Showing 18001 words to 21000 words out of 144990 words
da hannayenta keyi tare da kwanukan abincin shine abinda ka
i tsaye ya shaida masa cewa tsaf taji dukkanin shirinsu!
***
Karo na ba adadi Amina ta kalli agogon dakin, zuciyarta ta kara yin nauyi a kirjinta, rawar hannayenta ya karu, amma sai tayi saurin danne hakan ta hanyar daukan wani ƙaton mangwaro dake gabanta
.
A bangaren Inna Danejo suke wadda bayan fitar Ma'aruf Samirah tazo ta gaya mata isowarta don haka ta ƙulle gidan suka taho tare, inda ta tadda dukkan sauran jama'ar gidan kowa yazo don saukarta.
Kuma ba'a dade ba aka shiga hayaniyar rabon tsaraba kama
r yadda ta fahimci ana yi duk sanda Inna Danejon tayi tafiya ta dawo, su Msma Rabi dama wasu da bata san su waye ba sun zo ana ta faman kwance tsaraba kala-kala, Samirah ce ke gaya mata cewa in dai Inna Danejo taje Bakori to ba gidan kadai ba, tun daga far
kon layinsu har karshe kowanne gida sai an kai masa tsarabarsu, abubuwa ne kala-kala har da wanda ita bata taba gani ba ma sai faman rarrabawa ake yi bisa umarnin da Inns Danejon ke bayarwa.
Kusan ita dasu Mama Rabi ne ma ke ta aikin don Samirah ita nata n
a amfanin gida kawai take ta warewa, tana yi suna fadansu ita da Inna Danejon akan cewar tana diban komai da yawa, Munaya kuma tsince-tsincen duk abinda ta san zata iya ci take yayin da Surayya ke ta aikin danna wayarta taje ta nanike a jikin Inna Danejon
dake ta nan-nan da ita, wanda sai a lokacin Amina take jin wai sunan maman Inna Danejon aka saka mata, shi yasa duk gidan tafi shiri da ita akan kowa.
A lokacin ne kuma Samirah ke gaya mata cewar gobe Amaren da akayi bikinsu tare zasu zo, don haka duk tari
n taraddadin dake zuciyarta, sai taji itama tana murna da zuwan nasu, don aƙalla koyaushe tana jin hirarsu kala-kala a bakin su Samiran.
Ta cakuda hannayenta duka biyu waje daya lokacin da Mama Rabi ta karbi aikin da take yi tace taje ta huta, Inna Danejon
nkuma ta miko mata wata damammiyar fura mai gardi a cikin roba tana yi mata nata sannun itama, kuma duk da yadda take murmushi akan fuskarta hakan bai ƙarasa har cikin zuciyarta ba, don bai isa ya kore halin da zuciyarta ke ciki ba.
Ta samowa kanta mafita
ta sani sai dai duk da hakan mafitar bata canja daga umarnin Amma ba don ba zata ta
ɓ
a iya kin bin maganganunta ba, itace gatanta ta sani kamar yadda ta san maganganunta sune fitilar da zasuvgitar da ita daga duhunnda taje ciki, don haka a dole ta tsamo kan
ta daga rudanin zuciyarta ta yanke hukuncin aiwatar da umarnin Amma tare kuma da samawa kanta mafitar da take ganin zata jefi tsuntsu biyu ne da dutse daya.
Zata yi abinda Amma tace, zata aikata umarnin Kilishi ta hanyar samun gaskiya da kuma yardarta, san
nan zata yi jinyar Ma'aruf ta hanyar da hakan zai ƙara shaƙuwa tsakaninsu, a yanzu zuciyarta ta riga ta kar
ɓ
e shi da dukkan iyawarta, don haka zata ajiye komai a gefe ta gyara rayuwarsu kamar yadda ya roƙe ta, kamar yadda yake so... Idan tayi hakan ta san
zata samu sauƙi a zuciyarta na ganin laifi da kuma rashin kyautawarta.
