Showing 123001 words to 126000 words out of 144990 words
da wani bata lokaci ba, amma shi ya sani halin da ya shiga da kuma wuyar da ya sha a iya wannan
ɗ
an tsukin, idan za'a rarraba ta a zuciyar wani zai
ɗ
auki watanni kafin ya iya kai ƙar
shensa.
Shi kadai ya san abinda yaji shi kuma shi kadai ya san abinda ya fuskanta a cikin zuciyarsa da ma jikinsa, sannan ga tasirin dukkan abinda ya faru jiya, na yadda ya samu abinda baiyi zato ba bayan sun bashi tabbacin da shi kansa ba zai iya musantaw
a ba. kusan hotuna goma Hajiya Kilishi ta dauko masa na mahaifin nasa da takira da sunan Ibrahim Shanawa, kuma tun a hoton farko yaga kamar ya san fuskar kamar ya gane shi duk da cewa suna ta zuzuta kammaninsa dashi.
Sai da ya fara yi mata bayanin inda ya
taso sannan komai ya fito fili, wani ikon Allah da kuma wata sabuwar isharar ta fahimtar dashi cewa a tsawon rayuwar da yake tunanin ya shafe a hannun wasu mutane, ashe ba wasu bane, a cikin danginsa yake, a tsakiyarsu ma tunda tun kafin hawan Alhaji Bashi
r matsayin minista gidansa yake a matsayin centre guda ta family dinsu, kusan kowa yazo zai samu wajen zama babu takura, shi yasa a yanzu da yake matsayin ministan ƴan aikin dake tafiyar da al'amarin gidan su kansu wajensu daban.
Bai kira kowa ba, bai kira
su Hajiya Mardiyya ko kuma wani a gidan ba har yanzu, yafi son sai ya gama tara hankalinsa waje guda tukunna, yafi son sai ya saita iya abinda ke gabansa a yanzu, don ya sani gaggawa ba zata haifar masa da komai ba.
Ya ajiye wayar hannunsa a gefen gadon d
akin sannan ya nufi ƙofar toilet ya bu
ɗ
e... wanka yake so yayi ya canja kayan jikinsa shi yasa yake ta jinkirtawa don ta gaya masa cewa zata sa a kawo masa wasu, hoton fuskar Zainab ya gifta a ransa a lokacin, ba sau daya ba ba sau biyu ba tasha wanke masa
toilet, ta haka ya fara gane ta, ta haka ya fara gane cewa an canja masa mai gyara masa daki kafin ma ya fahimci wacece ita.
Ya cije lebbensa kadan yana ƙoƙarin tuno
ɗ
aya zagayen halin da yake ciki, sai dai hakan baiyi nisa ba lokacin da aka kwankwasa kof
ar
ɗ
akin, sai ya saki ta toilet
ɗ
in da yake riƙe da ita sannan ya matsa gaba ya bu
ɗ
e.
Wata yarinya ce, tun safe ya ganta a gidan bayan ya tashi daga bacci, don bayan an kawo masa breakfast ma ta zo daga baya ta kawo masa lemo da kuma Pringles tace ya kara,
bai ma san wacece ita ba, bai san matsayinta ba,yaji dai kawai suna koran sunanta da Ameera.
Bakinta ya tale da murmushin da yayi daidai a fuskarta.
"Yaya J, hope dai ban katse ka kana wani abun ba?"
Ya zura wayarsa dake hannu a aljihu sannan ya girgiza k
ansa yana kallonta.
"Kar ki damu I'm fine."
Sai ta sake wani murmushin sannan ta gyada kanta.
"Toh Alhmdlilah... Kaya ne Aunty tace in kawo maka."
Ta fada tana nuna ledar hannunta da yatsanta daya mai dauke da wani zobe dake kyalli a cikin fitilar wajen.
"
Nagode." Ya fada yana mika hannunsa fon ƙarba amma bata miko din ba sai tace.
"Can I choose a colour for u? Wanda zaka sa yanzu?" (Zan iya za
ɓ
ar maka kala?)
