Showing 93001 words to 96000 words out of 144990 words

Chapter 32 - FARAR WUTA COMPLETE



ɗ

akin hannuwansa da kafafunsa duka a

ɗ

aure, idanunsa suka bi kayan

da suka fadi sannan ya sake dawo dasu kan mutumin.

"Munyi yarjejeniya da kai Awwalu, ka san ni, na sanka kuma ka san ba'a a cin ku

ɗ

ina  a kwana lafiya..."

Ya fa

ɗ

i haka sannan ya

ɗ

ago daga kishingi

ɗ

ar da yayi, a gefensa katinan bankin Awwalun ne wanda suka

samu a cikin wallet

ɗ

insa, ya

ɗ

ebo su guda uku sannan ya watso su, suka taho tun daga inda yaken har zuwa kan fuskar Awwalun kafin su tarwatse a jikinsa.

"Babu komai a cikin wa

ɗ

annan accounts

ɗ

in, mun duba gidanka ma babu ko sisi..."

Mutumin ya hade hannay

ensa biyu sannan yace.

"Bana so in taba ka Awwalu ka sani, ka san wannan ne dalilin da ya sa na daga maka kafa tsawon watanni, ka san wannan ne dalilin da yasa na dade da yi maka shiru kuma ka san shine dalilin da yasa ni da kai muke kallon juna a yanzu...

"

Ya kai idanunsa kan agogon dake manne daga can saman dakin sannan yace.

"... Zuwa nan da ƙarfe shida, zaka iya zama tarihi Awwalu, don zan gwammace in kashe ka da ace ni da kai muna cigaba da rayuwa a duniyar nan kuma babu kudina a tsakaninmu."

Ya kai ka

rshe a lokacin da Awwalun ke kokarin gyara zamansa don duk abinda yake fada gaskiya ne ya sani, Ɗantaro abokin huldarsa ne da suka da

ɗ

e suna harkar cinikayya tare, a yanzu kudin da yake fa

ɗ

a miliyan tara, ku

ɗ

in wasu kayayyaki ne da ya karba a wajensa ya ai

kawa da wani kaninsa dake can garinsu don ya fara kasuwanci, kuma ba wai ya hana shi kudin saboda wani dalili bane ba, bai bayar bane saboda ya manta, a kwanaki biyun nan da al'amarinsa da na Kilishi ke cakudewa, kwakwalarsa ta manta da tarin abubuwan da b

ai san lissafinsu ba.

Lokacin da mutanen Ɗantaro suka shigo gidansa, yanayin shigar kayansu da yadda suka rufe fuskarsu, ya bashi tunanin cewa mutanen Kilishi ne don wannan ne kadai tunaninsa a yanzu, abinda yake gujewa kawai kenan, ya gansu ne da tunanin

ire-iren mutanen daya taba hada ta dasu ne wanda suka kashe Jamal.

Sai a lokacin da ruwan da aka watsa fuskarsa ya farkar dashi daga suman da yayi, ya bude idanunsa akan Ɗantaro da kuna yaransa sannan ya fahimci cewa zaren kaddarar tasa da saura, bai kai k

arshe ba har yanzu, yana da lissafin wasu kwanaki kafin a zo gabar da sa'ar da ya dade yana talawa zata ƙare, don ya riga ya sallama a yanzu, tunda har bai samu abinda zai bashi yardar Hajiya Salamatu ba shikenan duk wani shiri da kuma fatansa ya kare, don

a tsarinsa yana so yayi amfani da Hajiya Salamatun ne su boye laifinsa wajen tonawa Kilishi asiri.

Amma tunda bashi da wani mataimaki a yanzu, to ya san babu ta yadda za'ayi yaje ya tunkari iyalan Bakori don tonawa Kilishi asiri ba tare da ya bankada nasa

ba shima.

