Showing 129001 words to 132000 words out of 144990 words

Chapter 44 - FARAR WUTA COMPLETE

kwatance wa su Tantin da suka kira ta a waya, don haka bata bude idanunta ba

sai a daidai lokacin da ta kai ƙarshe a wayar wanda hakan yasa tana bude idon ta kula da ita

"Alhamdlilah, Amina kin tashi? Sannu..."

Ta fa

ɗ

a kai tsaye tana ƙarasowa gaban gadon.

"Sannu Amina, sannu...."

Ta sake fa

ɗ

a tana rike hannunta wanda ba'a saka ma

sa allurar drip

ɗ

in da take ji a jikinta ba, sai tayi kokarin miƙewa a hankali tana kama hannun Auntyn Ma'un sosai.

"Sannu..."

Ta ƙara fa

ɗ

a tana riƙe ta.

Bakinta a rabe yake ka

ɗ

an amma bata ce komai ba... Wani abu ya wuce ta maƙogwaronta tana ƙoƙarin gyara

zamanta.

"Bari in zubo miki abinci ki iara jin kargin jikinki.."

Aunty Ma'u ta sake fa

ɗ

a tana ƙoƙarin juyawa, sai tayi saurin kamo hannunta da sauri tana kallon ta.

"Aunty me ya faru? Su waye suka yi hatsari?"

Muryarta ta fito a bushe kamar yadda lebbenta

yake. Aunty Ma'u ta girgiza kanta.

"Bari ki fara cin wani abu  Amina..."

"Aunty dan Allah..."

Ta katse ta tun kafin ta ƙarasa. Tana jin yadda wani abu kamar kwalla na kokarin cika idanunta yayin da bugun zuciyarta ke dokawa ta yadda bata tunanin ko yawu z

ai iya wucewa ta makogwaron nata.

Sai kawai Aunty Ma'un ta dawo ta zauna a gefen gadon ba tare da ta saki hannunta ba sannan tana kalonta sosai tace.

"Ma'aruf ne yayi hatsari tare da Hajiya Kilishi Amina, amma ba wani abu ne ya same shi ba, jikin nasa da s

auki, kar ki daga hankalinki sun ce babu abinda ya same shi... Ki samu ki ci wani abu yanzu, Amma tace za'a iya sallamar ki a yau, sai mu je ki ganshi...."

Abinda ta fada mata kenan, abinda ta rude ta dashi har ta kwantar da hankalinta ta iya cin wani abu

a abincin da ta kawo ba tare da ta san cewa babu zance

ɗ

aya daga da yake gaskiya ba a duk abinda ta fada.

Don bayan Amma ta dawo har kuma an kira likita ya sallame ta, tun daga hanyar zuwa wajen ta fahimci cewar al'amarin yafi karfin yadda ta lissafa shi..

. Babu kowa a wajen lokacin da suka isa, su Hajiya Maimuna da duk dimbin jama'ar da suka taru a wajen lokacin da aka kawo shi duk sun koma gida, can gidan da a yanzu ya koma kamar gidan zaman makoki saboda ƙarancin tashin hankalin da ya wanzu a cikinsa.

Do

n haka ita kadai aka bari ta shiga wajen yayin da su Amma suka tsaya daga waje... Kuma Amma ce  ma ta danyi mata bayanin abinda ya same da taji daga wajen su Hajiya Maimuna lokacin da tazo ta same su... Likitocin sun ce bugun zuciyarsa baya tafiya daidai,

sannan ya farka sau biyu amma duka ba'a haiyacinsa yake ba... Sannan bayan haka numfashinsa ma baya iya fita daidai (Respiratory insufficiency).

Bata san tsawon mintunan da ta shafe tsaye a wajen ba,ta san dai kawai lokaci mai tsawo ya tafi zuciyarta na ta

sake-sake da tunanin ayyana halin da Ma'aruf ko kuma sauran ahalin gidn ke ciki kafin wata Nurse ta gaya mata cewa su Amman dake waje suna jiranta.