Hannayenta suka kara rawa lokacin da ta tuno yadda suka kasance dazu da safe, dama abinda ya rada a kunnenta kafin ya fita bayan tambaya karbi robar zogalen nan.
_You are really making
me insane, and I like it..._
Tana iya tuna yadda wasu abubuwa ke harbawa a cikin kanta wannan lokacin, dama yadda jikinta ya dinga rawa a cikin hanayensa kafin ya janye ta a hankali yana gaya mata cewar zai fita a cikin kunnuenta.
Sai dab da magariba sosa
i sannan komai ya natsa, suka gama ha
ɗ
a kan tsarabar nan tsaf, sannan ta samu tayi sallah, har kowa ya tafi sai ita kadai a bangaren Inna Danejon, don bata san me zata koma bangarensu a wannan lokacin tayi ita kadai ba, jira take amma bata san ma abinda ta
ke jira din ba, dawowar Ma'aruf ko kuma akasin sa??
Kuma da misalin karfe bakwai da rabi daidai, sai dukkan wani tunaninta dama kokwanton ta yazo kan ga
ɓ
a, sannan fatanta dama duk wani tsarinta ya tafi daidai lokacin da kiran Hajiya Kilishi ya riske ta.
Ma
ma Rabi ce ta shigo ta gaya mata sakon, kuma bayan hakan bata ce komai ba don haka Inna Danejon ma bata yi wani tunanin komai tayi mata sallama ta fito tare da tata katywar ledar kayan tsarabar.
A harabar gidan ta hango Mamin, tana tsaye a jikin motar ta
kirar Camry yayin da Malam Sani direba ke ciki ya kunna motar, hasken gitulun danjojinta na haskawa ta kowanne gefe, tafiya kawai take yi har suka karasa tare da Mama Rabin dake fadin.
"Hajiya ashe har kin fito."
Kuma Mamin bata amsa ba, sai ta kalli kayan
hannun Aminan kawai sannan tace da Mama Rabin ta karba ta tafi dasu.
Kwatanta yadda zuciyar Amina ke bugawa a kirjinta wannan lokacin wani abu ne da ba zai bayyanu ba, don kafafunta ma bata jinsu a jikinta kwata-kwata, yayin da jikinta yayi shafal kamar f
allen takarda.
"Amina..."
Hajiya Kilishin ta kira ta cikin sautin muryarta da ya fito tar a shirun harabar compound din.
Bata amsa ba don bata san me zata ce ba, tana kallonta ne kawai da dukkan taraddadin dake yawo akanta, kuma ga mamakinta kawai sai taga
tayi wani irin murmushi mai fadi da ya tabo har cikin idanunta kafin ta fadi abinda ya tsayar da duk wani hargitsin kanta cak!
"Ma'aruf yana asibiti, yanzu Ishaq ya kira ni yake shaida min!"
Maganganun suka fito tar cikin muryarta, kuma bata jira komai ba
sai ta miko mata wata takarda da sai a yanzu ta kula da ita a hannunta.
"Ga nawa albishir din Amina, kamar yadda kema kika bani naki."
Bata san tsawon sakanni nawa ne suka wuce kafin ta ita sa hannu ta karbi takardar amna idonta da kwakwalwar ta basa gane
ko meye a jiki balle har ta kai ga fahimta, kuma abinda Mamin ta gane kenan saboda haka tace.
"Appointment ne na wani asibiti a Indiya, za'a kai Aminu a gyara masa kafafunsa, na biya komai, saura shi da mai raka shi su fara fafutukar visa."
Ta fadi hakan
sannan ta yi shiru tana kallon yadda hannun Aminan ke rawa tare da takardar, sai kawai ta sake wani murmushin sannan tace.
"Me na gaya miki ne Amina? Komai mai sauki ne umarni na kawai zaki bi, shikenan sai in mayar miki da duniyarki kamar aljanna."
Abind
a bata sani ba shine a wannan lokacin Amina ba jinta take yi ba, kwata-kwata bata saurarar abinda take fada take yi ba, maganganun Amma mahaifiyarta ne kawai ke yawo akanta.
