Showing 75001 words to 78000 words out of 144990 words

Chapter 26 - FARAR WUTA COMPLETE

a cikin ku ukun, kika auri Alhaji Ibrahim Shanawa, mai kudin da kowa ya sanshi a wannan lokacin.

Kuma a sannan ne amincina da Kili

shi ya fara, don kamar yadda kika sani ni almajirin kakarta ne inda ta taso, a gidan nake aiki ana biyani da kuma bani abinci. Mun yi sabon da a wannan lokacin ta ksn gaya min yan kananun damuwarta, kuma tun daga lokacin auren naki, da taga irin kudin da a

ka kashe da kuma gidan da aka kai ki ta fara shiga damuwa.

Ta gaya min cewa duk a cikin ku ukun itace iyayenta masu karamin karfi, ta gaya min sanadin abotakar taku ma ya samo asali ne daga taimaka mata da kuke yi ta hanyar kudin makarantar da kuma sauran

abubuwan buƙata, saboda haka tace min tun a wannan lokacin tayi alkawarin samun dukiya itama,ta sa a ranta cewa zata yi ku

ɗ

in da zata kere ku duka, amma a lokacin sai gashi bata sami komai ba ke kin taka wasu matakan nasarar kala-kala.

Taji zafin hakan a l

okacin sosai ta hanyar da sai da ya zama a kullum tsakani na da ita bamu da wata hira sai taki, har ta kai tana gaya min cewa zata iya komai don ta tsayar dake daga cigaba da samun nasarar da tafi tata.

A haka har lokacin da kika sami ciki, zan gaya miki t

ayi baƙin cikin da duk duniyar nan bata iya nunawa kowa sai ni, kuma wannan shine mafarin lokacin da Kilishi ta fara jawo ni cikin zunubanta, a irin ku

ɗ

in da take samu a wajenki tayi min alkawarin wani kashi idan har zan taimake ta, na yarda ba tare da na

san abinda take shirin yi ba sai a watan da zaki haihu, ta same ni ta gaya min cewar ba zata iya jurar ganin kin samu magajin a wannan gidan ba, don haka tana son mu san yadda zamu yi mu kashe jaririnki bayan kin haihu kuma tun a asibitin.

Sai dai bamu sam

i wata mafita ba har zuwa ranar da kika haihun, ranar da aka kira ta cewa kina asibiti, a wannan ranar ne Kilishi ta sami mafitar da ta dade tana nema, bayan mun isa asibitin ni da ita ta sami hadin kan wata Nurse da ta yarda ta musanya miki dan da kika ha

ifa da wani matacce na wata mata mai tabin hankali da wasu mutane suka taimaka suka kawo ta asibitin ganin tana nakuda.

Ta shaidawa mutanen cewa dan matar ya mutu kuma za'a bayar a binne shi a asibitin sannan ta dauko gawar jaririn ta kawowa mijinki da kum

a yanuwanki, dan da kika haifa kuma ta danka shi a hannun Kilishi a blye ba tare da kowa ya gansu ba. Idan zaki tuna Kilishi bata asibitin a wannan ranar da kika haihu.

Ni da ita muka hayi mota muka fita har bayan gari tare da jaririn, a wannan wajen ta da

ge cewar mu kashe yaron, amma sai tausayinsa ya kama ni, ganin yadda aka dauko shi daga haihuwa, jikinsa duk jini don ko lokacin goge shi ba'a samu sosai ba, ana miko wa Nurse din shi bayan ta faki idon mutane ta canja shi da wannan mataccen, amma duk da h

aka baya ko kuka har muka isa bayan garin nan.

Saboda haka da kyar na shawo kanta ta bani yaron nan ta fasa kashe shi, nayi mata alkawarin zan dauke shi zuwa wajen da babu wanda zai taba sanin daga ina yake balle kuma asalinsa. A wajen ta bani kudin mota m

uka rabu, sai na kora wani abokina da yake almajiri shima na shaida masa komai,sai yabani labarin wata kanwar mahaifiyarsa dake aure a wani kauye yace min babu shakka ya san zata karbi yaron, fon haka muma tafi tare dashi.

