Showing 81001 words to 84000 words out of 144990 words
cikin wani kango a sume jini na fita ta hancinsa da kuma kunnensa.
Aphasia.
Haka likitoci suka kira cutar da ta same shi, sunce gefen kwakwalar sa dake ai
ki da bangaren magana ne ya sami matsala sakamakon toshewar jini zuwa wajen, farkon rashin lafiyar tasa yana iya magana amma a gutsirtsire, cikin sautin da ba'a ma fahimtar abinda yake cewa duk da cewar da kankantarsa a lokacin.
Likitoci sun bada shawarar
yadda za'a dinga taimaka masa maganar da yadda harshensa zai koma daidai don sun tabbatar da cewar babu wani magani kwakwara game da cutar amma da yake shi yaro ne mai zuciya, tun a lokacin yaƙi bada ha
ɗ
in kan hakan, ya daina maganar ma gaba
ɗ
aya babu yadda
ba'ayi ba
amma haka ya taso kowa yana kiransa Kurma, don ko makarantar da yake yi a can ƙasar ma ta kurame ce irinsa.
"Mami fulawa ta kare, ku
ɗ
in drawer kuma sun kare su ma..."
Muryar Samirah da ta fito daga kitchen ta fada a gabanta tana dawo da ita daga
tunaninta. Ta juyo ta kalle ta.
"Sati
ɗ
aya kenan fa dana ajiye kudin nan Samirah,yanzu har kin karar dasu?"
Da murmushi a fuskarta tace.
"Wallahi Mami, abubuwan ne wannan week din da yawa, kinga munyi abincin sadakar uku na jikar Mama Rabin nan data rasu,
sannan ga wannan shirye-shiryen dawowar Ya Abdurrahim
ɗ
in kuma, surprise party muke ha
ɗ
a masa tunda ya hana kowa zuwa can.."
"Amma ni duk ban san da wannan ba."
"Mami kwana biyu fa ba kya ko zama a gidan nan, kamar wani abu yana damunki shi yasa kawai muk
a ƙyale ki..."
Da murmushi a fuskarta sanda ta fa
ɗ
i hakan, amma da ta san tasirin da kuma yadda suka shiga cikin kan Hajiya Kilishi da watakila bata yi wannan murmushin ba.
_.... Kamar wani abu yana damunki shi yasa muka kyale ki..._
Wannan wajen ya maimai
ta a cikin kan Hajiya Kilishi fiye da yadda zata iya ƙirgawa a cikin sakannni kawai, ƴarta ce wannan, ƴar da ta haifa a cikinta... Itace take gaya mata cewa sun ƙyale ta saboda tana cikin damuwa, sun ƙyale ta ba tare da sun damu su ji abinda ke damun nata
ba a matsayinta na mahaifiyarsu.
ƙ
wakwalarta ta tariyo mata wani abu a lokacin, tabbas ba zata iya tuna rana guda da wani a cikin ƴaƴan nata ya ta
ɓ
a damuwa da damuwarta ba, Ma'aruf ne kawai... Ma'ruf ne kawai ke ta
ɓ
a nuna damuwarsa akanta idan har wani abu
ya same ta, ko a yau ma s gajiye ya dawo yadsa ta fahimta daga muryarsa, smma ssi da ya kira ya gaishe ta ya gsya mata ya gaji ba zsi iya shigowa ba kafin ya shiga gidansa, amma a vikin yan shekarun nan ba zata iya tuna rana guda da ta ta
ɓ
a ganin wata da
muwa mai zurfi daga wajen ƴaƴan nata ba har kuwa wa
ɗ
anda ta yiwa aure yanzu, su kan dauki lokaci basu kira ta ba sau da yawa sai dai taji su suna waya dasu Samira.
Wani abu ya wuce daga makogwaronta yana son dasa mata wani abu da ba zsta taba yarda ba, don
haka sai kawai ta gyada kanta sannan tace da Samiran dake tsaye tans kallonta.
"Bari na kawo miki, har da na cefanen wannan watan ma jiya Baffa ya aiko dashi kun fita."
"Yawwa Mami, Madallah."
