Showing 15001 words to 18000 words out of 144990 words
cikin mutanen na tambayar su waye a wajensa.
"Mami ta tafi tun dazu."
Amsar da ta fito daga bakin wani, itace a amsar da tun a wannan lokacin ta bawa Hajiya Maimuna wani tabbaci na cewar shikenan tayi biyu babu.... babu Jamal
ɗ
in kuma babu Ma'aruf din!
Don bata jin bayan addu'a tana da wani sauran fata a duniyar nan na dawowar Ma'aruf wajenta.
***
*Present Day.*
Tun da Munaya ta shigo tace da Hajiya Maimuna wai Ma'aruf ne ke zaune a falo yana jiranta hannayenta ke rawa wajen shiryawa, karfe goma sha
ɗ
aya
na safiya a lokacin sai kallon agogo take tana karawa.
A tarin shekarun da lissafinta ba zai iya ta tancewa ba, ta manta yaushe rabon da ta sanya idanunta a cikin na Ma'aruf din a wannan lokacin, iyakarta dashi bayan tsawon wasu kwanaki ne da zai shigo
ya gaishe ta kawai, zuciyarta ta da
ɗ
e da haƙura dashi game da wasu abubuwa da ta san cewar hakan ne ya kamata, ta dade da
ɗ
aga kasan ruhinta ta binne dukkan wasu al'amuransa, shi yasa har a yanzu dukkan maganganun ƴanuwanta game da hakan basa damunta sosai
.
Sai dai duk da dauriyarta, ta sani cewa bata isa ta canja cewar ita uwa ce ba, bata isa ta daure wannan kewar da zuciyarta ke ciki shekara da shekaru game dashi ba. Basu saba ba,
ɗ
awainiyarsa ka
ɗ
an ta sani, abinda take gayawa kanta kenan a kullum wajen t
ausar kanta, amma ta sani cewar babu wani abu a duniyar nan da zai yi daidai da dawainiyar rainon cikinsa da kuma haihuwar sa da tayi, shi yasa har abada a duniya uwa
ɗ
aya ce, kuma babu girman wani abu da ya isa ya canja matsayinta.
A zaune a falon kuwa ta
same shi baysn ta fito, hannunsa rike da wani dan karamin kwano mai kyau, yayin da idonsa ke manne da Tvn dake nuna tashar CNN.
Ya juyo ya kalle ta daidai lokacin da ta karaso hannunta yana danna buttun
ɗ
in tsayawa jikin keken tayar.
"Barka da safiya."
Mu
ryarsa ta gaishe ta ba tare da wata inkiya ba kamar yadda yake yi kullum, kuma a wannan lokacin dai taji hakan bai dame ta ba kamar yadda take ji a baya, ganinsa kadai a wannan lokacin ma ya isa ya mamaye dukkan tarin abubuwan da take lissafawa a kansa.
"B
arkanmu dai, kun tashi lafiya?"
Ta amsa farin cikin dake zuciyarta na nunawa akan fuskarta.
"Lafiya kalau, ya ƙarfin jiki?"
"Alhamdulilhi mun gode Allah."
Har yanzu idanunsa na ƙasa bai dago ya kalle ta ba, kuma tayi zaton iya abinda zaice kenan kamar yadd
a suka saba a kodayaushe, amma sai kawai taga ya dago ya kalle ta sannan yace.
"Kwanaki Baffa yace mun Abdurrahim ya kusa dawowa ko?"
Ba shiri ta daga kanta da murmushi.
"Eh, nan da sati biyu insha Allah."
"Ashe har ya tsayar da rana, the last time da muka
yi magana yace mun bai saka rana ba tukunna."
Mamaki ya shiga cinye ta a yadda take zaune, amma sai ta daure tace
"Yanzu ya kammala komai ai, don ma baya son taro ne amma ni da nayi niyyar wasu suje masa convocation din."
Sai ya gyada kansa.
"Haka yace mu
n nima, har Ishaq ma ya tambaye shi amma sai yace masa wai ba wani abu za'ayi ba."
