gidan, daga can gefe inda akayi shuke-shuken wasu bishiyu dama fulawowyi, Jawad ya shafo kan
hancinsa da daya hannunsa wanda baya rike da wayar da yake yi kafin yace.
"Na gaya maka naga motar, daga can gefen inda muke ta tsaya kuma ni naga mace da namiji a ciki, fuskokinsu ne kawai ba zan iya tantance maka ba."
"Babu ji, wannan mai sauki ne in dai
har ka tabbatar number motar da ka fa
ɗ
a daidai ne. Zanyi kokarin nemo bayani akan plate din sai muyi tracing , tunda na san dake zuwan nasu yana da alaka da dalilin rashin zuwan Ma'aruf wajen."
Jawad ya gya
ɗ
a kansa a hankali yana cije lebbensa.
A jiya bay
an sun shiga Kano, tsarinsu ya tafi daidai, sun yi komai kamar yadda Haro ya tsara kuma ma sun isa wajen da suke saka ran ganin Ma'aruf inda zai hadu da wadannan mutanen, sai dai sunyi tsawon jiran da har mutanen suka zo babu Ma'aruf din babu alamarsa, k
uma suna wajen har lokacin da motar mutanen ta juya suka bar wajen.
Kuma sai a yanzu Jawad ya tuna da motar da suka wuce akan titin kafin su sami wajen tsayawa, don haka ya kira Haron a waya yanzu yake gaya masa, don a jiyan bai ko bari ya kwana a Kano ba
yayi
booking jirgin dare ya dawo gida,yana da abubuwa da yawan da ba zai iya wasa da lokaci wajen ku
ɓ
ucewaru ba.
"Kar ka damu J, ai ba ƙasar ya bari ba, muna da lokaci muna dashi mara adadi, wannan opportunity din ma don naga yayi kusa ne nace muyi amfani
dashi kawai, amma yanzu damar ta fara Jawad kai ma ka sani."
Ya gyada kansa.
"Na sani, na san akwai lokaci Sadiq, fata kawai nake ne kar Rukayya ta shammace mu."
Haro yaja tsaki a cikin wayar.
"Haba Jawad, a cikin kwakwalwar wannan dakikiyar yarinyar har a
kwai abinda zata yi ne da zai fi namu? Kawai ka cigaba da harkokin ka, ba za'ayi dedewar da kake tunani ba insha Allahu, su kuma Wa
ɗ
annan mutanen zan saka a nemo mana su insha Allah."
Da haka suka gama wayar, Jawad ya kalli mintunan da duka gama fitowa a
jikin screen din kafin ya kashe ta ya zura a aljihu, yayi abu guda biyu da ya
ɗ
anawa tarko a safiyar yau bayan dawowarsa, saura na ukun wanda har cikin zuciyarsa yake jin tasirin faruwarsa, game da yarinyar nan, ƴar aikin nan.
Jiya bayan ya fito ya gan ta
a wajen nan kuma ya tabbatar da cewar taji dukkan maganganunsa da Haro, baiyi mata magana ba, bai ce komai ba, don ko Haron baya son ya san hakan, abinda zuciyarsa ta gaya masa shine dole ya san yadda zai yi ya rufe bakinta kawai don baya hango yadda alaka
rsa da mahaifiyarsa zata kasance idan har koda wasa ne ta fadi hakan a gabanta.
Ya zura wayar a aljihu, sannan kai tsaye ya fito daga wajen ya nufi hanyar da zata zagaya dashi baya zuwa
ɓ
angaren masu aikin gidan, bangaren dashi kansa gida ne guda mai ƙatuw
ar haraba da kuma shuke-shuke, ba zai iya tuna rana ta karshe da ya taka kafarsa zuwa wajen ba, kawai dai ya san kafin su kai ga tarewa a gidan da suka zo gaba
ɗ
aya tare da mahaifinsu da kuma sauran ƴanuwansa maza, sun zagaya koina har nan kuwa.
"Good morni
ng sir... Good morning."