Ƙ

afafunta suka dauke ta zuwa waje, dogon koridon asibitin inda t barsu a zaune, dogon hijabi ne a jikinta n

a Maryam wanda Baba ya dawo daga baya ya kawo mata, ta fita daidai lokacin da su Amman ke gisawa da Ishaq da kuma Abdurrahim wanda suka ƙaraso a lokacin, kuma kallon Ishaq din kawai tayi taji kwalla ta cika idanunta don haka kanta a sunkuye ta karaso gaban

su sanda suka shiga gaishe ta da jiki shi da Abdurrahim

ɗ

in da kawai

ɗ

ago mata hannu yayi.

Ta share hawayenta da bayan hannu sanda Amma ke gaya musu cewa ta kira su Hajiya Maimuna babu wanda ya

ɗ

aga idan yaje yace musu zasu tafi da ita gida zuwa jibi don t

a kara jin da

ɗ

in jikinta tunda Hamida ma na can tare dasu Maryam, Ishaq

ɗ

in ya amsa amma ko daga muryarsa ka

ɗ

ai Amina ta san cewar har yanzu ba'a haiyacinsa yake sosai ba, tashin hankalin da shi da kuma zagayen al'ummar dake gefensa ke ciki ya isa ya sa sh

i a kowanne irin hali.

Kowanne irin halin da mutum guda daya yayi  sandinsa ga tarin mutnen da a yanzu ita kanta bata san adadinsu ba....

Kilishi....!

****

Tana zaune akan kujerar da teburi ya raba ta da wadda

ɗ

ansandan dake kallonta ke zaune.

"Hajiya gwar

a ki bu

ɗ

e baki kiyi bayani kawai, komai yazo karshe, mun kama duk wani wanda kike mu'amala dashi a harkar ki, hatta sabon yaron ki Sadik Awwalu yayi mana kwatance munjeun taho dashi, sannan mun kama likitan da kika hada baki dashi a asibiti ma da cewar kin

makance, so ki bude baki ki yarda da laifinki, Shari'a sabanin hankali ce da za'a iya yi miki rangwame, baki da kowa kuma baki da komai a yanzu, don bana tunanin koa cikin iyalanki ko kuma yanuwanki akwai mai bin goyon bayan ki a yanzu.... Zai fi kyau ki

sallama ki saukaka mana aiki Hajiya..."

Dan sandan yayi dukkan wannan bayanin yana kallon Hajiya Kilishi, yana kallon fuskarta da take manne da baneji a wajaje da yawa da kuma karyayyen hannunta wanda aka sakale shi ta wuya bayan anyi mata gyara, idanunta

a tsaye suke cak!

A tsaye tana kallonsa, tsawon sakan

ɗ

aya biyu, uku... Kafin ya mayar da kansa kan file din dake bude a gabansa wanda akan farar takardar dake kai, jerin laifukan da ake zarginta dasu ne wanda tun farkon suka rubuta bayan an tabbatar da ka

ma ta da kwayoyin nan da kuma wanda a yanzu suka ƙara samu daga bakin yanuwanta bayan hatsarin da ta samu na biyu.

Baki da kowa kuma baki da komai...!

Sune kalaman dake maimaitawa a cikin kwakwalar Kilishi, suk sae dawowa suna komawa baya a lokacin... Tun

bayan lokacin da Ma'aruf ya fitar da ita daga asibitin nan, tun daga lokacin tunaninta ya tsaya, komai ya faru ne a idanunta kamar tatsuniya, kamar wani mummunan labarin dake faruwa a cikin mafarkin yaro, bata gama warware zaren daya kulle ta a cikin al'am

arin cewa yansanda na jire da ita suna nemanta ba, batagama lissafa hanyar mafitar ta da ta fara budewa ba,bata yi komai ba,tana cikin zagaye guda daya nesa kuma ga abinda zata ya kira da tashin hankalin duniya da kuma lahira ya riske ta.