A tasha muka sayi madarar jarirai

na samu na bawa yaron da kyar, sannan muka hayi mota guda zuwa wani kauye a hanyar Kaduna, wani kauye da ake kira da Garun Albasu, amma yanzu ance sunansa ya canja zuwa Yakura, anan muka sami matar kuma kamar yadda Ila ya shaida min ta karbi yaron babu wa

ni musu, nayi godiya sosai na bata ku

ɗ

i daga na hannuna sannan muka juyo.

Bayan na dawo na jinjinawa Kilishi komai kuma ta yaba min, daga wannan ranar ban sake komawa ƙauyen nan ba, ban sake tunawa da yaron ba sai bayan shekaru biyu, lokacin da naje wani a

iki da Kilishi ta tura ni a Kaduna.

Lokacin ne naje har gidan matar, aka shaida min cewa ta rasu shekara guda da ta wuce, na tambayi zancen yaron sai aka ce min babu wanda ya sanshi, sai da nayi bayani sannan da kyar aka sami wadda ta shaida min cewar tun

a washegarin ranar da na kawo shi aka sami wasu mutane da suka zo suka tafi dashi Abuja, da na ji haka sai kawai na share zancen na baro kauyen kuma ban kara bi ta kansu ba. Amma ina da tabbacin cewa da na kara bincikawa tsaf zan iya sanin inda yaron yake

a Abujan."

Awwalu ya kai ƙarshen dogon bayanin yana kallon fuskar Hajiya Salamatun da ko sau daya bata yi kokarin katse shi ba, kallonsa kawai take ui da idanunta da har yanzu basu canja ba, basu canja daga yanayin da suke tun a lokacin da ya fara magana b

a har zuwa yanzu, kallonsa take yi kamar kalma guda kawai ya furta tana jiran ya fara bayanin ne.

Amma a cikin kanta hotuna ne kawai suke wucewa, hotuna masu tarin yawa, tun daga wadannan shekarun da Awwalun ya dauko, lokacin da ta haihun aka shaida mata c

ewar ta rasa danta, lokacin da ta rike gawar yaron a hannunta, lokacin da take jin wani daci na sauka daga makogwaronta yana mamaye dukkanin jikinta, har lokacin da aka raba ta da abinda take tunanin shine natan, da yadda ƴanuwanta suka taya ta wannan baki

n cikin da fuskar Kilishi da tafi kowa nuna alhinin hakan,da irin hidimar data sha akanta don ganin ta dawo daidai.

Da yadda jama'a hatta ysnuwanta suka dinga yabawa abotarsu, da yadda bayan shekaru biyu ta kamu da wata matsananciyar rashin lafiya bayan ta

yi barin wani cikin, rashin lafiyar data taba mata mahaifa, da hoton fuskar likitsn dake yi musu bayani a wancan lokacin cewa da wuya ne idan har zata sake hsihuwa a rsyuwarta.

Da tarin rigingimun da tasha da wannan mijin nata kafin ya sake ta da cewar ba

zai zauna da juya ba, wani abu da ya zamo mafari kuma tushen tsanar maza a zuciyarta har ta kai duka aure biyun da tayi bayan nan ta kasa tsaida zuciyarta wajen hakurin zama musamman da mijinta na ƙarshe Alhaji Shamsu. Ga

ɓ

ar da har ta kawo ta cikin wannan

rayuwar da take kai, rayuwar da tun iyayenta na da rai suke kokarin hana ta har suka koma ga mahallincinsu.

Ashe duk wannan abin, aminiyarta ce sila? Kilishi ce silar da kalolin rayuwarta suka bambanta da buri da kuma tarin mafarkanta na zama uwa kuma mata

a gidan mijin da zata taso da nata ikon itama, ashe zalunci da kuma cin amanar Kilishi da kullum take yiwa hangen nesa ba'a kan kowa ya fara ba illa ita?