Don haka fatansa kawai shine ya bar garin Kano a yanzu, yayi nisa da arewa ma  gaba

ɗ

aya, ya tafi inda ko yanuwansa baza su sani ba, idan yaso da ya sami lokaci sai ya zauna ya gyara wadannan CD's din da ya dade yana recording muryar Kilishi a c

iki, ya cire duk inda ta ambaci sunansa da kuma muryarsa, idan yayi haka, sai ya turawa da Ma'aruf hakan yana daga inda yake, ya tonawa Kilishi asiri ba tare da kowa ya sanshi ba, idan yaso duk binciken da za'ayi idan basu gano shi ba, za'a karyatata ne a

dora laifin akanta ita kadai.

Don haka a yanzu da Ɗantaro ya kama shi zaiyi amfani da wannan danar ne kawai ya kwana biyu a wajensa, zai bari su rike shi ne har zuwa lokacin da hankalin Kilishi zai karkata daga kansa don ya san Ɗantaro karya yake ba iya ka

she shi zai yi ba, shi

ɗ

an kasuwa ne kawai mugu, amma muguntarsa ba ta tsallake wani geji.

Babban tashin hankalinsa kawai a yanzu shine wannan jakar da ya rasa, tunaninsa dama duk wani lissafinsa suna kanta ne, don idan har ya rasa ta bai san me ya kama ba

a rayuwarsa, dukka wani tanadi dama kuma nadamarsa zasu tashi ne a banza. Don haka a lokaci guda da Ɗantaro ya watso masa wa

ɗ

annan katinan a fuskarsa a lokaci guda wata dabara ta haska a cikin kansa.

Dabarar da ya san ba makawa itace kadai hanyar mafitars

a a yanzu, hanyar da zai tserar da kansa.

"Kayi hakuri Ɗantaro..."

Ya fada kai tsaye yana kallonsa.

"... wallahi banyi niyyar cutarka ba kuma ba guduwa nake shirin yi ba, kawai kwana biyu na shiga wani al'amari ya

ɗ

auke min nutsuwata gar na manta. Amma yan

zu zaka sami kudinka, wadanannan kananun accounts ne da katinansu ma sun dade da lalacewa, akwai wadanda nake ajiyar kudi masu yawa a ciki, su kusan duka dukiyata ma suna cikinsu ne, amma na barsu a cikin jakar dake hannuna lokacin da suka buge ni,ku duba

ciki zaku gani."

Dantaro ya kalle shi tsawon lokaci, ya kalle shi sosai yana nazarin sa, sai kawai ya murza yatsunsa biyu a iska suka fitar da wata kara ba mai yawa ba, amma duk da karancinta a lokaci guda kofar falon ta bude, wani katon mutumi ya shigo, A

wwalu ya gane shi a matsayin daya daga cikin wadanda suka kamo shi, banbancin kawai shine a lokacin fuskarsa a rufe take a yanzu kuma ya bu

ɗ

e ta.

Ɗ

antaro ya nuno shi kafin ya ce da mutumin.

"Kun ga jaka a hannunsa?"

"Eh yallabai, mun ga jaka amma babu koma

i a ciki sai wasu kaset don haka bamu taho da ita ba..."

"Ku koma gidan dauko ta."

Ya fadi hakan yana katse sauran bayanin mutumin kai tsaye wanda yayi saurin gya

ɗ

a kansa sannan yace.

"Yanzu kuwa yallabai."

Da haka ya juya ya fita. Ɗantaro ya sake juyowa y

a kalli Awwalu idanunsa akansa yace.

"Wannan gidan gona ta ne Awwalu, a bayan gari muke don haka idan har na gane cewa karya kayi min, ka sani cewa zan iya yi maka duk abinda na ga dama anan in gama ba tare da ka sami mai taimakon ka ba."

Awwalu ya gyada k

ansa.

"Babu dalilin da zani sa inyi maka ƙarya Ɗantaro, ka yarda dani idan har an samo wannan jakar baka da matsala."

Sai dai abinda daga shi har Awwalun basu sani ba shine, matsalar da yake fa

ɗ

a kuma matsalar da kowannensu ke gujewa, tana dab da taka kasa

r Nigeria a lokacin!

***

Wayar dake hannun Kilishi ta katse a karo na ba adadi da take danna lambar tana katsewa.

