Showing 12001 words to 15000 words out of 144990 words

Chapter 5 - FARAR WUTA COMPLETE

jigawa nace miki not there, not then, sai lokacin da z

uciyarki ta amince kuma kika bani dama Amina."

Allah yaso a jiyan da yake fada mata hakan cikin duhu ne, lokacin da bai nemi shawarar ta ba ya shigo dakinta bayan ta barshi a falo yana kallon zancen wata siyasar America, tayi masa sallama da cewar sai da s

afe zata je ta kwanta, kuma ya amsa mata suka yi sallamar Allah ya tashe su lafiya, sai gashi minti goma bayan hakan ya shigo dakin bayan yaje ya canja kayansa zuwa na bacci.

Ta rufe idanunta alamun bacci take yi har sanda taji ya hawo gadon, amma lokacin

da babu zato taji ya na

ɗ

e hannunsa daya waist dinta kafin ya jawo ta cikin jikinsa a hankali, babu shiri ta bude idanunta tana kallonsa, kuma a lokacin ne ya gaya mata wannan maganar, a yanzu kuma da safiyar Allahn nan yake neman amsarta.

Kuma abinda take

ji a yanzu ya wuce duk yadda zata iya fassara shi, yadda ya rike hannayenta duka biyu kadai tana jinta ne kamar wani kwan fitila da ya kama tar! Sannan tana jinta kamar tana shawagi a iska, kuma cikin hakan ne taji lokacin da ya saje cewa

"Duk abinda zaki

fada ina son kiyi considering cewa ba kowa ne zai baki irin wannan damar ba Amina, Allah ina da kirki sosai."

Bata san lokacin da wani murmushi mai kama da dariya ya subuce a bakinta, yace ya bata damar da zata fadi ra'ayinta amma kuma ya fara yiwa kansa

campaign tun bata ma ce komai ba. Sai ta dago tana kallonsa sanda shima yake murmushin. Shima ya sani ai, amsarta ba zata canja daga abinda yake fata ba, ya riga ya gama daure ta da jikyoyinta, kamar ya sace zuciyarta tun a farkon zamansu ya kulle ta a wan

i keji, kuma bai bude ta ba sai da ta gama sabawa dashi ta yadda a yanzu da ya baya muƙullin da kanta don ta bude kanta ya san ba inda zata iya zuwa... Dole da ta fito ta tashi zata dawo ne ta fa

ɗ

o cikin hannayensa.

Don Allah ya sani ko ba ita ba, bata ga

macen da zata iya kallon Ma'aruf a wannan lokacin tare da kyawawan halayensa tace bata son sa ba, idan kuwa har an samu yo tabbas ko waceve za'a iya jeranta ta cikin masu karancin sa'a a duniya.

Don haka a wannan lokacin Amina ta daure dukkan wani tunani a

zuciyarta, ta ture komai gefe, a karo na farko a rayuwarta tayi wani abu kai tsaye da zuciyarta ta gaya mata ba tare da tunanin komai ba, don a wannan lokacin ta ma manta kowa

ɗ

in kuma ta manta komai, babu wani kokonto a ranta ko kuma tunanin hakan bai da

ce ba, abinda ta sani kawai shine Ma'aruf ya tambaye ta abinda ke zuciyarsa ne kuma zata fada masa gaskiyar zuciyar tata.

Shi kansa bai yi zato ba sanda ta tattaro dukkan dauriyarta a hankali ta ƙara tsawonta ka

ɗ

an ta hanyar miƙewa kan kafafunta sannan ta

kai fuskarta daidai kunnensa, muryarta ta fito ne a hankali da kalaman da ita kanta sai a wannan lokacin taji su.

"You’re the piece of me I didn’t know was missing untill now."

(Kaine wani

ɓ

angare na da ni kaina ban san bani dashi ba sai yanzu.)

Ta sauke ƙ

afafunta a hankali tana kallon fuskarsa dake

ɗ

auke da tsananin mamakin da ita kanta take jin yana lullu

ɓ

e ta, taga yadda ya ha

ɗ

iye wani abu a cikin maƙogwaronsa kafin ya gya

ɗ

a kansa a hankali.

