Showing 60001 words to 63000 words out of 144990 words
kowa a gidan nan kaya set hudu na bikin, ke ba'ayi dake ba?"
Ta girgiza kanta.
"Ni nawa ma guda shida ne Hajiya ta bani."
"Ahaan..."
Ya fada
alamun neman ƙarin bayani, tayi shiru kamar ba zata ƙarasa ba sai kuma tace.
"Su Janifa ne suka ƙona nawa..."
"What?"
Yadda muryarsa ta sake
ɗ
agawa yasa ta ƙara rikicewa, ta dago tana kallonsa tana kara yin baya da ƙafafunta kafin tace.
"Wallahi bani nace
suyi ba, ina cikin gida na dawo da daddare suka
ɗ
ebo su suka ƙona su a gabana, dama duka sauran kayana ma haka duke yi musu guda biyu kawai suka bar min, dan Allah kar ka fadawa Hajiya..."
A lokacin da take fadar hakan ta kai ƙarshe da bangon wajen dining
din kuma rawar da hannayenta ke yi ta ƙaru, Jawad ya kasa daure kansa da abinda yake ji na tsoratar tata sai kawai ya ƙarasa gabanta ya riƙo hannun nata, ai kuwa kamar yadda ya zata ta bu
ɗ
e bakinta zata ƙwallara ihu amma yasa
ɗ
aya hannun nasa ya rufe shi d
a sauri.
"Shut it, kar ki sake ki min ihu."
Ya fa
ɗ
a hannun nasa rufe da bakinta dayan kuma rike da nata duka biyu, ta shiga daga kanta da sauri alamun ta fahimta kafin ta hadiye shi a cikinta, dukkaninsu suka yi ajiyar zuciya a tare kafin a hankali ya dauk
e hannunsa daga fuskar tata yana kallon idanunta.
"Su waye su Jennifer? Kuma su nawa ne?"
Muryarsa ta fito ne a hankali saboda yadda yake kusa da ita. Zainab ta ha
ɗ
iye ƙullutun wani abu da har a lokacin bai gama barin maƙogwaronta ba tana jin hannunsa riƙe
da nata da kuma ƙamshin turarensa da ya zagaye ta kafin tace.
"Ɗakinmu
ɗ
aya dasu, suma aiki suke yi. Su uku ne."
"Ya sunansu?"
"Da Janifa, da Uchi da kuma Amaka."
Ya
ɗ
aga kansa a hankali alamun ya fahimta, amma bai matsa ba ya cigaba da tsayawa riƙe da ha
nnunta kawai yana kallon fuskarta, ita ma tana kallonsa da nata idon da yake cike da tsoro da kuma rudani, sakanni suka wuce kafin tayi magiyar dake rubuce a ko'ina na fuskar tata dashi baya gani.
"Dan Allah..."
Ta fa
ɗ
i hakan ba tare da ta san ma me take r
oko ba, amma ga mamakinta sai magiyar ta fito kamar ta tuna masa da wani abu, kamar ta dawo dashi cikin hayyacinsa, yayi saurin sakin hannayenta sannan yayi baya ya juya, sannan ya koma cikin falon inda ya
ɗ
auko wayarsa da ya bari akan kujera.
Tana ganin h
aka gabanta na dukan uku-uku ta nufi hanyar waje da niyyar fita, amma ya katse ta ba tare da ya ko juyo daga inda yake tsaye ba.
"Ki koma ki zauna kici abinci."
Yana fadin haka ya kara wayar a kunnensa sannan ya juyo yana kallonta daga inda yake a cikin fa
lon.
Magiya da duk wani bayanin da zata yi na banza ne ta sani, don haka sai kawai ta juya hankali ta koma.
"Ki zuba nawa nima."
Ya fa
ɗ
i abinda ya sake saka ƙafafunta tsayawa, idan tace ta shiga uku, tana ganin kamar tayi wa halin da take ci rashin adalci,
don Allah ya sani zuciyarta na dokawa da tsoron rashin sanin manufar mutumin nan akanta ne a kowacce rana tun daga wancan lokacin, idan aka ƙara da taraddadin alkawarin da shi da mahaifiyarsa suka ci alwashin yi mata tare da mahaifiyarta dake can gida cik
in wata uƙubar kuma, sai ta tabbatar cewa ko ita kanta ba zata iya kwatanta halin da take ciki ba.