_"... A tafin hannunki zaki dora Kilishi Amina, a tafin hannunki zaki dinga juya
ta ba tare da ta sani ba, duk abinda kike so har ma da wanda baki roka ba zata yi, da kanta zaki sa tayi ta haƙa ramin binne kanta har sai yayi zurfin da zai rufe ta!"_
***
_Me ya faru da Ma'aruf?_
_Kun fahimci cewa mun fara wasa da hankalin Kilishi?_
_Kun
fahimci kudirin Amina?_
_Kun fahimci inda rayuwarsu ke shirin kaimu?_
_Me zai faru game da tsarin su Jawad?_
_Me ke shirin faruwa da Zainab? ( Ƴar aikin gidan su Jawad.)_
_Allah yasa baku manta da Hameda da kuma mamanta Rukayya ba... Suna nan tafe._
Litta
fin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
°°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*04*
~~~~~~~
_There are feelings that can't be explained._ _- Unknown_
**
A cikin asibitin, daga cikin wani dogon korido mai
ɗ
auke da kofofin kala-kala, Hajiya Kilishi na tsaye ita da Faruk yayin da daga gefenta kan kujerar masu jira na asibitin Amina ce ke zau
ne suna sauraren bayanin da Faruk din ke yi.
"Wallahi Mami mun gama duk abinda zamu yi, munyi sallama lafiya kalau da shi har ma da wanda muka hadu dashi din, kowa ya hau mota muka rabu a wajen round about din nan, to ni nayo gaba kawai sai go slow ya tare
ni kafin inyi nisa, anan naji wasu mashin da suka karaso suna hirar fadan da suka baro ana yi a baya, daya yana cewa wai ai ya san mai dukan sunansa Ma'aruf yana aiki tare damu a kamfani, naji yana bawa abokinsa labarin daya incident din a ya faru dashi d
a Daniel.
Da kyar na fita da go-slown nan na koma, kuma lokacin da naje ma har an raba su an dawo da Ma'aruf din motarsa mutane suna ta rike shi, ina masa magana amma kamar bai gane ni a lokacin ba, shine na kira Ishaq, sai da ya karaso sannan da kyar yasa
shi ya yarda ya baro wajen, amma tunda naje abu daya yake ta fada wai a barshi ya karasa kashe mutumin yana da sakon da zai bashi."
Hajiya Kilishi tayi ajiyar zuciyar dake shaida tsananin damuwarta kafin tace.
"Kuma ko bayan fitar tasa ma munyi waya sai k
uma na kira shi daga baya bai dauka ba."
"Ai Mami gabadaya wayoyin nasa ma da wallet da komai an kwashe, da yake bude motar kawai yayi ya fita a lokaci guda, to a wannan hayaniyar
ɓ
arayi suka samu dana suka kwashe komai, har mukullin motar sun tafi dashi,
ita kanta motar ma don baza su iya dauka a lokacin bane."
"Tana ina yanzu?" Kai tsaye ta sake tambaya.
"Tana wajen, nasa wasu dai sun tura ta zuwa gefen titi, sannan na basu kudi su kwana a ciki saboda ban ma san inda za'a nemo spare key dinsa a dauke ta b
a."
Duk wannan bayanin da Faruk ke yi, Amina dake zaune daga kujerar baya ta masu zaman jira a asibitin idanunta na manne ne da kayan Faruk din, farar shadda ce a jikinsa wadda gabadaya gabanta ya
ɓ
aci da jini har zuwa kowanne hannun na rigar, zuciyarta na
bugawa da motsin dake shaida girman laifinta da a yanzu take ganinsa karara, yayin da kalaman ke yawo a cikin kanta, tana yarda da kowacce kalma
ɗ
aya bayan daya dake maimaitawa daga cikinsu.
Suna gaya mata cewa tabbas babu abinda dan adam zai samu a duniy
ar nan cikin sauƙi, sannan kuma babu wani abu da mutum ya kamata ya fito yayi takama dashi a duniyar nan, don ana zuwa gabar da rayuwa ba zata baka zabi ba, zaka zo kayi wani abu da ko a mafarki ba zaka ta
ɓ
a tunanin aikata shi ba.