Ta sake yin murmushi.
"Rigimarsa tafi shi ai, nace masa ko kewar mu baya yi."
Shima murmushin yayi ba tare da ya sake magana ba, yana tausayin kannin nasa ya sani, duk sanda
suke magana ta hanyar text idan ya tuna cewar ba zai taba iya kiransa ba yana jin wani iri a ransa. Wani iri kamar yadda yake ji a yanzu da yake zaune gaban mahaifiyar tasa yana hira da ita, hirar da ba zai iya tara shekarun da aka rufa kafin ta iya tuna
lokaci na karshe da suka zauna irin haka ba.
Kai tsaye yaji wani
ɓ
angare na zuciyarsa ya shiga godewa Amina da tayi sanadin zuwan nasa, don yadda ta kalli idanunsa ta roƙe shi da Allah ya san ba zai taba iya kin ce mata A'a ba.
Kuma a wannan lokacin ba k
allon Hajiya Maimunan yake yi ba amma sai jikinsa ya bashi cewa robar dake hannunsa take kallo, kuma yaji shigowar sako a cikin wayar dake aljihunsa, ya san Faruq ne, shi yake jiransa don haduwarsu da Yakubu (mutumin da zasu tura nemo musu Mr. Okafor.)
Don
haka sai yayi saurin tasowa ya miko mata robar dake hannun nasa.
"Wai zogale ne na bayan gidan ta tsinko ta dafa shine tace in kawo miki Munaya tace mata kina so."
Yadda shiru ke ratsawa waje a lokaci guda ya kashe ƙarar komai haka Hajiya Maimuna taji a c
ikin kanta lokacin da ta karbi robar, kalaman suka shiga cikin kanta amma suka tsaya cak! Ta riga ta fahimci wa yaje nufi da itan ba sai ya fassara ba, amma hakan wani abu ne da bata taba tunanin faruwarsa a cikin lissafinta ba.
Ta kalli robar ta sake kall
onta, ba wani abu ne mai yawa ba, amma wannan lokacin tana jin kamar nauyin zogalen nan daje ciki yafi girman dukkan wata kadara da take shi, kwalla ta cika ramin idanunta a lokaci guda, don haka bata
ɗ
ago ba sai kawai ta daga kanta a hankali.
"Nagode sosa
i, Allah ya saka da alkhairi Ma'aruf, Allah ya ƙara ha
ɗ
a kanku, Allah ya baku zaman lafiya, ya kade dukkan sharrin da zai shiga tsakaninku, Allah ya baku zuri'a dayyiba."
Mami tasha yi masa addu'a, kala-kala ma, har da wadanda idan ta fada zai kara kallont
asau biyu kafin ya amsa, amma Allah ya sani ya dade baiji addu'ar da ta shiga har cikin zuciyarsa ta tabo wani abu da bai san da zamansa ba irin wannan. Kalaman Mami daban ne da irin wadannan, yawanci addu'arta tana tsayawa akansa ne kadai babu wani a gefe
da ya shafe shi, don haka tmya sani tun bayan lokacin daurin aure sa da Baffa da kuma Baba Usman suka yi musu makamanciyar wannan addu'ar, zai lissafa wannan a karo na biyu da yaji irin wannan addu'ar daga bakin wani.
Makogwaronsa ya bushe a lokaci guda
, amma yayi kokarin hadiyr wani abu a hankali kafin ya amsa sannan ya tsugunnna yana yi mata sallama, bai kara iya kallonta ba itama kuma baya jin ta sake kallon nasa, don wataƙila suna raba abu iri
ɗ
aya ne a zuciyarsu daga shi har itan.
Kuma karo na farko
a wannan ranar bayan ya shiga wajen Hajiya Kilishi yaji haka kurum baya son dadewa don ransa bai gana daidaita ba har a lokacin, yaji hirar da take yi masa ba fahimta yake yi sosai ba, don haka yayi mata sallama ya fito, sai dai kafin ya bar cikin dakinsa
i da yayi mata wata tambaya dake yawo a cikin kansa tun bayan lokacin sa Amina ta bashi robar zogalen nan.
