Showing 108001 words to 111000 words out of 144990 words
tunaninsa ba... tunaninsa
ɗ
aya ne, he's free at last! Don haka ta ina zai fara??
***
_Ta ina kuke tunanin kowa a wannan babin zai fara?_
_Ta ina Kilishi zata fara?_
_Ta ina Jawad zai fara?_
_Ta ina Hajiya Salamatu zata fara?_
_Sannan ta ina Awwalu zai fara?_
😅
_Wai ina Rukayya ne??
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatap
p number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
°°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*21*
_Sin makes its own hell, and goodness its own heaven.-Mary Baker Eddy_
~~~~~~
Ƙ
arar tashin jirgin ta rag
u a cikin kunnen Jawad, yana jin yadda tafiyar jirgin ke ƙoƙarin daidaita a sararin samaniya, yana jin kamar kafafunsa na bin gudun jirgin ne zuwa garin da suke dosa, yana jin yadda tasirin tazararsa da Kaduna ke yagewa a jikinshi, zaren na yin tsawon da b
ai san ta yaya zai kwatanta shi da wani sunan ba face cewar yana barin Zainab ne a baya, yana barinta a cikin halin da bai sani, halin da bai ko iya ganin fuskarta ba balle ya iya kintata halin da take ciki.
Sai kawai ya koma da baya ya rufe idanunsa, yayi
n da a hankali bi da bi abinda ya faru awannin da suka wuce tsakaninsa da Nura ya shiga dawowa cikin kansa.
*
"Karya yake..."
Abinda Nura ya fada kenan yana kallonsa a lokacin da yake tsaye a gabansa. Shi din da ya dawo ya sake nemansa lokaci kadan bayan r
abuwarsu, don a tunaninsa tun bayan lokacin da suka sauke shi sun dade da barin garin, sai gashi cikin abinda yake kasa da awa guda kiransa ya sake shigowa wayarsa da tambayar yana ina? Kuma bai bata lokaci ba ya shaida masa inda taken duk da mamakin da ya
kama shi, wajen da cikin abinda yake kasa da minti goma yazo ya same shi.
Tun kafin ya tsaya ya hango motar don haka ya taho ya iske shi a daidai jikinta bayan ya fito.
A wannan lokacin Nura zai rantse da Allah duk da ya dade da sanin halin mahaifinsa ba
karamin mamaki ne ya sake lullu
ɓ
e zuciyarsa ba lokacin da Jawad din ya shaida masa abinda ke faruwa.
Farko, yayi mamaki sosai da ya kasance yarinyar ta zama Zainab
ɗ
in da ya sani cewar a kwanakin nan an rasa zaman lafiyar gidansu saboda ita, ya san ya kall
e ta a lokacin da ya fara haduwa dasu amma baiyi mata kallon da zai gane wacece ita ba don a tunaninsa matarsa ce, matar aure ce, matar da babu dalilin da zai sa shi kare mata kallo, don duk bu
ɗ
ewar idanunsa duk irin tarin zunuban da yatsunsa zasu lissafa
ya aikata a rayuwarsa babu harkar mata a cikinsu, a kodayaushe a kowanne hali yana daraja mata, yana basu ƙima da kuma darajar da ya san Allah ya halitta su da ita, don haka mace ko wace iri ce ba saka ta a ransa.
Mamakinsa na biyu akan mahaifinsa ne, mama
kin yadda kai tsaye ya ha
ɗ
a ƙarya irin wannan don kawai ya kore alkhairin da ya san cewa ba zai shafe shi ba... Don halin da yake ciki bashi da alaka da zuwan Jawad ko rashinsa kwata-kwata, kawai yayi hakan ne don son zuciya da kuma ƙoƙarin kuntatawa yarin
yar da ko maraicinta ba zai kalla ba don ya sassautawa rayuwarta.
