Showing 87001 words to 90000 words out of 144990 words
ta ina tabbatar mi
ki babu ruwanki da tashin hankali akan abubuwa da yawa, kina daga zaune zaki dinga gyara matsololinki hankali kwance."
Hajiya Mardiyya ta gyada kanta.
"Na dade da haddace wannan karatun naki ai Aunty Sadiya, yanzu na aika a kirawo shi don haka ko yazo ma,
ba zan nuna masa kai tsaye cewa ya rabu da yarinyar ba, kawai zan nuna raina ne ya baci ta yadda ba zai fuskanci komai....."
Kalaman ta suka gutsire a iska sakamakon juyowar da tayi a zacen nata, juyowar da tayi a lokaci guda kuma kai tsaye siffar Jawad ta
shiga idanunta, yana tsaye rike da hannun kofar ban
ɗ
akin, yana tsaye yana kallonta da tarin abubuwan da ba zata iya lissafa su ba a jikin idanunsa, tarin abubuwan da suka sa babu shiri wayar dake hannunta ta zame daga kunnenta ta tarwatse a ƙasa!
***
A c
ikin tangameman
ɗ
akin baccin, Alhaji Bashir ya sauke wayar dake kunnensa daidai lokacin da matarsa ta biyu Hajiya Yagana, kwallin idanunsa kuma shalele duk a cikin matansa uku ke miƙo masa plate din data zuba abincin a ciki tun bayan farawar wayar tasa tsa
won mintuna da suka wuce
Kallon da take masa wani kala ne, wani kala ne da duk sanda ta yin yake zabge shekarunsa da nata a zukatansu gaba
ɗ
aya, lokaci ya ara musu wata dama da a cikinta suke
ɗ
an
ɗ
anar ruwan zumar da baya duba da yaro ko kuma babba.
"Ayi hak
uri mana Shalele, aikin his excellency ne, ni ban isa ince ba zan saurare su a yanzu ba."
Ya fada yana kallonta da murmushi, sai ta turo bakinta ka
ɗ
an alamun ba inda fushin nata yaje kafin tace.
"Kwana biyu ne an shiga hakkina da yawa ranka ya da
ɗ
e, a lala
ce nayi kusan wata ban same ka ba, duk ranar da kwana na yazo sai tafiya ta taso ko kuma wani abu ya faru... Hatta su Amal sun fahimta."
Ya sake yin murmushi mai armashi yana kallonta kafin yace.
"Kar ki damu, wannan duk labari kike bayarwa, yanzu dai ba g
ani ba kuma ga ki? ai zance ya ƙare kuma tsawon kwana ukun nan ni naki ne, ko office ba zan fita ba Yagana, idan ƙasar ma kike son mu bari ki zabi inda zamu je mu kwana biyu sai mu dawo..."
Idanunta suka wulkito tana sake kallonsa yayin da dadi ke ratsawa
har cikin zuciyarta, a duniyar nan bata da wani lissafi da ya wuce a kullum ta samu tarin hanyoyin kuntatawa kishiyoyinta, duk wani abu da zata yi su ji haushi shine kawai alkibilarta, don haka ta gya
ɗ
a kanta tana murmushi sannan tace.
"Garin masoya zamu t
afi Daddy, (Paris) ina son inga hasken fitulun garin nan na haska min fuskar ka a idanuna...."
Dariya da Alhaji Bashir yayi wannan karon mai sauti ce, dariya ce dake fitowa tun daga cikin zuciyarsa, kuma har ya bu
ɗ
e baki zai yi magana lokacin da kararrawar
(doorbell)
ɓ
angaren gaba
ɗ
aya ta
ɗ
auki ƙara, sautin ta ga mamaye ko'ina da amon da zaka san tabbas ba an danna ta ne sau
ɗ
aya ba.
"Waye wannan kuma..."
Hajiya Yagana ta furta tana ƙoƙarin danne zagin da taji ya biyo bakinta. Kuma kafin ta karasa wata karar
ta sake biyo baya, Sai kawai Alhaji Bashir dake gefe yayi murmushi yace.
"Je ki bu
ɗ
e ko waye na gida ne ai."
