Showing 84001 words to 87000 words out of 144990 words

Chapter 29 - FARAR WUTA COMPLETE

sunansa gaba

ɗ

aya.

"Ma'aruf Mansour Bakori..... ka dinga tunani irin na

mutane a cikin kanka dan Allah."

Ta fada tana ƙoƙarin miƙewa, bata je koina ba kuwa ya jawo ta suka koma kan gadon gaba

ɗ

aya.

"Zo ki koya min irin yadda ake yi tunanin mutanen..."

Abinda ya fa

ɗ

a bayan hakan ya saka ta kyalkyala dariya tana cusa kanta a ciki

n wuyansa, abinda ya cigaba da fa

ɗ

a kuma ya sata fa

ɗ

in.

"Inalillahi wainna ilaihir raji'un... Ma'aruf!"

Dukkaninsu suka kyalkyale da dariya, kuma abinda dukkaninsu basu sani ba shine, za'a

ɗ

auki wata tazara mai tsawo kafin sake faruwar irin wannan ranar a

rayuwarsu!

****

*Abuja.*

*No. 1146 C west, Maitama.*

Ta san dakin, amma idanunta suna kallonsa ne kamar bata ta

ɓ

a ganin sa ba, idan ma akace ta ƙirga bata san sau nawa zata kirga adadin data share kuma ta gyara shi ba, shi ka

ɗ

ai ne a ƙasa bayan falon, kuma

tasha tambayar kanta dalilin da yasa aka hada shi har da komai da komai alhali mai wajen baya amfani dashi ko ka

ɗ

an.

Bayan haka kuma zuciyarta tasha hasko mata yadda zata ji da

ɗ

in kwanciya akan gadon da yake dakin, don kalar labulayen cikinsa da kuma zani

n gadon

ɗ

akin da suke suke dukka kalar yalo, suna faranta zuciyarta haka kawai, tana jin kalar na shiga idanunta da tasirin da take jin kamar tana samun ƴancinta ne a ciki, kamar zata samu wani fiffike da zai miƙar da ita sama ta tsaya da kafafunta irin ya

dda take fata a kullum.

Amma yau da take tsaye a cikin dakin rike da ledar kayan dake hannunta bata jin dukkan wa

ɗ

annan abubuwan, bata jin komai, zuciyarta fayau take kamar fuskarta.

_"Zainab zaki aure ni?"_

Sune kalaman dake maimaitawa kawai a cikin kanta

, amonsu take ji yana ratsa ko'ina na tunaninta, tana ji kamar shaƙuwar data kwace mata a lokacin zata sake dawowa, don shaƙuwa kawai ta dinga yi yayin da idanunta ke ƙara zarewa akansa, kuma bai sake cewa komai ba sai kawai ya kai hannunsa ya shafa kansa

sannan ya juya ya bar wajen.

Bai sake cewa da ita komai ba har suka gama dukkan abinda za'ayi a asibitin ya kar

ɓ

o mata magani, binsa kawai take yi tana so ta tsayar da shaƙuwar da ta kasa tafiya, ya barta a mota ya shiga wani waje da ta kula cewa magunguna

ake sayarwa, kuma bayan ya dawo ne ya shigo motar ya miko mata robar ruwa har a lokacin bai sake cewa da ita komai ba.

Tana tuna yadda ta shanye ruwan gabadaya kasancewar ba wani girma ne dashi ba amma har a lokacin shakuwar bata tafi ba, sai kawai taga y

a sake miko mata wata robar daga cikin ledar maganin, a lokacin har sun fita daga cikin asibitin sun hau titi. Kuma ga wani mamakinta ba gida suka taho a lokacin  kamar yadda ta zata ba, idan zata tuna ma taga sanda suka wuce hanyar gidan suka tafi kai tsa

ye har wajen aikin sa.

Wajen da ya ƙara rikita ta, ya kara sawa ta raina kanta ta san cewa ita ba komai bace a duniyar nan, tun daga waje ginin wajen ya daki zuciyarta har suka shiga ciki, don bai bata wani zabi ba yace ta biyo shi, suka tafi har office di

n wata mata da taji yana kira da Aunty Mary, dattijuwa ce amma kuma arniya, ta saka kayan da basu matse kayion jikinta ba sannan tayi kitson ƙarin gashi.

