Showing 9001 words to 12000 words out of 144990 words
Awwalu, ta yaya hatsarina zai zo rana daya dana Jamal? Tsaftataccen aiki nake yi a kodayaushe ka sani, bana yin sajacin da zan bari ko da
ɗ
igon baki da zai kawo zargi a zuciyar wani na."
Awwalu ya gya
ɗ
a kansa yana cigaba da wan
i murmushin kafin yace.
"Na yarda dake wallahi Hajiya."
""Kaje ka siyo wata tayar, a daura sai mu tafi."
Kuma wadannan kalaman nata na lokacin sune tushe, shine sanadin faruwar wasu abubuwan da har a yau ba'a warware su ba, don Awwalu ya dauki tsawon lokac
i kafin ya iya samo sabuwar taya da kuma mai daurata kasancewar safiya ce lokacin, don haka kafin su koma gida matafiyan nan sun tafi.
"Mami, Ya Ma'aruf ya shigo yace ya kira wayarki a kashe, yace idan kin dawo in gaya miki ya bi Ya Jamal zuwa Abujan, zaku
yi waya idan kin dawo."
Kalaman da Salma ta fa
ɗ
a mata kenan bayan ta koma gida da misalin karfe goma saura na wannan safiyar.
Kuma a tarihin rayuwar Kilishi kaf! Idan zata misalta kalmar tashin hankali, zata kwatanta ta ne da wannan ranar, ranar da zuciya
rta ta buga a kirjinta, kafafunta suka zube gar a ƙasa yayin da idonta ya shiga hasko mata gawar Ma'aruf din da bata tsara a lissafinta ba tare da ta Jamal!
***
*
Present Day.*
"Halima."
Alhaji Sulaiman dake zaune a cikin
ɗ
akinsa ya kira sunan matarsa dake
shirin sa kai ta fita bayan ta ajiye masa flask din ruwan zafin da ta dafa a dawowarsu yanzu da safen.
Tsintsiya ce a hannunta wadda ta dauka don zuwa ta kara share falo inda aka kwantar da Aminun, taso ace tun jiya su Maryam sun zo sunyi sharar kafin su
dawo, amma haka kurum ta kasa kiran iyalan gidan Kawu Malam inda su Maryam suka tafi da wannan umarnin, tana da kawaici akan ƴaƴan ta kowa ya sani, abinda mutane basu sani ba shine tana ajiye wannan kawaicin a gefe idan har aka zo gabar da za'a cutar mata
dasu.
A kofar dakin ta saki tsintsinyar sannan ta juyo ta dawo ciki, don daga yanayin amon muryar Baban ta san magana ce mai muhimmanci zasu yi.
Ta sami waje gefensa ta zauna yayin da idanunta farare irin na Amina sak ke kallonsa, kallo na saurare da kuma
jiran umarni.
"Jiya na hango ki kina waya da ƴarki."
Ta gyada kanta sau
ɗ
aya bayan ta gane cewa Amina yake nufi.
"Akwai wata matsala ne da take fuskanta a gidan?"
Mamakin tambayar tasa ya kamata, sai kawai ta sunkiyar da kanta kasa a hankali, a shekarun za
manta dashi kaf! ya sani ko da sau
ɗ
aya bata taba zuwa ta bashi labarin wata matsala ba walau ta danginta ko kuma ta wani da ya shafe ta ba kuma shima baya taba tambayar abu makamancin hakan ba sai idan har zancen ne yazo a dole su fade shi, don haka abind
a ba'ayi a baya ba, ba za'a fara shi yanzu ba.
Amina yarsa ce, ta san yana da hakki akanta amma a tunaninta ya riga ya gama taka rawarsa akanta, yayi ruwa yayi tsaki wajen kaita rayuwar da babu ta hanyar da bata kalubalance shi ba. Shi da kansa ya fada cew
a ba zai iya tuna ranar da tayi masa musu akan wani abu ba, amma bai ko duba wannan kawaicin nata na tsawon shekaru ba, da yake shi namiji ne ya rufe idonsa ya juya mata baya, ya dora yar tasa a wani mizani da dole nasa umarnin zata dauka.