Ta karasa inda ta ajiye kwanukan a hankali lokacin da muryarsa ta ƙara shiga kunnenta.
"Kana wajen reception din ne?"
Daga cikin wayar aka bashi amsar da ya
sake cewa.
"Okay, akwai wani aiki da nake son kayi min ne da zarar ka dawo."
Gajeriyar amsar da ba ciki ya bashi yasa shi kai tsaye ya cigaba.
"Akwai wasu da nake son ka kor ñnña daga aikin ku ne... I don't care waye ya kawo su ko kuma wa suke wa aiki kawa
i ka tabbatar sun bar gidan nan a yau..."
"... Su uku ne, Jennifer, Uchi da kuma something Amaka."
Plate
ɗ
in tangaran
ɗ
in da Zainab ta riƙe a hannunta ne ya fadi har ƙasa tarwatse a wajen!
***
*NO. 38 Ramie Street, Nassarawa GRA, Kano.*
"Ke ma kanki Nafi k
in san babu haufi a zancena, da matar da kuka aika taga wannan layar da yanzu wani zancen muke ba wannan ba, amma tunda har an samu akasi..."
"Akasi?"
Rukayya ta fa
ɗ
a tana katse Hajiyar Sudan
ɗ
in dake bayani a gabansu, dukkaninsu suna zaune a falon dake sa
man gidansu ne suna tattauna matsalar bacewar layar nan da Mariya bata gani ba a cikin jakar Hamida, don tun bayan da al'amarin ya faru, sai a yanzu suka sami Hajiyar Sudan suke shaida mata kasancewarta mace mai tarin hidimomi akanta.
Kuma a yanzun da Ruka
yya ke tunanin zata basu wata kalwakkwarar hujja akan al'amarin, sai kuma taji tana kiran kalmar akasi, wane akasi za'a fara lissafi tun ba'aje koina ba?
"Nayi zaton kince babu wanda zai ga layar sai wanda ya wanke hannunsa da wannan ruwan? To wane akasi z
a'a samu idan har abinda kika fada gaskiya ne?"
Ta tambaya ranta a
ɓ
ace kamar yadda a kwanakin nan ta saba kasancewa a cikinsa. Hajiyar Sudan ta ha
ɗ
e nata ran itama sannan tace.
"Abinda na fada gaskiya ne,wannan aikin ba'a kanku aka fara yinsa ba, kuma duk
wadanda nake bawa, babu wanda ya ta
ɓ
a yi min ƙorafin ba'a sami daidai ba, to kuwa ai dole akasin daga gare ku yake... Kuma wannan shine karo na ƙarshe da zaki kara
ɗ
aga min murya kin ji ni ko?"
Kafin Rukayyan ta sake cewa wani abu, mahaifiyarta Hajiya Naf
isa tayi magana tana ƙoƙarin shiga tsakaninsu.
"Yi hakuri Sadiyavranta ne ya
ɓ
aci na sani, kwana biyu a haka take ne, nima tunda Mariyan ta dawo ai abinda nake ta fa
ɗ
a kenan, nace duk yadda akayi matsala aka samu wajen sakawar, fatanmu dai shine ace layar
ɓ
ata tayi ba, kar ya zama ita yarinyar ce ta gani."
Ta janye idanunta a hankali daga kan Rukayyan da har a lokacin ke kallonta sannan tace.
"Wannan ba matsala bace, ko yarinyar ta gani ko bata gani ba akwai wata hanyar da za'a bi ku sami abinda ake so ba t
are da illar wancan ya shafi wannan ba."
"Yauwa Sadiya, na san ai kowacce dama bata faduwa ƙasa banza a wajenki, shi yasa na dage sai kinzo din. Allah na tuba ba don ke ba ai da bamu san hanyar da muke bi ba a yanzu, ki ƙyale wautar Ruƙayya kawai a gefe, n
a tabbatar miki damuwa da kuma tunani ne kawai suka sa ta yin hakan."
