Showing 99001 words to 102000 words out of 144990 words
da sun ganshi sai a bata gawa ta taho da ita gida, inda daga nan zata samu hanyar da zata yi ta dauko jariri ta kawowa masu bukata su bata kudinta.
Aunty Sadiya tayi bayanin haka ce ta faru
dasu, a ranar da suka yi karyar naƙudarta ta tashi a ranar suka
ɗ
auki mota su biyu kawai ita ke tuƙawa suka nufi can wannan ƙauyen da a lokacin ake ce masa Yakura, amma a yanzu ya koma Garun Albasu, anan suka sami matar da babu wani bata lokaci suka bata
kudinta ita kuma ta basu yaro, inda murnarsu ta ƙaru ganin namiji ne.
Daga nan suka kama hanya suka dawo da cewar ta haihu kuma har an sallamo ta daga asibiti, kuma babu wanda ya zarge su aka shiga murna da shagalin suna... Kuma tun daga wannan lokacin suk
a binne wannan abin a tsakaninsu su biyu kawai ta yadda ko sauran ƴanuwansu basu ta
ɓ
a sani ba sai a yanzu da ƙwaryar da suke riƙe da ita ta fa
ɗ
i har kasa ta tarwatse.
Yana iya jin muryar Hajiya Mardiyyan a cikin kansa har yanzu, yana jin yadda take magiya
da kuma kukan gayawa Alhaji Bashir cewa wallahi sauran ƙannensa mata da ta haifa shekaru biyar bayan shi ƴaƴan su ne na cikinta, ita da ƴaruwarta sunyi garaje ne kawai na tunanin bata haihuwa na tsawon shekaru bakwai kafin lokacin da ta sami cikinta na gas
ke.
Ya rufe idanunsa a hankali ya bu
ɗ
e su kafin ya amsawa Aunty Sadiya da abinda take jira.
"Ina hanyar Kaduna..."
"Kaduna?"
Ta tambaya a lokaci guda.
"Inalillahi wainna ilaihir raji'un.... Haba Jawad me yasa zaka kama hanya da sassafen nan? Tun
ɗ
azu muke
nemanka, ina zaka tafi? Aƙalla ka saurare mu mana..."
Ina zai tafi? Ta yaya zai cigaba da zama a gidan nan alhali tun a daren jiya labarin komai ya zagaye gidan daga bakin Hajiya Yagana da bashi da tsntamar cewar ta ji dukkan tattaunawar da akayi.
Ta yaya
zai kara zama yana kallon idanun kowa ba tare da wani bayani mai gamsarwa da zai iya kare kansa a wajen su ba? Bai ce ba zai dawo ba don ko Alhaji Bashir da yaje yiwa sallama abinda ya gaya masa shine zai dawo bayan ya sami ƴanuwansa, kuma shi bai hana shi
ba ko yace masa yayi garaje sai su....?
"Ka yiwa Allah da ma'aikinsa ka dawo Jawad, ka sani a cikinmu babu wanda ta taba cutarka, kuma bamu yi komai don mu cuce ka ba, to me yasa ba zaka saurare mu ba Jawad? Me yasa ko sau
ɗ
aya ba zaka ji daga bakin mahai
fiyarka ba... Tunda komai ya fito fili ka tunanin zamu sake
ɓ
oye maka wani abu ne?"
Ya girgiza kansa a hankali kamar tana kallonsa.
"Kar ku damu Aunty Sadiya zan dawo...."
Abinda ya fa
ɗ
a kenan kawai sannan yatsun hannunsa suka ni kashe kiran, sai dai murya
rta ta sake kwararowa kafin hakan.
"Ina wannan yarinyar Jawad? Ina Zainab?"
"Tana tare dani."
Amsar ta fito cikin tattausan amon muryarsa da tsabar ru
ɗ
ani da kuma tashin hankalin da yake ciki ya haifar dashi.
Kuma daga shi har Zainab
ɗ
in, suna jin salatin
da Aunty Sadiyan ta ru
ɗ
e dashi kafin ya kashe wayar.