Satin sa biyu da dawowa garin lokacin da mahaifiyarta ta rasu... Ya dawo ya tarar bata da lafiya kuma zai rantse kafin mutuwar tata akwai ranar da kunnensa yaji tana roƙon mahaifin nasa akan
ya dawo mata da ƴarta don tayi jinyarta, wanda sai a sannan shi ya tuna cewa ma tana da ƴa guda daya da tsohon mijinta, kuma a lokacin ne ya fahimci inda yarinyar take don da kunnensa yaji mahaifin nasa na gaya mata cewa idan yarinyar ta dawo bai san kuma
da wanne kudi za'a dinga samu ana siyo mata magunguna ba don shi bashi da shi.
Rigimar da ake ciki kuma a gidan ta fara ne tun bayan rasuwar mahaifiyar tata inda yanuwanta da suka zo suka nemi yarinyar kai tsaye kuwa sauran matan kuma suka shaida musu cew
a ai mahaifin nasa ya kai ta can birni aikatau.
Saboda haka tun kafin a kai ga share makoki aka fara sa'in sa a tsakaninsu, suka tsaya akan cewar sai ya dawo musu da yarinyar, da kyar aka sulhunta wajen bashi wasu kwanaki da cewar ya dawo da ita, kuma basu
ko tsaya an kai kwanaki bakwai ba ana share makoki da kwana uku gabakidayansu suka koma kauyensu.
Sai dai shi tun daga kan haka bai kara bi ta kan zancen ba yaji inda aka tsaya ya shiga harkokinsa, don haka a yanzu da ya riski wannan labarin daga bakin Ja
wad, har da kuma sunansa da zancen cewar shi zai auri yarinyar dashi ko kammaninta ba zai iya zanawa a zuciyarsa ba, kafafunsa sunyi mutuwar tsaye ne na wucin gadi yayin da zuciyarsa ke maimaita kowanne batu
ɗ
aya bayan
ɗ
aya kafin ya girgiza kansa a hankali
yana kallon Jawad
ɗ
in.
"Ƙarya yake, wannan zancen ba haka yake ba, a gaskiya babu wani alkawarin aure tsakani na da yarinyar nan, ya fa
ɗ
a maka hakan ne don ka rabu da ita kawai..."
Wadannan maganganun su Nura ya fa
ɗ
a masa bayan ya ƙare masa dukkan wani ba
yani, kuna sune magan ganun da a lokaci guda suka ciccibo shi daga wata duniyar suka dawo dashi wata, yaji kamar ya saka hannu ne ya sauke masa wani tarin nauyi da yake yawo dashi a kirjinsa. Yana kallonsa lokacin da ya cigaba da fayyace masa komai...
"Ka
gane... Da shi da mahaifinta abokan juna ne, to bayan rasuwar mahaifinta nata ne sai ya auri mahaifiyarta, a lokacin kamar daga ita har yanuwanta sunyi tunanin zata samu sauki ne a wajensa ko kuma sun ga cewa sun sanshi ne sai kawai suka amince, to ni ban
san me yake faruwa ba bsyan na tafi amma dai na fahimci bata jin dadin auren, kuma da ya tashi tura yarinyar aikatau ya hana ta gayawa yanuwanta kamar dole yayi musu ne ya tura ta irin yadda yake yiwa sauran ƴaƴan nasa.
To sai bayan rasuwarta ne a yanzu sa
nnan suka dage akan cewar ya dawo musu da ita, sai kuma gashi yanzu kun zo, to ina tabbatar maka da cewar yanzu can wajen yan uwan mahaifiyar tata zai maida ita, kai kuma ya kore ka ne don ya san da zarar ya mayar da ita ba zai amfana da kai ba shi yasa ya
yi amfana
da wani abu naka ba, shi yasa yayi amfani da sunana ya gaya maka wannan labarin amma ina tabbatar maka duk abinda ya fa
ɗ
a babu gaskiya a ciki, don ni yanzu ma babu batun aure a gabana."
Tun daga farkon bayanin har zuwa karshe ya saurare shi ne da
dukkan nutsuwarsa, da dukkan hankalinsa da kuma tunaninsa wajen tantance gaskiya ko kuma akasin kalaman nasa, sai dai duk iya nisan da hasashensa ke kaiwa, dawowa yake yi wajen gaskata shi da kuma yarda dashi, idan aka cire muryarsa a idanunsa ka
ɗ
ai yana
ganin tabbacin kowacce kalma da yake furtawa.
