Showing 132001 words to 135000 words out of 144990 words
-manya da
yara farare da bakake, dattojai da yanmata wanda kowanne a cikinsu yake cigaba da rayuwarsa daidai kamar babu wanda yake da digon koda memory guda na wani abu daga bayan dogwayen katangar da suka zagaye su, kamar nan din shine mafari kuma farkon rayuwarsu,
kamar basu san akwai wata duniya dake wanzuwa bayan su ba.
Rayuwa bata da adalci, bata dashi ko kadan, wannan shine abinda Kilishi je maimaitawa a cikin kanta da fitowar kowacce rana da kuma faduwarta. Ta yarda rayuwa bata da adalci don babu abinda ke sak
a ta tsayawa, komai girmansa kuma komai kankantarsa ba abinda ke tsaida ita kamar dai ruwan daje zuba a yanzu, abubuwa suna cigaba da tafiya ne ba tare da wani ma yaje ko kusa da wajen da zai ji labarinka ba.
Damina ta dade da tsayawa ta yadda kusan kullum
ake kwara ruwan dake daukar awanni, kuma a duk lokutan da ruwan ke sauka, Kilishi na samun waje ne dab da wata yar karamar taga dake can sama ta zauna, ta zauna tana kallon tasirin zubar ruwan da kuma nauyinsa da take ji a zuciyarta, tana ayyanawa kanta c
ewa hawayenta ne wannan ke zuba, don irin kukan da ya kamata tayi kenan tunda a kirjinta dama idanunta babu danshi ko kadan balle ayi tunanin hawaye.
Ta kan so ayi ruwan lokacin da suke fita waje don ta zauna a cikinsa ya sauka a jikinta, ya sauka akan fus
karsa ta yadda zata ji sosai kamar hawayen nata... Idanunta a tsaye kyam suna shsida kamannin da ta sani cewa ba nata bane, ba itace wannan Kilishin da tayi wata rayuwa da zata rantse da ubangijin da ya halicce ta babu wata mace a cikin kurkukun nan da tay
i makamanciyarta.
Ba itace wannan Kilishin dake samun komai a zama daya da zuciya da kuma kwakwalarta ke sama mata mafita ba, sannan ba itace wannan Kilishin da ta shafe tsawon shekaru wajen gwagwarmayar samawa karshen rayuwarta tare da yayanta wata daddad
ar rayuwa da bata ko misaltawa ba.
A yanzu ita wata sabuwar halitta ce kawai, wata sabuwar halitta da ta rasa kowa kuma ta rasa komai, amma kuma zuciyarta ta kasa yarda ta karbi hakan, don idan ma zata yarda tana tunanin ya kamata ace ko da rabin mutanen d
uniya su jajanta mata, amma ba wai rayuwa ta cigaba da tafiya tamkar babu wani abu da ya faru ba.
_A tuhume ta akan kisan
ɗ
ana kawai yalla
ɓ
ai..._
Tun da aka fara wannan tashin hankalin, wannan maganar ta Baffa ita kadai ce abinda ya fitar da hawaye daga id
anunta bayan maganganun Ma'aruf, yace a ture dukkan wasu laifukanta a gefe, a tuhume ta kisan Jamal kawai wanda ta san yayi haka ne don ya tanadar mata wani abun daban.
Ko a lokacin da aminiyarta Salamatu ta baiyana a gabanta da tare da yanuwanta game da z
ancen raba ta da dan ta tsawon shekaru bata ji wsni abu sosai ba,don me take tunanin? Awwalu zai cigaba da lullube duk wani sirri nata da ya sani ne? Bakin cikinta daya ne ma da ya zamana akace Salanatun taga
ɗ
an nata, wani abu da duk da mamakin da ya bata
sai da taji ciwonsa har cikin kirjinta.
Salamatu bata taba taya ta mugunta ko guda daya ba,hasali ma ta kan kushe mata wasu idan ta kawo su, amma duk da haka tare suka faro tafiyar tana gaya mata dukkan sirrinta da kuma abinda take ciki don haka ko yaya n
e yaci ace itama ta karbi nata kamashon bakin cikin, ba'ace ita da Awwalun dai sune kadai zasu dandani zafin shari'ah ba.