"Nagode Amina, insha Allah ba zan ta

ɓ

a sawa kiyi dana sanin sa

nina a rayuwarki ba, zan kare dukkan hakkokin ki da Allah ya rataya min a wuya na, ba zan taba cutar dake ba, ina da tabo mai girma a cikin rayuwata, ina da abubuwa da yawa da ba zaki so saninsu ba, I'm a mess just like I told you, amma idan kika bani dama

nayi miki alkawarin komai zai tafi daidai Insha Allah."

Kuma bai bari ta sake wani tunani ba ya ha

ɗ

e tazarar dake tsakaninsu, ya rungume ta a jikinsa da wata irin shiga da taji kamar yana son kange ta ne daga dukkan wani hargitsi na duniyar nan, wani abu

daya dawo da ragowar hankalinta jikinta yana tuna mata da zagayen halin da take ciki, fuskar Amma da kuma ta Hajiya Kilishi ta haska cikin kanta a lokaci guda, dukkanninsu suna kallonta da jiranyen da ta san yana zagaye da ita, sai dai Ma'aruf bai bar haka

n yayi nisa ba lokacin da ya sake riƙe ta a jikinsa sannan a hankali ya lalubo kunnenta ya ra

ɗ

a a cikin kunnenta.

"Thank you so much Doll, I was dying to do this..."

Kuma bai

ɓ

ata lokacin wani tunani ba, lokacin da ya dawo da fuskarsa saitin tata sannan ya

hade dukkan wata tazara tsakaninsu, his lips were rough and urgent, sannan tana iya jin dukkan wani sakon da yake bata a cikin hakan, kuma cikin wannan sakon ne Amina ta samarwa kanta mafita itama, wata mafita da a lokaci guda ta haska a cikin kanta, wat

a mafita da zata jefi tsuntsu biyu da dutse

ɗ

aya!

Tsuntsu biyu, ba guda daya ba!

*****

Aka kwankwatsa kofar

ɗ

akin sau daya, biyu, uku....

"Who the hell is that?"

Muryar Jamal ta daka tsawa daga ciki yayin da yake na

ɗ

e cikin bargon makeken gadonsa.

Zainab,

ƴar aikin gidan dake tsaye cikin uniform dinta na masu aikin gidan ta zabura ka

ɗ

an tayi baya saboda yadda muryar ta firgita ta, ta saba a lokuta da yawa irin haka idan tazo dama da sigar da take samun amsar sa kenan, amma ta kasa sabawa har yanzu, ta kasa

sabawa tun sanda ta fara aiki a gidan.

"Hajiya ce tace in gaya maka tana nemanka."

Ta fada da karfi ka

ɗ

an yadda zai jiyo ta. Jamal yaja tsaki yana shafa kansa da duka hannayensa duka biyu. Ya tsani yarinyar nan, ya tsane ta har cikin ransa, matan mahaifin

sa uku ne, suna da ma'aikata fiye da hamsin a gidan kuma kusan rabinsu arna ne, idan ma akwai musulman to babu bahaushe ko

ɗ

aya a cikinsu.

Don haka ya rasa dalilin da yasa mahaifiyarsa ita kadai ta fita zakka ta

ɗ

auki irinta aiki, shi baya hausa ma tare da

ƴan aiki amma akan yarinyar nan ya fara. Kuma tun daga ranar da ya fara ganinta a

ɓ

angaren mahaifiyar tasa, sanda suka ci karo ta zuba masa miyar data dauko a kwanon hannunta yaji ya tsane ta har cikin zuciyarsa.

Har ya bu

ɗ

e baki zai bata amsa ya tuna ko

yayi turancin ma sai yazo ya fassara, don haka zata cigaba da tsaiwa a wajen tana kara maimaita masa abinda ta fada, ilai kuwa kafin ya gama tunanin yaji da wannan shakakkiyar muryar tata ta sake cewa.

"Hajiya ce tace in gaya maka tana nemanka."

Wai wa ya

gaya mata cewar Sunan Mamah Hajiya ne ma?

