Showing 3001 words to 6000 words out of 144990 words

Chapter 2 - FARAR WUTA COMPLETE

ga wata hanya da zamu iya neman mutumin nan cikin sauki ba tunda har su Salihu suka kasa, dole irin Yakubun zamu nema tunda

dama shi irin aikinsa kenan, ko ni da kai muka tafi ba lallai muyi abinda shi zai yi ba."

Faruk ya gya

ɗ

a kansa a hankali alamun ya fahimta daidai lokacin da wayarsa tayi kara daga can kan teburin, don haka ya miki yaje ya

ɗ

auka, kuma ganin number data fit

o a jiki yasa shi fadin.

"Excuse me." Sannan ya nufi kofa ya fita.

Kuma hakan ya tunawa da Ma'aruf missed call din Ishaq da ya gani a wayarsa shima har guda biyu, don haka ya jawo wayar ya shiga kokarin kiransa.

"Kana ina Kano ko Jigawa?"

Itace tambayar da

Ishaq din ya fara yi bayan ya dauki wayar, kuma a lokaci guda kalmar Jigawan ta gifta masa da fuskar Amina, wani abu ya fada a zuciyarsa yana tuna masa da cewar rayuwarsa akwai canji a yanzu, a ƙalla duk bayan wannan hargitsin yana da wani waje da zai sam

u nutsuwa.

A dazu lokacin da suna hanya, lokacin da ya sata ta kwafar masa wasu lambobi daga cikin wayarsa zuwa daya wayar, yana tukin yana kallonta, yana kallon yadda ta nutsu sosai tana aikin da ya saka tan,  kuma a wannan lokacin ne ƙwaƙwalwarsa ta fahi

mtar masa cewa irin abinda yake ji a zuciyarsa duk lokacin da yahe asibitin sa na MMB-6 haka yake ji idan yana tare da ita, wani irin bu

ɗ

ewa zuciyarsa take yi yana jin yana manta kowa dama komai sai iya abinda zai iya kawai.

Kuma ya san dalili, saboda ya f

ahimci duk abinda yace kawai shi take yi, duk abinda ya gaya mata shi zata yi ba irin Rulayya bace ita, Rukayya tana da ra'ayi tana da choices da expectations masu tarin yawa, shi yasa ko a lokacin aurensu da ya sa rai cewa zai samu nutsuwa a tare da ita,

sai abubuwa suka canja, suka yi juyin waina don ita kullum cikin tuna masa da abubuwan da ya bari a rayuwarsa ta baya yake yi, abubuwan da yake a Ma'aruf

ɗ

in da ta sanshi dasu wanda baya yi yanzu, shi yasa shi da ita basu taba daidaitawa ba, don yana son b

arin baya ne ita kuma tana jawo shi.

Amma Amina da a yanzu bata san waye shi a baya ba, bata san komai game dashi ba, bata da tunanin komai balle har tasa ran cewa zaiyi abu baiyi ba sai yake jin hankalinsa na kwanciya duk sanda yake tare da ita, zuciyarsa

tana kara amsawa da abinda ya fara ji akanta tunda daga ranar farko da ya ganta.

"Mun dawo

ɗ

azu."

Ya amsawa Ishaq din dake jiran amsarsa a cikin wayar.

"Honeymoon din har ya kare?"

Ba shiri ya zare idonsa.

"Ni na gaya maka abinda ya kaimu kenan?"

"Sai ka

gaya min? Wane sabon labari ne wai baka son tuƙin dare, inaga har Kaduna munje ni da kai bayan isha."

Sai kawai ya koma da baya ya kishingi

ɗ

a da kujerar da yake kai yana guntun murmushi, ya cusa yatsunsa

ɗ

aya cikin gashin kansa.

"To ka gama aibata ni sai k

a gaya min dalilin da yasa naga missed call

ɗ

inka har guda biyu."

Daga cikin wayar Ishaq yayi magana da wani don alama tafiya yake yi kafin yace.

"B kana sane jibi ne zaman shari'ar nan?"

"Yes, na sake duba takardar, na sani."