"Mami kina son zogale kuwa?"
Ta kalle shi kamar tana son gano wani abun kafin tayi murmushi tace.
"Haba ka manta ne Mai gaskiya, amma bana son zogale
tun asali."
Sai ya gya
ɗ
a kansa kawai sannan ya ƙara yi mata sallama.
_"Dan Allah zaka miƙawa Hajiya wannan? Zogale ne na bayan gidan nan tsinko na dafa, Munaya tace min Hajiya tana so, amma Mami ita bai dame ta ba."_
Haka ta gaya masa lokacin da ta tsaya
a gabansa rike da robar tana ta juya ta a hannunta. Wani abu ne ya faru smdashi bai gama gabe masa ba har yanzu, ya san dai kawai ba laifi suka yiwa Mamin ba amma kuma duk da haka yana jin wani iri.
Ya zaro wayarsa ya duba bayan ya shiga mota, sakon da ya
shigo dazu ba daga Faruk bane, daga mutane kamfanin RTL ne da suka yi dasu akan cewar gobe zasu je shi da wasu daga cikin board trustees
ɗ
insu su karbo kudin da suka siya dilolin kaya a hannunsu, haka kurum wanna karon ya yanke shawar cewa baza su karbi k
udi ta account ba gwara su karbi cash kawai, tunda an cuce su wancan karon kuma har yanzu basu gama da gano matsalar ba.
Sakon yana bayani ne kan wajen da zasu hadun da kuma lokaci da sauran abubuwa, ya kashe wayar ya tada motar daidai lokacin da kiran Far
uk ke shigowa, ya san ya riga shi isa wajen kenan kuma yanzu zai dame shi, don haka ya danna motar ya nufi hanyar titi daidai lokacin da idonsa ya kai kan robar zobo mai sanyin da Amina ta ajiye masa daga kasan dashboard din motar wajen da akayi musamman d
on ajiye roba dama.
Babu shiri wani murmushi ya subuce a bakinsa, yana da plan dama tarin tsaruka na ydda zai saita rayuwarsa tare da yarinyar nan, don tabbas ya gama yarda cewa ita din alkhairi ce a rayuwarsa, kuma mafi dadin abin shine ya same ta ne a lo
kacin da ba nema yake ba.
Wani abu da alokacin bai sani ba shine kwance a cikin zobon nan, sinadirin kwayoyin maganin Hajiya Kilishi ne ke yawo tun daga sama har kasa.
****
*Abuja.*
*No. 1146 C west, Maitama.*
A cikin ƙaton falon, baka jin komai sai ƙarar
A.cn dake hurawa ta kowanne bangare na falon, akwai manya-manyan royal chairs set uku da aka rarraba falon zuwa waje uku dasu. Jawad yana zaune daga kujerun gefe masu kalar ruwan madara, gajeran wando ne a jikinsa kuma wata t-shirt kalar ruwan kasa, a gab
ansa wani tebur ne da aka cima da kayan abincin safiya, hannunsa na rike da kofin mug yana ku
ɓ
ar shayin ciki yayin da mahaifiyarsa dake gefe Hajiya Mardiyya ke kallonsa tana sake maimaita maganganun da ba jinsu yake yi ba.
"Yanzu Babana ko don wadannan m
akiran matan mahaifin naka ba zaka saurare ni ko sau daya a rayuwarka ba? Kana ganin irin banbancin da ake nuna mana a gidan nan, kuma da nayi magana sai kace dani ba zaka yi ba babu kyau, bayan shi kansa mahaifin naku ai ya san abinda su Suraj din ke yi,
kawai bai damu bane kuma yana sane yake barinsu. Kowa na diban kason sa amma kai so kake mu mu tashi a tutar babu? Ba don ma Perm Sec. ya shiga zancen mahaifin naku ba kai ka sani da yanzu bama kan wannan kujerar.