A lokacin ne ta rufe idanunta a hankali, tana jin zuciyarta na bugawa, da wani irin bugu da bata dan

ganta shi da komai ba sai na cewar ita uwa ce yanzu, ita uwa ce... Ta zama wannsn uwar da a kodayaushe taje mafarki, Allah ya mallaka mata wannan dsnar ya dawo mata da matsayin da kubce daga hannunta tsawon shekarun da taje jin nauyinsu a kirjinta. Kuma ab

inda ta sani a wannan lokacin shine ko zata ga dan nata ko ba zata ganshi ba, zata yi abu guda daya ne da take jin kamar Allah ya bar mata numfashinta tsawon wannan lokacin don ta zama sanadinsa.

_... haka kurum nake jin cewa kamar jibin nan ba zata karasa

ba wani abu zai faru._

Kalaman Kilishi a dazu da suka yi waya ya dawo cikin kanta, tabbas ta yarda da kalaman Awwalu, ta yarda Kilishi kamar wani rabin shaidan be ya fado duniyar nan, jikinta ya bata wani abu zai faru tun kafin Awwalu ya shigo gidan nan t

un kafin ita ta san komai.... Abinda kawai bata sani ba shine ashe ta hanyarta din, ta hanyar ita din da take gayawa karshenta zai fara.

Zaren labarin ya fara ne tun daga wannan ranar da tazo cikin gidan nan take gaya mata sauran tsarukan da take shiryawa,

tun daga wannan lokacin da suke wannan dariyar take jin zuciyarta na yin wani iri akan al'amarin aminiyar tata duk kuwa da a sannan tana jin cewa ba zata ta

ɓ

a iya tona mata asiri ba, sai gashi ba'aje ko'ina ba a wannan

ɗ

akin, a wannan

ɗ

akin dai da suka za

una tare nan

ɗ

in shi zai zama mafarin ƙaddarar da bata ta

ɓ

a lissafawa da ita ba.

"Na san da wuya ne ki yarda dani..."

Muryar Awwalu ta cigba da magana, sai kawai ta girgiza kanta a hankali tana katse shi, kuma tare da ta bu

ɗ

e idanun nata ba, kalamanta baki

nta suka fito, sautinsu ya fito da wani amo a hankali amma kuma wanda ya kara

ɗ

e falon...

"Ka kaini muje ƙauyen Awwalu, idan har na tabbatar da abinda kake fa

ɗ

a, zan taya ka mu tonawa Kilishi asiri a idon duniyar nan...!"

Ta fa

ɗ

i haka a daidai lokaci guda

da adadin mintunan kiran dake tafiya a cikin wayar Hajiya Salamatu ya katse dib!

***

*No 38 Ramie Street, Nassarawa GRA, Kano.*

Karo na biyar kenan da Ruƙayya ke sake kiran nambar, amma da ya tafi kamar zai shiga sai ya katse kawai, ba sai wani yayi mata b

ayani ba, ta san ya rufe layinta ne daga shiga cikin wayar tasa, tunda dazu ta gwada da wani sabon layin ta kuma ya shiga, sai dai ba'a dauka bane.

Sai kawai tayi wulli da wayar kan gadon da take kai, ta tafi kamar zata fadi zuwa

ɗ

aya karshen sai kuma ta t

saya bata karasa ba, hannunta ya dauko daya wayar tata dake gefe, ta sake lalubo nambar Jawad din

a ciki, har zata sake danna nambar da niyyar kira sai kuma ta tsaya, wata zuciyar ta gaya mata cewa babu dalilin da zata cusa masa muryarta idan har ya nuna c

ewa baya so, sanin cuwon kai a rayuwa ma wani abu ne.

Don haka ta nufi bangaren rubuta sako, cikin abinda yake kasa da minti guda ta rubuta dalilin nemansa da take yi. Sakon ya tafi a daidai lokacin da mshaifiyarta ta turo kofa ta shigo dakin.