Ta fa
ɗ
i hakan lokacin da Rukayya ke sunkuyar da kanta cike da takaici, ta kusa kaiwa bango, ta kusa ƙurewa, daga mahaifiyar tata har Hajiyar Sudan ta kusa daina saurararsu, ta kusa fara
bin hanyarta, don bata ga inda suke motsi ba a wannan ga
ɓ
ar... Amma lokacin da Hajiyar Sudan tayi ajiyar zuciya tace.
"Aikin gaske zamu yi mata, Nijar zata shirya mu tafi, akwai wajen da idan muka je ina tabbatar muku babu haufi akan komawarta."
Sai kawai
wani murmushi ya su
ɓ
uce a bakinta, irin wannan aikin take so tabbas! Wanda za'ayi kamar da gaske ake yi, don ita da gaske take yi, da gaske take har cikin ranta, ba ma ta ƴarta take yi ba, wannan lissafin daga baya ne, fatan ta kawai ta sake mallakar Ma'ar
uf a karo na biyu kuma ko tawacce hanya!
***
*Karfe tara da rabi ba dare.*
Amina ta sake gyara kwanciyarta akan gefen kafadar Ma'aruf, film din da suke "The life we had" wanda sai a yau Allah yayi zasu sami damar kalla baiyi ko rabi ba, amma Ma'aruf yayi k
orafi yana kushe shi da tun tana ƙirga shi har ta daina.
Karfe tara da rabi na dare ne a lokacin, Hamida ta gama nata kallon tayi bacci akan kujerar dake gefensu, don yau tasha zirga-zirgar da bata saba ba, Ma'aruf ya kaita makaranta anyi dukkan wani proce
ss na registration an gama shi a yau da cewar ranar monday zata fara zuwa, sai murna take yi tun yanzu duk da su Hajiya basu so hakan ba, musamman Inna Danejo da suka shiga wajenta dazu, tana ta korafin cewa islamiyya ya kamata a fara saka ta zuwa wata she
karar tukunna.
Hajiya Maimuna ce kadai bata ce komai ba, amma ko Mami bata so ba sai dai bata hana ba duk da ta fahimci cewar sai da Ma'aruf din yayi shawara da ita tukunna, don tans kara saninsa ne tana kara sanin cewa kusan kashi tamaninn na al'amarim ra
yuwarsa tare da Mamin yake fara yin shawara.
Yau tunda ya dawo daga office yana tare dasu Baffa akan zancen dawowar Abdurrahim gobe sai wajen takwas ssnnan ya shigo gidan yana gaya mata dalilin dadewar tasa, ta san Abdurrahim dun a lissafin jerin ƴaƴan gid
an amma bata san komai akansa ba don basu yi hirar dasu Munaya ba kuma Mami bata ta
ɓ
a gaya mata komai akansa ba,da alama wani abu bai taba hado hanyarta dashi bane.
Mami, Hajiya Kilishi... Hajiya Kilishin da har yau bata sake ce mata komai ba, ko
ɗ
azu da s
uka shiga wajenta, sun gaisa ne kawai amma bata ce komai akan zancen Hamida ba da take jira ba, ta kula kamar wasu abubuwa sun fara shan gabanta ne ba zancen Hamidan ne a lissafinta ba ko kuma na bincikar wa
ɗ
annan pills din magungunan da tace ta dinga sha,
wanda ko a satin da ya wuce ta tambaye ta game da hakan har sau biyu kuma ta tabbatar mata da abinda take son taji cewar tana sha
ɗ
in... Jitmra kawai take yi lokacin da amsar da zata bata ta gaske ta fito.
"Doll seriously na gaji da film din nan, I want s
omething else..."
Muryar Ma'aruf ta janyo ta ta daga tunaninta, idanunta akan Tv ba tare da ta
ɗ
ago ta kalle shi ba tace.
"Something kamar me?" Muryarta ta fito a hankali cikin duhun dakin da hasken Tvn ne kawai akwai, don Ma'aruf ya kashe sauran fitulun d
akin saboda suna damun Hamida a baccinta, tana ta juyawa sai da aka kashe tukunna ta nutsu.
Sai ya juyo bangarenta a hankali sannan yace.
"Kamar..."