Kamar ba zata tashi ba, don sai dai ta kirga wasu sakanni zuciyarta na biya tsinuwar dake tafiya ga ko waye a bayan kofar nan kafin tayi kwafar
da ita kadai taji ta ta mike, ta miƙe sanda Alhaji Bashir ke fadin.
"Zan same ku anan falo."
Kafafunta suka dauke ta zuwa cikin falon da shi zaka fara tararwa bayan ka fito daga
ɗ
akin, ta wuce ta isa ga falo na karshe a bangaren sannan ta kama handle din m
akekiyar kofar ta bu
ɗ
e bayan ta murda mukullin, kuma fuskar wanda ke tsaye daga wajen, fuska ce da ta sake bakanta ranta a lokaci guda, tasa zuciyarta matsewa a kirjinta... Wai har yaushe Jawad ya fara shiga rayuwarta ne? A kodayaushe ita mantawa take dash
i ma a lissafin dukkanin ƴaƴan gidan don ko zama a gidan bai cika yi ba, to don me yasa yanzu zai dawo ya saka ta a gaba kuma?
Tayi niyyar gaya masa magana amma sai yanayin fuskarsa ya tsaida ita, don duk da ba wani sanin halinsa tayi sosai ba, ta sani cew
a bata ta
ɓ
a ganinsa a irin yanayin da yake yanzu ba, fuskarsa fayau take yayin da idanunsa ke haskawa da wani abu da bata san meye ba, sai kawai ta saki kofar sannan ta juya ciki ba tare da tace dashi komai ba.
Ta juya daidai lokacin da Alhaji Bashir ke fi
towa, nasa idanunsa shima suka sauka akan Jawad din dake shigowa, yana kallon yadda bai ko cire takalman kafarsa ba, balle ya rufe kofar da ya baro a bayansa.
Kuma ga mamakin Hajiya Yagana, tana juyuwa da niyyar biyo bayansa su dawo cikin falon sai kawai
ya
ɗ
aga mata hannunsa guda.
"Ki shiga ciki Yagana, zan shigo."
Ita kanta ta sani cewa a yanayin Jawad din, babu ta yadda za'ayi ya fa
ɗ
i abinda ya kawo shi a gabanta, bata jin ma ko da gaishe da mahaifin nasa ne zai yi idan har tana wajen, don haka bata ce
komai ba sai kawai ta juya ta koma ciki, kuma ta shiga cikin ba tare da ta rufe ƙofar
ɗ
akin gaba
ɗ
aya ba.
Alhaji Bashir ya ƙaraso cikin falon ya samu waje ya zauna, kuma sai da ya zauna
ɗ
in sannan Jawad ya ƙarasa ƙarasowa cikin shima, ya sami waje a daidai
jikin kujerar dake fuskantarsa ya durkushe har ƙasa kan lallausan carpet
ɗ
in dake shimfi
ɗ
e a wajen.
Alhaji Bashir ya kalli yadda ya zaune a gabansa, idanunsa na cigaba da nazarin fuskarsa, zai kafa hujja da cewar tunda yake bai ta
ɓ
a ganinsa a irin wannan y
anayin ba, don haka sai kawai ya ajiye wayoyinsa da ya fito dasu a gefe sannan ya kira sunansa.
"Jawad, me ya faru?"
Muryarsa ta fito ne a hankali, cikin wani amo irin na manya, irin na manya a lokacin da suka fuskanci wata matsala game da ƴaƴansu ko kuma
duk wani wanda suka san zai iya samun mafita daga gare su.
Sai dai abinda Jawad
ɗ
in ya bu
ɗ
i baki ya fada a wannan lokacin, wani abu ne da ya shallake dukkan tunani da kuma hasashen Alhaji Bashir, wani abu ne da idan za'a tattaro dimbin abubuwan dake kansa
a jera sunya tabbata ba za su taba kaiwa ga magana irin wadda ya fada a wannan lokacin ba...