Ɗ
ib kiran ya katse a kunnen Zainab, yana sake tonawa kanta sautin zuciyarta dake bugawa a ƙirjinta, kuma bata juyo ba, bata juyo ta kalle shi ba, kanta na sunkuye tana kallon yatsunta dake girgizawa akan
cinyoyinta, nemanta suke yi ita ta sani, shi tasa ko baccinta na jiya ta cika da mafarkai masu nauyi... Watakila gani suke tana da hannu a duk abinda Jawad ke yi.
Kuma ta sani ko a gaba suka sa ta bata da yadda zata iya yi musu bayanin cewa bata san komai
ba, bata san me yake yi ba ko kuma su abinda suke yi, kamar koyaushe a rayuwarta babu wanda ya taba bata zabi a rayuwarta, komai faruwa kawai yake a gaban idanunta yayin da take jin tamkar an rufe bakinta an kuma daure hannayenta, kamar tana tsakiyar wani
waje ne da bata da mafita kotawanne
ɓ
angare,kamar tana cikin kwale-kwale ne a tsakiyar teku ta yadda ruwa ya zagaye kowanne bangarenta... Don haka bata da wani za
ɓ
i illa ta zuba ido taga yadda Allah yayi da ita kawai.
Tana ji sanda ƙarar wani kiran ta cik
a motar, sannan taji sanda muryar wani namiji ta amsa.
"Oga sir.."
Shine abinda ya fara fa
ɗ
a bayan sallama. Ta gefen idonta taga sanda ya dafe kansa yana yin baya dashi kafin ya amsa.
"Sulaiman ina ga a location dina saura bai fi minti biyar ba na kusa isa
zuwa garin, ka tabbata mutumin da zaka hada ni dashi
ɗ
i yana nan a gari?"
Daga cikin wayar Sulaiman din yace.
"Yana nan Yallabai, bai fi minti biyar ba .a da muka yace min ya riga ya fito bakin titi yana jiranka, sunansa Nura, na gaya masa kalar motarka t
o da ka iso zai gane ka kawai."
Ya gya
ɗ
a kansa sau biyu yana fa
ɗ
in.
"Shikenan, nagode."
Sannan ya kashe wayar. Taji ƙarar sanda ya ajiye ta a gefen dake tsakaninsu kafin abinda bata yi zato ba ya biyo baya...
"Zainab zaki ci wani abu?"
Muryarsa a hankali
ta fito,cikin amon dake shaida mata cewa nasa ne, ya dawo daidai ba kamar
ɗ
azu da ta tabbata baya cikin hayyacinsa ba.
Sai kawai ta rufe idanunta a hankali tana jin
ɗ
umin kwalla na kokarin cika su.
"Kina jin yunwa?"
Ya ƙara tambaya a hankali, sai ta girgiz
a kanta a hankalin itama ba tare da tace komai ba, shiru ya sake ratsa motar na wasu sakanni kafin ya kunna ta su sake hawa kan titin, kuna tafiya yar kadan ta isar dasu cikin wani tsohon gidan mai da ya koma kasuwa kuma maciyar mutanen hanya, wajen da ya
hada da tarin kantinan da kusan duk wani abinda matafiyi ke bukata zai samu.
Bai kashe motar ba ya barta a kunne har da mukullin a jiki sannan ya bude ƙofar motar ya fita, Zainab ta bishi da kallo ta cikin mutanen dake wajen, kayan jikinsa wani kalar yadi
ne mai ruwan toka, tafiyarsa kadai ta banbanta da tarin mutanen wajen har zuwa sanda ya bacewa ganinta, Idonta ya shiga yiwa cikin gidan man kallon sani amma nan da nan ta ƙaryata kanta, ta dawo da idonta ya dawo kan mukullin motar.
Zuciyarta ta ayyana ma
ta yadda zata koma mazaunin direban ta murda shi, da zarar ta tashi sai tashi sai ta juya kanta ta fita daga wajen, ta komawa dukkan hanyar da suka biyo a baya har zuwa cikin gidansu. Wataƙila idan tayi hakan zata iya wanke kanta a wajen Hajiya Mardiyya da
kuma Deluwa, watakila zasu iya yafe laifinta su mayar da ita gida wajen mahaifiyarta komai ya ƙare, komai... Har dashi kenan? Wani bari na zuciyarta ya ayyana mata, kuma rashin sanin amsar yasa ta ha
ɗ
iye wani abu a maƙogwaronta.
