Showing 6001 words to 9000 words out of 144990 words
yafi so, shikenan sai ya zama saukinta itama, Samirah kawai ta kira a waya tace a taimaka mata da k
anwa da kuka, nan da nan kuwa ta gama abinta, dama tana da yaji mai da
ɗ
i da Samiran ta kawo mata tun kwanaki, ta yanka vegetables a gefe guda don bata sani ba ko yana so, sannan ta hada haddadden zo
ɓ
onta da ta kusan shanye rabi kafin ta zuba a jug.
Yanzu m
a fridge ta bu
ɗ
e ta sake debo shi a kofi da niyyar ta koma
ɗ
aki ta fito da kayan da ta tara na wanki kafin magriba tayi, kuma ta fito daga kitchen
ɗ
in daidai lokacin da taji ƙarar ƙwanƙwasa kofar gidan, ƙara guda uku da yatsa daya, don haka ta riga ta san
ye duk kuwa da cewar bata ji karar bude gate ba.
Sai kawai ta ajiye kofin hannunta a gefe Tv wata zuciyar ta gaya mata cewar ta kwance mayafin ta yafa shi amma wata zuciyar ta kore hakan kai tsaye.
****
Da wuri ya bar Office yau, don yana yin sallar La'asa
r ya fito tunda sun riga sun gama dukkan abinda zasu yi na yau, dawowar Baffa a gobe kawai ake jira a gabatar masa da komai kafin su fara fuskantar wasu sababbin ayyukan.
Kuma bayan shigowarsa gida kai tsaye ciki ya nufa, yayi minti goma da kyar a
ɓ
angaren
Hajiya Maimuna kafin ya fito ya nufi inda yafi wayo, a falo ya kuwa tadda Mamin ita kadai tana zaune tana
waya da wani faffadan murmushi a fuskarta, kuma har ya zauna bata gama ba sai dai ya lura bata ƙara cewa komai ba bayan sauraren da take yi.
Ta ajiy
e wayar yana tsokanarta cewa Allah yasa kwangila ta samo musu kafin su gaisa, sunyi hirar shari'ar Hamida dake shirin faruwa a jibi inda ta dage akan cewar kar ya yarda ya mayar musu da ita gwara ya dawo da ita wajensa kamar yadda ta jaddada masa tun farko
, kuma haka kurum sai ya samu kansa da amsa mata kawai ba tare da ya baiyana mata irin tsarin da yayi ba.
Daga nan suka shiga hirar wani sabon gidan gona da take son bu
ɗ
ewa, tana cewa zata
ɗ
ora shi a matsayin manajan wajen yana roƙonta ta taimaka ta rufa
masa asiri abubuwan dake gabansa sun ishe shi.
"Mami Slides
ɗ
ina ne zasu ha
ɗ
e dana kaji, sai nazo ina presentation a meeting kawai in bu
ɗ
e kaji suna cin abinci. Baffa will sack me for days."
Dariyar da take ƙyalƙyale da ita, dariya ce dake fitowa tun daga
ƙ
asan zuciyarta, kuma shi kansa ya sani cewa ko tare da Baffa bata irin wannan nishadin balle kuma duk wani wanda zai biyo bayansa, shi daban ne a lissafinta ba sai ya rantse ba ya sani, ya san Mami na kaunarsa da dukkan irin ƙaunar da uwa ke yiwa
ɗ
anta, w
ani abu na gaya masa cewa zuciyarta tana yin fiffike ne ta tashi sama ta zagaya a duk lokacin da yake zaune a gabanta irin haka, shi yasa a kullum yake addu'ar Allah ya bashi ikon faranta mata a tsawon rayuwar da zaiyi.
Ya baro cikin gidan da wannan farin
cikin a zuciyarsa ya iso bangarensu, kuma har zai bu
ɗ
e ƙofar da mukullin dake jikin na motarsa, sai kuma ya fasa kawai ya kwankwasa, sau daya biyu, uku yayin da yake tsaye dab da ƙofar hannayensa harde a kirjinsa. Kuma ba'a wani jima ba, aka mur
ɗ
a handle d
in a hankali sannan jikin ƙofar yayi baya.