"Ƴan sanda zasu zo gidan nan, nan da minti ka
ɗ
an Daddy, babu wanda zasu ta
ɓ
a kuma babu wanda zasu kama, kawai so nake ta gansu ta tsorata ta gaya min gaskiya, tace
ni ba
ɗ
anta bane ba ita ta haife ni ba, don haka so nake ta gaya min su waye iyaye na kuma meye asalina... Wannan kawai nake so in sani Daddy!"
***
*Ƙauyen Garun Albasu ( Yakura).*
*12:15Pm.*
Awwalu ya gyara zamansa a gaban motar da suke ciki, motar dake
tafiya cikin wani tsukin lungu na ƙauyen da suka shigo kusan awa gyda da ta wuce, kuma a wannan lokacin suka shafe suna faman tambayar gidan wata mata mai suna Hanne kamar yadda Awwalun yace itace wadda a wancan lokacin ta shaida masa cewar yaron da yake n
ema yana can Abuja, kuma a cikin awa gudar an kaisu ga gidajen mata masu sunan Hanne fiye da goma, kowacce Awwalu yana fadin ba ita bace da zarar ta fito.
Lokacin da suka shigo cikin kauyen kai tsaye ma yace zai iya gane gidan da ya sami matar a wancan lok
acin, amma tun kafin tafiyar tayi nisa, canje-canje da kuma sabbin tsarin da aka samu a koina ya shaida masa cewar abinda ya sani a wadancan shekarun da kuma yanzu daban ne, don haka suka shiga tambaya, tambayar da ta kaisu ga lissafin mutane kusan tara ka
fin a samu wanda ya fa
ɗ
a musu cewa matar ta da
ɗ
e da barin garin amma akwai wata Talatu da zata iya basu labarin inda take.
Tun a hanya Hajiya Salamatu ta sani cewar zai iya yiwuwa matar ta mutu, zai iya yiwuwa su zo su sami labarin wucewar wasu shekaru da
mutuwarta, ace musu ta rasu tare da labarin abinda suka zo nema, abinda shine zai zamo ginshiƙin canjawar rayuwarta da ma ta adadin wasu masu yawa.
Amma bata san me yasa ba a yanzu zuciyarta ke gaya mata cewar bai kamata ta biyewa Awwalu rana tsaka ba, bai
kamata ta yarda da wani daban akan aminyarta da suka shafe tarin shekaru tare ba, wa
ɗ
annan shekarun da a cikinsu baza ta ta
ɓ
a cewa ga rana guda da wani abu ya shiga tsakaninsu ba, kokwanton kawai guda daya ne... idan ta tuna cewa sauran mutanen da take az
abtarwa wanda suma haka zasu bu
ɗ
i baki su ce.
Sannan kuma har yanzu Awwalu bashi da wata shaida, bashi da wata shaida ko guda
ɗ
aya da zata tabbatar mata da dukkan labarinsa, zai iya yiwuwa yazo yayi amfani da ita ne don kawai ya sanarwa kansa mafita, idont
a ya sauka akansa daga gaban motar, shi kansa ba abin yarda bane, shekara nawa ya shafe yana aiki tare da Kilishin, shekaru nawa yayi yana taya ta wajen kuntata rayuwar wasu? Me yasa bai ta
ɓ
a tuba ba sai a yanzu? Shekaru sun fara ja masa amma ko aure bai t
a
ɓ
a tunanin yi ba, bashi da wani mutunci ko kuma wani abu kwakwkwara da rana tsaka kawai zata yarda dashi.
Sai dai idan har bata yarda da Awwalun ba, to tabbas kuwa ba zata yarda cewa Kilishi ba zata iya aikata abinda Awwalun ya fa
ɗ
a ba.
Lungun da suke bi
a yanzu wani
ɗ
an tsuki ne da ba don direban nata yace zai iya bi ba, zata ce su fita su tafi a ƙasa ne, don a yanzun ma dukkan mutane da kuma samarin dake zaune sai da suka mike suka dage bencinan da suke zaune akai don bawa motar waje, idanun kowa na bins
u da kallon rashin sani kamar yadda suke gani a koina duk inda suka tsaya tambaya.
"Wancan kwanar ce, yaron yace kwana ta farko zamu karya."