Cikin abinda yake ƙasa da
minti goma Jawad ya dawo har a lokacin tana sake-saken a ranta, bata ko ganshi ba sai ji tayi an bu
ɗ
e ƙofar gefenta, kuma kafin ta dago ya ajiye tarin ledojin hannunsa akan cinyarta sannan ya mayar da kofar ya rufe.
Idonta yabi ledojin da kallo tana jin ka
nshin kayan abinci kala -kaka da kuma nauyin robobin ruwa dana lemo da suke cikin tasu ledar daban, a cikin wata ƴar karamar leda fara, ta gano magunguna, irin magungunan da ya siyo mata jiya sak wanda suka bari a falon
ɓ
angarensa.
Mamaki ya kamata, tsanan
in mamakin wani irin mutum ne Jawad da kuma halayensa, sai dai wannan mamakin bai kai koi'ina ba sai a lokacin da suka isa kofar shiga garinsu 'Garun Albasu' minti biyar bayan barinsu daga gidan man nan, a lokacin da ta
ɗ
ago kanta jin ya rage gudu suna kok
arin sauka daga titi, lokacin da ta
ɗ
ago da idanunta suka sauka akan kasuwar ƙauyensu ta bakin titi kafin ka dangane da cikin garin, da kuma fuskar
ɗ
anuwanta Nura, (
ɗ
an mijin mahaifiyarta) yana washe baki yana tunkaro motar tasu da saurinsa.
A wannan lokac
in abinda taji yayi kama da fadowar zuciyarta a cikin kirjinta, taji kamar ta fa
ɗ
o ne ta fice ta ƙasan motar, tayoyin baya kuma suka bi ta kanta suka tarwatsa ta, jininta ya fallatsa a koina na jikin motar!
***
A cikin harabar tsakar gidan, mata ne kala-ka
la da kuma yara dake wasan su, matan na ayyukansu na yau da kullum wanda ya ha
ɗ
a da girke da kuma surfen hatsi kala-kala, kusan rabinsu na goye ne da ƙananun yara a bayansu yayin da suturarsu ka
ɗ
ai idan ka kalla, banda gini kasan dake zagaye da tsakar gida
n zai shaida maka cewa mutanen karkara ne.
A wannan lokacin ne kuma sallamar wani dattijo ta kara
ɗ
e koina a tsakar gidan, sau daya ya furta sallamar amma a lokaci guda yanayin wajen ya canja, yara suka mike a guje suka nufi kasan rumfar dake barandar dakun
a suka taru waje daya gabadayansu yayin da matan kowacce ta mike tsaye suna amsawa, yan tsofaffin dake zaune suna aikin busa ne jadai basu mike ba.
Mutumin ya shigo sanye da vabbar rogarsa wadda ta banbanta da yar ciki, hular kansa mai kyau ce wadda dattin
dake tattare da ita ya boye hakan.
"Ina Talatu? Talatu, Talatu....!"
Kakkaurar muryar tasa ta fada yana karasowar ciki. Matar dake amsa sunan Talatun tayi saurin sakin itace da ta debobdon kara wutar girkinta tayo gaba tana fa
ɗ
in.
"Gani Malam.."
Kuma tsay
e ya nuna ta yana fadin.
"Wato Talatu rashin mutincin naki bai kai karshe ba dama? Sakin da na dannewa zuciyata ban yi miki wancan karon ba shi kike nema?"
Ba shiri Talatun ta dafe goyon ƴar dake bayanta sakamakon fa
ɗ
uwar gaban da taji ta ratsa har ta baya
nta tana shirin kwance goyon.
"Inalillahi wainna ilaihir raji'un Malam me kuma ya faru? Wallahi Malam vabu abinda na kara yi."
"Babu abinda kika kara yi? Karya nake yi miki kenan? Ko kuma shi wancan ƙaton Gardin da Nura
ɗ
an gidan Malam Sadi ya rako min sh
i har majalisa suka zo nema ki dake ƙaryar suke? Dududu kwana nawa kenan da kika shigar min da mutum har
ɗ
akin aurenki? amma ace duk uw*r tarzomar da aka sha baki hankalta ba? Allah wadaran auren jinin Hanne wallahi...!"