Jawad ya ƙara kallonta, zuciyarsa na kokarin gaya masa wani abu da ba shine ransa ba yanzu, sai kaw
ai ya sake miƙe hannunsa yace.
"Kar ki damu zan
ɗ
auki duk wanda yake a sama ne kawai."
Yayi zaton zai ga canji a fuskarta, amma sai jawai ta ƙara yin murmushi mai fadi tace.
"Shikenan, muna jiranka."
Da haka ta miƙa masa kayan sannan ta tsaya tana cigaba d
a kallonsa da murmushin a fuskarta ba tare da ta juya ba. Wani abu da ya ratsa zuciyarsa kenan yasa duk yadda ya kai ga jinsa wani iri sai da wani guntun murmushin ya sauka a lebbensa.
"Nagode."
Ya fa
ɗ
a yana rufe ƙofar, ta ka
ɗ
a masa yatsu biyu a gefen fusk
arta tana cigaba da murmushin kafin ya rufe ƙofar a fuskarta.
Ya rufe kofar daidai lokacin da wayarsa dake cikin aljihu ta shiga kara, hannunsa ya jawo ta da sauri ya duba, sunan Nura ya baiya na tar a jiki don haka ba shiri ya daga ya kara a kunnensa tare
da sallama.
Daga cikin wayar Nuran ya amsa da sautin muryar da ya sanya zuciyarsa tsalle tun kafin Nuran ya kai ga fa
ɗ
in abinda ke bakinsa.
"Yallabai an samu matsala, wallahi yau da safe da muka tashi ba mu ga yarinyar nan ba, tun safe ake nemanta har yan
zu babu labari....!"
***
_A cikin shafi biyu masu zuwa a gaba, labarin Farar wuta zai kai ga tsayawa insha Allah..._
_Nagode da tarin haƙurin ku, Allah ya sani na fiku damuwa ganin yadda lokaci ke ta jan mu, da kuma yadda nake ta yawo da nauyi a ka._
Litta
fin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
°°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*24*
_There are no happy endings, endings are the saddest part, so just give me a happy middle and a very happy start..._
~~~~~~
"Sai gyada Hajiya, sai gyada ci ko tsaraba.."
Wata yarinya dake
ɗ
auke da bokitin tallan gyadanta ta fa
ɗ
a tsaye daga bakin wata hayis
dake dauke da fasonjoji wanda mafi akasarinsu mata ne dsuke da yara da kuma wasu a goye, banda hayaniyar cikin tashar akwai ta cikin motar ma da baka jin komai sai sautin muryoyin matan kawai dake ta kacaniya suna kuma ciye-ciyensu kala-kala.
Wani dattijo
ya taso ya tsaya daga bakin ƙofar hannunsa riƙe da littafi zai fara kar
ɓ
ar ku
ɗ
in mota da kuma rubuta sunaye, wata mata dake
ɗ
urawa yaronta wani farin kunu a leda tace.
"Motar fa bata cika ba..."
Ya gyada kansa.
"Na sani ai Hajiya ba saura mutum
ɗ
aya ba,
kowa ya fito da ku
ɗ
in motarsa... Ke ya sunanki?"
Ya fa
ɗ
a yana ƙoƙarin rubuta sunan mace ta farko dake bakin ƙofar yayin da kowa a motar ya shiga ƙoƙarin binciko ku
ɗ
i daga jakarsa, mutumin ya gama rubuta sunan ya dago da kansa daidai lokacin da idonsa ya sa
uka akan wata yarinya da ta karaso jikin motar sanye da wani farin hijabi dogo.
"Ƴan mata ina zaki je? Jaji ko kuma Kawo?"
"Sameru zanje..." Muryarta ta fa
ɗ
a kusan a shake sautin na fitowa a hankali, sai ya girgiza kansa.
"Ga motocin Sameru can a wancan la
yin... Kudinki dari takwas ne, amma zan miki ragi, kawo dari bakwai a rubuta sunanki tun daga nan kafin mu isa."