Ya ja tsaki kafin yace.

"Ina zuwa."

Shirun da yaji bayan wasu sakanni yasa ya fahimci cewa ta tafi, don haka ya kara jan wani tsakin kafin ya jawo wayarsa a gefe, karfe sha

ɗ

aya da rabi na safe, laifin me aka cewa

Mamahn ya sake yi da zata turo a tashe shi da sassafen nan? Missed call

ɗ

in Haro ya gani har guda tara don ya saka wayar a silent, gayen bashi da hankali wani lokacin.

Yana shirin sake maida wayar ya ajiye sai ga shigowar wani kiran nasa na goma. Ya

ɗ

auka

ya ƙara a kunnensa.

"Ina ka shiga ne J? Ka bar gari ne?"

"Yes, ina gida."

"Dole ka baro Abuja yau Jawad, don na gano hanyar da zamu lalata yarinyar nan?"

Ba shiri Jawad ya miƙe zaune yana sake rike wayar a kunnensa, kusan bakinsa na rawa yace.

"Me ka samo

? Me zamu yi?"

Daga cikin wayar Haron ya ƙyalƙyale da dariyar shakiyancinsa kafin yace.

"Ma'aruf Mansoor Bakori!"

**

_Me kuke tunani ya zama karshen hatsarin nan shekaru goma da suka wuce?_

_Wace mafita kuke tunanin Amina ta samo?_

_Ga dai Awwalu can na bi

n Baba..._

_Me ya Haro yake nufi da sunan Ma'aruf a matsayin hanyar da zasu hukunta Ruƙayya?_

_After all this, what do you think about the love Birds??_

_I'm here singing Confession Song by Omah lay..._

_Ku shirya ganin wasu Confessions

ɗ

in daga MMB...

😅

_

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details

0251365383

Wema bank.

Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.

#fikrawriters

#FararWuta.