Jiya rana ce da b

ata ta

ɓ

a tunanin tunanin Allah zai haiccce ta ba a duniyar nan, a dukkan tsare-tsare da kuma lissafin da a tsawon rayuwarta bata ta

ɓ

a hangen irin abinda ta gani ba a jiya, tana tsara komai kuma komai din yana tafiya daidai, kawarta Salamatu ce ma kawai kan

tuna mata da cewar a duniya take ba'a aljanna ba cewar wani abun zai iya zuwa mata a karkace, amma ko yazo din, tana daga kwance take sa hannun guda ta gyara shi.

Alah ya bata tarin nasarori a rayuwar nan, bata jin akwai abinda ta taba zanawa zuciyarta da

bai faru ba, bata jin ta taba ko da hasashen manufarta ne kuma hakan bai kasance ba, to dan me yasa sai a yanzu da rana tsaka kawa komai zai gargitse mata kuma ta yarda?

Ta yarda ta rasa Ma'aruf, ta rasa shi ta rasa kulawa da kuma ƙaunarsa. Babu kalamansa

ko a cikin kanta, ta ji su a lokacin da ya fade su kuma ta barsu a wajen, babu abinda ta dauko sai ciwo da kuma takaicin rasa shi da tayi ta wannan hanyar a raywarta, ta shirya dama, ta shirya barinsa don haka ta dade tana ywa zuciyar tata tanadi na wasu

abubuwa da zasu dauke hankalinta bayan ta bar cikin rayuwarsu, amma da hakan ya faru a lokacin da bata shirya ba sai ya dake ta da tsananin tashin hankalin da bata ƙara ganin wani abu da ya tsorata ta ba bayan hakan ba.

Ko sanda ya danna kan motar suka taf

i suka daki bishyar nan, bata ji tana tsoron mutuwa kamar tashin hankalin cewa an riga bude ainihin kammaninta a idanunsa ba.

Da kuma sanda ta kalli idanun su Baffa, Baba Usman, Ishaq, abokin Ma'ruf mai suna Faruq da kuma Abdurrahim... Ta kalli idanunsu ne

tana jin zuciyar fayau yayin da tunaninta yake wasai, don tunda zuciyarta ta kar

ɓ

i tashin hankalin wajen Ma'aruf bata tunanin kuma akwai wani abu a duniyar nan da zuciyar tata zata sake rusunna masa, hatta Baffan kuwa, hatta shi din da ya zame mata tsani

kuma hanya wajen aikata dukkan abinda ta wanzar a rayuwarta.

Tana kallon kowa ne kawai tana kuma jin abinda suke cewa, amma yadda bata furtawa Ma'aruf ko da kalma guda ba, haka babu abinda tace har wayewar garin yau, abu daya kawai take so ta yarda dashi s

hine cewar ba zata yi biyu babu ba, ba zata rasa Ma'aruf ta kunyata a idon duniya a rana guda ba sannan kuma ta rasa burin rayuwarta ba, ba zata ta

ɓ

a iyawa ba, ba zata yarda an zo ga

ɓ

ar da zata je ƙasa ba kamar yadda ta shar'antawa kanta a baya ba, har yan

zu tana da yardar cewar damarta bata ƙare ba, dole ne ta fidda kanta kamar yadda ta sa ba.

Dan sandan yace bata da kowa a yanzu,ta yarda, ta yarda da hakan... Don tun da ta rasa yardar Ma'aruf ta sani cewa ko yardar ƴaƴan ta ba zata samu a yanzu ba, don ha

ka ta yarda zata barsu, zata bar kowa nata sannan zata bar kowa da ta sani, abinda bata yarda ba shine da yace bata da komai, wannan ne zuciyarta bata amsa masa ba don ita ta san tana da abinda zata kare kanta ko a gaban wane alkali ne a duniyar nan.

Amma

ba za'a kai nan ba ma, ba zata je gaban kowanne alkalin ba, zata yi nisane da kowa, zata yi nisa zuwa wani waje da zata kafa sabuwar rayuwarta, sabuwar rayuwar da ta san a cikin lokacin da zai ja mata... Dole ne yayanta zasu dawo gare ta, dole ne watarana

zasu juyo su waiwaye ta, don meye yake raba ya'ya da uwarsu a duniyar nan?!