"Wani abu ki

ke yi?"

Ba shiri ta girgiza kanta tana kallonta, sai ta gyada kanta sannan ta karaso ciki,da kowanne taku da take yi Ruƙayya na jin zuciyarta na bugawa sanin cewa bata da amsar abinda tazo nema din.

"Yazun nan muka gama waya da Hajiyan Sudan, ta gaya min c

ewa ta gama shirya komai tafiyar taku jibi ce."

Cewar Hajiya Nafisan va tare da ta zauna ba, daga kan gadon daga inda kafafunta suka lume gabadaya a cikin lallausan bargon Rukayya ta daga kanta sannan tace.

"Nima ta gaya min Maamah,

ɗ

azu da safe ta kira ni

a waya ta ce min tayi settling komai sai tafiyar mu kawai."

"To kin fito da kudin?"

Ku

ɗ

in. Abinda take gudu kenan, tambayar da take gujewa kenan, kwanaki hudu kenan da mahaifiyar tata ta tuna mata da wasu kudi da ta taba bata ta ajiye mata a bankinta, kud

ade ne masu yawan da a yanzu ta manta ainihin lissafinsu, sai skayi rashin sa'a a lokacin ta samu matsala da bankinta na ajiyar kudi, don haka ba tare da tunanin komai ba ta bawa Jawad da cewar shi ya saka a

ɗ

aya daga cikin bankunansa zuwa sanda zata tashi

nema.

Ya karba din tun a lokacin kuma ya ajiye, sai dai daga shi har ita sunyi mantuwa da hakan ta sigar da bata sake tunawa ba sai a yanzu. Sai a yanzun da mahaifiyarta ta gaya mata cewa ta fito da ku

ɗ

in dasu zasu yi komai, shi yasa a yanzu bata san ta y

aya zata fara yi mata wani bayani ba da ta san ba fahimta zata yi ba, don haka ta gya

ɗ

a kanta da sauri sannan tace.

"Anjima zan fita Mamah, anjima zan dauko su gabadaya."

Sai ta gyada kanta alamun ta fahimta sannan tace.

"Yau Daddynku zai dawo kin sani, ki

saki jikinki ki nuna masa kin hakura a yanzu da zancen Hamidan, idan ba haka ba kuma zai

ɗ

auki matakin da zai lalata mana al'amari kin sani. Kuma kar ki sake ko da wasa ki bari ya san da zancen tafiyarki, ni na san abinda zan ce masa."

Sai tayi kokarin fi

to da wani guntun murmushi daga siririn lebbenta sannan ta gyada kanta.

"Ba zan yi komai da zai kawo matsala ba Mamah kin sani, idan nayi haka na san kaina na

ɓ

ata."

"Sannan duk wanda ya kira ki da zancen Hamida kice musu kawai ta fara zuwa wajen mahaifint

a ne hutu. Kar ki kara komai daga haka."

"Me yasa ma sai an gaya musu hakan Maamah, ba dai daga

ɓ

angaren Daddy bane masu tambayar, ni babu wayar wanda zan daga."

Hajiya Nafisa tace.

"Na gaya miki ne ko da zaku yi magana da wani..."

Bata karasa ba wayar han

nunta ta shiga kara, don haka ta dauka ta kara a kunnenta sannan ta juya ta fita daga

ɗ

akin taiba magana, Rukayya ta bi ta da kallo, wani abu ya zarce a makogwaronta, ta san halin mahaifiyarta sarai, ba son dukkan wata mu'amala da ta danganci Ma'aruf take

ba, kawai tana yin komai ne saboda ita kawai don haka idan har zata yi saken da za'a kasa samun kudin nan akan lokaci,komai zai iya tsayawa m, zata iya yin wasa da damarta ta ƙarshe a yanzu.