Zainab dake tsaye tana kallonsa ta ha
ɗ
iye a wani abu a makogwaronta kafin ta girgiza kanta a hankali.
"Bani da kudi malam, dan Allah..."
"Baki
da kudi?"
Ya tambaya sautin muryarsa na juyewa zuwa wani abu kamar izgili.
"To rawa zaki yi su kai ki Samerun ko kuma ya za'ayi?"
"Haba bawan Allah, kace mata babu mota kawai mana, sai ka bi ta da bakar magana."
Wannan matar ta fa
ɗ
a daga cikin motar, vai s
aurari daya daga cikinsu ba ya juya kawai ya cigaba da neman sunayen mutanen dake cikin motar.
Wani abu ya sake wucewa ta makogwaron Zainab a lokaci guda da ta shiga murza yatsun hannunta daga cikin hijabin, ƙwalla ta sake cika idanunta a lokaci guda, kafa
funta sun gaji, tayi tafiya mai nisa kafin ta kawo tashar, tayi tafiya tun daga cikin kauyensu inda ta fito ta baya har zuwa wannan ƙauyen dake gabansu inda anan babbar tashar da ake samun mota zuwa ƙauyuka daban -daban a wannan hanyar take.
Kuma bayan iso
warta kai tsaye aka nuna mata wajen da ake hawa motocin inda take son zuwa, Sameru... Ƙauyen da ƴan uwan mahaifiyarta suke... Wajen da ta san cewa duk duniya bata da inda yafi shi a yanzu, babu wani waje ko kuma wani masaukin da wani zai bata da matsayinsa
a idanun al'umma dama nata gaba
ɗ
aya zai kai can.
Hadiza, wata yarinya da tayi kusan sa'arta a cikin gidan mijin nahaifiyarta da ta baro ita ke shaida mata dukkan abinda ya faru a lokacin rasuwar mahaifiyar tata, yadda yan uwansu kowa da kowa ya hallara a
gidan da kuma tarin rigimar da aka sha da mijin mahsifiyar tata skan aikin da tmya tura ta.
Wani abu da lokacin da tana Abuja babu abinda take tunawa kamar hakan, yadda yanuwan mahaifiyar tata suka yi iya kokarinsu wajen ganin ta basu ita sun rike a lokaci
n da zata yi aure, amma ta ƙi haksn,tace ta san zsi tike ta da amana kamar mahaifinta tunda amininsa ne, sannan ta kafa hujjar cewa duk duniya ita kadai take da ita a matsayin ƴa kuma bata tunanin sake samun wata haihuwar a yanzu duba da shekarunta, don ha
ka babu yadda suka iya suka bar ta a wajenta.
Kuna tun daga farko zaman gidan baiyi dadi ba sam! Sun sha wahalar da duk da karancin tunaninta tasha lissafa musu mafita ta hanyar mahaifiyar tata ta rabu dashi, amma bata yi hakan ba har karayar arziki tazo t
a same shi inda babu bata lokaci ya shiga tura ƴaƴan sa aikatau, wanda daga baya ya hada har da ita da tarin hujjojin da mahaifiyar tata bata iya ƙarewa ba.
Tana tuna ranar da ta tafi, ranar da ta tafi ta barta, tana tsaye daga kofar dakinta tans share haw
aye da bakin zaninta, kwana suka yi tana bata hakuri da kuma shawarwarin da zata kare kanta yayin da itama ta shafe daren tana saƙe-saƙe cike da tunanin haƙuri irin na mahaifiyar tata da kuma taraddadin inda zata je da abinda zata tarar.
Ashe dukkan tarin
abinda zata tarar din bai kai wanda zata dawo kuma ta iske ba, ƙofar dakin mahaifiyarta a ƙulle da wani ƙaton jwado a daidai lokacin da ta taka kafarta cikin tsakar gidan, da kuma idanun mutanen gidan da yadda suke kallonta da mamaki da kuma wani abu da ba
ta iya fassara shi ba sai a lokacin da mutumin nan yake gaya mata cewa babu mahaifiyarta...