Awwalu ya fada yana nunawa direban kwanar dake damansu, zuciyarsa fayau take a kirjinsa, yana jin kamar allon kirji
n nasa baya
ɗ
auke da komai, kamar iska ce kawai ke yawo a cikin gangar jikinsa da take fanko, yana jin yadda bugawar zuciyar ke amsawa a cikin kunnuwan shi.
Rayuwarsa gaba
ɗ
aya a yanzu ta ta'allaka ne ga inda zasu je da kuma abinda suka taho nema, nasararsa
da akasinta tana ga irin amsar da zasu tarar ga tambayarsu, idan har bai samu gamsaahshen bayanin da zai tabbatarwa da Hajiya Salamatu ba, bai san me ya kama ba, bashi da wata mafita ko za
ɓ
i illa ya tattara komai nasa ya bar garin Kano zuwa wajen da ya ta
bbata Kilishi ba zata taba riskarsa ba.
Kuma wannan ba shine babbar matsalarsa ba, ya san yana da ilimi da kuma takardun da zai iya neman aiki a koina, kuma ya san yana da yan ku
ɗ
a
ɗ
en da zai iya gina sabuwar rayuwar da zai fara a ko'ina, amma wannan ba shi
ne burinsa ba, ba shine fatansa ba... Bashi da wani jin da
ɗ
in da zai wuce ya ga fa
ɗ
uwar Kilishi, ya ga tarwatsewar ta tare da dukkan mafarkanta, yana so ko sau
ɗ
aya ne Allah ya bashi damar da zai zama sanadin da Kilishi zata
ɗ
an
ɗ
ani ko da rabi ne na irin b
aƙin cikin da ta shafe rayuwarta tana jefa al'umma a ciki.
Bayan sun shiga kwanar, motar ta tsaya a daidai gida mai bunun da akayi musu kwatance, kuma daga Hajiya Salamatun suka fito suna barin direban a ciki, kafafun Awwalu suka ƙarasa da sassarfa ya ƙara
sa wajen wasu samari dake zaune a kofar gidan ya shiga yi musu bayanin abinda suka zo nema.
Akan idon Hajiya Salamatu wani saurayi ya miƙe ya shiga cikin gidan bayan yayi wa Awwalun bayanin cewa zaiyi masa iso da matar da suke nema, tana ganin yadda Awwalu
n ke juyowa yana kallonta daga inda yake tsaye, sai kawai ta juyar da kanta gefe guda ba tare da tace dashi komai ba, sharadi ne sun rifa sun yi sho tun kafin su taho.
Zata yafe masa,ba zata ce komai ba, ba zata ce komai ba,ba zata tona shi a gurin Kilishi
ba, zata barshi yaji da neman hanyar tsira da rayuwarsa,komai zaiwuce kamar bai faru ba, niyyar taimakonta da yayi zata kore duk wani sharri da da zata iya shirya masa, amma idan har akasin hakan ce ta faru, komai ya tabbata zuwa gaskiya... to tabbas zata
nunawa Kilishi wata sabuwar siffar cin amanar da a tsawon rayuwarta kaf! bata taba saninta ba.
Cikin abinda yake kasa da minti biyar, wannan saurayin ya fito yana fa
ɗ
in ance su shiga ciki. Awwalu ya juyo ya sake kallonta alamun ta taho kuma bata ce komai
ba har a lokacin ta gyada masa kai kawai.
Suka nufi ciki inda bayan sun wuce soron bunun ƙatuwar haraba ce irin ta gidajen ƙauye, akwai tarkace mai yawa wanda ya ha
ɗ
a da tarin tirame da kuma wasu abubuwan da baza su lissafu ba, ginin ƙasa ne a ciki na
ɗ
aku
na kala-kala kowanne na fuskantar junansu yayin da wasu suke daga can gefe, mata guda hudu suka tarar a tsakar gidan, uku da hijabi a jikinsu da alamun shigowarsu ce ta sa suka sanya sai kuma wata tsohuwa daje surfe daga can gefe, dukkaninsu suka amsa sal
lamar su.
Wannan saurayin da ya shige gaba shi ya jagorance su har wani daki dake can karshe, kuma tun kafin su shiga suke jin muryar dake ciki na fa
ɗ
in.