Wasu ƴan aikin guda biyu dake shanya tarin kayan wankin yara suka tsugunna suna gaishe shi, ya gya
ɗ
a kansa alamun amsawa sannan ya tsaya yana kallonsu, ya rasa ma me zai ce musu saboda ko sunan yarinyar bai sani ba, ya san dai ya t
aba ji Mamah ta ta
ɓ
a kiranta a gabansa, watakila fiye da sau
ɗ
aya ma amma baya jin zai iya tunawa.
"You want something sir?" ( Kana bukatar wani abu ne yallabai?)
Daya daga cikin ma'aikatan ta fa
ɗ
a, sai dai kafin ya bu
ɗ
e bakinsa yayi magana idonsa ya hango
masa ita, ta karyo kwana ta shigo wajen, hannunta dauke da wani katon farin nokiti da ta ciko kayan miya a ciki, ko daga nesa ya san bokitin yayi mata nauyi daga yadda yake kokarin rinjayarta ta gefe guda.
Sai kawai ya juya ya nufi wajenta, kuma har ya ta
ho bata lura dashi ba sai da ya iso daidai gabanta tukunna, da farko idanunta basu shaida shi sosai ba, watakila ko bata taba zaton ganinsa a lokacin kuma a wajen bane, amma a lokaci guda sai idanun nata suka haska da tsananin mamaki da kuma fargaba.
Yana
ganin yadda ta saki bokitin da sauri zuwa kasa kafin itama ta bishi kasan ta durkushe kan gwiwoyinta sannan tace.
"Ina kwana... Barka da safiya."
Duka kalar gaisuwar guda biyu shi ka
ɗ
ai, kuma har ya bu
ɗ
e baki zaiyi magana sai idonsa ya kai kan wasu mata da
ga ginin dake gabansu sun leƙo ta window suna hangensu, wani tunani ya gifta a cikin ransa don haka sai kawai ya maida kalaman da yayi niyyar fa
ɗ
a yace.
"Me kuka dafa a bangren Mamah?"
Tambayar ta shiga kan Zainb da tsananin mamakin da ya fi na farko, don
ta tabbata ba abinda ya kawo shi kenan ba, ya za'ayi ya bato bangaren ya taho tun daga can har zuwa nan don ya tambayeta kawai abinda aka dafa? Mutumin da idan hr ba fita zai yi ba kowa ya haddace cewar baya tashi sai rana ta miƙa, amma ƙarfe nawa yanzu? T
ara da mintuna...
Ta yaya ne ma yake mata magana muryarsa a ƙasa, ta zata ai idan har ba tare da mahaifiyatsa yake ba baya iya magana babu hantara. Sai tayi saurin hadiye abu a bakinta sannan tace.
"Ba'a gama abincin duka ba, an dai yi wasu."
Ya gyada kans
a.
"Ki debo wanda aka gama ki kawo min."
Da haka bai kara cewa komai ba yayi gaba. Zainab tabi bayansa da kallo gabanta na faduwa kafin ta mike a hankali.
Kuma minti goma bayan hakan, ta kwankwasa kofar
ɗ
akin nasa
ɗ
auke da farantin kayan abincin, kallon d
a sauran manyan ƴan aikin gidan suka dinga binta dashi bayan ta gaya musu inda zata kai abincin.
"Shigo."
Muryarsa ta fada daga ciki, kuma karo na farko ta murda hannun kofar ta shiga, dakin kamar yadda ta zata ne, ƙato mai cike da hadaddun kayan kamar na
sauran ƴanuwansa mata, sai dai har gwara nasu ma yafi kyale-kyale akan wannan da komai tsilla-tsilla ne. Yana zaune daga gaban gadon dakin a tsakiya, ya dora hannayensa kowanne akan cinyoyinsa yana kallonta, kuma da yatsu biyu kawai yayi mata alamar cewar
ta karaso.
Ta taho
ɗ
in, amma muryarsa ta tsaida ta.
"Koma ki rufe kofar."
Gabanta ya sake faduwa, amma babu yadda ta yi ta koma
ɗ
in ta rufe ta a hankali sannan ta sake juyowa, tana ta tahowa bai ce ta tsaya ba, kallonta yake yi ta sani amma ita idanunta na
kan farantin.