Ya fada muryarsa na dagawa, dagawar
da tasa sauran matan dake gefe murmusawa suna kallon junansu. Talatu ta sake talkafe goyon bayanta tana girgiza kanta.
"Wallahi Malam, bani da masaniyar komai, ni ban san me suke nema a wajenta ba, ban san ma me yi musu kwatancena ba..."
"Ina zaki sani Ta
latu? Dama ina zaki sani... Muna zaune a majalisa kawai mota ta faka aka ce wai gidana ake nema, kin kunyata ni a cikin jama'a, ace ina zaune a gida da mata amma wasu maza daga waje suna zuwa nemanta? Wallahi darajar Malam da na karbi aurensa a wajenki kaw
ai kike ci Habiba, amma anyi na farko anyi na biyu, na rantse da kabarin ubana aka sake samun wani
ɗ
an kaza-kazan da zai zo nemanki sai kin bi shi, billahillazi kafar sa kafarki, na gama zaman aure dake..."
Talatu ta gyada kai cikin amincewa da sauri sanna
n kafafunta suka durkusa har kasa cikin kasar wajen tana neman afuwa. Kuma sai da ya gama cikarsa ya bayse sannan yayi kwafa yace.
"Ɗauko hijabinki, suna soro muje inji me ke tafe dasu."
Sai ta girgiza kanta, tana kallonsa tace.
"Wallahi Malam ba sai na fi
ta ba, wa
ɗ
ancan mutanen da suka zo sun bar lambar wayarsu suka ce in kira su idan na samu wani labari, to indai suma Hanne suka zo nema zan basu lambar su nemi wa
ɗ
ancan su gaya musu komai, ka yarda dani Malam wallahi bani da wata alaƙa dasu."
Muryarta na r
awa cike da tsoro yayin da yake kallonta idanunsa na haskawa da dimbin bacin rai da kuma fushin da a zuciyarta take kirga adadin kwanakin da zasu wuce kafin ta sake samun fuskarsa.
Muryarsa cike da ba'a, yace.
"Akwai abinda zasu nema ne da ya wuce Hannen?
Duk danginku akwai mai jawo muku tsiya ne kamar ita?"
Talatu bata ce komai ba tana tsugunne a gabansa, hannayenta dake tallafe da goyon ƴarta na rawa a ƙasan goyon, kuma bata san lissafin da yake yi ba tsawon wucewar wasu mintuna kafin yace.
"Tashi ki
ɗ
auk
o lambar, wannan shine na farko da kuma na ƙarshe a lamarin nan na gaya miki Talatu..."
Ba shiri sai ta miƙe tsaye, kuma bata ko damu da karka
ɗ
e kasar da ta
ɓ
ata kafafunta ba, ta miƙe da sauri ta nufi ƙofar
ɗ
akinta, kuma cikin abinda bai wuce minti guda ba
ta dawo riƙe da wata farar takarda da take a miƙe sam
ɓ
al, ya fizga tamkar zai yaga sannan ya juya ya nufi hanyar fita.
A ƙofar gidan ya tadda Jawad da kuma Nura dake tsaye suna jiransa, ya juya ya kalli motar da suka bari a can gaban gidan, wannan yarinya
r dake ciki har yanzu tana nan, ta juyo tana kallonsu idanunta na na
kallonsu a zare, sannan ya kalli tarin yara har da matasan da suka tsaya daga can nesa suna kallo su, don labarin maƙudan kudin da aka bashi ya danna a aljihu bayan ya fara fadan babu mai
ganin matarsa ya kusa biye kunnen duk wanda ya sanshi a lokacin.
Ya ja tsaki mai tsawo yana fadin.
"Allah wadaran munafukai...!"
Sannan ya juyo ya sake kallon Jawad
ɗ
in dake a gabansa.
"Yallabai, matata tace bata da wani bayani da zata yi maka don Hanne t
a rasu shekaru shida da suka wuce, amma ga wannan lambar, idan ka kira watakila zaka sami wani bayani a wajensu, don suma kamar kai sun zo nemanta kwanaki."