Tana da tsananin fara'a da kuma kirki, anan yace ta zauna zai je ya dawo, kuma bayan ya tafi haka tayi

ta mata magana duk da ta fahimci ba ganewa take sosai ba, don idan ma zata gane

ɗ

in, taraddadin dake cikin zuciyarta na tunanin Hajiya Mardiyya da nemanta da za'ayi ba zai barta ba, a haka ta zauna cikin tunani da tsoro har sanda wani ma'aikacin wajen ya

shigo rike da leda mai dauke da abinci da kuma magungunan da aka siyo.

_"Hajiya ga shi yace ki ci abincin kuma ki sha magungunan."_

Tana tuna fuskar mutumin da ya kira ta da Hajiyar, zata iya rantsewa zai kai sa'an mijin mahaifiyarta da ta baro a gida, amm

a kamar bai ga kankantar ta ba ko kuma dogon hijabin data zura wan

ɗ

anda basa shaida wani abu na Hajiyar da ya kira ta.

Matar nan da kanta ta gaya mata cewa lokacin sallah yayi, ta bu

ɗ

e mata ban

ɗ

akin cikin office

ɗ

in ta shiga tayi alwala sannan bayan ta fit

o ta shimfida

ɗ

ankwalinta akan carpet din wajen tayi sallah, haka ta zauna idanunta na cigaba da zarewa har sanda ya dawo, kuma a lokacin kallonsa kawai tayi taji shakuwar

ɗ

azu ta dawo, haka ta dinga yinta tana kokarin boyewa har suka koma motar kuma ya sa

ke miko mata wani robar ruwan ba tare da yace komai ba, wani abu da duk rikicewarta sai da ya saka ta murmushi a lokacin.

Sun dawo gidan jikinta na rawa kamar yadda zuciyarta ke yi na tarin abinda ta san zata tarar, abinda ke jiranta wanda kwakwalarta ta k

asa hasaso mata shi, amma bai ko bari tayi hanyar wajensu ba yace ta biyo shi bangarensa.

Kafafunta sai da suka tsaya cak jin hakan yayin da wani shiru ya ratsa ta tana jin yadda komai ya

ɗ

auke a cikin kanta amma bayan yayi gaba ya sake juyowa ya kalle ta

da wadannan idanun nasa sai kawai ta kasa cewa komai ta biyo bayan nasa suka shigo har bangarensa, ya bu

ɗ

e mata kofar wannan dakin ya bata ledar kayan dake hannunta a yanzu yace ta shiga ta shirya.

Ta shirya. Shiryawar da bata san ma'anarta ba har yanzu, k

allon

ɗ

akin kawai take yi kamar a cikinsa zata samo amsoshin da take nema.

Ta tsugunna a hankali har ƙasa, ta bu

ɗ

e ledar hannunta ta zaro kayan ciki, wata farar riga ce mai tsawo da kuma laushi, akwai wani dogon wando kakar adon jikinta pink, sannan da hij

abi fari tas wanda ta san zai kai mata ne har ƙasa, mamakin inda ya samo kayan ya kamata, Allah ya sani bata san me yake nufi ba, bata gane komai ba har yanzu, so take kawai ya barta ta fita ta samu Hajiya Mardiyya ta gaya mata duk abinda ya faru ta kuma r

oƙe ta gafara, don ƙwakwalarta na shaida mata cewa itace gatanta ba Jawad da al'amarinsa ba.

Kusan minti talatin tana zaune a kasan carpet

ɗ

in

ɗ

akin ta jingina bayanta da jikin gadon yayin da kwakwalwarta ke ta faman lissafin wucewar lokaci tana jira yazo

ya sallame ta tafi, kuma saboda gajiya da kuma zazza

ɓ

in da bai gama barinta ba har a lokacin, sai ta fara gyangyadi zaune a wajen har zuwa sanda aka kwaknkwasa kofar dakin, sau biyu kawai kafin kofar ta bu

ɗ

e.