Abinda tace kenan kawai sannan ta juya tana gayawa su Zahra ab
inda zasu yi. Sai itama ta juya tana jin kamar zuciyarta tayi nauyi da abinda ya faru, amma kuma
kwakwalarta ta cigaba da gaya mata cewa hakan ba komai bane, da zarar lokacin da zata kammala komai yazo, su da kansu zasu gane gatan da ta da
ɗ
e tana yi musu,
yaushe aka ta
ɓ
a halittar ƴaƴan da suka juyawa uwarsu baya a duniyar nan? Shaidan ne kawai ke kokarin cin galaba akanta.
Ta isa cikin dakinta lokacin da idonta ya kai kan wayar da ta bari akan gado, mitunan kiran na da suka yi da Hajiya Salamatu na nunawa
akan fuskar wayar har yanzu, mamakin yadda akayi bata kashe ba kuma itama Salamatun bata lura ba ya kamata, sai kawai ta ƙarasa ta
ɗ
auke ta, har zata kashe sai kuma taji wani abu kamar murya na magana don haka ta kara ta a kunnenta kuwa daidai lokacin da t
a jiyo muryar Hajiya Salamatun daga can ciki tace.
_...a idon duniyar nan...!"_
Mamaki ya gifta a ranta na ma'anar hakan, amma sai wani gefen tunaninta ya bata cewar watakila hirarta ce kawai da wasu mutanen tunda gidan nata baya rabo da jama'a, don haka s
ai kawai ta kashe kiran ta ajiye wayar akan gadon sannan ta tafi daukowa Samirah ku
ɗ
in.
Da ace dan adam yana da ikon dawo da lokaci baya zuwa sanda yake so, da tabbas Kilishi zata so dawo da wannan ranar kuma wannan lokacin fiye da sau dubu a rayuwarta.
**
*
*Ƙarfe tara na safiya.*
Amina ta kunna gas
ɗ
in da ta
ɗ
aura frying pan da mai a cikinsa, idanunta suka tsaya akan man har lokacin da ya fara zafi, yayi zafin yama fara shirin ƙonewa kafin ta farga ta zuba ha
ɗ
in ƙwan da ta ha
ɗ
a akai.
Minti talatin kenan, m
inti talatin tun bayan dawowarsu daga asibiti, don a
ɗ
azu da asuban nan bayan ta gaya masa abinda take tunani yace ta shirya su fita, ya kira Munaya yace tazo ta dauki Hamida zasu fita.
Tun gari bai gama haske ba ta shigo ta dauke ta zuwa cikin gidan tana
bacci ma bata san me ake yi ba, kuma tana ta tambayar inda zasu je amma bai ce mata komai ba sai da suka tsaya a gaban wani
ɗ
an karamin Private asibiti da a samansa aka rubuta 24hours, (awa ashirin da hudu.).
A asibitin aka ha
ɗ
a ta da wata Nurse bayan ya y
i musu bayani, kuma minti takatin bayan hakan aka tabbatar musu da abinda suka zo nema cewar da gaske tana da cikin.
Ta sani, tunda Amma ta gaya mata ta yarda kuma tana ji a jikinta ma, amma a wannan lokacin sai take ji kamar wani sabon labari ne, kamar an
tabbatar mata da wani abu ne da a baya yake yawo a iska, kuma tun a cikin asibitin nan ta sani kwatanta irin murnar da ta gani a idanun Ma'aruf, wani abu ne da bata tunanin yana da geji, sai kuma tazo ta tankwa
ɓ
e komai a lokaci guda da ta gaya masa cewa b
ata so zancen ya fita ko'ina tafi son ya barshi a tsakaninsu.
Bata so ayi wani na ukunsu da zai sani, ta gaya masa tana da dalilinta kuma zai san hakan a gaba, amma bai fahimce ta ba, tayi kokarin ƙara yi masa bayanin amma sai kawai yace ta kyale shi kuma
a wannan lokacin da ta kalli idanun nasa ta san babu abinda ya fi dacewa illa ta kyale shin, don ta kasa tantance tsakanin farin ciki da kuma rashin fahimtar tata wanne yafi yawa a cikinsu.