Yana jin yadda zuciyarsa da kuma kowanne abu mai hankali a jikinsa ke yarda dashi, don haka a lokacin da ya kai karshe, bai
ɓ
ata lokaci ba ya shaida masa abinda yake son yayi masa bayan Nuran ya shaida masa cew
a mutumin ba zai
ɗ
auki lokaci ba wajen sa wa a maida ita wajen yanuwan nata tunda har an riga an ƙaiyade masa wasu kwanaki da shara
ɗ
in ya dawo da ita.
"So nake kayi kokarin da zai mayar da ita wajen yanuwan nata da wuri, sannan ka bi su har can ka gano ƙau
yen sai ka kira ni ka gaya min, zan biya ka ko nawa ne Nura..."
Yana tuna alkawarin da Nuran yayi masa, tarin alkawarin cewa komai zai tafi daidai kuma bai san me yasa ba haka kurum ya yarda dashi, ya
ɗ
ebo adadin wasu kudade daga cikin wanda ya fito dasu a
cikin dashboard
ɗ
insa ya bashi da cewar ya kula da ita har zuwa lokacin da komai zai daidaita, kuma bai sake bukatar komai ba ya juya motarsa ya bar ƙauyen, ya riga ya fahimci cewa gaggawa shine mataki na farko da zai bata hanyar mafitarsa.
Bashi da wani
ƙ
arfi ko kuma wani iko akan mutumin nan ya sani, babu yadda zai iya dashi a yanzu tunda har Zainab ta riga ta shiga hannunsa, don haka zai bi shawarar Nuran, zaiyi hakuri har zuwa lokacin da zata bar cikin ikon nasa, wanda yake saka ran saka ran hakan da w
uri kamar yadda ya gaya masa, shi yasa bai ko damu ba a yanzu kafin tasowarsa da Nuran ya sake kiransa a waya ya shaida masa cewar mahaifin nasa ya ajiye Zainab ne a can cikin dakin uwargidansa inda ba zai iya zuwa ba don haka ba zai iya hada shi da ita a
waya ba kamar yadda suka yi kafin rabuwarsu.
Wani abu ya wuce ta makogwaronsa a hankali yayin daya tuna babban al'amari na biyu dake shirin faruwa da rayuwarsa, bai san takaimaimai me zai faru ba, bai san na abinda zai je ya tarar a garin Kanon da yake nuf
a a yanzu ba, abinda ya sani kawai shine, tun kafin haduwarsa da Nura, bayan ya baro kofar gidan mutumin nan, kira ya shigo wayarsa da wannan lambar da aka bashi,lambar da yake saka ran ko yaya ne zata bashi hanya ta kuma saukaka masa wahalar tafiya neman
abinda ya fito dashi har hakan ya shafi rayuwar Zainab.
Sai dai kuma ya fahimci kamar yadda yake neman wani abu haka ma matar da ta amsa wayar take, bai tabbatar ba don wataƙila baya cikin haiyacinsa a lokacin amma ya fahimci ba lallai ne idan tana da wata
kwaƙƙwaran bayani da zata iya bashi ba, zai je ne kawai don ya sami wani abun akan iya abinda yake dashi, don ya tabbata ita ta da
ɗ
e tana nema, don haka tabbas zai samu wani abun da zai fi nasa.
Shi yasa ya yanke shawarar tahowa inda ta gata masa take a l
okaci guda, ba zai koma Abuja ba, hatta wajen aikinsa ya riga ya rubuta takarda tun da asubahin yau ya tura musu na daukar hutu tsawon wasu
kwanaki, kuma ya sani bashi da matsalar hakan don a shekaru biyu da suka wuce ko hutun karshen shekara da ake bawa k
owanne ma'aikaci shi bai ta
ɓ
a karba ba.