A lokacin da dansandan nan yaki karbar tayin kudin da tayi masa, a lokacin da ya kalli nambobin da ta rubuta ya dago ya sake kallonta
sannan ya girgiza kansa, a lokacin wata wuta ta kunno a cikin kirjinta, wata wuta dake zafi tana kona duk wani ragowar emotion da take dashi tana kuma kara zafin kunci dake cikin zuciyarta wanda karara yake nuna mata cewa da gaske ne tata ta kare babu wata
sauran mafita kuma.
Daga wannan lokacin ta koma kamar wata gunki da aka sassaka ko kuma karfen dake motsi kawai, numfashi kawai take tana kallon tarin mutanen dake zuwa koyaushe wajen mata tambayoyin da bata ko fahimtarsu, ciki har da ƴan jaridar da tayi
zaton zasu watsa labarin nata zuwa kusufa-kusfar da zai sa duniya ta tsaya wajen jimanta mata, amma kamar yadda tace rayuwa bata da adalci, ba abinda ya faru!
Bata yi magana da kowa ba sai da akaje kotun sannan ta amsa dukkan tambayoyin alksli kai tsaye ba
bu wani musantawa ko kuma kokwanto, tana bayar da amsar tana kallon idanunsu Baffa, Baba Usman, Ishaq, Abdurrahim da kuma tarin wadu yanuwanta da acikinsu har da mahaifin Amina, Alhaji Sulaiman.
To don me ba zata amsa ba, ai ba su kawo wanda zasu daure ta
da jijiyoyin ta a jikinta ba, basu kawo wanda da yana wajen ta sani bakinta ba zai taba budewa ta amsa laifukan da aka zaiyano a cikin kunnensa ba... Ma'aruf!
Ya sani, ya san komai, ya san komai din da ya zamana ta san baya cikin haiyacinsa ma a lokacin, a
mma duk da haka da ace yana wajen, yana cikin kotun nan a lokacin da ake sauraren shari'ar, zata rantse da ubangijin da ya halicce ta cewa ko alkalin zai ce a kwantar da ita ana yankar naman jikinta
ɗ
ai-
ɗ
ai da
ɗ
ai-
ɗ
ai, ba zata ta
ɓ
a iya amsa wadannan laifuk
an a gaban idon Ma'aruf ba.
Amma har Baffa tana kallonsa ne kawai tana amsawa tare da tunanin abinda zai ji amma ba wai ita ba, har aka gama shari'ar aka yanke mata hukucin shekaru goma sha takwas bata jin ko da wucewar sakan guda taji nauyin wani daga vik
in mutanen dake wajen nan.
A yanzu ma ƴaƴan ta kawai take tunawa, tana jin yadda rashin ganinsu ke
ɓ
angarar da wani abu a cikin zuciyarta, yanuwanta da yawa sun zo, musamman wadanda take yiwa alkhairi, wasu ma bata ko fita ganinsu saboda bata ga abinda hak
an zai tsinana mata ba.
Don haka a yanzu rashin ganin yayan nata shine abu mafi tashin hankali da take fuskanta bata ko lissafin shekarun da zata kwashe a cikin wajen nan,don gani take kamar an fade su ne a kotun nan kawai, kamar an fade su ne kuma an rubu
ta amma baza su kasance a gaske ba... Gani take kamar zata iya fita, kamar idan ta yunƙura zata samu hanyoyin da zata fitar da kanta.
Amma matsalar shine har yanzu zuciyar tata ta kasa fahimtar komai a wajen na balle har ta fara tunanin hanyoyinta, Baffa
yana kassarata da wucewar kowanne lokaci a duniyar nan wajen hana ta ganin fuskokin ƴaƴan ta, ita Kilishi ce, mai zurfin tunani da hangen nesa, shi yasa a lokacin da yace a ture dukkan wani laifi a hukunta ta akan abu daya kawai ta zubar da hawayenta.