Sai da ta karaso nesa dashi kadan sannan ta tsugunna ta ajiye farantin a saitin gabansa, kuma kafin ta mike kamar yadda daga shi har ita suka san shine abu na gaba ya sake magana.
"Zauna."
Ta hadiye wani kullutun abu a makogwaronta sannan ta
gyara tsugunnon nata a hankali alamun ta zauna
ɗ
in, tambayarsa ta gaba ta kada ƴaƴan hanjinta a lokaci guda.
"Daga ina kike?"
Sai ta dago ta kalle shi.
"Nace daga ina aka kawo ki?"
Ya sake maimaitawa, ya sake maimaitawa yana fadada tambayar da ta riga ta
fahimta din kuma ta san ina take dosa.
"Sunan garinmu Yakura, a kusa da Kaduna yake." Muryarta tana rawa.
Ya gyada kansa.
"Waye ya kawo ki nan?"
"Abokin babana ne."
"Ina baban naki?"
A hankali tace.
"Ya rasu."
"Ina babarki?"
Sai da ya lura ta hadiye wani a
bu sannan tace.
"Tana nan, matarsa ce ita yanzu."
Kalaman suka daki kirjinsa da wani abu da bai san meye ba, amma dai ya san nazarinta yake yi, nazarin shekarunta da ya kasa ƙiyasinsu.
"Ita me yasa bata hana shi kawo ki ba?"
Sai ta sake dagowa ta kalle shi
, idanunta na nuna wani abu da ya kasa tantancewa, idan ma tunani take cewa muryarsa ta fito da damuwa ne, zai goge mata hakan yanzun nan.
"Bashi da kirki, Naani baza ta iya hana shi ba."
Kalmar Naanin da ta fada ya fahimce itace mahaifiyarta don haka kai
tsaye ya sake tambaya
"Yaya sunanki?"
Wannan karon da mamakin da yafi nasa ta kalle shi, bai san sunanta ba? Bai san sunanta ba yake tambayar labarinta?
"Sunana Zainab."
Sai ya sake gya
ɗ
a kansa yana kallonta.
"Zainab, I know you heard us...."
Maganar tasa
ta katse tuna cewar a banza zai yi bayanin ko ta cigaba.
"Na san kin ji mu ranar nan, kinji duk abinda muka fada ni da wanda yazo...."
Ta riga ta sani dama, tasan zancen da zai yi mata kenan, ta san ta shiga uku, ta san karshen rayuwarta a gidan nan tazo t
un daga wannan lokacin, Allah ya sani tana jin da
ɗ
in zaman gidan nan fiye da sauran gidaje biyu da tayi aiki dasu a baya saboda yadda mahaifiyarsa ke kyautata mata, amma tun daga ranar da ta ci karo dashi har ta zuba masa miya a kaya, tun daga ranar hannay
enta suka fara lissafin kwanakin barinta gidan, sai gashi ta samu talalar wasu watannin kafin shekanjiya ta tabbatar mata cewar wa'adin kwanakin nata yazo karshe.
Don haka taji yadda iska ta wuce cikin busashshen makogwaronta kafin ta tattaro dukkan karfin
ta ta daga kanta sau daya.
Jawad ya gya
ɗ
a nasa kansa shima.
"Good. Shi yasa na kira ki nan."
Ya fadi hakan sannan ya gyara zamansa.
"Ba zaki so in zama abokin babanki na biyu ba Zainab balle kuma har in fi shi, don ina rabbatar miki zan iya kuntata rayuwar
ki fiye da yadda bakya tunani idan har kika zabi yin wasa dani.
Abinda kika ji sirrina ne, kuma duk da babu yardata ya iso gare ki, na baki amanarsa a yanzu, kuma in so ki barshi a cikin ranki, ki barshi kamar yadda yake a tsakanin mu yanzu, idan har shiga
kunne na biyu musamman kunnen mahaifiyata Zainab..."