"Kuma har yanzu kana nan akan

bakan ka ba zaka nemo kowacce irin shaida ba?"

"Eh." Ya tabbatar yana gyada kansa.

"Har yanzu baka gaya min dalilinka ba." Ishaq din ya sake fada a lokacin da yake tura kofar wani waje, don yaji karar da kofar ta bayar a cikin kunnensa kafin ya fara magan

a.

"So nake naga iya abinda zasu yi shi yasa na

ɗ

auki wannan matakin Ishaq, Hamida ƴata ce, idan har zan rike ta it should be in a respectful way, bana son wani yaga cewa nayi amfani da ƙarfi ne na kar

ɓ

e ta har ita Rukayyan kuwa, don idan hakan ta faru was

u abubuwan zasu biyo baya ka sani.

Shi yasa ba zanyi wani yunkuri ba Ishaq, don kamar yadda ka fada ne a yanzu doke shari'ar zata fi karkata ne a

ɓ

angarensu ba. Wannan wasan nasu ne su suka kawo ƙarar nan don haka mu basu filin da zasu taka rawar su ba ta

re da mun

ɓ

ata musu ba, Cox idan na tashi nawa shirin Ishaq, ina tabbatar maka zanyi komai ne ta hanyar da za'a sami fahimta tsakanina da kowa, tunda a yanzu ina gujewa duk wani abu da zai jawo min tashin hankali Ishaq."

Tun daga farkon bayanin, aganganun

ƙ

arshe su suka

ɗ

auki hankalin Ishaq ba duka sauran abinda ya fa

ɗ

a ba.

Kalmai ne ka

ɗ

ai, amma tasirin da suka yi a zuciyar Ishaq suna da yawa, don shi ya san waye Ma'aruf, yana tare dashi tsawon lokaci tun daga shekarun farko na ciwonsa har zuwa yanzu, kuma

a baya babu irin naci da ƙorafin da baiyi ba akan ya dinga duba yanayin ciwonsa kafin ya aikata abubuwa, amma rashin yin hakan shine babban abinda ya kawo su ga matakin ciwonsa na yanzu.

Sai dai ya fahimci cewa tunanin Ma'aruf ya fara canjawa tun daga rana

r da ya farka a London ya gaya masa matakin da ya kai a cutarsa, ya lura ya fara canja abubuwa da yawa a rayuwarsa tun daga wannan lokacin, kuma a yanzu da yayi wannan auren nan, ya ƙara fahimta cewa yana samun nutsuwa tare da yarinyar nan fiye da aurensa

na farko, duk da har yanzu ba zai iya cewa ga takamaimai tunaninsa game da ita ba.

Sun ƙarasa wayar yana yarda da tsarin Ma'aruf

ɗ

in ba wai don zuciyarsa taso ba ko kuma a matsayinsa na lauya hakan ya san hakan daidai ne, sai don ya san cewa kome zai fa

ɗ

a

a wannan lokacin ba zai canja tunanin Ma'aruf din ba.

****

*Karfe biyar da rabi na yamma.*

Ƙ

afafun Amina suka fito daga cikin toilet

ɗ

in

ɗ

akin bayan ta gama yiwa kanta fa

ɗ

a da gargadin wankan yamma, amma babu yadda zata yi ne, don a yinin ranar kaf wannan

shine ka

ɗ

ai lokacin da ta iya samu na yin wankan, wankan da take jin kamar ya zame mata dole ne  don karkade tarin abubuwan dake yawo a cikin kanta, sai dai duk yadda ta kai ga goge jikinta tare da zubar ruwan bata jin ko kalma guda ta fara ko

ɗ

ewa a cikin

dubunnan dake kanta balle tasa ran cewa zasu fita.

Idonta ya kai kan wayar dake yashe a gadon

ɗ

akin, wayar Ma'aruf ce da ya bata a safiyar yau bayan yasa ta debe masa nambobinsa zuwa cikin daya wayar tasa, bai ce ya bata ba har yanzu, amma zuciyarta na ay

yana mata cewa hakan ce zata kasance.