Idonta ya sauka akan tanadin data gama yi akan Awwalun, tanadin da yazo a safiyar yau da aka kawo mata har airport taje ta karba, a cikin kwal

i yake a rufe, amma duk da haka sai da ta bada dubu dari biyar ga ma'aikatan wajen na toshiyar baki sannan aka bata shi ta taho, don duk da basu san meye ba, jikinsu ya basu cewar ba abu ne da hukuma zata yarda dashi ba, tunda ko daga can kasar da aka kawo

shi ma, cikin sirri wani ma'aikacin jirgin ya fito dashi.

Babu wanda ya san menene, kuma kudin data basu ya toshe musu bakin tambaya, sai a yanzu da ita ta bude sannan ta ga meye a ciki ta kuma karanta komai dalla-dalla.

Allura ce, allura ce da ruwanta a

cikin wata yar karamar kwalba da sai da ta saka gilashinta ta ita karanta rubutun dake jiki.

Ruwan dake ciki high dose ne na Ritalin, cocaine, Adderall, da kuma wasu amphetamines Alcohol Hallucinogens Opioids, dake tafiya kai tsaye zuwa cikin kwakwala su l

alata wasu

ɓ

angare a cikinta ta yadda hankali zai gushe.

Bayan haka ta gama tsara komai, ita kadai ba tare da taimakon kowa ba, tasa an kama mata hayar wani gida acan hanyar Na'ibawa inda zata kira Awwalun can, sannan ta samu wasu inyamurai guda biyu da za

su taimaka mata. Tunda har da kudi komai ba matsala bane a wajenta.

Idan komai ya kammala kuma, ita da Sadiq zasu je gidan nasa su

ɗ

ebo duk wani abu da yake taƙama dashi akanta sannan su goge duk wani abu da zai iya bawa jami'an tsaro  wani bayani akanta t

unda ta san dole al'amarin zai ha

ɗ

a da hukuma idan har Awwalu yayi kwanaki baya gidansa.

To amma idan har ta gama wannan tsarin me zai sa kuma ta nemi Awwalun a yanzu ta rasa, lebbenta ya cije ta gefe guda ganin kiran ya sake tafiya kuma ya katse, ƙarya ne

ace Awwalu ya iya gano cewar tana yin shiri akansa, mataimakinta ne ta sani, amma bata bashi damar da zaiyi wannan tunanin ba, zuciyarsa da ta ru

ɗ

e shi ta ja shi wajen tunanin bijire mata bata isa ta haska masa wani abu akanta ba.

Hannunta ya lalubo lamba

r Sadik a cikin wayar, wanda bugu

ɗ

aya biyu ya

ɗ

auka.

"Kana ina?"

Daga cikin wayar Sadik yace.

"Ina Yankaba Hajiya."

"Yaushe rabonka da gidan Awwalu?"

"Ai Hajiya tun ranar da kika ce kar na koma idan bashi ya kira ni ba, to shima kuma bai kira ni ba shi ya

sa kawai na shiga harkata."

Ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya.

"Ka tafi gidan yanzu Sadik, ka gano min me yake faruwa, yana nan ko baya nan."

Sadik din ya gyada kansa.

"Shikenan Hajiya, amma nima ina son in tuna miki fa cewa lokaci fa yana ƙara tafiy

a, naji shiru kuma, gashi ni ina son hada kaya in bar kasar nan kin sani Hajiya."

Kilishi ta gyada kanta kusan sau biyu a lokaci guda.

"Kar ka damu Sadik, ina tunanin daga yau zuwa jibi ma mun kammala komai na sallame ka, kai dai kawai yanzu kaje ka nemo m

in Awwalun, da mun same shi shikenan, rabin matsalar mu ta warke m u ma."

Sadik ya danyi shiru kafin ya gyda kansa yace.

"Shikenan, Normal Hajiya, sai kin ji ni."

Yana fa

ɗ

in haka ya kashe wayar gaba

ɗ

aya. Kilishi ta sauke tata daga kunne tana sake yin wata

ajiyar zuciyar, fata take da dukkan abinda ke cikin ruhinta na ta sami Awwalu a yanzu... Don taga alamun komai na shirin tsaya mata ne idan har ta rasa mafita a wannan al'amarin nasa. Shi yasa a

ɗ

azu bayan ta fita zuwa airport ta dawo, bayan ta tabbatar ma

ganin nan yana hannunta, zuciyarta ta lissafa mata cewa ta fara rage sauran abubuwan dake gabanta kawai.