Ba shiri Ma'aruf yaji wani murmushi ya sauka a lebbensa, don duk yadda zuciyarsa ke hassaso masa yadda zai dawo ya ganta, a yanzu ta wuce hakan, a lokaci guda kalolin rigarta dama yadda ta rigar ta zauna a jikinta
suka
ɗ
auki hankalinsa, yaji wani abu ya motsa a cikin kirjinsa, sai kawai ya cije lebbensa yana murnushin kafin yace.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaikum salam."
Ta amsa a hankali tana sakin hannun ƙofar, ƙafarta tayi taku biyu zuwa ciki amma sai ya cigaba da
tsaiwa bai shigo ba, kuma har tana kokarin juya ciki jikinta ya bata cewa a tsaye yake don haka ta juyo ta sake kallonsa, yana tsaye a yadda yake, ya harde hannuwansa a ƙirji yayin da wayoyinsa da kuma muƙullin motar da ya rike ya fito ta kowanne gefe, ma
maki ya nuna akan fuskarta don haka ta dawo ta tsaya kuma kafin tayi magana sai kawai yace.
"I'm sorry, ina neman wata ne mai suna Amina, ance min anan take, zaki ganta wata ƴar ƙarama haka tana da idanu masu kyau, kuma ta iya murmushi."
Ba shiri murmushin
ya su
ɓ
uce a bakin Amina, murmushi da ya fito tun daga zuciyarta saboda da gaske ya bata dariya, yadda yayi da fuskarsa idan tare da wani ne zai rantse cewa da gaske kwantancen yake yi, kuma haka kurum sai taji wani abu a cikin ranta yana wucewa, don haka
ta girgiza kanta a hankali tace.
"Bana jin na santa."
"Saboda me?" Muryarsa ta fito tare da godiyar biye masan da tayi.
"Saboda ni ka
ɗ
ai ce Amina anan, kuma ni duk ban kai yadda ka fada ba."
Ta sake fa
ɗ
a a hankali tana murza yatsunta. Ya kalli yatsun nata
sannan yace.
"Zaki yi mamaki idan nace miki a yanzu kinfi ƙarfin kwatance na ma, you look stunning Masha Allah."
Amon muryarsa na fitowa da zurfi.
Murmushin ta ya ƙaru a lokacin da take kallonsa har yanzu da mamaki a fuskar ta, sai kuma yayi saurin girgiz
a kansa kamar ya tuna wani abu sannan yace.
"I'm really sorry na manta ban tambaye ki ba idan Aminar da nake nema matar aure ce, kar in kwana a inda ban shirya ba."
Murmushin ta ya sake karuwa kafin ta
ɗ
aga kanta sau biyu tana cije lebbenta.
"Ya Salam!" Ya
fa
ɗ
a yana sakin hannayensa.
"Saurin me kika yi haka? Me yasa zaki yi aure tun yanzu?"
Sai da ta zare idanunta tana dariyar da bata san daga ina take fitowa ba kafin tace.
"Saboda me?"
A lokaci guda ya karaso, ya tako zuwa cikin falon, ya tsaya dab da ita
sannan yace.
"Cox I want you, bai kamata ki auri wani ba, ko Allah ya san nine mijinki."
Sai da Amina ta cije lebbenta sannan ta rufe idanunta tana murmushi, kuma kafin ta bu
ɗ
e idon ya sunkuyo daidai gefen fuskarta yace.
"I apologize if this is a little bi
t forward, but you just look so.... Woww!"
Abinda taji kenan kafin taji ta a cikin hannayensa. Numfashinta ya yanke daga huhunta a lokaci guda, ƙafafunta suka karbi hannayenta wajen rawa, zuciyarta ta sake komawa ruwa, ta sake komawa irin duniyar jiya, dun
iyar da take manta komai sai Ma'aruf kawai da irin abubuwan da yake nuna mata.
Ya tallafi fuskarta ka
ɗ
an yana sawa ta kalle shi, don ko ka
ɗ
an ta kasa rufe idanunta ma yanzu, idanunsa cikin nata yace.
"You are making my world so much more beautiful Amina."
(Kina kara ƙawata duniyata Amina.)