°°°°°°°°°

*FARAR WUTA 2.*

*©AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*03*

~~~~~~~

_The best part is, I wasn't looking when I found you._ _- Unknown_

**

*Shekaru goma da suka wuce.*

Lokacin da aka shigo da gawar, lokacin da gidan ya sake hargitsewa da tarin jana'ar dake da ta shigowa da kuma masu kuka da salatin da muryarsu

ke

ɗ

agawa, lokacin Hajiya Maimuna ta bude fuskar gawar danta da aka shimfude a falon Baffa, hannunta ya rike zanin atamfarta da aka nanna

ɗ

o shi a jiki, danshin jinin dake jikin atamfar ya a ratsawa har tsakiyar kanta, a lokacin ne kuma abinda ya faru tsak

aninta dashi jiya ya dawo cikin kanta.

"Mimi...

Muryarsa lokacin da ya shigo cikin gidan ta ratsa kunnuwanta a jiyan. Tun da yayi sallama da Ladi ta bude masa ƙofar yake kwala kiran har ya shigo gidan, a lokacin tana kitchen, ta jiyo shi tana ta amsawa ama

shi bai jiyo ta ba gashi babu kowa a gidan, don safiya ce dukkan yammatan gidan sun tafi makaranta, don haka tana jinsa sai da ya zagaye kusan kowanne daki a gidan yana kiran sunanta a yadda shi kadai yake gaya mata wato Mimi, kafin ya dangana da kitchen

din.

Kuma shirun da tayi bayan ya bu

ɗ

e kofar kitchen

ɗ

in ya saka ta juyowa daga tukin tuwon da take yi. Ya tsaye riƙe da hannun ƙofar kawai yana kallonta, ta manta rabon da ta ganshi da manyan kaya, kullum cikin kananun kaya yake sune shigarsa a kodayaushe

, don shekara wajen biyar ya shafe a Cairo yana karatu don haka dasu ya saba.

Amma yanzu da ya dawo gida kuma ya karbi aikin kamfanin Bakori wani abu da yake burinsa kuma mafarkinsa tun yana yaro, sai ya zama dole manyan kayan su zasu zama kayansa.

Jamal y

afi kowa kyau a gidan, hakan wani abu ne da ba sai an lissafa ba, tun daga kan yayanta har zuwa na Kilishi babu wanda yake ko kama dashi, tun yana yaro mutane da yawa na cewa ma ba ita ta haife shi ba duk da cewar itama fara ce, amma baya kama da ita kuma

baya kama da kowa banda hancinsa da wasu suka ce yana shige da na Baffa don na Baffan ma dogo ne kamar nasan, akwai lokacin da yana shekara bakwai har sai da jama'a suka sa mata kokonto a ranta game dashi itama ta shiga tunanin ko anyi mata canjansa a asib

iti ne sai da Baffa ya dakatar da ita tukunna.

"Raina yana ta tashi har nayi zaton ko bakya gidan ne, muryarsa mai zurfi ta fada yana kllonta,.

"Allah ya sawwake maka, ta ina rai yake tashi Jamal?"

Ta fa

ɗ

a tana dariya kafin ta juya.

Ya karaso ciki ya tsaya

a kusa da ita yana kallon tukunyar dake jan gas din da take tuka tuwon da ita.

"Mimi kice min wannan miyar waken ce?"

Ya tambaya sanin cewar ta gaya masa tana da miyar tun jiya.

"Itace dai yanzu zan dauko ta daga freezer, kawai tashi nayi yau ina sha'awa

r tuwon."

"Alhamdlilah." Ya fada yana zura hannunsa cikin gashin kansa.

"Dama banci komai ba wallahi, ina tashi naga wai yaran nan dankali aka soya musu."

Shi baya son duk wadannan kayan cimar na zamani, abu kadan yake ci a cikinsu yafi son abincin gargaji

ya duk kuwa da zamansa a kasar waje, bama shi kadai ba kusan duka yayanta haka suke, har Ma'aruf idan bata manta ba.

A lokacin ne ya zaro wasu kudi daga cikin aljihunsa ya ajiye a gabanta, gaban flask din da ta gama kwashe tuwon a ciki, kuma ganin yawan ku

din shi ya tsayar da ita cak daga karasa abinda taje yi.

"Baffa ne yace in kawo miki."

Ya fada da sautin muryarsa da ya canja a yanzu, tana iya tuna yadda wani irin daci ya mamaye kirjinta a lokaci guda kafin ta yi kokarin ture hakan, hannunta ya kai kudin

tana fadin "Allah ya saka da alkhairi', amma sai Jamal yasa nasa ya dafe nata kafin ta dauka.

"Kudin cefane ne ko?" Ya tambaya, muryarsa na shaida irin bacin ran dake cikinta, bata amsa ba ya cigaba.

"Tunda Baffa ya bani kudin nan bake binsa da kallo, bai

ce min komai ba amma na fahimci baya miki magana tun last week, kuma na tambaye shi amma bai bani amsa ba, bana son inyi komai akan zargi Mimi, ki gaya min abinda nake tunani haka ne?"

"Jamal..." Ta fada tana kallonsa.

"Dan Allah." Yayi saurin katse ta.