Su Hajiya Mardiyya kuwa bai ƙara ganin kiran daya daga cikinsu ba tun dazu, ya gaya musu zai dawo, kuma ya san hakan kadai ua ishe su su fahimci cewa ya riga ya yanke hukuncin da babu wani kuma da ya isa ya saka shi
ya canja, tunda sun sanshi, sun san halinsa da kuma abinda zai iya tun kuruciyarsa.
Matar ta turo masa da address
ɗ
in inda take, a tunaninta a garin Kano yake shima, don kai tsaye ta gaya masa cewa zata jira zuwansa a yau din, shi yasa ya tabbatar da cewa
itama nema take kamar shi.
Ya bude idanunsa a hankali sannan ya zura hannunsa cikin aljihun rigarsa, rigar da ya canja a cikin garin Kaduna inda ya nufa bayan rabuwarsa da Nura, Gidansu wani abokinsa Hashim ya nufa kai tsaye inda yaci sa'a Hashim din kuwa
na nan, a gidan ya bar motarsa sannan yayi wanka ya canja kaya zuwa wasu riga da wando da ya tsaya a wani boutique ya siya, rigar kamar ta sanyi ce amma bata da nauyi, tana da hula mai girma wadda ya jawo ta ya rufe kansa da ma kusan rabi na fuskarsa, baya
n kayan babu abinda ya dauja sai wayarsa da kuma wallet dinsa inda ya jera mint din kudaden da ya ciro.
"Maigida..."
Saurayin dake zaune a kujerar gefensa ya fa
ɗ
a a hankali, ya juya ya kalle shi yana yin baya da hular rigarsa, wanda hakan yasa Saurayin ya
kara yin murmushi kafin yace.
"Nace dan Allah ko zaka taimaka ka dan dauke ni a hoto, this is my first time hawa na jirgi, so ina so nayi posting a acconuts dina na social media ne..."
Ya fa
ɗ
a yana ƙoƙarin miƙo masa wayar hannunsa, babu yadda zai yi sai ka
wai ya gyada masa kai sannan ya karbi wayar ya danyi baya kadan yayin da saurin ya gyara zamansa a jikin kujerarsa dake kusa da taga, ai kuwa yayi masa hotuna guda biyar masu kyau sannan ya mika masa.
"Nagode, Nagode sosai, It means alot sir!"
Cewar sauray
in yana murmushin jin dadi har da hade tafukan hannayensa biyu, kuma bai san me yasa ba sai kawai ya nuna masa kwalin wani abu a hannunsa da ska rubuta 'Free-dat' sakon kai abun ne yasa mutanen da suke do suka bada kudin jirgi a kawo...
"... Idan ba haka,
babu abinda zai sa in hau jirgi a wannan matakin da nake a rayuwata."
Bai san lokacin da murmushin da bai shirya masa ya subuce a lebbensa, ba wai kuma murmushin abinda ya fada bane, murmushin jiye wa matashin dadin rayuwarsa yayi, dadin wannan lokacin da
yake ciki da bashi da wata damuwa mai yawa, tazarar shekarunsa bata da wani yawa sosai ya sani, amma shi yanzu ne lokacin da komai yake hargitse masa, rayuwarsa ma gaba
ɗ
aya ta canja a cikin kwanakin da basu fi ƙarfin ƙirgen yatsunsa ba. Ya rasa identity
ɗ
i
nsa sannan kuma yana shirin rasa yarinyar da yake ganinta a matsayin wani
ɓ
ari na rayuwarsa.
Ya tabbbata laifinsa ne ke bibiyarsa, ko ma ya fara, don shi da kansa ya sani cewa wanda ke aikata laifi irin nasa karya ne rayuwarsa ta dinga tafiya daidai,karya
ne ka sabawa Allah akan haninsa kuma ace baka
fuskantar wani kalubalea ruywarka, idan kuma hakan ta faru to kuwa tabvatas ka ji tsoron haduwarka da shi... Don ko hausawa sun ce 'Alhaki kwikwiyo ne, duk inda kayi sai ya bi ka.'