Ta zauna daga gefen gadon ta

ɗ

auko ta, ƙirar Samsung ce kamar sabuwa ma, ta tuna yadda tayi nacin samun wata Samsung kamar ba gobe lokacin da take ganin hotunansu a wayar Aminu, amma yau gata da Samsung

ɗ

in a hannu kil

a ma wadda tagi waccan amma zuciyarta fayau take, babu

ɗ

igon wani abu da zata iya dorarwa akan wayar koma wani abun a gefe.

Ta dawo ta tarar Tvn gidan ma an hada ta, an siyo reciver da komai jiya da basa nan an ha

ɗ

a, Samirah ce ke gaya mata a

ɗ

azu da ta sh

igo kawo mata jakarta da ta manta a

ɓ

angarensu, don a

ɗ

azu bayan fitowarta daga dakin Hajiya Kikishi rike da magungunan nan a hannunta, bata jin jijiyoyin dake cikin kwakwalwarta sunyi aiki mai kyau har ta iso ta dawo bangarensu.

Allah ne kawai ya taimake

ta bata hadu da kowa a hanya ba kasancewar sagiya ce, in banda masu wanki da ta jiyo tarin hayaniyarsu daga can gefe da kuma su Mama Rabi dake shiga bangaren Inna Danejo suna gyara kasancewar yau zata dawo kuma cikin sa'a dukkansu basu kula da ita ba.

"Tar

ko biyu ta

ɗ

ana miki Amina."

Abinda Amma ta fara fada a wayar kenan bayan ta ƙaraso ta kira ta kuma ta gama sauraren dukkan bayaninta.

"Baki fahimce ni ba na sani kamar yadda kika kasa fahimtar hakan tun lokacin da kina gabanta.."

Muryar Amman ta cigaba da

fitowa a lokacin da hatta yawun bakinta ya tsaya cak! saboda ru

ɗ

ani.

"Tace miki a yanzu magungunan sa sun dawo hannunki Amina, amma ta

ɗ

auko sauran  da yake sha ta baki su? Ko kuma shi ta gaya masa cewa zai dinga karbar maganinsa a hannunki?"

Kuma tambaya

r ta wuce da wani shiru mai tambarin nazari kafin ta iya amsawa a a hankali.

"A'a Amma, wadannan din kawai ta bani."

"To kiyi tunanin ki gani Amina, da sunan maganin me zaki dauki waddannan ki bashi kai tssye? Wane bayani zaki yi masa da zai gamshe shi ya

kar

ɓ

a? Idan ma ya kar

ɓ

a

ɗ

in yasha kuma ciwon nasa ya biyo baya me kike tunanin zai faru? Daga shi har sauran jama'ar dake kewayensa me zasu yi tunanin akanki Amina?"

"Kowa zai zarge ni Amma."

Amsar ta fito kai tsaye tun daga zuciyarta, don babu wuya ta zaƙ

ulo ta daga cikin tarin abubuwan dake yawo a cikin kanta, kuma kai tsaye itama Amman ta cigaba.

"Tabbas kowa zai zarge ki Amina, ai babu wani kewaye-kewaye akan hakan. Kilishi mugun ice ce na gaya miki, irinsu ne mutanen da zasu sa ka kashe kanka ba tare d

a ka san kana soka wuƙar ba, kuma na gaya miki tun farko, dole ki maida ƙwaƙwalwar ki ta koma irin tata Amina, dole ki dinga tunani irin wanda take yi idan ba haka ba a kurkusa zata dulmiyar dake ba tare da kin ya fahimta ba.

A yanzu ta baki iya wadannan m

agungunan ne  don ta gwada ki, taga ta yadda zaki cika umarninta kuma ki kare kanki a lokaci guda, taga ta yadda zaki iya bashi magungunan ba tare da kin shafawa kanki jan fenti ba kema. Tunaninki take son ta gwada, taga idan har zurfinsa ya kai ta saka ki

cikin lamuranta, sannan kuma a lokaci guda ta tabbatar idan har da gaske kin goyi bayanta kamr yadda kika ce, kuma ina tabbatar miki Amina, idan kika fadi ko guda daya a cikin wadannan tarkon nata biyu, shikennan kin fara rusa darajarki a wajenta.