"K

i gaya min gaskiya, ki san gyarawa zanyi, kin san ba zanyi abinda bai dace ba."

Wucewar wasu sakanni kafin ta gya

ɗ

a kanta a hankali tana cigaba da kallonsa.

"Akan zancen zuwa hutun su Munaya ne a Abuja, yace bai yarda ba kuma suna son zuwa, shine nayi masa

maganar cewa ta kanaya suje din, amma sai bai fahimta ba, sai laifin ya dawo kaina, yace sun fara girma sun fara raina maganganunsa ni kuma ina biye musu."

Ya kalle ta tsawon waucewar wasu mintuna kafin ya zura hannunsa cikin gashin kansa.

"Kiyi hakuri Mi

mi, insha Allah duk irin wadannan abubuwwan sun kusa zuwa karshe, na sha gaya miki akwai sa hannun wani a irin wadannan abubuwan dake faruwa tsakaninki da Baffa amma nq kusa gyara komai a gidan nan da yardar Allah, rayuwarmu ba zata cigaba da tafiya a haka

ba."

Sai ta girgiza kanta.

"Nima na sha gaya msaka cewa ka daina irin wannan tunanin Jamal, ka daina saka zargi a zuciyarka, wannan matsala ce dake faruwa a kowanne irin aure ba wai wani abu ba, duk sanda kayi naka zaka fahimta kaima. Amma babu ruwan kowa

a wannan al'amarin, kana gani dai ko Kilishi da muke kishoyoyi bata da matsalar komai to waye kuma zai saka mu a gaba? Akan me?"

Ya zura hannunsa daya cikin gashin kansa.

"Matsalar kenan Mimi, ba kya bari zuciyarki ta bude abinda yake kasan zuciyar mutane

, shi yasa ba kya yarda dani a kodayaushe, amma insha Allah kwanan nan zan nuna miki wani abu da zaki san ba zargi nake yi ba Mimi, so nake kawai in tabbatar in dai ina raye komai ya kusa zuwa karshe insha Allahu."

Haka ya fada a lokacin, amma ita kallo sa

kawai take yi tana son gaya masa cewa a wannan lokacin ba wannan ne fatanta ba, ba wannan ne buri ta ba, burinta bai wuce cewa yayi kokarin jawoata Ma'aruf zuwa kusa da ita ba, tana fatan hakan daga yadda take ganin alakarsu na tafiya, fon tun a wancan lo

kacin maganganun ƴ ƴanuwanta dun fara zama a zuciyarta, musamman a lokacin da Ma'aruf din ya kammala

karatun secondry dinsa, tana ganin ma'anar kowacce kalma da suka sha fada mata game da alaƙarta da

ɗ

an nata.

Sai gashi kwata-kwata awannin da hakan ya faru

basu karfin na kwana guda ba, yace in dai

Ina raye... Kamar wani abu a lokacin na gaya masa cewar zai iya rasa ran nasa da wuri.

Tana jin kukan su Shukra da sauran jama'ar gidan daga wajen falon, tana jin tashin kukan kowanne a cikinsu yayin da mazan dake

wurin ke ƙoƙarin basu baki, don an hana kowa shigowa a wannan lokacin, Baffa yace babu wanda zai ga gawar a wannan yanayin sai an shirya shi tukunna, itama ta shigo ne don ita mahaifiyarsa ce, babu wanda zai iya kallon idonta yace ba zata ganshi ba.

Idanu

nta na kallon gawar da tayi kaca-kaca da jini, kirjinsa ya dagargaje, ance bishiyar da suka daka shi ta soke don a saitinsa take, kuma har a yanzu ma akwai wasu kananun itacenta da suka hade da jikinsa da aka kasa cire su, jini yana malalowa a hankali har

yanzu daga jikin gawar yana jika kayanta a lokacin, don tana tsugunne a gabansa, sanye da wani tsadadden leshinta da tayi shirin zuwa biki dashi a ranar.

Tana jin yadda danshin jinin nan ke jiƙa kayanta, yana gaya mata cewa jinin Jamal ne,

ɗ

anta guda na fa

rko a duniya,

ɗ

an dake mutukar sonta fiye da komai a duniya,

ɗ

an da tun yana karaminsa zuciyarta ke cin buri akansa, wannan kyakkyawan Jamal

ɗ

in da kowa ke yabawa, kyakkyawan

ɗ

an da take alfahari dashi a kowacce, a yanzu vabu wannan kyan, babu kamanninsa m

a ko kadan, dogon hancinsa ne kawai ake iya ganewa a cikin kumburar da fuskarsa tayi ba. A cikin kunnenta muryarsa kawai take ji yana ce mata...

_Zafi nake jin Mimi, ko'ina a jikina ciwo yake yi..._

Haka yake ce mata duk lokacin da bashi da lafiya a makara

nta idan suka yi waya.

"Limamin ya iso."

Taji wani a cikin mazan dake bayanta yana fa

ɗ

a, sannan taji muryar Baba Usman yana cewa.

"An kira waya yanzu, ance an shiga da Ma'aruf din tiyata, likitocin sun ce anyi sa'a babu internal bleeding."

Sannan taji wani

a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login