Sai kawai ta mika hannunta mai lafiyar ta janyo file din dake gaban

ɗ

an sanda, ya dago ya bita da kallo fuskarsa na shaida mamaki da kuma tunanin abinda take shirin yi, ta ajiye fi

le din sannan ta sake mika hannunta alamun ya bata biron da yake rike dashi, sakan daya, biyu... Kamar ba zai bata ba sai kuma kawai ya mika ma tan, bayan ta karba yana kallon yadda yatsunta dama rubutun da take yi ke rawa, rawar dake shaida rikicewar da y

anayinta ke

ɓ

oyewa.

Lambobi ne, lambobi ta rubuta guda goma wanda ba sai ya tambaya ba ya san lambar asusun banki ne (account number), ta ajiye biron akan file din sannan ta sake turo masa shi gabansa.

Idonsa ya kalli lambobin sannan ya dago ya sake kallon

ta, a lokacin ne kuma tayi magana ta fa

ɗ

i abinda ba ga

ɗ

ansandan ba kadai, har ga ita kanta ya tabbatar mata da cewar har yanzu tana nan a matsayin Kilishinta.... Tanan bata canja ba!

"Akwai kudi sama da miliyan dari hu

ɗ

u a cikin account din nan, ka taimak

e ni in fita daga wannan wajen, ka taimake ni inyi nisa daga dukkan wadannan matsalolin dake rubuce a cikin file dinka, ni kuma nayi alkawarin zan baka rabin kudin da nake dashi, zan gyara rayuwarka ta yadda har ka koma ga ubangijinka ba zaka taba sanin

ɗ

a

cin Babu ba!"

Ta kai karshe a lokacin da idanun

ɗ

an sandan ke kallonta da wani irin yanayi mai wuyar fassara a lokaci guda!

***

A cikin

ɗ

akin asibitin ba ka jin komai sai ƙarar ka

ɗ

awar iskar Acn da ya kaure ko'ina.

Hajiya Mardiyya ta girgiza kanta riƙe da

wayar dake kare a kunnenta kafin tace.

"Kar ku damu Khadija, ki bawa su Innan ma hakuri, tahowarmu ba zata wuce gobe zuwa jibi ba insha Allah, ni ban san haka wannan asibitin yake ba da muka dauko ta wancan na gwamnatin muka kawo ta nan, su bamu refferal k

awai abu na neman gagara... Ashraf dai yace yayi magana da likitan dazu, ni ko bai yarda ba zan dauko ta ne kawai mu dawo ba zan jira ba."

Ta gyada kanta sannan ta sake cewa.

"Eh, Ahmad ne ya taho yau, da asuba ya kira ni yace Babansu yace yazo ya kawo min

saƙo... Amma shi kadai ya taho banda sauran."

Wadda suke wayar a ciki ta amsa kafin ta ta lashe wayar tana ajiye ta a gefen bedside drawer dake kusa da gadon, kusa da gadon da Rukayya ke kwance idanunta a rufe.

Kusan awa guda kenan da ta samu bacci, awa g

uda bayan ta farka da tarin surutan da a ciki basa iya gane komai sai sunan Hamida ƴarta da kuma Hajiyan Sudan da take ambata, Ashraf yace zai iya yiwuwa shine abu na ƙarshe da ta dinga fada lokacin da hatsarin ya faru, ta ga Hajiyan Sudan din a wancan asi

bitin na farko da suka je dauko Rukyya, ita bata ganta ba kuma bata bari ta ganta din ba, babu kowa a wajenta kafafunta na karye duka biyun an nade su da bandeji an kuma dage su zuwa sama.

Tana ji wata Nurse na fa

ɗ

an cewar har yanzu ba'a sami wani danuwant

a da zai zo ya biya kudin treatment da akayi mata ba... Bata ce komai ba suka biya kudin Rukayyan kawai suka karbi sallama suka juyo.

Don abu na karshe da zata yi a rashin hankalinta shine ta nuna wata mu'amala tsakaninta da Hajiyan Sudan

ɗ

in a gaban Ashra

f, ta sani kashinta ne zai bushe idan har mijinta ya san da hakan... Ya san abinda ta tura Rukayyan yi a Niger kuma tare da ƙawarta. Don haka bata ce komai ba har suka bar asibitin suka kawo ta wannan.