Wallahi idan na shiga lissafo maka kadaror
in da matan nan suka tara yanzu zaka rike baki Jawad, amma ni gida uku fa kawai nake dashi har yanzu, ba don nayi fafutuka ta ma ba da bana jin ina da ko daya ai, kai kuwa banda motarka bana jin ka tara wani abu, karfi da yaji ka maida mu talakawa alhali m
una iyo a cikin kudi Jawad?"
Ya lumshe idanunsa a hankali lokacin da ta kai karshe sannan ya juyo ya kalle ta.
"Mamah amsata ba zata canja ba kema kin sani,abinda nake gaya miki kullum shi zan kara gaya miki a yanzu, ba zan saci kudin mahaifina ba ba zan d
auki abinda ba nawa ba, shi yasa nake aiki kin sani, su sauran matan nasa da yayansu ke zuwa su debo musu ai basu suka saka su a gaba suka roke su ba, kowa ganin damarsa ce tasa shi yin hakan, don haka me yasa ni zaki takura min, ba ga su Khairat nan ba? (
Kannensa mata biyu) Ki koya musu wata hanyar da zasu samo miki mana, ai ba maza ne kadai suka iya samowa ba."
Ya ajiye kofin hannunsa sannan ya mike tsaye, sannan yace
"Zanyi bako anjima, Dan Allah Mamah ki sa ayi mana abinci, wadannan duk basu yi min ba.
"
Ya fada yana nufin tarin cimar dake kan teburin daya tsallake, kuma bai jira abinda zata ce ba yayi gaba, ya zaro wayarsa ya kira Haron da suka yi akan lallai ya shigo Abujan don ta nan ne zasu hau jirgi zuwa Kano, ya gaya masa shi ba zai yi tafiyar mota
ba.
Kuma awa guda bayan hakan sai gashi ya iso, suka zauna daga falon kasa na
ɓ
angarensu yayin da Haron ke ta mita akan tason shi da yayi babu shiri.
"Kaifa kake bukatar abin nan J, amma ni ka takurawa na taho rana tsaka, ina ga dole mu maida harkar nan m
a taciniki don na fahimci ni zan sha wuya a banza."
"Ko nawa ne ka san zan biya ka, I never regret anything indai akan Rukayya ne ka sani."
Haron ya kalle shi lokacin da ya tsiyaya wani lemo mai sanyi a daya daga cikin tambulan
ɗ
in da aka kawo musu sannan
yace.
"Shi yasa ni kuma nake iya kokarina don inga na ciro ka daga wannan masifar, Haba ka kalli fa inda kake rayuwa, ni ban ma san kun canja wannan gidan ba, amma ka kallafa ranka akan wannan shashashar yarinyar, in the first place ni ban san ma me yasa z
aka neme ta ba idan har ka san aurenta zaka yi."
Jawad ya gyada kansa alamun ya fahimta yana kallonsa sannan yace.
"Ina ga duk mun wuce wannan stage din Haro, mun karaso wajen da kace zaka taimake ni, ni kuma nake jiran inji ta hanyar da zaka taimake ni di
n."
Cike da takaici Haron yana kallonsa kafin ya bu
ɗ
e briefcase din da yazo da ita a gefensa sannan ya zaro wasu hotuna guda uku ya miko masa, ba tare da bata lokaci ba kuwa Hawad yasa hannu ya karba.
Hotunan mutum daya ne a mabanbantan llokuta har guda uk
u, na farko kamar ranar daurin aure ne, don a cikin jama'a yake sanye kuma da kaya masu babbar riga, na biyu kamar hoton wajen aiki ne, yana sanye da suit da kuma sumar gashinsa wadda aka gyara cikin wani style mai kyau, sai na karshe a bakin titi ne yana
waya, hoton yayi kama da cewar a boye aka dauke shi sosai.