Shi
mijinta ne, ta san halinsa tsawon shekaru,ta san yadda yake iya hukunta mai laifin dake hannunsa cikin salama ba tare da kowa ya sani va, hukuncinsa mai sanyi wanda zai daskarar da jinin jikinka hankali kwance yadda duk ihunka babu wanda ya isa ya ji ka,
shi yasa yake da kai zuciya nesa a komai na rayuwarsa, da wuya kaga ransa ya baci akan wani abu don idan har ya bacin to shi kansa ya sani cewa hukuncin da zaiyi daban ne,ta san wannan... ta san wannan tun a shekarun farko data aure shi.
Shi yasa zuciyarta
take rabewa da kowanne motsawar lokaci idan ta tuna hakan, idan ta tuna yadda rayuwar kowa ke cigaba da tafiya babu ita kuma kamar ba'ayi ta din ba, don yanuwanta sun gaya mata cewa har sake gini anyi a gidan an rushe bangarenta.
Mamakin yadda rayuwa ke j
uyawa dan adam baya a lokaci guda shi ke dada cinye ta, kamar badu saba ba, kamar ba itace mai yarje mata komai ba, kamar ma bata santa ba, ace komai ya ƙare a lokaci guda? Komai din da zai hada har da ya'yanta, banda wannan tarin dukiyar da ta shafe sheka
ru tana ajiyarta, shi yasa a kullum take fada tana karawa rayuwa bata da adalci, bata dashi ko kankani....
Tana zaune ne kawai a yanzu ba tare da wata mafita ba, abu biyu kawai take hasashe shine watakila idan har ta mike da ƙarfinta da kuma dabararta ba l
allai ne ta kai wannan shekarun da aka gindaya mata a kotu ba, amma kuma matsalar shine bata da karfin, a kullum kuma a kowanne wayewar farin Allah Baffa yana kara kassarata ne da hukuncinsa na hana ta ganin yayanta... Shi yasa duk yadda ta kai ga ture wan
i tunani a zuciyarta tana ji kamar zata yarda dashi akan cewa.
Karshen tika tika dole TIK ne! Dole ne ta yarda cewa komai ya kare mata, kuma dole nrme ta yarda da abinda Ishaq ya kalli cikin idanunta ya fada mata a ranar da za'a kawo ta gidan nan...
*'Wata
shari'ar sai a lahira Mami...!'*
Rugugin tsawar da ake yi ya cika iska a lokacin, walkiya ta haska tar ta kuma haskawa a cikin duhun hadarin, sai kawai ta sake
ɗ
aga idanunta tana kallon zubar ruwan ta cikin tagar
ɗ
akin, ta cikin hayaniya da kuma dararraki
n mutanen dakin, kuma ba tare da tayi zato ba a lokacin wata guntuwar ƙwalla ta cika idanunta tana gangarowa kan fuskarta, wannan shine karo na uku da taji dumin hawaye a kan fatarta, kuma wannan lokacin shine karo na farko da tambayar da taƙi bari ta yiw
a kanta tun a zamanin farko ta
ɗ
arsu a cikin zuciyarta... Wannan tambayar da take gujewa, tambayar da bata ta
ɓ
a lissafa ta ba balle ta yi tunanin matsayinta na Kilishi zai kai ta ga yinta....
Ta yaya zata mayar da rayuwarta baya shekaru goma da suka wuce?
Dana sani....! Yau Kilishi ce da dana sani!
Dana sani a lokacin da komai ya kure!
Dana sani irin wadda kowanne musulmi ke gudu a duniyar nan!
Dana sani tun ta duniya kafin a je ga ranar da ƙafafunta zasu durƙushe a gaban ubangijin da shaidan ya janye hannu
nta ga barin umarninsa!
Abinda Kilishi bata sani ba ma shine kamar yadda Ishaq ya fa
ɗ
a ne... Wata shari'ar sai a lahira!
Hakki yana rama kansa ne cikin halaye biyu... Tun a duniyar da kuma lahirar dake jiran kowanne bawa!