Idonta ya sauka akansa tana ƙoƙarin wartsakewa,

yana tsaye sanye da wata jallabiya baƙa, hasken fatarsa ya ƙara fitowa sosai alamun wanka yayi, yayi shirin da ita bata yi ba.

Jawad ya tako har ciki yana kallonta, da alama inda ta tsaya bayan ya barta a dakin a wajen ma ta zauna, Babu alamun ta matsa ko

'ina, me yasa take so ne ta kara masa matsala bayan tarin abubuwan da yake fuskanta?

Shi ka

ɗ

ai ya san yadda ya daurewa kansa yayi aiki a office yau, zai rantse da Allah bai ta

ɓ

a ganin tsoro a idanun kowacce mace a duniyar nan ba kamar yadda ya gani a nata

lokacin da ya tambaye ta idan zata aure shi, shi yasa ko da ya barta a Office din Aunty Mary, sau biyu yana kiranta yaji idan tana nan bata gudu ba, wannan shakuwar ka

ɗ

ai da ta dinga yi tayi yawo a cikin kansa ta yadda da ƙyar ya goge ta yayi aikin dake ga

bansa.

Da gaske yake, da gaske yana ganin zai iya aurenta shi yasa har ya tambaya, don bai taba jin wani abu da ba zai ta

ɓ

a kasancewa ba sai a lokaci da Mamah ta gaya masa cewar wai aure iyayenta zasu yi mata, ya sani bashi da iko akanta fiye dasu ko ma wa

ni a duniyar nan, amma a lokaci guda yaji cewar babu mahalukin da ya isa yasa hakan ta kasance, babu wanda zai bari yayi nasarar dauke ta daga gabansa, shi yasa a lokaci gudan ya yanke shawarar tambayarta idan har zata aure shi.

Don a wannan lokacin yana j

i kamar idan ta amsa shikenan komai ya tabbata, shikenan ta zama tasa sun kaucewa dukkan wasu abubuwa.

Burinsa kawai ya cigaba da wayar kowacce safiya yana ganinta a gefensa ko da ba zai iya ta

ɓ

a ko yatsanta ba, ya riga ya fahimci a yanzu rauninta yake so,

shine babban abinda ke jan hankalinsa akanta, wannan rauni da kuma rikicewarta da suke banbanta masa ita da Rukayya, Rukayya mai ji da kanta da kuma taƙamar tsayawa da kafayrta a kodayaushe, komai nata yayi hannun riga da Zainab, shi yasa tun a farko zuci

yarsa ta fara tsayawa akanta don yana neman duk wani abu ne da zai sa ya manta da Rukayya a lokacin.

Da lokaci ya cigaba da tafiya kuma sai yake jin zuciyarsa ta saba da wannan banbancin sabon da baya jin a karo na biyu kuma zai bari ya sake rasa wani abu

irin haka a rayuwarsa.

Tun kafin ya karasa shigowa

ɗ

akin ta miƙe hannayenta na ƙoƙarin fara rawa riƙe da rigar da ta

ɗ

auko a cikin ledar, ya cije lebbensa ka

ɗ

an yana daurewa abinda ke ƙoƙarin tasowa daga zuciyarsa.

"Me yasa baki shirya ba?"

Ya tambaya kai

tsaye yana kallonta, ta girgiza kanta da sauri kafin tace.

"Ba komai, so nake in koma

ɗ

akinmu dama sai in shirya acan."

"You are not going back to that place..."

Idanunta suka tsaya akansa da kallon rashin gane abinda ya fa

ɗ

a duk kuwa da yadda take a tsora

ce, sai ya

ɗ

an kalli gefe alamun mantawa da hakan sannan ya sake juyowa.

"Anan zaki zauna, ba zaki koma can ba,idan akwai abinda kike bukata a cikin kayanki sai ki saka a dauko miki.."

Ai tun kafin ya ƙarasa kwalla ta cika idanunta ta shiga girgirza kanta

da sauri.

"Dan Allah kayi hakuri ka barni in tafi, wallahi Hajiya fa

ɗ

a zata yi min, yau ma tace za'a mai da ni gida kuma..."