Kuma ba sai Haron ya sake yi masa bayani ba, ya riga ya fahimci waye tun da wuri, don idan zai iya tunawa ma ya tabacganinsa sau daya a wani taron harkar kasuwanci da ya halarta shekara guda baya,
idonsa ya manne akan fuskar sa yana son ya gano banbancin dake tsakaninsa dashi, wannan banbancin da yasa Rukayya ta juya masa baya, banbancin da yasa ta rufe idanunta akan tarin kyautatawar da yayi wa rayuwarta ta kasa ganin kokarinsa, ko ma rabewar da zu
ciyarsa ke yi a lokacin da take gaya masa cewa bata dauke shi komai ba face abin wasa kawai, abin wasanta!
"Na gama samun duk wani background information akan gayen, ashe har aure ma ya sake yi..."
"What?"
A lokaci guda ya katse Haron da ke kokarin fara ba
yaninsa. Fuskarsa na kallonsa da tsananin mamakin da ya kasa tantance daga ina yake fitowa yana shiga jikinsa.
"Yes, ya sake aure ƴan kwanakin bayan nan, amma naji ance kamar bashi matar kawai akayi don tare akayi auren dana sauran yanuwansa."
Sai kawai ya
gyada kansa a hankali ba tare da ya san me zai ce ba, hakan yasa Haron ya cigaba da maganarsa.
"Ka san ni bana sanya a al'amarina, so na samu labari ance min zai hadu da wasu mutane gobe, na samu details
ɗ
in da komai daga bangarensu, so kawai zamu yi ma
sa aiki ne a lokacin."
Jawad ya dago ya kalle shi."
"Aiki? Wane irin aiki?"
"Plan dina shine mu kama shi for now, kar ka tambaye ni me zai faru bayan nan, mu fara gama wannan din tukunna."
Jawad ya kalle shi tsawo sakanni biyu.
"Ba zan tambaye ka ba, amma
ka sani cewa I wont sign for any shit, idan har kashe shi ne plan dinka..."
"Wa yake maganar kisa anan J? biyu babu muka ce zamu sa yarinyar nan tayi, you want to make her pay ko ba haka ba? Then we are just going to make her pay kamar yadda kake so, ka ya
dda dani kawai."
Jawad ya sake kallonsa na wani lokaci kafin ya gya
ɗ
a kansa.
"To meye plan din?"
"Ba ma zamu bari ya isa wajen mutanen da zai hadu dasu ba, kafin ya isa za'a tare shi kawai sannan a juyo da motar, yaran da nasa sun nemo titin da komai har m
a da daidai wajen da zasu tsaida shi din, shi yasa nace maka dole mu bar Abuja yau."
Jawad ya gyada kansa alamun ya fahimta.
"Idan har babu zancen kisa a al'amarin nan, I think hakan yayi daidai."
Haro ya girgiza kansa.
"Wannan gayen ba irin mutanen da za'
a kashe su maganar ta wuce kamar iska bane J, daga shi har mahaifinsa suna da tarin connections din da ban san iyakarsu ba, don haka wasa kawai zamu yi dashi mu cimma manufarmu."
Kalaman ƙarshe suka tafi kai tsaye cikin zuciyar Jawad suka yi masauki.
Wasa
kawai zasu yi dashi, wasa... Ya cije lebbensa na kasa yana sake maimaita kalmar a ransa. Yanzu yake ji cewa da gaske Haro ya dauko hanyar cimma manufarsu, tunda har zsi bashi damar da zai nunawa Rukayya cewa mutumin da take wa kallon duniyarta, take wulank
anta shi akansa shima bai fi karfin ya zama abin wasan a wajen sa ba.
Yana jin Haron na kokarin yi musu booking jirgin da zai tashi zuwa Kano lojacin da ya miƙe don zuwa dakinsa ya fara shiri, a lokacin ne kuma yaci karo da ita, wannan yarinyar, wannan ya
rinyar da ya ƙi jinin ganinta, 6ar aikin mahaifiyarsa, tana tsaye daga koridon dake jikin falon haunnuta rike da wani katon faranti da ta shako kayan abinci dasu, kuma ba sai tace komai ba, rawar