Idanun Jawad na kallonsa har yaje karshen zancensa, ba haka yaso ba ko kadan, yaso akalla yaga Tala
tun yaji bayanin komai daga wajenta, tunda sun sha tambaya tare da wannan matashin Nura amma babu wanda ya gane Hannen da suke nema sai da kyar aka samu wanda ya fa
ɗ
a musu cewa matar ta da
ɗ
e da barin garin amma akwai wata Talatu da zata iya basu labarin in
da take.
Kamar zai yi magana, amma sai zuciyarsa ta shawarce shi da cewar yabi mutumin a haka, don ya lura idan ya matsa za'a iya samun matsala, yau ya fara nema ba lallai ya samu komai a yau ba dama... Don haka sai kawai ya gyada kansa sannan hannunsa ya
kar
ɓ
i takardar kafin bakinsa ya furta godiyar da bai san ta wace sigar kalamai suka fito ba... Idanunsa suka manne da suna da kuma nambobin dake rubuce a jikin takardar lokacin da mutumin ya juya yana zagin jama'ar dake shirin taruwa a kodar gidan bunun.
H
ajiya Salamatu.
080673....
****
Ruwan da ya sauka akan fuskar Awwalu mai tsananin sanyi ne fiye da na farko da Ɗantaro yasa aka watsa masa awanni ka
ɗ
an da suka wuce.
Ya bu
ɗ
e idanunsa cikin tsananin firgita, yana kallon wadanda ke tsaye a gabansa, da farko
inuwoyi idanunsa suka fara nuna masa kafin fuskar Ɗantaron dake saitinsa ta fito tar cikin hasken safiyar dake ratsawo cikin fankon
ɗ
akin da aka kawo shi aka kulle tun a daren jiya.
"Ni zaka yiwa shunen ƴan sanda Awwalu? Ni zaka sa in aika yarana gidanka a
lhali ka aika ƴan sandan can? Ni zaka yaudara Awwalu?"
Ƴ
an sanda! Kalmar Ƴan sandan ta doka wata irin tsawa a cikin kan Awwalu a lokaci guda tana sa shi wartsakewar da ba shiri.
"Ƴan sanda suka gani a gidan nawa?"
Muryarsa ta fito tare da shakku da kuma ta
shin hankali da baya neman tabbacinsa, kuma Ɗantaron bsi yi maganar ba sai kawai ya girgiza kansa sannan yayi wa yaransa biyu daje tsaye da bokitai alama da su karasa zuba masa ruwan bokitan dake hannunsu wanda
ɗ
aya na zafi ne
ɗ
aya kuma na sanyi, mai rike
da na zafin ne ya fara juye masa tun daga saman kansa sannan na sanyin ya kwara masa shima har ƙasa.
Tasirin zafi da kuma sanyin da suja ratsa jikinsa suka sa dukkanin jijiyoyinsa riƙewa baki
ɗ
aya, ya shiga kokawa da dawowar numfashinsa a kirjinsa kafin ya
muryar Ɗantaron ta ratsa kunnensa.
"Kai baka isa ka tona min asiri ba Awwalu, wallahi, wallahi daga yau taka ta kare!"
Kuma ga mamakin Ɗantaro sai kawai Awwalun yayi murmurshi, murmushi mai fadi sannan ya girgiza kansa, don abinda Dantaron bai sani ba shin
e su duka biyun ne tasu ta ƙare! Tunda ya riga ya jawo shi jikinsa shikenan tasu ta kare gaba
ɗ
aya!
***
_Me kuke tunani ya ha
ɗ
a Kilishi da
ɗ
an sanda?_
_Kuna tunanin hakan wani shirinta ne?_
_Shirinta na gaba wato kashe Baffa?_
_Ko kuma wata kaddarar ce dab
an?_
_Me kuke tunani ya faru lokacin da su Jawad suka shigo Garun Albasu?_
_Zainab bata shaida masa Garinsu bane? Ko kuma Nuran da yazo bai gane ta bane?_
_Jawad ya samu lambar Hajiya Salamatu, me zai biyo baya?_
_Mabudin komai dai, ya riga ya iso!_
Littaf
in nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
°°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*20*
_
Inch by inch. Life is a