Don haka a karo na biyu kafafunta suka sake kaita zuwa

ɓ

angarensu Ma'aruf, Su Samirah na can na shirye-shirye a cikin gida don haka ta tabbata babu wan

da zai neme ta har ta gama abinda ya kaita.

Tana tuna yadda idanun Aminan suka yi a lokaci guda bayan ta bu

ɗ

e ƙofar taci karo da ita, yarinyar ta riga ta gama tsorata da ita ta sani, shi yasa bata da wata fargaba akanta yanzu, ta san zata yi duk abinda ta

sanya ta don tsirar da lafiyarta da kuma ta iyayenta da ƴanuwanta.

Abu biyu kawai ya rage mata a yanzu, abu biyu kawai, idan har tayi mata aikin Hamida sai kuma ta kwantar mata da Ma'aruf nan gaba kadan lokacin da zata gama da Baffa, da anyi hakan, ita ta

san ta yadda zata yi kuma ta raba aurenta da Ma'aruf

ɗ

in kafin tafiyarta, don babu ta yadda za'ayi ta tafi ta barta a cikin rayuwarsa, ta haska shi da ita ne kawai don cikar nata burin ba don nasa ba.

Ita kadai take so Ma'aruf ya zama yana tunawa a kodayau

she, ita kadai take so ya dauwama yana danganawa da duk wani abu taimako da kuma jin dadi na rayuwarsa

_"Wannan shine maganin da zaki yiwa Hanifa amfani dashi Amina, gashi nan kamar kwalli yake, ki tabbatar kin sanya mata shi a idanunta kullum, abinda kawa

i nake so daga ke kenan, idan har naga tasirinsa a cikin kwanakin da suke a lissafe, a cikin wa

ɗ

annan kwanakin iyayenki zasu mallaki sabon gida Amina..."_

Abinda ta gaya mata kenan bayan ta mika mata garin da yake baƙi a cikin wani hadadden kwanson sa kama

r kwalli, kuma a idanunta ta lura da cewar kamar yarinyar ta canja amma sai zuciyarta ta kasa danganta hakan da komai sai na canjin waje da kuma jin dadin da take ciki sabanin gidan iyayen ta.

Ta wullar da abinda tunaninta yake so ya fara, don ko kwanaki A

minar da kanta ta kai mata sachet din magungunan hana

ɗ

aukar cikin da ta bata da bayanin cewar ya ƙare... Kuma da hannunta ta dauki wani ta bata da ta san shima babu makawa zata shanye shi ne gaba

ɗ

aya, don haka bata ce komai ba bayan zancen maganin Hamidar

har ta baro wajen.

Ta dawo tana lissafin yadda abubuwa ke fara gara mata, yadda komai ke kara tafiya cikin tsarinta da kuma hangenta. Abinda bata sani ba shine, tsarinta dama damar ta take gani kuma take taƙama da ita sun kawo wata ga

ɓ

a da zata kai ƙarshe

n kowannensu.

Ta gama rufe maganin da ta bu

ɗ

e a cikin kwalinsa, sannan ta mike ta mayar dashi cikin kayanta, bangaren nasu sgirun yake ba kowa, don su Samiran gaba

ɗ

aya sun tattara sun koma

ɓ

angaren Hajiya Maimuna inda suke shirin tarbar Abdurrahim din a ca

n, tana ji Surayya na waya da Amina tana gaya musu cewa da ta gama nata aikin zata shigo itama, wani abu da ya da

ɗ

a tabbatar mata da cewar bata da wata matsala da yarinyar nan zata yi duk abinda tace hankali kwance.

Ta mayar da murfin wardrobe

ɗ

in ta ru

ɗ

e

a lokaci guda da wayarta ta

ɗ

auki ƙara. Sanin ko waye yasa ta dawo da sauri kuma sunan Sadik da ya haska a kan fuskar wayar yasa ta

ɗ

auka babu

ɓ

ata lokaci, kamar yadda babu bata lokacin muryarsa ta kwararo cikin kunnenta.