Ba zata

kore ki a lokaci guda ba, amma zata dauki wani mstakin kwatankwacin yadda tayi wa Aminu don ta ƙara tsorata ki, sannan zata ƙara gwada ki, idan akayi rashin sa'a a karo na biyu kika sake faduwa shima, zata juyo kanki ne a lokacin, zata lahanta ki ta yadda

zaki ji a jikinki ki san da gaske take sannan ta sake gwada ki...."

Muryarta ta

ɗ

an tsaya kafin ta cigaba.

"... a karo na karshe ne Amina, idan ta sake baki wani abin kika kasa, ina tabbatar miki da cewar Kilishi zata iya rufe kawar dake gabadaya!"

A wann

an lokacin Amina taji sanda zuciyarta ta buga a kirjinta kafin fatar bakinta ta shiga maimaita kalaman hasbunallahu wa ni'imal walkil da fatar babu tsayawa, kuma sai da Amman ta tabbatar kalaman sun gama shigewa cikin kanta wucewar wasu sakanni sannan ta c

igaba.

"Amina, wannan abin da nake gaya miki gaskiya ne, don mutane irin Kilishi suna aikata abinda yafi haka ba tare da sunji ko

ɗ

ar! a ransu ba, shi yasa nake son tun a yanzu ki tattara hankalinki waje guda ki saurare ni, kiyi duk abinda nace, ki yarda d

a maganata ta cewar da kifi ake kama kifi, kin fahince ni ko?"

Ta san ta

ɗ

aga kanta a lokacin kamar Amman na kallonta, amma bayan hakan ba zata iya tantance yadda zuciyarta ta dinga tsere a ƙirjinta ba, ta san kawai ta damƙe wata kwalbar turare dake gefent

a a lokacin don tattara dukkan nutsuwarta, kuma bata san ya akayi hakan yayi tasiri ba, don tayi nasarar ture  dukkan hargitsin daje cikin kanta ta cigaba da sauraren mahaifiyar tata.

"Ki narka magungunan a cikin lemo Amina ki bashi yasha ba tare da ya san

i ba, ki kwantar dashi kamar yadda ta gaya miki ba tare da shi kansa ya sani ba Amina, ki nunawa Kilishi da gaske kike kin goyi bayanta, ki bu

ɗ

e mata zuciyarki ta yadda zata sakanksnce ta kar

ɓ

i yardarki, ki nuna mata zaki iya, zata ga hikimarki, zata jinji

na miki, kuma zata jawo ki jikinta. Wannan shine matakin farko da zamu fara cin nasara akanta Amina."

Ta sani cewa ta yarda da dukkan maganganun mahaifitar tata, ta san haka ne, ta san gaskiya ne... Ta san wannan itace sahihiyar mafitarsu, amma zata iya? 

Zata iya? Idanun Ma'aruf kawai idan ta hango sai zuciyarta ta ƙara nanata mata cewar ba zata iya ba, ba zata iya ƙarawa akan wahalar da yake sha yanzu a rayuwarsa ba, idanunsa kadai idan ta kalla tana jin kamar zata iya tsinto tarin abubuwan dake damunsa

ɗ

aya bayan

ɗ

aya, yana yawo dasu a kirjinsa da kuma kafa

ɗ

arsa.

To ta yaya kuma zata iya zama karin wata matsalar bayan duk bayanin da yayi mata jiya cewa yana son samun sauƙi a wajenta? Bayan haka ma idan tana tare dashi ta lura cewa ƙwaƙwalwar ta bata iya t

una duk wannan hargitsin sosai mantawa take da komai kawai sai shi da ka nasa maganganun.

Wani abu ya wuce ta makogwaronta da ba ta san meye ba, taji hannayenta da ta rike wayar dasu duka biyun suna rawa, sai kawai ta ajiye ta a gefe sannan ta mike, man da

take shafawa tun zuwanta gidan ta dauko akan mudubi, har zata bude sai kuma ta tsaya tunanin anya ba fari yake sata ba kuwa, don ita kanta taga ta canja kwana niyu sannan ma Aminu yana ta tsokanarta cewa tayi haske, kuma ta san wannan ba sharrinsa bane.