A yanzu anyi hak
an, komai ya wuce ba tare dacta nuna fushinta ba, kuma gashi sun fara fuskantar kalubalen da ta guje musu shi, to don me yasa zai tambaye ta kuma?
Ta fahimci har yau Sulaiman bai gama bu
ɗ
e halayenta ba, don da ya san wacece Halima da bai
ɓ
ata bakinsa ma wa
jen tambaya ba, bata gori, bata cewa 'dama na fada...' zata yi iya kokarinta ne a farko don ganin ta kawar da matsala daga karasowa gare ta, idan kuma ta kasa, sai ta fara shirin tunkararta ta hanyar da zata iya kawar da ita, wannan shine babban abinda ke
riƙe da zaman lafiyar gidanta dama zamanta tare dashi. Shi kansa idan zai tuna yana da zafi da kuma zuciya a lokacin kuruciyarsa har zuwa aurensu, amma da wannan halayen nata ta canja shi a lokacin da bai ma sani ba.
Don haka sai ta gyara zamanta kawai a h
ankali sannan ta girgiza kai.
"Babu wani abu, wata yar matsala ce kawai tamu ta mata."
Ya kalle ta tsawon wasu mintuna kafin ya sake kiran sunanta.
"Ina fata a yanzu kin daina ganin laifina Halima, don kowa shaida ne daga ganin yarinyar nan an san tana cik
in nutsuwa."
Babu shiri murmushi ya subuce a bakin Amma, mazan kenan! bata jin har abada za'a zo lokacin da kwakwalwar kowanne namiji zata bude game da al'amarin mata, suna ikirarin sun san komai a kullum, amma tarin abubuwan da ake lullube su a ciki suna
da yawa, wanda hakan na
ɗ
aya daga cikin abubuwan dake juya duniya, don da zasu san kowacce kissa da dabara irin ta matan to da zaman auren ma zai gagari kowa ce ƙabila a duniyar nan.
Tun a lokacin da aka jawo kayan kefen Aminan kallo
ɗ
aya tayi wa akwatunan
da aka zuba kayan kwalliya zuciyarta ta
ɗ
arsa mata wani abu da sai a yanzu take ganewa. Kilishi ta narka maƙudan ku
ɗ
a
ɗ
e na gaske wajen siyan tsadaddun kayan gyaran jikin da zasu karbi fatar Amina, ta yadda a waje kowa zai sanya ta cikin layin nutsuwa da k
wanciyar hankali da kallo daya, yadda komai zurfin da zuciyarta zata yi babu mai iya gano hakan don za'a shagala da kallon canjawar fatarta maimakon damuwarta, gashi kuwa hakan ya fara aiki har akan mahaifinta da ya kawo ta duniyar nan, wai sau nawa ne zat
a fada? Kilishi mugun ice ce da gaske!
Sai kawai tayi wani murmushi a hankali sannan ta gyada kanta tace.
"Haka ne."
Shima ya gyada nasa kan.
"Sai dai mu bisu da addu'ar dorewar zaman lafiya.
"Tabbas kuwa."
Amman ta sake fada tana jin wani abu kamar raha n
a ratsa zuciyarta, tana ƙara yarda cewa mata duniya ne, Allah ya basu damar juya namiji duk girma da tsufansa a tafin hannunsu, kawai da yawa ne basa amfanin da danarsu.
"Mun yi waya da Kawu Mallam yanzu, yace za'a rako su Maryam din anjima, tunda kike ta
kallo na a hanya na san abinda kike so kice in tambayo miki kenan."
Ta girgiza kanta.
"Ni ban aike ka ba, idan zasu kara kwana ma ba zan damu ba."
Kice zaki iya bacci babu Hafsatu a gidan nan?" Ya tambaya
"Kafin in same ta fa?"
"Kina da Amina."