"Maraba, maraba... Sannun ku."
Hajiya Salamatu ce ta fara shiga ciki kafin Awwalun ya biyo bayanta,
ɗ
a
kin bashi da girma sosai, akwai gado da kuma wasu kayan tarkace na kwanuka daga gefe, sai daga gaban gadon kuma aka shimfi
ɗ
a wata sabuwar tabarma, matar tana daga gefe sanye da hijabi itama sai washe baki take yi tamkar ta sansu.
"Barkan ku dai, maraba..."
Ta sake fa
ɗ
a bayan sun zauna, Awwalu bai shigo ciki ba don ko takalminsa bai cire ba, tsugunnawa yayi kawai daga ƙofar
ɗ
akin yana amsawa kamar yadda Hajiya Salamatu ke yi.
"Ai Yakubu da ya shigo ya gaya min abinda ke tafe daku, yace bayanin Inna Hanne kuk
a zo nema ko?"
Awwalun yayi saurin gya
ɗ
a kansa da sauri.
"Tabbas, indai itace Hanne, to ita
ɗ
in muka zo nema, wani Malam Tanimu ne ya kwatanta mana nan gidan yace ke ƴarta ce zamu sami bayanin inda take a wajenki."
Matar da har a lokacin basu san sunanta b
a ta gyada kanta sannan tace.
"Tabbas, ai da yake ta jima da barin ƙauyen nan, tayi wani aure ne a can Hayin Shehu, wani kauye dake gabas da nan, hi isa mutane da yawa ta
ɓ
ace musu."
Hajiya Salamatu ta gya
ɗ
a kanta kafin tayi magana, maganar da ta zarce ga
abinda ya kawo su kai tsaye don har yanzu ita bata ga dalilin shigowar su gaba
ɗ
aya da kuma tarbar da matar ke yi musu ba.
"Shi yaron yayi miki bayanin abinda ya kawo mu?"
Sai kuwa ta gyada kanta a lokaci guda da amon muryarta ya canja.
"E, yace nemanta kuk
a zo yi..."
"Ƙauyen Hayin shehun kawai zaki kwatanta mana da kuma gidan wa zamu nema idan har mun je."
Awwalu ya fa
ɗ
a yana katse abinda take shirin fa
ɗ
a. Sai ta girgiza kanta a hankali idanunta na kallonsa, sannan ta fa
ɗ
i kalaman da yake gudu, kalaman da y
ake tserewa, kuma kalamai na ƙarshe da zai iya tunanin ba da ransa akai idan har zai iya tare su daga fitowa daga amon kowanne mutum a duniyar nan.
Kanta ne yayi sama ya koma ƙasa alamun gyadawa sannan sautin muryar tata ya fito fili.
"Haka ne, sai dai Inn
a Hanne ta riga ta rasu shekaru shida da suka wuce!"
***
Ƙ
arfe shida na yamma, Awwalu ya bu
ɗ
e kofar falon gidansa, kuma bai jira komai ba ya shigo har ciki ba tare da ya ko cire takalman kafafunsa ba.
Ya wuce falon ya tafi har cikin
ɗ
akin kwanansa, inda an
sn ma ma bai bata lokaci ba hannunsa ya janyo wani akwatinsa da yake yawan tafiye-tafiye dashi, ya shiga ya ba
ɗ
e drawer
ɗ
akin a gurguje yana kwaso gogaggun kayansa dake nibke a ciki yana jefa su cikin akwatin, kuma sai da ya tabbata ya kwashi fiye da rabi
sannan ya rufe akwatin da ƙyar ya sake jawo wata jaka irin ta matafiya daga ƙasan wardrobe din.
Ya bu
ɗ
e zip
ɗ
in cikinta ya tabbatar da tarin cd's
ɗ
insa dake ciki suna nan sannan ya wawuro wata computer dake ajiye kan bedside
ɗ
in gadon ya cusa ta a ciki ita
ma ya shiga ƙoƙarin rufe zip
ɗ
in.
Wayardmsa da ya cillar akan gadon dakin ta shiga kara tana nuna wata sabuwar lamba, da sauri ya dauko