Yayi shiru yana cije lebbensa kafin ya fadi abinda yasa ta zare idanunta a lokaci guda ta dago tana kallonsa, hannayenta dama ilahirin jikinta gaba
ɗ
aya suka shiga kakkarwa yayin da idanunta ke haskawa d
a tsoron da bsta lissafa dashi ba a duk wani lissafinta na ukubar rayuwar da take tunanin fuskanta!
****
*Kano.*
*No. 58 Mafara Street, NNDC Shara
ɗ
a Quaters.*
*Ƙarfe Goma na safe.*
A cikin dakin, cikin uwar dakin Hajiya Kilishi ta dubi kawarta Hajiya Sal
amatu wadda isowarta kenan a wannan safiyar bayan fitar Mama Rabi wadda ta shirya musu abun motsa baki fal a wani katon faranti.
"Kinyi min nisa da yawa Salamatu, china tayi min nisa tunda ni ba harkar social media din nan nake yi ba. Na kulla abubuwan da
yawa wanda babu tayawarki a ciki balle har mu kai wa tufkar ƙarshe mai daukar ido."
Hajiya Salamatun ta cire dankwalinta ta ajiye shi a gefe, mikakken gashin kanta da yasha gyara ya shiga nuna maikonsa cikin hasken dakin kafin tace.
"Ni iyaka ta dake ai sh
awara Kilishi, wasu ma ba
ɗ
auka kike ba idan na fada, to don me zaki yi kewata? Yanzu kawai ki gaya min me ya faru? Me ya faru daga inda na barki."
Hajiya Kilishi ta juya idanunta tana murmushi sannan ta kalli aminyar tata dake zaune daga bakin gadon dakin
tace.
"Abubuwa da yawa Salamatu, don haka mu kyale ƙananan ma a gefe, mu fuskanci manyan.
Na riga na gama da yarinyar nan, ta san komai kuma ta yarda da komai..."
"Haka cikin sauki?"
Salamatun ta kasa daure namakin da yasa ta katse ta wajen tambaya.
Sai
kawai ta
ɗ
auki kofi guda akan farantin, ta tsiyaya lemo a ciki ta mikowa Hajiya Salamatu kafin ta bata amsa.
"Ba cikin sauki bane, nayi abinda ba zata iya bijire min bane kamar yadda ta fada da bankinta. Kin sani Salamatu, kin san yadda bana wasa da dukkan
abinda nasa a gaba, kuma kin san yadda nake bawa abinda nake so muhimmanci."
Hajiya Salamatu ta kur
ɓ
i lemon sannan tace.
"Na sani Kilishi, ba sai kinyi wannan bayanin ba, na yarda kin samu yarinyar bayan ita kuma sai me?"
Tayi wani sassanyan murmushi tana
kallonta.
"Sai burin da na
ɗ
anawa tarko, burin cike kan wadannan kudaden."
"An samu?"
Ta tambaya bayan ta ajiye kofin lemon.
"Kwarai, an samu Salamatu, wani ciniki suka yi na makudan kudaden da har suka fi gejin da nake nema ma."
"Kince min ya gano waccan
hanyar taku ta hacking account din kamfanin da akayi aka tura musu da alert din bogi. To wannan karon me kika yi?"
Kai tsaye Kilishin tace.
"Kwantar dashi nayi kamar yadda na saba kuma zaki yi mamaki ta hanyar yarinyar nan hakan ta faru."
Wannan karon da
mamaki Hajiya Salamatun ta kalle ta kafin ta kyalkyale da dariya.
"Irinki basu da yawa a kowanne ƙarni Kilishi, shi yasa nake gayawa duk mai takura min akan rayuwa cewa ya kyale ni kawai, da nayi niyya zan rayu a duniyar nan kamar a aljanna ne saboda ke."
(Waiyazubillah.)
Kilishi ta gyada kanta tana daukan cake guda a cikin farantin fake gabansu.
"Ni kaina na sani Salamatu ina da laushi fiye da dukkan tunanin mai zato, laushin da zan iya ru
ɗ
ar ko waye a duniyar nan ya dulmiya zuwa cikin tarko na da bashi d
a ƙarshe. Shi yasa tun farko