Sai kawai t
a mike tana dariya, ta
ɗ
auki tsintsiyarta ta fita. Alhaji Sulaiman ya bita da kallo yana jin zuciyarta wani iri, kamar bai gama yarda da kalamanta ba, amma kuma babu yadda zaiyi, matarsa daban ce a cikin mata ya sani, halayenta wani abu ne da ba zai taba i
ya kwatanta su ba, juma abinda bai sani ba shi e matarsa iri daya ce da kowacce mace, natan ne kawai basa gane cewar nutsuwar zuciyarsu a kowanne fanni na rayuwarsu taba zaune cikin ƙwaƙwalwar su.
Awanni biyu bayan hakan ya baro cikin gidan, Ya fito ya nuf
i titi don tafiya ga sana'arsa.
Daidai lokacin da Awwalu dake zaune cikin motarsa a can gefen layin ya tada motar shima yabi bayansa.
****
*A wannan safiyar.*
Ma'aruf ya tako cikin gidan a hankali, hannunsa daya na sanye cikin wandon shaddar dake jikinsa
kalar ruwan toka yayin da
ɗ
ayan ke rike da wayar dake kare a kunnensa, kayan jikinsa kalar ruwan ƙasa ne wanda ta haska cikin safiyar, ƙafafunsa na tahowa cikin falon a hankali yayin da yake saurarar bayanin da Faruk ke yi masa a cikin wayar.
"Mutumin nan
sh*ge ne B, Ƙarfe biyun dare ya kira ni wai shi daga sannan yake amsa waya, wallahi har na zata yan fashi ne suka shigo mana."
Yayi murmushi ka
ɗ
an.
"Baka da hankali Faruk dan fashin ne zai fara kiranka a waya ya gaya maka cewa gashi nan zai shigo tukunna?
ka gaya min yaya kuka yi dashi kawai?"
"Yes, ya karba. But sai mun bashi wani abu tukunna, kuma ka san shi cash yake baukata, kuma gayen yana da matsala wallahi don yace dole yau yake bukatar ku
ɗ
in, shi yasa tun farko ni raina bai kwanta da mu saka shi cik
in al'amarin nan ba."
Ma'aruf ya girgiza kansa.
"Kar ka damu, zanje na ciro ku
ɗ
i anjima sai ya gaya mana inda zamu same shi."
"Shikenan, I will talk to him zuwa yamman, zan gaya maka."
Da haka wayar tasu ta kare, daidai lokacin da Ma'aruf ya shiga hanyar k
oridon zuwa kitchen, inda ƙarar motsin kwanuka ke tabbatar masa da cewar tana ciki.
Da gaske yake abinda ya fa
ɗ
a mata jiya cewa tana ƙara ƙawata duniyarsa, don duk da har yanzu bata gama sakin jikinta dashi ba, ya sani cewa shigowarta cikin rayuwarsa ya fa
ra samun wata nutsuwa da shi kansa baya gane mata, abinda kawai ya sani shine abinda yaji tun daga ranar da ya fara ganinta shi yake jan ragamar sa akanta.
Tsakanin jiya da yau ka
ɗ
ai yana jin sunyi sabon dashi da Ruƙayya basu sami hakan a
ɗ
an kankanin loka
ci ba, ya nuna mata cewar da gaske yake wajen gyara alakarta dashi, kuma hakan bai bashi wuya ba don da gaske ne yarinyar bata da matsala, tana da hankalin da bai san da me zai kwatanta shi ba, tana da hankalin da ya fahimta sosai a cikin dukkan amsoshin d
a ta bashi don sunyi hira sosai a jiya, yayi mata tarin tambayoyin daya fahimci kusan rayuwarta gabadaya a dunƙule.
A lokacin ne kuma ta juyo ta kalle shi, hannunta daya rike da plate din da take wankewa a cikin sink, lbakinta yayi masa murmushin nan nata
dake tafiya har cikin zuciyarsa. Wani abu daya lissafa shi cikin nasarorinsa na kwanakin nan kenan, yana gaya masa cewa da gaske yayi kokarin da ya fara rusa wasu abubuwan dake tsakaninsu, shi yasa a jiya ya daure yayi mata tambayar da yake fatan amsar da
zai samu amsa daga gare ta, amsar da yake fatan ta zama abu na karshe da zai cire duk wani hijabi a tsakaninsu.