Zata karbi abinda yake nata a yan
zu, kuma zata karbi abinda yake nata a can, ga rayuwar kurkukun da bata fara ganin komai a cikin ta. Gata nan... ita
ɗ
in ce dai Kilishin da take ce, da lafiyarta da karfinta har ma da tunaninta da komai da take takama dashi, kuma a cikin duniyar da take ga
nin ita da ita aminan juna ne ta kowacce hanya, sai gashi tasirin wasu katangogi ka
ɗ
ai!
Tasirinsu ka
ɗ
ai ya hana mata dukkan abinda take takama dashi da kuma iyawarta, tasirin shari'ar duniyar ka
ɗ
ai, ba ma akai ga mutuwa ba, balle kwanciyar kabari ko kuma t
ashi a gaban Mahaliccin da ta bijirewa da dukkan iyawarta!
***
*Kano.*
*Mai ƴaƴa Street, Bawo Road.*
*04:30pm.*
_So here we stand in our secret place_
_Where the sound of the crowd is so far away_
_You take my hand, and it fees like home_
_We both understa
nd, it's where we belong..._
An dauke ruwan, amma har yanzu garin da danshi, iskar da take kadawa mai sanyi ce, Zainab tana jinta akan fatar ta da kuma wuyanta yayin da mai kwalliyar dake gabanta ke ta aikinta na fente fuskarta, sassanyar wakar qmwestlife
ta queen of my heart kuma na tashi daga cikin Mp3 din studion...
"Kiki, miko min brown liner nan..."
Mai yin kwalliyar ta fadawa wata yarinyarta dake gefe, Zainab ta bude idanunta bayan Aysha ta juya karbar liner, idonta ya gane mata wata ita din daban a c
ikin mudubin dake kallonta, wata kyakkyawa mai kama da ita din da da take ganin kamar ba ita ba, powder da aka saka da komai ta bi fatar jikinta tsaf ta kwanta tana fito da kowanne tsini da lankwasar sa, musamman hancinta da taga ya ƙara tsawo fiye da yadd
a da ta sanshi, ga kwsllin da ya fito da idanunta tar yana shaida hasken ƙwayar cikinsu.
Gabanta ya fadi ya kuma faduwa hannunta yayi nauyi yayin da surutun da yan mata biyun dake bayansu ya cika kunnenta, ds kuma muryar Ameerah dake waya can gida akan a k
awo mata takalminta da ta manta.
Can gida, can gida yana nufin gidan Hajiya Salamatu mahaifiyar Jawad da kusan komai na harkar bikin da ake yi yake hannunta da kuma yanuwanta.
Watanni shida kenan da Jawad ya same ta a cikin tashar nan, watanni shida kenan
da rayuwarta ta canja, don tun daga wannan lokacin tun daga wannan ranar abubuwa suka fara sauki a rayuwarta, Jawad ya mayar da ita har gida can wajen yanuwan mahaifiyarta, inda baya nan aka sha artabu tare da mijin mahaifiyarta akan cewar ya barta ta
ɓ
ata
, babu wanda ya nuna masa cewa tana can hatta dansa kuwa Nura, sai da hankalinsa ya tashi ya fita daga haiyacinsa baki
ɗ
aya ya tabbatar ana shirin kaishi kotu sannan yazo ya bada hakuri.
A lokacin ya san tana wajensu, kuma ga mamakin kowa sai ya fa
ɗ
i magang
anu san ransa sannan ya tashi ya tafi. Kuma tun daga lokacin tun daga lokacin da hankali sa ya fara kwanciya, sannan Jawad din ya koma Abuja ya dawo bayan wasu kwanaki, sai ya zama babu abinda ake yi sai maganar bikinsu wanda ba'a samu wata matsala da yan
'uwan mahaifiyar tata ba wajen amincewa.
Kuma sai bayan nan ne sannan ya shaida mata dukkan abinda ke faruwa a tasa rayuwar, abinda ke faruwa tun a lokacin da ya
ɗ
auko ta daga Abujan nan game da rikicewar rayuwarsa da kuma yadda Allah taimake shi ya samu m
ahaifiyarsa a cikin ƙanƙanin lokaci, dama babban abin manakin na cewar tsawon rayuwar tasa da ya shafe tun daga yarinta a gidan yayan mahaifinsa yayi ta ba wai a wani waje da yake bare ba.