Ta ƙarasa soya ƙwan gaba
ɗ
aya, ta fito da dankalin da ta soya a dee
p fryer, ta hada komai waje guda tare da kayan shan tea, sannan ta koma ta kwaba fulawa da kwai da butter tayi wani pancake da yayi taushi sosai guda uku.
A hannunta ta
ɗ
auko woven tray
ɗ
in da ta jera komai akai tana barin flask
ɗ
in ruwan zafin a kitchen d
in, kafafunta suka fita daga kitche
ɗ
in har zuwa hanyar koridon
ɗ
akunansu, wata doguwar riga ce a jikinta ta atamfa, dinkin jikinta mysi kyau ne don ko ranar da ta fsra saka ts su Samirah sun yaba dinkin sosai, ta daura dankwalin kawai a gaban goshinta, ba
yan
ɗ
aurin ya tokare da tudun gashinta mai laushi da yake a tsefe ya fito ko tawanne gefe ana ganin sa.
Fuskarta fayau take, don duk da halin da take ji suna ciki akwai murna kuma a ƙasan ranta fal, godiya ga mahallicinta kawai take mikawa a cikin ranta, t
ana jin cewa kamar babu wani abu a duniyar nan da zai iya daukar irin farin cikin dake cikin zuciyarta.
"Assalamu alaikum..."
Muryarta ta fa
ɗ
a bayan ta murda kofar dakin nasa, labulayen da iska ke motsawa ta fara gani a idanunta kafin shi, yana zaune daga
ƙ
arshen gadon
ɗ
akin kusa da bedside drawer dake kunne da fitila akanta, hasken fitilar da shi ka
ɗ
ai ne a cikin
ɗ
akin, kasancewar labulayen windunan sun hana hasken ranar da ya fara fitowa a waje shigowa ciki kuma sauran fitulun dakin duka a kashe suke.
Faf
fadar kafadarsa da kuma bayansa su ke kallo ta yayin da kamar kodayaushe hannunsa daya na riƙe da wayar dake kare a kunnensa.
Taji kamar ya amsa amma bata tabbatar ba don maganar da yake yi ma bata jin ta sosai, kafafunta suka taka a hankali zuwa ciki kuma
maimakon ta samu waje ta ajiye tray din hannun nata sai kawai ta tafi gabansa ta tsugunna gaba
ɗ
aya da kayan a hannunta, idanunsa suka kalle ta kuma kafin ta gama tantance idan fushi yake yi ko akasin haka, sai kawai ya kamo hannunta guda daya ya riƙe shi
a cikin nasa.
"Zuwa 11 na fito Insha Allah, ina ga muna da two hours kafin lokacin da zanje
ɗ
auko Abdurrahim..."
Ya fada a cikin wayar da ta san ba da kowa yake yi ba Faruq ne. Idanunta suk cigaba da kallonsa yana sauraren bayanin Faruq
ɗ
in, ba ma sai yace
mata ba, tana iya karantar cewa ransa a
ɓ
ace yake a cikin idanun nasa da kuma yadda jijiyoyin gefen wuyansa ke fitowa suna motsi su ka
ɗ
ai, gashin kansa ma wani bayanin ne ƙarara, gabadayansu a hargitse wasu sun durƙusa kamar zasu yi sujjada.
Sai kawai ta
zame farantin daga hannunta ta ajiye shi a ƙasa sannan ta miƙe zuwa gabansa ta zauna akan cinyarsa a hankali, da yatsan hannunta da bai riƙe ba tta shiga shafa gefen wuyansa a hankali kuma tana jin yadda makowagronsa ke tamkewa da ta
ɓ
awar da take yi, sai k
awai ta karya wuyanta ta cusa fuskarsa ta gaba
ɗ
aya a cikin nasa wuyan, tana jiyo muryar Faruq
ɗ
in dake bayani tar daga cikin wayar.
"... Yaron bashi da hankali B, yana gaya min wai baya tunanin nambar ma wani ya ta
ɓ
a yi mata rijista? Akwai layin da yake am
fani babu rijista ne?..."