Ta rasu, babu ita a duniyar nan, ta rasu sati biyu da suka wuce... Ta rasu babu wanda ya gaya mata, babu wanda yabi ta inda aka tura ta ya gaya mata. Mahaifiyarta i
ta kadai take da ita a duniya, guda daya ce babu wata... Amma ta rasa ta babu wanda ya iya zuwa ya gaya mata sai da ƙaddara ta dawo da ita da ƙafafunta sannan ta samu labari, fuskar Jawad ta haska cikin idanunta a sannan, lokacin da ya riko hannunta kafin
ta kai ga fita daga motar ya gaya mata cewa yana jiranta, zai jira ta a wajen har ta gama abinda zata yi ta dawo...
_"Ba zan iya tafiya babu ke ba, amma nayi alkawarin zan dawo dake insha Allah Zainab..._
Haka ya fa
ɗ
a da sautin muryarsa da duk da ba ta shi
take yi a lokacin ba sai da ya ratsa har cikin zuciyarta, bata san me suka fito nema a lokacin ba, bata san me ya kawo shi har cikin garinsu ba, amma zata kiyasta cewa yana cikin kwatankwacin matsalarta ne a lokacin, ko ma wadda tafi tata.
Kuma ta tabbata
abinda ke gabansa shi yasa shi barinta a lokacin, idan ba haka ba ta sani,ta san Jawad ta fahimci galinsa a dan kankanin lokacin da ta sanshi, baya fadin abu sai idan har da gaske yake kuma ya tabbatar dashi har cikin zuciyarsa don idan ya fada
ɗ
in, to ba
bu wani kuma a duniya da ya isa ya canja ra'ayinsa, ko a bakin Hajiya Mardiyya tasha jin tana bawa kannensa hakuri akan su hakura da wani abu, tace ko ita tsoro sa take yi idan ransa ya baci.
"Malama idan baki da kudi gwara ki koma gida, alkur'anin Allah b
abu wanda zai dauke ki har Sameru kyauta a wannan tashar..."
Wannan mutumin ya sske fada a lokacin da ya gama rubuta sunaye ya shiga ha
ɗ
a kan yan canjin da aka tattara masa, a lokacin kuma wani mutumi ya ƙaraso ya biya nasa kudin aka gama cika mitar,direba
n ya zagayo ya karbi kudinsa ya cire kamashon tasha sannan ya shiga ya tada motar.
Sai kafafunta suka matsa daga wajen ta koma gefe, gefe kusa da wasu kanti da kuma rumfuna ta tsaya, tana kallo motar ta juya ta fita ta nufi hanyar fita, idonta ya koma kan
jerin motocin da akace mata sune ke nufar garin da take son zuwa, mutane na ta hada-hada a wajen ana lodi da kuma jera kaya yayin da masu karbar kudi ke yi.
Bata da ko sisi, bata ma san inda zata same su ba, amma alƙawari ne ta yiwa kanta cewa ba zata sake
komawa cikin Yakura a yanzu ba, watakila watarana zata dawo ko don ziyartar kabarin mahaifiyarta, amma a yanzu ta yarda cewa babu abinda zao sake maida kafafuwanta wannan gidan.
Tunanin Jawad ya sake haskawa a cikin kanta,ta san zai dawo zai neme ta, amma
rashin samun nata da zaiyi bai dame tasosai akan tunanin samawa kanta ƴanci da take son yi ba.
_"Babu abinda zanyi miki Zainab, wallahi babu abinda zanyi miki, I just want to feel you close to me... So nake kawai in dinga jinki a kusa dani. Shi yasa na ta
mbayeki idan zaki aure ni saboda zan je har wajen iyayenki ne in nemi aurenki, babu ruwana idan ma akwai wanda suka tsara zasu baki Zainab, ko shari'a zan iya yi da kowa idan akace za'a hana ni aurenki..."_
Abinda ya fada mata kenan da yabayin fuskarsa dak
e tabbatar mata da kowacce kalma da yake fada a lokacin, don haka ta yarda idan har da gske yana son ta, zai nemo ta a duk ind take tunda ta san va zata yi nisan da hakan zai gagare shi ba.