Shikenan! Sai komai a cikin kan Amina ya sake rushewa, kalaman Hajiya Kilishi har ma dana Amma dake kokawar miƙewa, dukkan wani abu mai hankali a cikin kanta ya shiga gaya mata cewar da gaske ne ba zata iya taba lafiyar M
a'aruf ba!
*****
A cikin dakin, a cikin wayar, muryar Hajiya Kilishi ta ratsa da tsananin yaƙinin dake fitowa daga zuciyarta.
"Mahaifinta shine a lissafi Awwalu, munyi wata ya shaida min cewa sun dawo
ɗ
azu, don haka gobe zai fita aiki ina so ka fara bibiya
rsa tun daga safiya, duk inda zaije ka kasance tare dashi kuma a shirye, wa'adin lokacin zuwa yamma ne kamar na yaron nan. Idan har ban sami abinda nake so zuwa sannan ba, zaka ga umarni na."
Daga cikin wayar Awwalu yayi dariya mai cike da mamaki yace.
"Mu
tumin nan fa shine
ɗ
anuwanki Kilishi, ina laifin ki sake ta
ɓ
a wani daga cikin ƴanuwan nata kawai? kuma shi bashi da wata matsala ma naga, let the man be! Ki duba iyalinsa ki kyale shi."
Ko bai ganta ba ya san ranta a hafe yake sanda tace.
"Tun yaushe muka
fara la'akari da wani abu a cikin lamuran mu Awwalu? Ka amsa min kawai, bana buƙatar dogon surutu."
Sai ya sake kyalkyalewa da wata dariya mai armashi irin tasa sannan yace.
"An gama Hajiya, umarninki shine abin aikatawa ta!"
**
_Ku gaya min cewa Amina tan
a shirin kaimu ta baro..._
_Ko kuma laifin na Ma'aruf ne?_
_Ga dai mafita tiryan-tiryan Amma ta fitar, amma kamar Amina kuma kuna ganin cewa da matsala?_
_To wace matsalar kuka zaba?_
_Ta Amma dake cikin mafitar?_
_Ko kuma ta Kilishi da zata biyo baya?_
Li
ttafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
°°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*0
2*
~~~~~~~
_The act of love is Confession._ _- Unknown_
**
*Shekaru Goma da suka wuce.*
*Ƙarfe takwas na safiya.*
A bakin titi ne, daidai bayan dogon banki wajen da Babu mutane sosai musamman a safiya irin haks, motar da Hajiya Kilishi da kuma Awwalu take
tana daka fake a gefen titi an zuge duka gilasanta da bakin tint mai duhun gaske, don musamman don wannan fitar Hajiya Kilishin tace da Awwalu yaje ya saka tint
ɗ
in.
A cikin motar, Kilishin taja tsaki tana kallon agogon tsakiyar dashboard kafin tace.
"Muta
nen nan sun fara vata mana lokaci Awwalu, saninka ne fa ko Baffa bai san na fito ba."
Awwalun dake gaba mazaunin direba ya gyada kai shima yana kallon titin yace.
"Ki bari kawai, ni kaina ina da aji ƙarfe takwas
ɗ
in nan, kuma wallahi mai muhimmanci ne."
"A
ji?" Da mamaki a fuskarta ta tambaya.
Sai ya juyo ya kalle ta.
"Au na manta ban gaya miki ba, na koma makaranta fa, Bayero na samu ina yin English saura shekara
ɗ
aya ma na gama."
Kilishi taji ranta ya kara baci, har tana shirin bude baki tayi masa korafin
ta yadda har ya shekara biyu a University ba tare da ta sani ba sai kuma taga meye damuwarta a ciki? Rayuwarsa ce, zata hana shi ne idan har hakan ba shafarta zaiyi ba, kuma ma tun asali ta san Awwalu mai son karatu ne, don tun yana yaro farkon zuwansa alm
ajiranta da kudinsa yasa kansa a makaranta har ya gama firamare kafin daga baya kakarta ta shiga tallafa masa, kuma shekaru biyu bayan ta gama shima ya fita daga sakandiren, don haka karatunsa bai kamata ya dame ta ba.