Shirun da yayi bai karasa ba yasa ta haƙura da kallon Tvn ta juyo da fuskarta itama tana kallonsa, tazarar
dake tsakanin fuskokinsu bata jin ta kai ta inci guda don tana kwance ne a jikinsa sosai, idonsa ya sauka zuwa kan lebbenta a hankali, kuma ganin haka yasa tayi saurin juyowa ta dawo da fuskarta yadda take da farko a saman kafa
ɗ
unsa, kumatun ta na shafar s
aman dogon hancinsa kafin ta juya din.
A lokaci guda kuwa yasa hannunsa
ɗ
aya ya dawo da fuskar tata tana fuskantar tata sannan ya
ɗ
ora goshinsa akan nata yana kallon idanunta bakinsa
ɗ
auke da wani guntun murmushi amma bai ce komai ba, sai ta dago da hannun
ta na dama ta dora akan gefen fuskar tasa itama, dogwayen yatsunta na shigewa cikin gashin kansa, hakan tasa shi lumshe a hankali idanunsa kafin yace.
"Ishaq ne yake gaya min cewa wai yana son Munaya."
Muryarsa ta fito a hankali yana kallonta, kuma bata sa
n me yasa ba amma wani abu a cikin muryar tasa ya gaya mata cewa itace mutum ta farko da ya fara gayawa hakan, hakan yasa a lokaci guda wani murmurshi ya sauka a fuskarta.
"Da gaske? Wow! Masha Allah. Nayi farin ciki sosai wallahi, this is a good news Alla
h ya sanya alkhairi."
Ya fadi Amin din a hankali sannan kawai yayi shiru yana kallonta, sai tace.
"Me ya faru? Are you not happy?"
Sai ya girgiza kansa.
"Kawai ban san me nake tunanin bane, gani nake Munaya har yanzu yarinya ce, level two take fa..."
Gira
guda
ɗ
ayan da Amina ta dage ne yasa shi yin shiru ba tare da ya shirya ba.
"Yarinya? Munayan? Sa'a ta ce fa."
"Da gaske?"
Ya tambaya kamar bai sani ba, sai kawai ta cije lebbenta sannan tace.
"Kuma aka ka gaya masa?"
Yadda take ƙoƙarin hade fuskarta yasa s
hi sake girgiza kansa.
"At first na gaya masa hakan, amma
ɗ
azu a office yazo mun sake magana har mun tsayar cewar zan je in fara samun su Baffa ma in gaya musu."
Ta gyada kanta a hankali.
"Nayi zaton haka kace masa, da nima idan naje gida gobe kaga sai iny
i zamana ince maka ni yarinya ce."
Murmushin da yayi mai fadi ne kafin ya saje hade goshinsu waje daya.
"Our story is different, labarinmu daban ne Doll, ni na san yadda zanyi handling
ɗ
inki, na san yadda nake sace zuciyarki cikin ruwan sanyi..."
"Da gaske
? Ta tamvaya.
"Ta yaya kenan?"
Muryarta ta sake fitowa a hankali tana kallonsa kuma maimakon ya bata amsa sai kawai taji hannunsa a bayanta, kusa da wuyanta sosai, kuma kafin tayi wani tunani ya zura hannunsa cikin wuyanta a hankali sannan ya shiga zana wa
su abubuwa a gefen wuyan nata, jikinta ya shiga rawa sannan numfashinta ya fara ha
ɗ
ewa, tayi niyyar sake magana amma ta kasa, sai kawai ta rufe idanunta a hankali gaba
ɗ
aya tana saurarensa, har zuwa sanda taji wani abu kamar tashin zuciya da ya sata saurin
riƙe hannunsa.
"Saboda me?..."
Muryarsa ta fito cike da ƙorafi ba tare da ya fahimci dalilinta ba.
"Wai meye ban gani bane?"
Tambayar ta saka ta kyalkyala dariya, wata ƴar siriiyar dariya kafin ta ture shi gabadaya ta miƙe, ya bita da kallo daga kwancen da
yaje yana cije lebbensa, ta dauki Hamida a hankali sannan tayi hanyar
ɗ
aki tana cigaba da yi masa murmushi, kuma kafin yayi wani motsi sai wayarsa dake gefe tayi ƙara, ya mike zaune ya jawo ta daga kan centre table
ɗ
in dake gabansa.