Ta jawo

ɗ

aya wayar tata ta duba tarihin asusun da take dashi a ya

nzu na banki, kudin ciki basu fi rabin abinda Hajiyan Sudan ta nema ba, babu mai bata kudi a cikin ƴanuwanta ta sani, Ashraf ne kadai zai iya kallonta da wannan rahamar amma shima a yanzu wannan fetsararriyar matar tasa da baya yin komai sai da shawararta

ba zata bari ba.

A wajen mahaifinta ne kadai zata iya samun wani abu amma shima ta sam wanda bai taka kara ya karya ba, don tunda yayi ritaya ya shiga hsrkar buga-bugar kwangila baya son fitar da kudi sam wanda hakan halinsa ne tun a baya, kawai suna da wa

datar da ba'a ganewa ne... Kuma hakan ba daya daga cikin wani babban dalili da yasa mahaifiyarta ke dagewa kan ta auri mai kudi, don su samu ta wani

ɓ

angaren tunda ita mai son busasha ce.

Ta dafe kanta da duka hannayenta biyu, yatsun hannayen nata na shiga

cikin gashin kanta, Jawad ya sha bata kudi, yasha bata kudin da tana tarawa ta san ta wuce wannan lissafin a yanzu, amma bata karba din ne da hujjar cewa ba lada take nenya a wajensa ba, don ta yarda da cewar mu'amalarsu na tafiya ne saboda haka take so,

saboda ita take amfani dashi ba shi ba, saboda kuma bata son ya kalle ta da wani ƙasƙanci ko na ka

ɗ

an.

Tayi ajiyar zuciya a hankali tana sake kallon text

ɗ

in da ta tura wa Jawad, ita kanta ta sani a bayan wannan neman da take masa kuma akwai wani abu kamar

damuwa, damuwar da bata san dalilinta ba, a baya ta danganta hakan ne da shirunsa kawai, amma idan har zata yiwa kanta adalci ta san akwai wani abu ksmar kewsrsa a can kasan ranta, kawai tana danne shi da tarin dalilin da take bawa kanta a kullum.

Sai kaw

ai ta mike tsaye iskar dake shigowa daga winfon dakin na kada lallsusar rigar baccin da 'ke manne a jikinta, idonta ya ksi ksn siffarta acikin mudubin

ɗ

akin, waye zai ta

ɓ

a cewa tayi aure har da haihuwar ƴa? Ai ko don kyawunta ta san ba zata ta

ɓ

a asara ba,

shi kansa Ma'aruf

ɗ

in bata son zubar da ajinta a wajensa ne shi yasa ba za ta tunkare shi ba.

Taso ganinsa lokacin shari'ar nan amma tunda har abubuwa sun canja, jiran nasa ne a yanzu, shi zai jira har zuwa lokacin da zai kasa lissafa asarar da yake yiwa k

ansa, tayi murmushi a hankali, siraran lebbenta suna talewa, da ta samu Ma'aruf ko meye a cikin tata zuciyar zai manta da Jawad shima.

Sai kawai ta kada kanta tana sake yin baya da gashinta sannan ta nufi bandakin dake cikin

ɗ

akin.

***

*Abuja.*

"Bata da la

fiya kamar yaya?"

Jawad ya tambaya tsaye daga kofar

ɗ

akin, yana kallon wata yarinya mai suna Kristy dake tsaye tana gaya masa hakan.

"Eh Yallabai, baya da lafiya tun jiya bai fita ba, as a matter of fact ma snce ne yau zata tafi gida."

Yarinyar da ta fadi

haka cikin gurbatacciyar hausarta jin ceqar tambayar da yayi matan da Hausa ne, ya cije lebbensa yana kallonta, wani tunanin ya gifta a cikin kanta na sakanni biyu, tun jiya bai ganta ba ance masa tana aiki sai wata banzar inyamurar aka aiko ta kawo masa a

bincin da bai ci ba don mukullin mitarsa ya dauka ya bar gidan kuma bai dawo ba sai dare, a yau ya farka ne babu tunanin komai akansa sai na son ganinta, to kuma ta yaya zai zo ace bata da lafiya? A cire ma maganar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login