"Babu inda zaki, idan kin warke zan kai ki gidan ki gansu sai mu dawo."

Ya fada yana sawa ta tsaya cak tana kallonsa, don hatta kwa

llar data taru a idanunta bata zubo ba.

"Ba dawowa zanyi ba idan na..."

"Dawowa zaki yi, 'Coz babu inda zaki je ki zauna a duniyar nan da ya wuce nan."

Ya fa

ɗ

i hakan kamar cikin tursasawa don har yanzu a tsaye take cak tana kallonsa, sai kawai ya shafo ka

nsa da duka hannayesa biyu shima yana kallonta, yayi kokarin saita kansa sannan muryarsa ta saje fitowa.

"Babu abinda zanyi miki Zainab, wallahi babu abinda zanyi miki, baki ga har hijabi na siyo miki ba? I just want to feel you close to me... So nake kawa

i in dinga jinki a kusa dani. Shi yasa na tambayeki idan zaki aure ni saboda zan je har wajen iyayenki ne in nemi aurenki, babu ruwana idan ma akwai wanda suka tsara zasu baki Zainab, ko shari'a zan iya yi da kowa idan akace za'a hana ni aurenki..."

Ya fa

ɗ

a yana kallon yadda take kallonsa har a lokacin, a tsaye kyam amma kuma idanunta na haskawa da dukkan wata ma'anar tsoro na duniya kamar ma bata fahimce shi va, ba sai kawai ya girgiza kansa sannan yace.

"Ko ke baki da za

ɓ

i yanzu Zainab, zan aure ki ko bak

i gama yanke shawara ba, idan yaso daga baya zan koya miki yadda zaki so ni."

Yana fa

ɗ

in haka ya juya yayi hanyar kofar dakin, sai dai taku hu

ɗ

u kawai ya tsayar da kafafunsa kafin ya ƙarasa, ya juyo ya sake kallonta, tana tsaye yadda take har yanzu kamar t

ana jira ne wani ya ta

ɓ

a ta ta fa

ɗ

i, sai ya juyo ya dawo da saurihar gabanta, kuma bai jira komai ba ya janye hijabin kanta zuwa ƙasa, gashin kanta da akayi wa wasu manyan kitso mai suna 'Doka' guda uku suka baiyana da jelarsu ƴar gajeriya a baya.

Sai dai

shi ba ta su yake ba ma, hannyensa yasa duka biyu a wuyanta, yatsunsa dukkansu suka zagaye dan siririn wuyan nata har zuwa baya, dumin jikinta ya ratsa zuwa tasa fatar a lokaci guda da ta rufe idanunta gaba

ɗ

aya, wannan kwallar da ta taru tana samun damar z

ubowa. 

Dukkaninsu suka sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya a tare yayin da Jawad ke kallon fuskarta yana ji kamar ya ƙarasa da tasa ya ha

ɗ

e goshinsu waje daya, amma ya daurewa kansa ya ha

ɗ

iye wani abu a kirjinsa sannan muryarsa ta fito, a hankali cikin

sautin da baiyi kama da wanda ya gama magana dashi yanzu ba.

"Maganin ki yana wajen dining, ki ci abinci ki sha, zan je wajen Maamah yanzu zan dawo, kinji?"

Kuma ga mamakinsa sai kawai ta

ɗ

aga kanta sau

ɗ

aya bata ƙara ba kuma har yanzu idanunta a rufe suke

, ya cigaba da kallon fuskarta na tsawon sakanni idonsa na sauka akan siraran le

ɓɓ

enta yana jin yadda kwakwalar sa ke kokarin saita kansa daga abinda yake tunani kafin ya zare yatsunsa daga wuyanta a hankali.

Kuma bai ƙara cewa komai ba ya juya ya nufi han

yar kofa fitar, zuciyarsa na goge hoton ta da na mahaifiyarsa a cikin idonsa, Hajiya Mardiyya... missed call dinta ne a wayarsa kusan goma sha biyar, bayan wayar da suka yi sau hudu yana gaya mata inda suke da kuma sanda zasu dawo, yanzu ma ya tabbata bata

ji shigowar motarsa bane da tuni ya ganta tazo.