To a yanzu Ashraf din ya dame ta da tambayar wacece Ha

jiyan Sudan din da Rukayyan ke kira, ta gaya masa cewa itama bata san ta ba amma kallon da yayi mata bayan ta gaya masa hakan ta san ba na yarda bane.

Ta sake kallon Rukayyan, ciwonta da sauki ba kamar yadda suka zata a farko ba, mild stroke ne mutuwar bar

in jiki wanda likitoci suka tabbatar masu da cewar ba zai dauki lokaci ba zata warke ta koma daidai idan har za'a bi dokin da da kuma kaidojin da suka dace... Ita ta sani dama, ta san Allah ba zai jarraba su ta wannan hanyar ba, kyawun yarta ha

ɗ

e kuma kyaw

un jikinta wani abu ne da ba zai nakasa ba.

Don haka hankalinta ya dan kwanta ta yadda bata hango komai sai komawarsu Nigeria don su cigaba da jinyarta acan ba tare da asirinta ya tonu ba.

Lokaci ya nuna karfe biyu daidai yana tuna mata da sallar azahar di

n da bata yi ba, don haka ta mike ta shiga toilet din dakin ta dauro alwala sannan ta shimfida slaya a gefen gadon ta tayar, zuciyarta cike da fatan kafin idarwar tata, Ashraf ya dawo tare da Ahmad din da yaje daukowa daga airpot.

Ai kuwa sai fatan nata ya

karbu don a sallamar raka'a ta karshe su ma suka yi sallama suka shigo dakin.

Ta amsamusu a lokaci guda da ta fahimci rashin fara'ar dake kwance akan fuskarsu... Ahmad din ne ke gaishe ta yayin da Ashraf ya samu kujera ya zauna fuskarsa na numa tsananin b

acin ran da ta dade rabon da ta ganshi a fuskarsa.

"Me ya faru? Wani abu ne ya faru kuma?"

Ta tambaya tana kallon dukkanninsu... Kuma Ahmad din dake gabanta bai ce komai ba sai kawai yasa hannu ya ciro wata takarda daga aljihunsa ya dora akan sallayar da t

ake kai.

"Sakon da Daddy yace in kawo miki ne."

A lokaci guda zuciyarta ta buga a kirjinta, bata san meye a cikn takardar ba, bama tayi tunanin menene din ba, amma daga yanayin fuskokin yayan nata kadai ta san ba abu ne wanda zata so shi ba, dn hak ta yank

ewa kanta nisan taraddadin, ta mika hannunta a hankali wanda ke rawa ta dauki takardar, kuma tun kafin ta kai ga bu

ɗ

e ta, taji kwalla ta na neman cika idanunta yayin da kwakwalar ke gaya mata cewa ita ta riga ta karbi sakon tun kafin ma ya iso.

A rubuce a

ciki,  Hajiya Nafisa ta tadda kalaman da sune abu na karshe da kunnen kowacce mace zai so yaji su daga sautin mutumin da take raba rayuwarta tare dashi!

***

_Ƙaddarar dake jiran labarin nan a gaba ya danganta ga amsar da Hajiya Kilishi zata samu daga bakin



ɗ

ansandan nan...._

_Me kuke tunani?..._

Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300

Account Details

0251365383

Wema bank.

Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.

#fikrawriters

#FararWuta.

°°°°°°°°°

*FARA

R WUTA 2.*

*©AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*25*

_They tell you to be grateful for what you have, but you are also allowed to be sad for what you have lost..._

~~~~~

*Bayan watanni Shida.*

**

*Kano.*

*Central Prison.*

*03:00pm*

Ruwan ya cigaba da dukan rufin

dakin da wani irin ƙarfi fiye da kodayaushe. Karar tsawa da ake yi lokaci-lokaci tana cika iska da sautin da duk karfinsa baya disashe tarin surutun daje cikin dakin, tarin surutun dakin kurkukun wanda yake cike da fuskokin mata kala-kala. Manya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login