Ta juya tana kokarin kallon wani mai
teburin shayi daga can nesa dadu dake ta kokarin hada wutar itacensa, amma itacen yaƙi bashi hadin kai duk kuwa da iskar sanyin da ake hurawa a lokacin. Ba shiri taji murmushi ya subuce a bakinta, zuciyarta ta cika da jin dadin yadda dattijon ke ta goho ya
na firfita wutar, tana son irin wannan abin, tana son taga wani nata wahala akan neman bukatunsa har sai zuciyarsa ta ƙeƙashe ta daina rauni, shi yasa ko kallo bata cika yi ba, don bata ganin amfanin yadda mutane ke tsara finafinan su cewa mai kirki ne zai
ci galaba a kodayaushe.
Taja tsaki bayan wutar ta kama babu da
ɗ
ewa, ta dawo da idonta cikin motar tana ƙoƙarin lalubo wayarta, sai kuma ta tuna ai ta kashe ta don kar ma a neme ta, kuma a daidai wannan lokacin sai ga wata mota katuwa ƙirar jeep Prado tazo
ta sha gabansu, nesa kadan tayi fakin ta tsaya.
"Ina ga gasu nan Hajiya."
Cewar Awwalu yana kallon motar.
"Fita zanyi kenan?"
Ya gya
ɗ
a kansa.
"Ai bana tunanin shi ne zai fito."
Sai ta kuma jan wani tsakin.
"Mutanen nan suna cin alfarmarta da yawa Awwalu,
ba don dole Jamal ya bar duniyar nan ta hanyarsu ba, bubu abinda zai hana ni zaba musu irin tasu ƙaddarar su ma."
Awwalun ya juyo yana kallonta.
"Haƙuri zaki yi Hajiya minti biyar ne ba su isa su sake ganin fuskarki ba har abada, harbin tayar mota tana gud
u ba aikin kowa bane banda irinsu da suka san duk wani tactis na abin...."
Bata ko jira jin ƙarshen zancen nasa ba ta sauke nikabin da ta daura a fuskarta sannan ta janyo wata ƴar madaidaiciyar jaka dake gefenta tare da wata farar takarda ta bude kofar mot
ar ta fita.
Kanta tsaye ta isa wajen motar ta tsaya daga daidai ƙofar baya, kuma daga inda Awwalu ke zaune yana hango sanda aka zuge gilashin ita kuma tasa hannu ta sake
ɗ
age nikabin nata.
Wani mutum ne zaune a ciki, fari tas dashi irin farin da yake komaw
a tamkar zabiya, sannan ilahirin fatarsa kaf, koina akwai wani
ɗ
igo-
ɗ
igon bakin wani ciwo da ya fito ya warke. Idanunsa na sanye da wani katon gilashi baƙi ta yadda ba'a ko ganin kwayar idanunsa, a lokaci guda yayi wani murmushi da ya baiyana jerin haƙoran
sa wanda rabinsu suna rufe da ƙarfe ne irin wanda ake cewa hsƙorin makka kalar ruwan gwal don haka sun haska tar a cikin hasken safiyar.
"Barka da zuwa Hajiya, sai haƙuri da irin aikinmu na gaya miki ni bana mu'amala da jakada, shi yasa kika ganni nima da
kaina."
Hajiya Kilishi bata yi murmushin ba, tana kallonsa idanunta a tsaye tace.
"Tun da har ka ganni anan ai ka san wannan maganar ta wuce kuma."
Sai ya
ɗ
aga mata girarsa daya cikin duniyanci irin nasa sannan ya nuna jakar hannunta yace.
"Sune wadannan?"
Sakan
ɗ
aya biyu tana kallonsa hankalinta na kokarin danne takaicin dake yawo a zuciyarta kafin ta
ɗ
ago jakar ta miko masa, ya kuwa kar
ɓ
a ya zura ta cikin motar sannan ya bu
ɗ
e, idanunsa suka yi nazarin ku
ɗ
in dake ciki.
"Kince yau da misalin karfe tara zai
fita sannan shi kadai ne a motar ko?"
Ta gyada kanta sau
ɗ
aya sannan ta mika masa wannan farar takardar hannun nata.