A baya zata rantse da Alk
ur'ani wajen karyata duk wanda zai zo ya shaida mata cewar zata iya aikata wani abu najamancin wannan, amma sai gashi a yanzu da hannunta ba tare da tursasawar kowa ba tayi abinda take jin tambarinsa ya
ɗ
arfanu a zuciyarta ta hanyar da ba zai taba goguwa b
a, don idan har za'a lissafa da sunanta a cikin wanda suke da kamasho a yau wajen faruwar wannan tashin hankalin, wajen zama sanadin da har mutane biyu ke kwance a asibiti, da kuma fitar jinin da take kallo har a jikin Faruk yanzu, to kuwa ta tabbata bata
da kalaman da zasu wanke ta ko a gaban waye.
"Ka ce bai ji ciwon sosai ba ko?" Sai a wannan lokacin muryar Mamin ta shiga kunnenta, tana tambayar Faruk din da ya gama amsa wata waya wafda da alama fuk akan abinda ya shafi al'amarin ne.
Ya daga kansa sau da
ya.
"Ba sosai ba, na wancan mutumin ne yafi yawa, tun a can muke fatan Allah yasa bai fasa masa ido ba, don dukansa yayi tayi Mami, yana cewa a kyale shi ya kashe wai yana da sakon da zai bashi."
"Inalillahi wainna ilaihir raju'in... Bari na kira Baffa."
T
a fa
ɗ
a amon muryarta na fitowa da tsananin damuwar da babu wanda zai kasa shaida hakan, Amina ta bita da kallo baya ta juya ta bar wajen, kuma a wannan ya lokacin ne wata Nurse dake cikin
ɗ
akin da suke jira a kofarsa ta fito, hannunta dauke da farantin kay
an dressing wanda ya cika fal da tarin auduga mai jini.
Idanun Amina ya sake bin hannunta da kallo har ta
ɓ
acewa ganinsu, abinda take ji a ranta yayi yawa a lokacin don haka sai kawai ta damƙe hannayenta biyu duka waje daya ta a shirin kore kwallar dake ta
ruwa a idanunta. Munaya wadda suka taho tare da ita ta karaso daga fitar da tayi tana gama waya da Hajiya Maimunan da ta sake kira tana tambayar halin da ake ciki.
Taji sanda ta zauna a gefenta bayan tayi sallama da Hajiyan don haka ta juyo ta kalle ta.
"Z
a'a barmu mu ganshi yanzu?"
Sai ta girgiza kanta.
"Wallahi ban sani ba, amma ko sun ce ma ai inaga Mami ce kadai zata shiga."
Idon Amina ya nuna da mamaki kafin ta tambaya.
"Saboda me?"
"Saboda idan yana wannan yanayin bai kamata aje kusa dashi ba, Mami ta
fada mana hakan tuntuni."
Bakin Amina ne ya bude a lokaci guda, mamakin dake idonta ya karu tana kallonta.
"Waye yake kula dashi kenan?"
"Yaya Ishaq ne, yawanci ma ba anan suke zama ba, akwai asibitin da yake ganin likita a London, can suke tafiya sai ya
sami sauki tukunna. Amma lokaci kadan ne, da mood din nasa ya dawo zaki ga koma daidai."
A lokaci guda sai taji hankalinta ya kasa
ɗ
aukan maganganu da Munayan ke fa
ɗ
a, kallonta kawai take yi yayin da take jin kamar kwakwalwarta na washewa, komai yana gogew
a, don bata san yadda zata dauki wannan al'amarin ta ƙara akan sauran tarin abubuwan dake kanta ba.
Tunaninta ya kasa lissafa wace irin zuciya ce da Hajiya Kilishi, a kowanne irin ma'auni na duniya ta rasa a wanne iri za'a dora zuciya irin ta Kilishi tayi
kama da ta mutane... Abubuwan da ta aikata a rayuwarta kaf idan za'a tara su waje
ɗ
aya bata jin duk raunin imanin mutum a duniyar nan za'a sami wanda zai kalla bai ji zuciyarsa ta motsa ba.