Hannunta ya tafi daga wuyan nasa zuwa bayansa kuma a hankalin ta shiga zana masa harafan da ba lallai ta san ya fahimta a lokaci guda ba, don haka ta shiga yi tana ƙara sakewa... SORRY.
Har a lokacin kanta yana cikin wuyansa, tana
jin yadda ko'ina a jikinsa ke amsawa da abinda take yi amna kuma bai ce komai ba, baiyi wani motsi ba ko kuma ya kalle ta tun bayan riƙe hannunta da yayi.
"Zan kira ka Faruk ina zuwa."
Taji ya fa
ɗ
a a cikin wayar muryarsa na fitowa wani iri, kuma tana jin
wayar ta tsinke sai ta ƙarasa da fuskarta daidai kunnensa tace.
"I'm sorry Sugar, dan Allah kayi hakuri."
Muryarta ta fito da sautin da taji da ace dare ne zata iya tayar da hasken taurari su haska masa fuskarta sosai don ya fahimce ta, ta fadi hakan sanna
n ta janye kanta a hankali zuwa baya tana kallon fuskar tasa, kallonta yake yi kawai babu alamun zai ce wani abun amma duk da haka tana iya jin yadda zuciyarsa ke bugawa kamar tata.
Komai fushin da zaiyi da ita, bata jin zai karasa har cikin zuciyarsa, ita
mai rangwame ce akanta ta sani, sai kawai tasa tafin hannunta duka biyu ta rike kowanne gefen fuskar tasa.
"Ba fushi nake yi ba, me yasa kike bani hakuri?"
Ya yanke shawarar fada muryarsa na fitowa da wani irin amo da bai yi nata dadi ba, amon da yasa bab
u dalili a lokaci guda taji hawaye ya cika idanunta, bai fahimce ta ba har yanzu, bai fahimci dukkan bayanin da tayi masa ba, bata ta
ɓ
a tunanin kuma zai kasa fahimtar tata irin haka ba.
Zuciyarta ta matse da tunanin irin fassarar da yayi mata tun kafin ma
ta sani, tana jin wani abu na narkewa a cikin jikinta kamar ƙarfen da ake ƙonawa a cikin wuta, wannan yaƙinta ne ta da
ɗ
e da gayawa kanta hakan, babu wanda ya san wannan manufar tata a duniya bayan shi, ko Amma bata furtawa ba, shi ka
ɗ
ai
ɗ
in ne ta san ya za
ma dole ya sani kuma shi ka
ɗ
ai take tunanin zai fahimce ta su rufawa junansu wannan asirin duk da bai san komai ba, amma idan har yana yi mata wani tunani na daban nasarar me taci kenan?
Sai kawai ta girgiza kanta tana cigaba da kallonsa.
"Da zan iya zan t
attaro komai a duniyar nan Sugar, zan tattaro du gaba
ɗ
aya in jera a gabanka don su zama shaida cewar ba zan ta
ɓ
a yin wani abu da na san zai bata ranka ba, so nake kawai ka fahimce ni, ba zaka gane yanzu ba na sani, kuma lokacin da zaka gane
ɗ
in ma na tabat
a ba sai na sake yi maka bayani ba.
Roƙon ka kawai nake yanzu ka bani ha
ɗ
in kanka, bayan shi bana son komai Ma'aruf, kaine inuwata kuma kaine tallafi na, bani da wani mai kare ni a duniyar nan da ya wuce kai, bani da wani da zan dogara dashi
a duniyar nan
bayan ubangiji da ya wuce kai, kuma ba zan ta
ɓ
a daina godewa Allah ba da ya kawo min kai cikin rayuwata a lokacin da ban tsara ba kuma ban taba tunani ba, I will always love you in a way that I will never hurt you..."
A yanzu bata jin wannan kwallar data t
aru a cikin idonta, wani abu take gani a idanunsa take kuma ji a jikinta kamar kwarin gwiwar da ya sata ƙarasa maganarta.