Ya sani cewar ya biyewa shed
an a rayuwarsa,ya aikata rarin abubuwan da sanari da yawa a wannan zamanin ke ganin cewar ba laifi ne, kamar suna halattawa kansu ne ma wasu sabon Allahn a cikin lissafin morewarsu ta duniya, amma zai rantse da ubangijinsa tun daga lokacin da zuciyarsa ta
fara fuskantar Zainab da kuma al'amarinta, ko shisha bai kara dandanawa a bakinsa ba, yana jin kansa ne kamar ya zama commited na tarin irin abubuwan nan da yake ganin bashi da lokacinsu, ko abokinsa Haro a yanzu su kan dade ma basu yi waya ba ganin yaki m
aida hankali game da shirin da suke yi akan Rukayya.
Rukkaya. Ya lashe lebbensa kadan sabida ambatar sunan da zuciyarsa tayi, tana ina a yanzu? Me ke faruwa a cikin tata rayuwar? Don ya tabbata ba shi kadai ne yake fuskantar sakamakon laifin da suka dade s
una aikatawa a rayuwarsu ba, kwarai ko da ga nesa ne zai sp sanin halin da take ciki don ko layin da take samunsa dashi ma a yanzu baya wajensa, ya da
ɗ
e da bawa wani masinja a Office
ɗ
insu kyautarsa tare da sabuwar waya bayan ya kawo masa korafin rasa waya
rsa da yayi.
Jirgin ya sauka a Kano da misalin ƙarfe 7:24 na yamma, yayi sallama da wannan saurayin mai sakon Free-dat sannan bai bata wani lokaci ba kasancewar bashi da kaya ya fito daga wajen, a cikinnairpot din ya samu mai motar da yayi haya har zuwa ad
dress
ɗ
in gidan da matar ta turo masa.
***
*No 1856L, Sulaiman Crecent Kano.*
*Gidan Hajiya Salamatu.*
Babu irin sake-saken da Hajiya Salamatu bata yi a zuciyarta ba bayan sun gama waya da mutumin da ya tabbbatar mata da cewar shine ya turo sako cikin waya
rta game da matar nan Hanne, kuma ya tabbatar mata da cewar zai same ta har inda take a yau.
Ta dauki wayarta da niyyar kiran tarin mutane amma tana fasawa, sai karshe da tunaninta ya tsaya kan kaninta mai bi mata da shima yake zaune anan cikin unguwar da
take sannan ta kira shi, kuma a wayar ta kasa shaida masa komai sai da yazo gidan tukunna.
Kallon da yayi mata bayan ta gama yi masa dukkanin bayanin da Awwalu yayi mata da kuma yadda suka je har Garun Albasu nemsn Hanne da ma sakon da ta samu a yanzu,kall
o ne da bata taba gani a idanunsa ba, kamar yana shirin cewa watakila ta samu cutar tabin hankali ne ko kuma zaiyi mitar ta taso shi akan abinda yake kamar almara, amma sai ya girgiza kansa sannan muryarsa cikin kokarin kwantar mata da hankali yace.
"Zaman
in nan babu abinda ba ya iya faruwa Ya Salamatu, mutane sun haukace akan kudi yanzu, babu ta hanyar da ba za'a biyo ba don a yaudare ka yanzu, kar ki bari wasu suyi wasa da hankalin ki. Ni shaida ne da Kawu Muhammad da Yaya Murtala Allah ya jikansu, su suk
a binne jaririn da kika haifa matacce tun a wannan ranar...."
Saita girgiza kanta taba katse shi tun kafin ya karasa.
"Wallahi Nasir tun a wannan ranar da na rike jaririn da aka bani ban ga kamanni na ko kuma na Ibrahim a fuskarsa ba... Kuma banji komai ba
, banji sani abu da ya danganta ni da wannan yaron ba."
Yana kallonta sai kawai yayi dariya ya girgiza kansa.
"Ba fa jiya ko shekaranjiya muke zancen al'amarin nan ba Ya Salamatu, shekaru kusan talatin da nawa kenan... ?"
Sai ta