"Hajiya akwai matsala fa, motocin

ƴ

ansanda ne gasu nan zagaye da gidan, na tsaya daga gefe ba zan iya karasawa ba...."

Muryar Sadik din ta fa

ɗ

i kalaman da a lokaci guda suka dako zuciyar Hajiya Kilishi da wani irin tasirin da tunda take a rayuwarta bata taba jinsa ba.

Abinda bata sani ba s

hine, wani abu da zai zama sanadin tarwatsewar zuciyar tata gaba

ɗ

aya yana dab da taka kasar Nigeria a lokacin!

****

"Ta kawo min maganin Amma..."

Muryar Amina ta fada tsaye daga cikin kitchen din tana kallon tukunyar tuwan data tarawa ruwa a cikin sink

ɗ

in

dake gabanta.

"Tace yana aiki ne a lokaci ƙanƙani, tace ba zai

ɗ

auki lokaci ba komai zai fara, don haka zata saka ido ta gani, idan har komai ya tafi daidai, alkawarinta ba zai canja daga yadda ta fa

ɗ

a a farko ba."

Amma dake zaune a tsakar falonta tayi mu

rmushi mai fadi kafin tace.

"Kar ki damu Amina, ki kwantar da hankalinki komai ya riga ya fara ai... Dama ita kadai muke jira!"

***

_Meye yake dab da taka kasar Nigeria?_

_Me kuke tunani zai zama jam'in dukkan waddanan gibin?_

_Kuna tunanin abinda Amma ke

shiryawa yana da alaka da tonuwar asirin Kilishi?_

_Muna dab da fa

ɗ

awa cikin ramin dai...!_

_Kar ku manta da Jawad fa, tasa gudunmawar na nan tafe soon Insha Allah._

_Ku gaya min ƙiyamar Kilishi ta tsaya!_

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account

Details

0251365383

Wema bank.

Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.

#fikrawriters

#FararWuta.

°°°°°°°°°

*FARAR WUTA 2.*

*©AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*19*

_The fight between your heart and your mind i

s never easy..._

~~~~~~

"Mami..."

Sabon sunan da Hamida ta ra

ɗ

awa Amina ya ratso ta cikin hayaniyar kitchen din. Shigowarta kenan bangaren bayan ta gama aikin nata tuwon ta kuma gama waya da Amma, wayar da ta sanya ta farin ciki a lokaci guda, ya kore dukk

an fargaba da kuma damuwar da Kilishi ta saka a ranta bayan ta bata maganin nan.

Zuciyarta ta wanku tas da tsarin da Amma ta fitar musu, tsarin da babu shakka duk wayo da kuma hange irin na Kilishi bai isa ya tsallake dabarar tasu ba, don kamar yadda Amman

ta fada ne...

_"Na gaya miki takunta zamu bi Amina, da kifi ake kama kifi,kamun da baya ganewa har sai ya ji shi a cikin komar masunci... Idan kika bi irin takun da take bi, to kin riga ki gama tsallake tunaninta har abada._

_Tun kwanaki na gaya miki cewa

na fara shiri akan hakan, na gaya miki yarinyar zata makance a idanun Kilishi ne kawai amma ba'a zahiri ba. Don haka tsarin da nayi shine akwai

ɗ

an gidan Baffa Saliyo abokin mmahaifinku na unguwar Sharada, kin gane shi?"_

Kuma a lokacin kwakwalarta bata s

ha wahala ba wajen hasko mata fuskar saurayin da Amman ke fadi ba, shine Babba a gidan abokin mahaifin nasu kuna kwanan nan ya kammala karatunsa na likita har ma ya samu aiki a asibitin malam Aminu Kano. Don haka ta gyada kanta da sauri tana gaya mata cewa

ta gane shi.

_"Shi nasa aka kira min har cikin gidan nan Amina, sati guda da ya wuce, kuma yazo ya same ni da daddare har cikin falon gidan nan... Nayi masa bayanin komai ta sigar da ba zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login