"Sannu da zuwa" Muryarta ta fito a hankali.
Bayan asuba ya sake fita wajen ƙarfe bakwai na safe, ya tafi can yamadawa inda ya halarci janaizar w
ani abokin Baffa da ya rasu a daren jiya, da Baffan suka yi waya a jiyan ya gaya masa cewa yaje ya wakilce su shi da Baba Usman tunda basa gari, sai gobe ne suke shirin dawowa daga Kadunan.
Don haka can ya tafi kuma har bayan an kai mutumin sai da ya sake
komawa gidan don bai shiga ciki yayi musu gaisuwa ba, ya san matarsa guda
ɗ
aya, don a shekarun baya kafin ya auri Rukayya daga ita har mijin nata sunyi kokarin hada shi da wata ƴar su Nafisa, kuma shima saboda hankalinta ya so yarinyar a lokacin amma sai n
aci da kuma dagiyar Rukayya ya tsallake nasu.
Yanzu ma da yaje yaga yarinyar, tana zaune a gefen mahaifiyar tata riƙe da wani yaro mai kama da ita sak wanda hakan ya shaida masa cewar tayi aurenta itama, kuma sunji mutukar dadi na ganin nasa, don bai san m
e yasa ba kai tsaye yake iya fahimtar farin ciki da kuma yabawa a fuskar mutane, kamar yadda a jiya ya fahimci da
ɗ
in da Amina taji a lokacin da yake godiya da kuma yabawa girkin da tayi masa.
Ya karaso cikia hankali sanda da ta kashen famfon tana rike da k
ofi na karshe a hannu ta.
Ya tsaya a gabanta.
"Anyi jana'izar?" Ta tambaya bayan ta kalle shi ta sunkuyar da kanta. Ya daga nasa kan kafin ya amsa.
"Anyi tun
ɗ
azu, makabartar babu nisa da gidansa." "
Yaga kamar ta hadiye wani abu a makogwaronta kafin tace.
"Allah ya jikansa."
"Ameen."
Ya amsa yana cigaba da kallonta, kuma abinda yake gani a fuskar tata bai tafi ba, don da alama mutuwar ta
ɗ
an ta
ɓ
a ta duk da bata san mutumin ba, yaga hakan a fuskarta tun daga lokacin da ya gaya mata inda zai je da safe bayan
ya shiga dakinta ya same ta zaune akan dardumar ta har a lokacin.
Kayan dake jikinta a yanzu wata doguwar riga ge ta atamfa Green, kuma akwai wani abu a cikin kalar rigar da yayi mata kyau yake kunna wani abu kamar wuta daga ƙasan zuciyarsa tun sanda ta
shigo kitchen din.
"Har kinyi breaskfast?" Muryarsa ta tambaya da wani irin amonta mai sanyi yana katse shirun dake son faruwa.
Ta girgiza kanta a hankali sanin cewa kofin hannunta yake kallo.
"A'a, nayi amfani dashi ne."
Ya zaro wayarsa daga aljihu ya kal
li lokaci.
Ƙ
arfe goma har da kwata.
"Dama ba kya cin abinci da wuri?"
Ta sake girgiza kanta.
"A'a ya danganta kawai."
Sai taji yayi wani abu kamar murmushi kuma kafin ta
ɗ
ago ta kalle shi ya sunkuyo da fuskarsa kusa da tata yace.
"Ya danganta da lokacin da
na dauka a waje kina jirana kafin na dawo?"
Wani irin abu ya lullubeta a lokaci guda tun daga kai har ƙafa, ta dago ta kalle shi idonsa yana kanta kamar yadda ta sani.
"Ki gaya min gakskiya dan Allah ba zan fadawa kowa ba... kawai ce miki zanyi nagode." Y
a roje ta a hankali.