Nambar Yakubu da ta fi
to
ɓ
aro-
ɓ
aro akan screen din ta motsa zuciyarsa kafin yayi saurin danna wajen amsa kiran ya kara ta a kunnensa.
"Na sami mutumin, gashi nan a hannu na."
Shine abinda Yakubun ya fada kai tsaye bayan ya dauka.
Hannunsa ya shiga cikin gashin kansa a take kafi
n muryarsa ta fito fili.
"Ka ganshi Yakubu? Ka ganshi? Mr. Okaforn da gaske?"
Yakubun ya gyada kansa.
"Kwarai gashi nan ma
ɗ
aure gabana, dashi da iyalinsa bakidaya... Kuma ya gaya min iya abinda ya sani, labarin mai tsawo ne amma yace sunan mutumin dake sa
ka su aikin Awwalu.!"
Awwalu!
***
_Kuna tunanin Awwalun Kilishi ne??_
_Ku gaya min me ya sha kan Kilishi ne da har yanzu bata bawa Amina hodar nan ba?_
_Ina kuke hango tafiyar Jawad da Zainab? Allah yasa kar in shallake tinaninku!_
😅
_Wannan tashin zuciyar
na BabyDoll
ɗ
in Sugar...?_
😍😅
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
°°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.
*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*13*
~~~~~~
_"If you want to keep a secret, you must also hide it from yourself." –George Orwell, 1984_
**
Ƙ
afafunsa suka shigo cikin tangameman falon a hankali, kai tsaye ya shiga wuce tarin wajajen dake cikin falon har zuw
a inda ya san zai sami mahaifin nasa, yana bi ta kan tausasan carpet
ɗ
in dake wajen kala-kala har ya karasa wajen a daidai lokacin da idonsa ya shaida masa mutanen dake zaune bayan mahaifin nasa.
Mahaifiyarsa, matar mahaifinsa ta biyu mai suna Yagana, sai
kuma shugaban ma'aikatan gidan Joshua, yana kallon yadda kayan Hajiya Yaganan ke ƙyalli tare da na mshaifiyarsa a cikin fitulun wajen kamar masu shirin tafiya fadar shugaban ƙasa.
Ya karasa da sallama sanda mahaifin nasa ya sauke jaridar dake fuskarsa san
nan shirun da suka yi dukkaninsu ya tafi tare da amsawar sallamar daga mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa su ka
ɗ
ai yayin da Hajiya Yaganan ta shiga jefo masa hararar da sau
ɗ
aya ya gani ya
ɗ
auke kansa.
"Barka da Safiya Abba."
Ya gaishe da mahaifin nasa yana z
ama kusa da Joshua.
"Yawwa mun tashi lafiya?"
Amon muryar mahaifin nasa ya fito babu yabo kuma babu fallasa.
"Lafiya kalau Alhmdlilah." Ya amsa kafin mahaifin nasa ya sake cewa.
"Ai ban san kana gari ba ma har akayi bikin ƙannenka, sai yau da na tashi da ƙ
orafin ka da aka kawo min."
Kafin ya amsa muryar Hajiya Yagana ta cika falon da cewar.
"Ƙorafi? Ai ba ƙorafi bane Daddyn su Amal, laifi ne yayi kuma shi kansa ya san da hakan."
Ta kira sunansa tana kebanta shi da ƴaƴan ta saboda Hajiya Mardiyyan dake zaune
. Kuma maimakon mahaifin nasu yayi maganar katse shin da tayi a zancensa, sai kawai yace da Jawad
ɗ
in.
"Me yasa ka korar mata ƴan aiki har mutum uku Jawad?"
Jawad ya gyara zamansa yana fuskantar inda zancen ya dosa kafin yace.
"Ni ban san ƴan aikinta bane,
laifi suka yi min nace da Joshua ya kore su, kuma ko a karkashin wa suke aiki a gidan nan haka zan ce."
Alhaji Bashir ya gya
ɗ
a kansa alamun ya fahimta.
"Laifin me suka yi?"
Kai tsaye ya sake cewa.
"Wata yarinya suka ƙonawa kayan sawarta gabadaya, sunanta
Zainab."
Amsar ta fito da zare idon da Hajiya Mardiyya tayi a lokaci guda tana