"Jawad dan ub*nka a matsayin me ka dauki yarinyar nan ka kaita har wajen aikin ka?"

Haka take gaya masa lokacin da yace mata suna office tare.

Bata taba zaginsa ba, zai rantse bai ma ta

ɓ

a jin kalmar zagi a b

akinta ba, sunansa kadai akan shafe watanni bata furta ba, a kullum kuma a gaban kowa shi baban ta ne, amma yau da girman sunan da take ji da komai ta ha

ɗ

a ta zage gabadaya.

Ya hadiye wani abu a maƙogwaronsa lokacin da ya fita zuwa  waje gabadaya, haka kaw

ai yake jin kamar ko ita bata isa ta shiga tsakaninsa da yarinyar nan ba.

Yana isa

ɓ

angaren nata kannenta ya fara tararwa tare da wasu cousins dinsu sun zo gidan, sun ha

ɗ

u akan wani katon tray da suka dafa wata tarin indomie da kifi a ciki, kowacce ta tatt

are kayanta sun baje suna ci ga wasu manyan-manyan jugs na zo

ɓ

o a gabansu.

Gaisuwarsu ta amsa a cikin kansa cikin amo

ɗ

aya na siririyar murya, kuma bayan ya amsa bai jira komai ba kafafunsa suka karasa zuwa hanyar koridon da zai tarar da dakin mahaifiyar t

asa.

Kofar a bu

ɗ

e take, ya tura ta a hankali ya shiga ciki da sallamar da ta tsaya iya maƙoshinsa, sai dai idonsa bai gane masa kowa ba alamun bata ciki, kuma har ya juya zai koma lokacin da kunnensa ya jiyo masa muryarta daga cikin ban

ɗ

akin

ɗ

akin wanda ko

farsa bata rufu sosai ba.

"Yanzu duk ba wannan ba Aunty Sadiya, mu fuskanci maganar nan, ina jin kamar zan iya komai don in gyara abubuwa su koma daidai, ba zan yi wahalar banza ba tsawon shekarun nan Aunty Sadiya, na ka

ɗ

e idan har Jawad ko waninsa ya san

cewar ba ni na haife shi ba....!"

****

_Yau na ha

ɗ

e muku lovebirds

ɗ

in mu a Chapter

ɗ

aya..._

🥰😍

_Ina kuke tunanin muna tafiya?_

_Kun san na saba wasa da tunaninku...

😅

_

_Ku shiryawa abinda ke shirin faruwa... Ku shiryawa alkawarin da na da

ɗ

e ina daukar mu

ku..._

_Komai mai sauki ne idan har kun yarda dani._

_ƙullin ba gab! da kwancewa._

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details

0251365383

Wema bank.

Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.

#fikrawriters

#FararWuta.

°°°°°°°°°

*FARAR WUTA 2.*

*©AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*17*

~~~~~~~

_Hope is a waking dream._ _— Aristotl

e_

***

"Yanzu duk ba wannan ba Aunty Sadiya, mu fuskanci maganar nan, ina jin kamar zan iya komai don in gyara abubuwa su k

oma daidai, ba zan yi wahalar banza ba tsawon shekarun nan Aunty Sadiya, na ka

ɗ

e idan har Jawad ko waninsa ya san cewar ba ni na haife shi ba....!"

Haji Mardiyya ta fada tana dafa sink din daje gabanta a cikin ban

ɗ

akin, daga cikin wayar, yayar tata mai sun

a Aunty Sadiyan tace.

"Duk ba za'a kai ga wannan ba insha Allahu, yanzu dai kawai abinda nake so shine kiyi kokari ki samu ki raba shi da yarinyar kawai, idan har ta tafi sauran mai sauki ne.

Kawai lokaci zamu ja sai idan ya takura mu samu wani kauyen mu k

aishi, da mun fan sunna wa wasu a cikin garin yan ku

ɗ

a

ɗ

e sai ya same su a matsayin iyauenta kawai ace masa ta mutu, kinga wannan dole ya hakura ai, komai fa dabara ne Mardiyya, rayuwar mace gabadaya akan dabara take tafiya, idan kika iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login