"Ga lambar motar koda wancan text
ɗ
in ya gige."
Ya karbi takardar ya kalla sannan ya sake
ɗ
agowa ya kalle ta.
"Hajiya zan so ace babu maga
na biyu a cikin wannan al'amarin namu, zamu ƙirga kudin nan idan sun cika zaki ga aiki, idan kuma akwai matsala, to kuwa za'a sami matsalar da gaske."
Sai da ta
ɗ
auke kanta gefe cike da takaicin yadda yake mata maganar sannan tace.
"Idan kuma har babu mats
alar ta yaya zan tabbatar da cewar zaku yin?"
Ta dawo da idonta kansa lokacin da yake sake wani murmushin.
"Tabbaci kike nema?"
Bata amsa ba, shima kuma bai jira amsar ba, sai kawai ya
ɗ
aga yatsansa
ɗ
aya a iska yana cigaba da murmushi.
Kuma bata gama tuna
nin me Ke shirin faruwa ba lokacin da ta wata irin ƙara ta baƙunci iska, tsananin karfin ƙarar yasa duk dauriyarta sai da ta firgita, kafafunta suka yi baya yayin da tasa hannayenta duka biyu ta toshe kunnuwanta lokacin da idonta ya kai kan wasu maza da su
ka juya da gudu bayan sun karyo kwana, sannan ta hango wannan mai shayin ma ya kwanta a gaban teburinsa yana kakkarwa, tabbas ƙarar ta bindiga ce ba wani abu ba.
"Wannan shine tabbacinki Hajiya, yarana basa wasa da aikinsu, hannu kawai nake
ɗ
agawa shikenan
duk abinda nace zai wakana ko akan waye kuwa."
Bayaninsa yazo daidai da lokacin da idonta ya sauka akan tayar motarsu ta gaba, gabadaya ta dagargaje ta kuma wargaje a lokaci guda, motar ta tuntsira tayi gefen titi, yayin da Awwalun dake ciki ke kokarin bu
ɗ
e kofarsa don ya fito kar ta kara hantsilawa dashi.
"Na barki lafiya."
Ta sake jin muryar mutumin kuma ko kafin ta juyo ta kalle shi, direbansa yaja motar sun yi gaba da wani irin saurin da har sai da tayar motar ta gurzu da titi ta bada wata irin ƙara.
Babu shiri murmushi ya subuce a bakin Hajiya Kilshi karo na farko a wannan safiyar, tabbas ta bakin Awwalun ne, mutanen nan sun iya aikinsu, rainin hankalinsu ne kawai a gefe. Taji murmushin nata na sauka har cikin zuciyarta da tunanin cewa ba za'a samu ak
asi ba, a yau Jamal zai bar duniyar nan, ai ta gaya masa... ta gaya masa lokacin da ya juya mata baya zai tafi.
_"Na so zan yi dukkan shirina in bar cikinku ba tare da na taba wani ahalin Baffa ba, nayi maka katanga mai yawa Jamal, na da
ɗ
e ina kange ka dag
a sharrina, amma ka rufe idonka ka tsallako ka iso... Ina jiye maka takaicin barin duniya da ƙuruciyarka, ina taya ka alhinin barin duniyar nan a lokacin da ya kamata ka fara cin ganiyarka, don daga yanzu ni da kai, mutane ne da baza su ta
ɓ
a iya rayuwa a l
okaci guda cikin duniyar nan ba."_
Ta sake wani murmushin tana cije le
ɓɓ
enta, zata so ace zai tuna wadannan maganganun nata a lokacin yake bin ruhinsa da kallo zuwa sama. Awwalu ya karaso wajenta a lokacin da nasa murmushin shima, fuskarsa na
ɗ
auke da yana
yin da ko bai furta ba ta san me zaice.
_"Me na gaya miki? Mutanen nan zasu iya aikin ki."_
Sai kawai ta juya ta kalli motar tasu a lokacin da Jama'a suka fara taruwa suna ƙoƙarin zagayeta.
"Zaki yi waya a kawo mana wata motar ne?"
Ya tambaya, ta girgiza k
anta.
"Baka da zurfin tunani