D

on haka ta shiga duba jikin robar kuma gaba

ɗ

aya babu inda aka rubuta hakan sai ma wasu abubuwa dake shaida mata tsadarsa, har yaushe zata dinga tunawa ne cewa masu kudi ta aura? Don tabbas a cikin wannan auren nata mazajen biyu ne, Kilishi da Ma'aruf sanna

n matan ma biyu ne ita da Amma, kuma kowa da irin rawar da yake takawa.

Sai kawai ta cije lebbenta da murmushi tana tuno kalaman Hajiya Kilishin na ƙarshe kuma mafiya tasirin da suka fi zama a zuciyarta.

_Ba zan hana iya Ma'aruf kula ki ba idan har yayi ni

yya, amma ba zan dauki wani abu wai shi ciki ba...!_

Bata shaidawa Amma wannan zancen ba don ta yarda daga Kilishin har Amman wannan ba huruminsu bane, wannan yaƙinta ne kamar yadda Amma ta gaya mata, kuma ta yarda ba komai Amman zata iya mata ba, don kama

r yadda ta fada mata ne ita hanya kawai take nuna mata amma duk wani taimako da zata yiwa kanta yana hannunta, dole ne sai ta tsaya da kafarta ta fuskanci nata yakin, don haka ba zata dorawa Amma wannan nauyin ba.

Kuma Hajiya Kilishi bata isa ta yanke irin

wannan kaddarar tata ba, wannan huruminta ne, hakkinta ne, idan ta yarda da Ma'aruf, bata jin akwai wani mutum kuma a gefe da zai gaya mata yadda zata yi da jikinta ko ma abinda zai zama rayuwarsu a gaba.

Wani murmushin ne ya sake subucewa a bakinta da wa

nnan tunanin, wai rayuwarsu? Ma'aruf din da har yanzu bata dan me take ji game dashi ba, ta san dai kawai zuciyarta ta narke jiya da tayi bacci a cikin hannunsa, kuma bata gama bushewa ba sanda ya sake rungume ta a yau, amma a cikin wannan gulbin

zata tsin

to cewa tana tsananin ganin kwarjini da kuma girmansa, watakila shi yasa take manta komai idan yana gabanta.

Wata doguwar riga ta

ɗ

auko (flowy and Maxi) kalarta fara ce, a jikinta anyi mata prints

ɗ

in lilac flower kalar Pink da kuma Pitch, hannunta ya bude

har zuwa rabin nata hannun, kalarta tayi kyau sosai da kuma

ɗ

aukan hankali, amma ita ba wannan yasa ta dauko ta ba, rashin nauyin ta ne tasa ta zabo ta don shafal take sosai, tana daga cikin kayan da Aunty Safiyya ta bata, kuma ko sanda ta bata

ɗ

in sai da

su Aunty Ma'u suka yi ta

ɗ

aga ta suna fadin laushi da kuma rashin nauyinta.

Don haka abinda ta tuna kenan a yanzu ta lalubo ta, don tare da nauyin dake zuciyarta dama cikin kanta bata jin zata iya da wata atamfa ko makamancin hakan. Tana da mayafi shi far

i ne gabadaya, ta sake taje gashinta ta daure shi sannan ta daura mayafin akanta.

Hannayenta har yanzu rawa suke, amma ta san tunda basu yi komai ba tun sanda tana girkin da tayi da kyar a cikin tarin tunaninta, to yanzu ma babu abinda zai same su.

Bata ko

saka slippers din da take yawo dashi a cikin gidan ba ta fita daga

ɗ

akin, sanyin tiles din gidan na ratsa fatar ta har ta isa falo, idonta ya kai kan ƴar jar fitilar Tv da ta kama tana tuna mata cewa zata iya kunnawa a yanzu, amma bata hango kallon ko a ƙ

arshen lissafinta na yau, don haka ta juya Kitchen don karasa abinda ke gabanta.

_....ina son

ɗ

anwake ma._

Shine abinda ya gaya mata jiya a cikin abincin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login