Ta shigo cikin rayuwar mutanen nan da ƙarfi da yaji, ta gurgunta m
ahaifiyarsa, ta ƙwace shi daga gare ta, ta shuka tarin ƙananun abubuwa a cikin rayuwarsu da watakila ita kanta ba zata iya lissafawa ba, kuma duk da bata sani ba tana tunanin wataƙila itace sanadin ciwon nasa ma amma duk wannan bai ishe ta ba sai ta daƙile
shi kuma a dukkan
ɓ
angare na kulawa irin wannan.
Bata san irin ciwon Ma'aruf ba, bata san komai game dashi ba, amma tayi imani cewar babu wani ciwo a duniyar nan da baya bukatar kulawa, ko da na hauka ne kuwa, to ta yaya za'a ce ayi nesa dashi a lokacin d
a yake tsananin bukatar kulawa?
Farkon zuwanta gidan tana ganin komai ne daidai, tana sha'awar mu'malarsu da komai shaƙuwarsu na mata yawo a ido kodayaushe, amma sai a yanzu take ganin tarin ramukan dake gewaye dasu, sai yanzu take fahimtar cewa ba daidai
komai yake tafiya ba kamar tunaninta.
Mutane ne su masu hankali, ƴan boko kuma masu ilimi, amma Kilishi ta dauke su gaba
ɗ
aya ta sanya a wani rami da babu mai iya haurowa, tana daga sama sai iya amon muryarta da kuma umarninta kawai suke ji, suna yin dukka
n abinda ta furta ba tare da sun sani ba, ba tare da sun san ma me saka su ba. Taji zuciyarta ta matse a lokaci guda wani abu a cikin kanta yana gaya mata cewa wannnan yana daya daga cikin abubuwan da zata fara canjawa.
Tana jin Munayan na cigaba da waya d
a wata classmate dinta a lokacin, tana jin suna tattauna wani abu da ita ba fahimta take yi ba har sanda Mamin ta dawo, ta shiga gayawa Faruk da ya dawo cewar yaje gida ya canja kayansa, don mutanen dake wajen duk wanda zai wuce sai ya kalle shi, amma yace
mata bari likitan ya fito tukunna su ji abinda zai ce, don har ga Allah baya jin zai iya tafiya ba tare da ya san halin da ma'aruf ke ciki ba.
Zuciyarsa ta yage har karshe tun daga lokacin da yaga yadda yake rike Ma'aruf a wajen nan yana yi madmsa magana
amma babu alamun ya a gane shi alhsli yanzu-yanzun nan suka rabu lafiya, lokacin da al'smarin Daniel din nan ya faru a Office zuciyarsa tana bada wani kamashon laifin ga Daniel din, yana ganin har da laifinsa wajen tunzura Na'aruf din, amma abinda ya gani
yau, yafi karfin dukkan wani tunaninsa.
Don haka yana tsaye har lokacin da Ishaq ya bude kofar wajen ya fito, kayan jikinsa kalar maroon ne amma duk da haka ana ganin inda ya samu nasa rabon
ɓ
acin jinin shima.
"Ishaq me ake ciki? Me suka ce?"
Mami ce ta fa
ra jero tambayoyin cikin zaƙuwa. Kuma da muryarsa a hankali kamar kodayaushe yace.
"Mami ki kwantar da hankalinki, ciwonsa ne dai ya tashi, dama munyi sa'a ne kwana biyu mood din nasa ya saisaita, kuma ban san me ya tada shi yanzu haka a lokaci guda ba. S
ai dai na yi musu duk bayanin da suka bukata kuma sun bude file sun rubuta hakan, yanzu an bashi alluran bacci yana hutawa."
"Abinda zasu iya yi masa kenan?" Ta tambaya.
Ya gyada kansa.
"Mami ai ko irin magungunan nasa na basu dasu anan, guda daya kawai ak
a samu, so na gaya musu zamu taho da na wajenmu