"Zamu haifi babyn nan cikin kwanciyar hankali insha Allah Sugar, babu abinda zai faru, ka cire tunanin komai a ranka dan Allah ka yard
a dani, kamar yadda kake yarda da Faruq
ɗ
in nan."
Sai kawai ya girgiza mata kansa a lokaci guda sannan yace.
"Kar ki ta
ɓ
a ha
ɗ
a kanki dashi Babydoll, matsayinki da nasa daban ne a cikin zuciyata, there's no way ma da kuka zo kusa."
Ya fadi hakan yana matso
da ita jikinsa, kusa dashi sosai ta yadda take jin ƙarar bugun zuciyarsu ya ha
ɗ
e waje guda akan zare guda, sanyi da zafi, mai nauyi da mara shi da kuma siririn da ya yake ha
ɗ
ewa cikin dan'uwansa.
"Na yarda dake Noor, na yarda I'm just curious ne, abubuwa b
e suke neman ha
ɗ
e min ha
ɗ
e min waje
ɗ
aya matsalar office da kuma..."
Ya fa
ɗ
a hannunsa na kokarin lalubo zip din rigarta a hankali, wani abu da yake son wasa dashi a kodayaushe. Sai kawai ta girgiza mata kanta a hankali.
"Babu ruwan gidan nan da office my R
anger Handsome, ka bani damar da zan sa idan ka dawo wajenmu kaji kamar wata duniya daban ka shigo, kamar mun koma Mars ne mun bar musu duniyarsu da hayaniyarsu."
A lokaci guda murmushi ya su
ɓ
uce a fuskarsa yana kallonta.
"Really BabyDoll? Kamar me kenan?"
Ya tambaya yana
ɗ
aga mata gira
ɗ
aya, sai ta cije lebbenta na ƙasa alamun tunani kafin tace.
"Zamu zama iyaye nan da watanni masu zuwa..."
"Alhmdulilah." Ya katse ta yana gya
ɗ
a kansa.
Bata tsaya ba ta cigaba.
"... Kuma yau muka sani, yau aka gaya mana... S
o let's celebrate!"
Ya ƙara gya
ɗ
a kansa murmushinsa na ƙara yawa, yayin da a cikin kanta take godewa Allah ganin yana dawowa yanayinsa na Ma'aruf
ɗ
in ta.
"We should BabyDoll, me kike so muyi yanzu? I think ina da two hours kafin in fita."
Ya fada yana
ɗ
ora
goshinsa akan nata, hancinsa na ta
ɓ
a saman nata.
Ta sake cije le
ɓɓ
enta tana kallonsa sannan ta girgiza kai, duka fuskarsu ta girgiza a tare.
"Yanzu lokaci yayi ka
ɗ
an, kayi breakfast ka fita, celebration
ɗ
in zai fi da
ɗ
i da daddare."
A lokaci guda hannunsa
ya tsaya da ta
ɓ
a zip din rigarta da yake yi, ya janye fuskarsa daga tata yana kallonta sosai, da idanunsa da take jin kamar yana sace ruhinta daga jikinta, har a lokacin da murmurshi a fuskarsa yace.
"Tabbas zai fi da
ɗ
i sosai Babydoll..."
Ta gyada kanta it
ama.
"Zan nemo restaurant hadadde wanda suke da fitulu sosai 'cox we are going to take pictures na tarihi wanda zasu zauna har tsawon shekar...."
Bata ƙarasa ba lokacin da Ma'aruf ya kyalkyale da dariya yana
ɗ
ora kansa a gefen kafadarta ta dama.
"Menene? M
e ya faru?"
Ta tambaya tana murmushin da bata san na meye ba yayin da hannunta ke kokarin
ɗ
ago da fuskarsa. Tana jin yadda jikinta ke girgizawa da dariyar da yake yi.
"Na kasa ganewa, wai menene?"
Ta ƙara fa
ɗ
a sanda tayi nasarar dago da kan nasa, ya kalle
ta sosai yana girgiza kansa kafin yace.
"Babydoll da kika ce celebration kuma kika ce da daddare, abinda nake hangowa daban..."
Bata san lokacin da ta ture shi ba tana kiran sunan sa,