Tana yawan son korewa kanta nauyi a kodayaushe, ta yarda babu wan
i ingantaccen abu da rauni ke samawa mutum a duniyar nan, don haka ba zata bari rauninta ya rinjaye ta wajen zama jiran Jawd ba, idan har ta mike da kafafunta, ta tafi wajen da zai tabbatar da darajarta tun kafin yazo da ma bayan yazo din, abubuwa zasu can
ja daga kalar yadda suke tafiya a baya, shi kansa zai san cewa bai same ta ne a wani hali na rashin gata da madafa ba.
"Har yanzu kina nan?"
Mutumin nan ya fada bayan ya dawo zai wuce, hannunsa babu littafin nan a yanzu. Ya ja ya tsaya a gabanta sannan ya
gyada kai.
"Lallai da gaske kike, hala mutuwa akayi muku a can din ko?"
Kalmar mutuwa ta sake dawo mata da zagayen halin da take ciki, sai kawai idanunta suka ciko da kwalla sannan t ja hancinta kadan kafin ta gyada kanta. Sai shima ya girgiza nasa kan.
"A
llah ya jikan musulmi, ai kuwa kya so tafiya... Kuma zan taimake ki tunda haka ne."
Ba shiri ta dago ta kalle shi da idanunta da har a lokacin suke rine da kuka, ya sake gyada masa kana alamun ya tabvatar da hakan.
"Akwai shugabanmu anan wajen, wallahi ba
wani abu zai yi miki ba, kawai dai taimakon juna zaku yi ki sami abinda kike so, ke fiye da hakan ma zai baki a yau din nan, babu wanda zai sani kuma babu wanda zai ganki."
Wani abu ya doka a kirjinta da jin hakam,don tsaf ta fahimci inda zancen nasa ya do
sa, ta zare idanunsa akanta tana kallonsa cike da tashin hankalin da shi bai fahimta ba ya cigaba da cewa.
"Kuma walkahi ma ni a duk wadanda nake kai masa babu irinki, duk yan kauyen nan ne dake kawo tallan kaya cikin tashar nan, to suma baki fa abinda su
ke samu ba balle kuma ke... Ai ina gaya miki sa'ar da zaki raka yau..."
"Kayi hakuri Malam, amma ba zsn iya abinda kake nufi ba."
Muryarta ta fito a hankali tana katsse shi, kuma dukda hayaniyar cikin tashar yaji abinda ta fada da yake hankalinsa na kanta
.
Zainab ta juya zuwa batanta inda wajen yake da rumfa daga gefen wani shagon container ta cire takalmanta ta zauna tana jin yadda hakoran bakinta suka kasa tsayawa waje guda sakamakon kukan da yake shirin kubce mata tana danne shi, mutumin ya kalle ta dag
a inda yake tsaye, takaicin asarar kudin da yake hangen zai samu a wajen shugaban nasa na bi ta kan zuciyarsa.
Har zai juya yaji ba zai iya dannewa ba, don ba karya yayi mata ba, shi dai ta hanyarsa ya sani cewa bai taba kaiwa Alhajin wata mace kamar ta ba
, fatarta kadai wata kala ce dake tsakanin fari da kuma ruwan ƙasa, wata kala mai
ɗ
auke da kuma daukar hankali, bata da shahararren kyan da a lokaci guda zaka gane shi, amma ƙirar jikinta ka
ɗ
ai da yake gani tun daga cikin hijabin, ya sani ba kowacce mace
take haka ba.
Don haka a lokaci guda ya canja shawara, shawarar daya san tunaninta ba zai iya kufce masa ba.
Bai sake cewa komsi ba ya juya ya tafi kuma sai a lokacin ƙwallar dake tare a idanun Zainab ta ganganro kan kumatunta, bata taba yiwa kanta wannan
fatan ba, bata taba fatan za'ayi ranar da zata zubar da mutuncinta don biyan wata bukatar ba... Zata gwammace ta koma inda ta fito da tayi wani abu makamancin hakan, a hankali ta