Ta da
ɗ
e tana mamakin kasancewar hakan, sai dai duk mamakinta bai k
ai na yadda har a lokacin Jawad ya dage akan aurenta ba, don har a cikin yanuwanta daga mazan har matan wa
ɗ
anda basu furta cewa tayi sa'a ba kadan ne...
Ita kanta ta sani, ta san hakan ne kawai suna tuna mata ne da irin sa'ar da tayi, shi yasa bata da wa t
a cewa a dukkanin abinda ake yi, don ta sani bata da wani gata a yanzu idan ba Jawad ba, ko su yanuwan nata da suke faram-faram da ita don na doki ne da kuma tausayawa rashin mahaifiyarta da tayi da kuma
wahalar da ta sha a hannun mijin mahaifiyar tata, s
annan bayan haka ma ta sani cewa da yawa suna mutunta ne kawai saboda ganin Jawad
ɗ
in.
A can garin nasu aka daura auren, yanuwansa da yawa sun je har dasu Hajiya Mardiyya daga can Abuja da kuma dangin sabuwar mahaifiyar tasa, don haka fadar tarin mutanen d
a ta gani ranar daurin auren nan, wani abu ne da ba ita kadai ba har dangin nata sunyi mamaki... Kuma a ranar ta sha kuka kamar me tayi kukan rashin mahaifiyarta sannan tayi kukan farin cikin da bata san irin yadda zata fallasa adadinsa a kirjinta ba, Tayi
hamdala ta godewa Allah fiye da yadda zata iya kirgawa a lissafinta.
Bayan haka kuma tayi kukan fargaba na irin rayuwar da zata je ta tarar a gaba, don ta sani a yadda zata shiga rayuwar Jawad bata da komai kuma bata da iyaye tsayayyyu dole ne ta fuskanci
wasu abubuwan daga mutanen dake kewaye dashi wanda na lallai suyi mata dadi ba... don ko a ranar daurin auren nan ta raina kansa a cikin kowanne bangare na yanuwansa sau dubu tana sakewa...
Kuma a wannan ranar ne aka basu ita suka taho Kano yayin tare da
wasu yanuwan nata yayin da su Hajiya Mardiyya duka wuce Abuja. Sun taho tare da kuma tarin kayan da su Jawad
ɗ
in suka kai wanda har a yanzu bata mayar da hankalinta wajen ganinsu ba kasancewar yadda aka dinga rububin kallon kayan a can garin nasu.
Kuma bay
an sun zo ne suka tarad da gagarumin bikin da mahaifiyarsa ke shiryawa wadanda ta ga kamar sun fi karfin tunaninta, don kusan komai an gama shirya shi hatta kayan da zata sa an gama dinka su, sai bayan da tazo aka gwada aka ga wajen da yayi mata yawa sanna
n aka mayar aka da
ɗ
a gyara su.
Kallon komai kawai take tana kuma kallon kowa tare da ita da yanuwan nata da suka zo kawai, an hada ta da wata yarinya Ameerah da kusan ita ke jan ragamar komai nata, ita ta gaya mata dukkan shirye-shiryen da suke yi na cewa
r za'ayi walimar iyaye ne (mother's eve) a yau washegari da safe kuma za'ayi budar kai tare da yini sannan jibi zasu tafi can Abuja tare da Jawad din su kuma tari nasu Hajiya Mardiyya da suke shiryawa suma kafin a dangana ta da sabon gidan da ya kama kusa
da wajen aikinsa.
Sai a lokacin da taji hakan ne sannan wani sabon kukan ya sake cike kirjinta, ta sani yanuwan mahaifiyar tata sunyi nasu kokarin, don da karo-karo da kuma gudumawa kala-kala aka hada mata kudi dubu hamsin bayan sadakinta da aka kawo na du
bu hamsin din shima da cewar ta siya wasu kayan amfanin idan taje gidanta, ko da kayan kitchen