Bata san lokacin da tayi wani guntun murmushi ba sannan ta daga kanta sau daya tana cigaba da kallonsa.
Wani abu da yasa a lokaci guda Ma'aruf yaji wasu abubuwa kamar chemical concoctions na zubewa a cikin zuciyarsa.
"Now I feel like p
osting it on my Facebook wall."
(Naji kuma yanzu kamar inje in rubuta a shafi na na Facebook.) Ya fada muryarsa can ƙasa.
Sai kawai tayi wani murmushin mai fadi sannan ta juya, ta nufi wajen da take ajiye kofunan a kitchen din ta ajiye na hannunta sannan t
a debo wasu containers da ta juye su Madara da Milo a ciki ta juyo, ya jingina da gefen sink
ɗ
in har yanzu yana kallonta, kamar yana son yace wani abu.
"Sauran kayan suna falo."
Ta fada tana nufin sauran kayan breakfast din, kuma da haka ta taho zata wuce
ta gabansa, amma kamar yadda zuciyarta ta ayyana mata zai faru, sai ya tsayar da ita, ya riko hannunta ya dawo da ita gabansa.
"Baki bani amsata ta jiya ba Amina."
Kai tsaye ya fada yana karbar kayan hannunta ya ajiye su akan sink din.
Sai ta kasa kallonsa
wannan karon, ya riko hannunta
ɗ
aya sannan muryarsa ta cigaba da magana a hankali.
"yunda na tashi da safe tunanin da nake yi kenan har naje na dawo, ko aikina da tarin mutane ke karkashina baya damuna kamar yadda a yanzu jiran abinda zaki ce ya dame ni,
I always have the last and final say a kamfaninmu, but zuciyata bata damuwa da abinda zan fada kamar yadda a yanzu ta damu da abinda zaki fada min, so Please save me from this boredom and just say it now. Na gaya miki ko a yaya amsarki tazo zan karbe ta a
hakan ba tare da wani tunani ba, I just want to hear your mind out." ( So nake kawai inji abinda yake a zuciyarki.)
A lokaci guda Amina taji makogwaronta ya bushe, taji tana shakar wata busashshiyar iska tana wucewa har cikin cikinta yayin da maganganun da
ya fada mata jiyan ke dawowa cikin kanta.
"Amina ban san tunanin ki gane dani ba har yanzu, auren mu daban ne da irin wanda kowa yake yi, ban taba ganinki ba sai a ranar da kika zama matata kuma na san kema haka, kowanne mu bai san yaya
ɗ
aya yake ba balle
halayensa har aka ha
ɗ
a rayuwarmu tare, bamu da wannan sanin ko kuma fahimtar junar da mutane da yawa ke samu kafin aure.
Sai a yanzu ne muke fara gina tubalin da muka baro a baya, kuma ba zan boye miki ba I think I have started falling in love with you s
ince from day one da na ganki a cikin gidan nan, ban san me yasa ba I just did... Kuma a yanzu da na ƙara sanin ki nake sanin komai game dake Amina, zuciyata ta bani tabbacin cewa da gaske ne ina son ki ba tunani nake yi ba, zuciyata tana godewa Allah a ko
dayaushe da ya zamo kece wacce Mami ta zaba min a matsayin matata.
Saboda da bake bace Amina da labarin zai canja, ko sau
ɗ
aya kar kiyi tunanin cewa da kowacce mace aka kawo cikin gidan nan zan kar
ɓ
e ta kamar yadda na kar
ɓ
e ki. Na san me nake so Amina na s
an abinda bana so, kuma ina da tsarina a kowanne
ɓ
angare.
Don haka kema ina son inji tunaninki game dani, bana son in matsa miki da komai Amina, idan zamu gyara alakarmu mu cire komai a tsakaninmu ina so ya zama da yardar dukkaninmu ne, bana so ya zama don
ni ina so ke kuma ya zane miki dole, so nake mu ajiye duk wani tunani a gefe tare mu kar
ɓ
i junanmu da zuciya daya, I want us to ignite our hearts together and get lost because we wanted to, shi yasa a